Sashe 8
Aisha Siddiqa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sawa ranki damuwa har ta kaiga bp?” Aisha-Siddiqah dai dai bata ce komai ba, ta sunkuyar da kai tana wasa da siraran yatsunta, amma gara mata zaman asibitin nan sau dubu akan gidansu Nenne, musamman data fahimci Princess Fatima ta sauya mata fuska yanzu. Wani kallo ma take mata mai zafi cikin ido. Nenne ta zuba madarar hollandia a tambulan mai tsaho ta mika mata, ba musu ta karba tana sha a urunce ji kake mukut-mukut, hadidiye madarar kawai take yi don yunwa, mamaki da haushin iskancin Aisha-Siddiqah ya ishi Nenne, ji dai yadda take shan madarar a yunwace mai nuna jiya bata ci abincin dare ba ta shige daki ta kudundune ta kwana da yunwarta, duk da ta ce da Femi abinda Aisha take so zata dafa, an kuma tambayeta tace tuwo, haka ta bar su da tuwon masara da miyar kubewarsu ya kwana a dining wanda akayi saboda ita ta yi barcin wuri duk don kada ta ci girkin Femi. Nenne Sappa ta nisa, sannan tayi kwafa tace. “Aishah, nace me yayi zafi na yiwa kai horon yunwa? To kwantar da hankalinki ki sauke jinin da kika dora a can sama, in sha Allah rana ita yau zan maida ke Gombe ince ko shikenan? Amma na rantse miki na sake rantsewa tafiya ce mai dawowa. Zaki yi dawowar da babu komawa sai dai da yawo in Allah ya yarda. In yaso in ga karshen kabilanci”. Siddiqah dai shan madararta take har da murmushi don hankalinta ya kwanta, tunda Nenne ta yarda zata maidata gida zance yak are, sauran zancen da tayi a karshe bata ji bama balle ta fassara shi da wata manufa don hankalinta ya kwanta yanzu. Shikuma Dade wato Engnr. Idris Akanni a ranar ya tashi zuwa Ilorin. Kafin Dade yaje Ilorin, saida yasa ‘yan uwan Nenne na Gombe suka yi masa duk wani bincike akan Malam Yunus da asalinsa, nasabarsa da sana’arsa, kuma duk abinda aka gaya masa din akan malam Yunusa Hamza na kwarai ne na sam barka. Malam Yunus ya samu duk kyakkyawar shaidar da ake nema ga mutumin kwarai mai kula da iyali da sadaukarwa akan su iyakar karfinsa. Haka matarsa ta samu kyakkyawan yabo na kula da hakkin makwabtaka da tarbiyyar Siddiqah kasancewar Allah bai bar mata ‘ya’yan da take ta Haifa ba sai Siddiqah din wadda suke tsaye kan jiki kan karfi wajen ilmin ta na addini dana boko. Siddiqah na cikin yaran kwarai da ake alfahari dasu a unguwar jeka da fari sannan tun tana shekaru 13 tayi haddar Alqur’ani a Tahfiz dinsu. Da wannan kyakkyawan albishir din Dade Engnr. yayi tattaki har Ilorin ya samu mahaifinsa Emir Abdulrasheed dan Abdullateef Akanni da maganar zabin da Nenne ta yiwa Abdulrasheed. Sarki da yake akan tsini shima, sai yaji kamar an masa allurar tuni da wani babban al’amari da duk suka zuba ido akai, yaji kamar an zaburar dashi ga wani muhimmin abu da ya saka shiririta a ciki, ya tuna cewa babban jikan nasa Prince Abdulrasheed ya wuce shekaru 40 a halin da ake ciki yanzu, burin sa a lokacin kowa ya san na Prince Abdulrasheed yayi aure yana raye ne, har in zai samu ganin ‘ya’yan jikan nasa zai yi farin ciki, amma meyasa ya biyewa gudun zuciyar Abdulrasheed har yau bai yi wannan yunkurin ba sai yanzu da mahaifiyarsa Sappa ta gaji da kawaicinta na fullata akan rashin auren dan nata tayi tattaki da kanta ta nemo masa aure da kanta? Shi kansa ya san son da yake yiwa Prince Abdulrasheed yayi yawa, shiyasa har baya iya tankwara shi akan duk abinda yace baya ra’ayi. Gaskiya ne duk wata kauna mara illah tabi bayan ta uwa gad anta. Ai sai nan da nan yace a kira meeting na gaggawa na duka ‘ya’yansa kamar yadda suka saba akan duk wani muhimmin al’amari da ya tunkaro iyalinsu. Kowanne cikin ‘ya’yan Emir of Ilorin su tara da ya haifa ya baro abinda yake yi a garin da yake zaune haka na cikin Ilorin duk sun baro ayyukansu sun taho fadar, har babban Yayansu Waziri wato Engnr. Idris mahaifin Prince su goma kenan duka sun samu halartar kiran mahaifin nasu na gaggawa, sarki mai ran karfe Emir Abdulrasheed Akanni na zaune a kan karagar mulkinsa sun saka shi a tsakiya hagu da dama, a gefen sa mutum biyar a hagu mutum biyar a damansa, kowa ya sunkuya ya kawo gaisuwa ta al’ada Sarki na amsawa daki-daki da harshen Yoruba, kafin ya yi musu addu’a ta hadin kai a tsakaninsu kamar yadda ya saba sannan ya shafa kan kowanne in ya sunkuya a gabansa kamar yadda suka saba, duk sanda akayi irin wannan zaman haka yake yi musu tare da nasiha akan su guji duk abinda zai raba kansu, yak an fadakar dasu akan cewa kada su taba bari ‘ya’ya su shiga tsakanin su, Sarki yace ‘ya’ya da daukiya fitina ne, sune manyan abubuwanda ke farraqa zumunci, a karshe ya shaida musu abinda yasa ya kirasu akan auren dan su Prince AbdulRasheed ne. Mahaifiyarsa Hajiya Sappa ta samo masa mata a Gombe, amma ba ‘yar sarauta ba. Shiru ya dan gifta. Kafin su balle da yarbanci a junansu na resentment. Kowa da irin abinda yake fadi a falon ganawar na Sarki, mafi yawan ‘yan uwan Dade sun ce ne ta yaya AbdulRasheed zai kasa samun mace a gidan sarautar Ilorin, dama duka masarautun kasar Najeriya sai a cikin ‘ya’yan talakawan garin Gombe? Uncle Abdulfatahi yace. “Kamar ance ‘ya’yan sarauta dana manyan attajirai da suke hada auratayyar abota (family friends’ marriage) da ‘ya’yansu sun kare?” Abu daya da zai burgeka a wannan zaman shine cikinsu babu wanda yayi magana akan banbancin yare dana al’ada dake tsakanin Yoruba da Fulani. Musulman Yarbawan Ilorin nada kyakkyawar alaqa da Fulanin Najeriya. Sun fi karkata sukar tasu da cewa iyayen Aisha basu da sarauta (ko ta mai unguwa). Kamar yadda na fada a baya, masarautar Ilorin (is a Yoruba-Speaking Fulani Emirate) hakan yasa ko kusa basa kin auren Fulani a tare dasu. Babban abinda ya kara wanke Fulanin Gombe a idon zuria’ar Sarki AbdulRasheed Akanni shine auren Gimbiyar Gombe wato Nenne Sappa da akayi da jimawa kuma aure na farko a zuri’ar Akannis, wadda har gobe alkhairinta kadai suke gani a tare da zuri’arsu, kodayake ita ta fito ne daga babban gida irin nasu, duk da haka baka rasa korafin matansu da ‘ya’yansu akan Hajiya Sappa din na cewa ta mallake Engnr. Idris da surkullensu na Fulani. Idris Akanni bai kara kallon kowacce mace ba da sunan kara aure har zuwa yanzu da ya fara tsufa bayan ita, yan uwansa kuwa daga mai uku sai mai hudu. Korafi dai da kananan maganganu irin na mata wanda baka rasa shi cikin kowanne gidan yawa, na talakawa ko na masu dashi ko na sarauta. Uncle din Abdulrasheed na hudu wato Mutawalle ya dage a kan bakansa na cewa a baiwa Abdulrasheed mace cikin ‘ya’yansu kawai, ko yana so ko baya so, a wuce maganar aurensa haka. Su basu yarda ya auri diyar talakkawa ba. Emir yace dashi cikin lallashi da harshen Yoruba (kasancewar Mutawalle baya jin kowanne yare sai harshensa na yoruba). “Oloruko mi o fe ni nkankan se pelu oye gege bi Baba e na. Mi o fe ke fi tipa je kanse nkanti won o ni ife si”. Ma’ana; ku cire takwarana a cikin lissafin sha’anin SARAUTA sabida shi da ubansa babu tunanin gadon sarauta a cikin rayuwarsu, to ku cire musu abinda basa ra’ayi daga zama dolen su”. Da kansa Emir ya mike ya taka da kyar ta hanyar dogara sandar girmansa zuwa kuryar turakarsa, ya dauko wata akwati ya kawo gabansu ya ajiye. Yace “Ga dukiyar aure da duk abinda za’a nema wajen gudanar da auren (Kehinde), na daukewa kowannenku wannan nauyin, a matsayinsa na jikana na farko, kuma wanda bai taba yin aure a cikin jikokina ba. na dauki nauyin komai da za’a kashe wurin aurensa. Na umarceku da ku amince da zabin da mahaifiyarsa tayi masa, ita kadai ta san dalilinta, a matsayin ta na wadda tafi kowa kusanci dashi, don haka ta fi ku sanin matar data yi masa daidai”. Da wannan magana ta karshe Sarki ya kashe korafin kowannensu akan auren Prince da diyar da bata sarauta ba, don a karshe bai ma kara bada wata dama ta wani cikin su ya kara fadin ra’ayin sa ba, yace umarni yayi musu su tafi su auro ma takwaransa zabin mahaifiyarsa, bai yarda ma a tuntube shi ba (Abdulrasheed din) sai bayan an daura auren. Abu idan Ubangiji ya rubuta faruwarsa shi shine sai kaga in lokacin faruwarsa ya zo ya faru nan da nan bagatatan, kodayake shi aure lokaci ne kuma kamar habo yake sai sanda Allah ya nufa kadai yake tabbata. Abu kamar wasa hausawa suka ce sai ga karamar magana ta zama babba. Aisha-Siddiqa da Nenne na ta zaryar ganin likita a Legas, a can Ilorin da Gombe kuma ana shirin daurin aure, shiri ake sosai babu kama hannun yaro daga dukkan bangarorin guda biyu ba tare da Siddiqah ko Prince dake can matatar man Fetur a birnin Qatar sun san ana yi ba. Akanni’s (‘ya’yan Emir) duka sun bi umarnin mahaifinsu babu wanda ya kira Prince ya gaya ma an karba masa aure. Dade yana Ilorin suka yi gangami da ‘yan ’uwansa da wakilan Sarki suka sauka a fadar Gombe ana sauran kwana biyu daurin aure wanda akasa za’ayi ranar Juma’ah bayan sakkowa sallahr juma’ah. Likitan su Nenne ya gama baiwa Siddiqah kyakkyawan treatment yadda ya kamata saida ta kwana uku a asibitin, ya sabunta mata inhaler. Yace da Nenne, Siddiqah tayi babbar sa’a asthma dinta ba mai tsanani bace kamar ta Firdausi (mild asthma) ce wadda in an guji allergy dinta zata dade bata tashi ba. Ita kanta Nenne Dade bai gaya mata me ake ciki akan maganar auren ba saida suka kama hanyar Gombe shi da sauran ‘yan uwansa daga Ilorin. Ya kuma ce ta kame bakinta har a daura baya so ko Taiwo ta samu labari. A ‘yan kwanakin nan da Aisha-Siddiqah Yunus ke tare da ahalin kawar mahaifiyarta Hajiya Nenne Sappa, tunaninta mara kyau akan Yarbawa sai ya fara canzawa gradually. Ta fasa bude zuciyarta tana gane su waye ‘yan kabilar Yoruba. Mutanene masu matukar