Sashe 24
Aisha Siddiqa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
dashi wanda shi kadai ta rike a kamanninsa, “Tabon Sallah_shaidar Sujjadah” wanda ke shimfide can farkon saman goshinsa. He didn’t give her a second look either… Iya abinda ta hango a tare dashi kenan, bata hango maraba ko rashin maraba da ita a tare Abdulrasheed ba. Kai ko kai ne Sigmund Freud ko Wilhelm Wundt wurin karantar dan adam bazaka karanci komai akan Siddiqah a tare da shi ba. Nenne na kara jin karfin jikinta, ta koma harkokinta na cikin gida, aka maida Aisha makarantar su Kiki ta jeka ka dawo. ***** **** **** Malamar da aka daukowa Siddiqa ma Bayerabiya ce mai suna Mrs Yemisi. Ana saura kwana biyu ta fara zuwa makaranta wato asabar malamar ta fara zuwa suka soma karatun bita. Muhimmin abinda zata koya mata shine Lissafi da Ingilishi. Siddiqah ta fara karatu daga takardar transfer da Babanta ya karbo mata daga FGC Billiri, ya aikowa Dade, ta fara ne daga (first term) na aji shidda inda daga shi sai zango na biyu sai zana jarrabawa Ranar data fara zuwa a darare take, ba abinda take tsammani a makarantar sai yaran yarabawa zasu yi mata “Atule bahaushiya!” Irin wanda take yiwa Bisola. Tunda ta gama saddaqarwa alhaki kwikwiyo na Bisola keta walagigi da ita a cikin Yarbawa. Amma akasi ga tunaninta daliban kowacce harkar gabanta take yi babu wadda ta lura da ita balle su kula cewa ita din bahaushiya ce, har saida form master din ajin ya gabatar da ita ga sauran dalibai a matsayin sabuwar daliba daga Gombe suka ji sunanta na hausawa ne. Tun yinin rana ta farko a makaranta Siddiqah ta san cewa makaranta tazo, wadda ta amsa sunan makaranta, ta ko’ina ta zarta Billiri zafin karatu, ba hadi ko kusa. Turancin makarantar har yaso yafi karfinta. Don haka Siddiqah ta dan ture kabilancin nata a gefe ta soma karatu tareda ‘yammata Yarabawa da sauran kabilu, amma yorubawa sun fi yawa. Har bada jimawa ba ta soma tsinttar wasu kalmomi na yarbanci irin su “Zo” (Wa) “Jeka” “bari” “good morning” (Ekaaro) da sauransu. Ta ga cewa ma akwai hausawa tsilli-tsilli a ajinnasu, wadanda galiban aiki ya kawo iyayensu jihar Lagos, don taji ana kiran jakadiyar ajin (class monitress) din da suna Maijidda Sulaiman Yabo. Cikin sati daya Aisha Siddiqah ta saki jikin ta a makaranta. Mrs Yemisi kuma na kokari da ita a gida, don ganin cewa ta haye Ingilishi daa Lissafi a yayin zana jarrabawarta ta kammala sakandire. **** ***** **** KIKI A karshen wannan watan da ake ciki ne Kiki ta kusa kammala course din da take yi a LA tazo Lagos hutu don gaida Kakanninta. Da shigowarta babban falon gidan ba wanda idonta yayi tozali da shi sai Aisha-Siddiqah, a lokacin tana zanawa Firdausi lalle a kafafunta. Sha’awar abun ya kama Kiki ba kadan ba, don Kiki akwai son abubuwan hausawa amma bata da kawaye hausawa, Aisha sai kallon Kiki take tana admiring komai na Kiki a ranta; ga tsayi, ga kiba kamar Aunty Murja, don ita Siddiqah duk wani mutum mai cikakken jiki sha’awa yake bata, ta kasa gane cewa jikin ta ma abinso ne musamman ga wadanda ke neman weight loss. A shirye suke dasu biya makudan kudade in zasu samu irin jikin ta. A ganinta Kiki komai ta hada, ga iya ado sannan ga kibar, ga hutu yabi jikinta, ya hadu da iyayi da rawar kan wayewar 'yammatan zamani masu yawo a duniya, duk wannan ya nuna a tare da Kiki. Ita kadai amma duk ta ishi gidan da karadi. “Nenne bakuwa kukayi ne, halan daga Gombe? So Pretty and Georgeous!” Nenne ta sha mamaki da Taiwo bata gayawa Kiki maganar Siddiqah ba, sannan shima duk yadda yake da Kikin ace bai mata zancen ba. wannan kadai zai nuna maka (how uncared they are) da zancen Aisha daga Taiwo din har Kehinde dinnata. “Umh!” in ji Nenne cikin takaicin Murjanatu, tafi takaicinta fiye da Kehinde saboda da ace ta karbi Aisha 100% da kyakkyawar fahimta akan zabin da ita Nenne tayi da komai zai zo da sauki, don ita kadai ce zata iya convincing din shi ya kalli Aisha da idanun rahma, har ya fahimci alkhairin dake tare da ita don da farko shi da bakinsa ya yabe ta kafin yaji maganar aure a tsakaninsu, Taiwo da taga dama zata iya taimakawa kwarai Kehinde ya bude zuciyarsa ya samar ma Aisha gurbi ko yaya, ya manta da komai da ya jima da sakawa ransa a kan mata. Amma har gobe tana kan bakanta na bazata cusa Aisha ga Prince ba, ta ma fara tunanin da Aisha ta gama karatun data sa aka katse mata a garinsu ta karbi sakamakonta na WAEC sai ta maida ita Gombe hannun iyayenta cikin salama. Ta san Aisha akan dole take zaune tare dasu don ba yadda zata yi ne amma zuciyarta tun fil azal bata son mu’amala da yarbawa balle alaqa mai girma ta aure. Fin karfinta iyayenta suka yi, sai kuma kirki da karamcinsu iyayen Abdulrasheed din a gareta ya taimaka wajen kwantar mata da hankali ta zauna. Amma Prince da al’amarinshi basa gabanta. Har Nenne ta soma ganin laifin kanta ta dinga tunanin anya bata dauki alhakin Aisha ba, data hada wannan auren? Ita dai tasan manufarta kyakkyawa ce akai, ta kwadaitu da hada tsatso da kyakkyawan iri ne, mai addini mai albarka, sauran kuma Allah shine shaida amma bata da wata manufa cikin hada auren Siddiqah da Prince. Bata san ya zata yi ta fahimtar da Taiwo da Kehide hakan ba. Idan Taiwo bata yi na’am ba, mawuyaci ne ya zama Kehinde zai taba yin na’am, because they share each others’ feelings. A tunanin Nenne Taiwo da Kehinde sun hada baki ne akan su yi wa Aisha kora da hali, wanda aka ce yafi kora da sanda, akan wannnan gallafirar Haseenah din rainon Taiwo. Ita kuma zata kyale su suyi abinda suka ga dama. A rayuwarta bata matsawa kowa yayi abinda ba ra’ayinsa ba, ta dauka farat daya Murjanatu in taga Aisha zata karbeta da hannu bibbiyu da zuciya daya, ta zamar mata uwar daki a cikin su, shikenan ta Kehinde zai zamo mai sauki, amma har gara shi din, bai kushe ba amma bai ce komai ba. Ita kuwa Taiwo muraran ta kushe Aisha har tace a mayar da ita ga iyayenta kai tsaye. ‘Ya’yan yanzu ne ba’a tuka su, musamman a shekaru irin nasu shida Murjanatun, babu karamin yaro a cikin su da zata tankwara ta karfi akan dole yayi abunda take so, musamman Abdulrasheed yadda yake gudun bacin ranta da gudun zuciyarta yake iya kokarinsa wajen kyautata mata da ‘yan uwansa, itama bazata yi abinda zai takura shi ba, duk da cewa in ta takura din zai bi, tunda ta lura da gaske bashi da lafiyar yin aure duk da ya musanta hakan ita yanzu ta yarda da hakan, ta kuma barwa Allah ikonsa, tana addu’ar Allah ya bata ladan kyakkyawar niyyarta na dabbaqa Sunnah a tsakanin Siddiqah da Prince, ya bata karfin zuciyar fuskantar iyayen Siddiqah ranar ta mayar da ita su yarda da hujjarta na Prince baida lafiyar auratayya koda bai fadi ba. Amma namijin duk da za’a baiwa lafiyayyar mace kamar Siddiqah a gaya masa matarsa ce ta Sunnah ba tareda ya kashe ko kwabonsa ba, zuciyarsa ta kasa motsuwa to ba namiji bane mai lafiyar mazantaka. Don in babu SO to akwai SHA’AWA a tareda kowanne Da namiji. Ita bata kin Haseenah din da Taiwo take so dashi, kawai tsatsonta ne tace bata yarda ya gauraya a cikin tsabtataccen jininta ba, ba kuma don komai ba sai don babu tabbacin halaccin haihuwarta. Amma tunda daga Taiwo har Kehinde su suna ganin abinda a wurinsu ita bata gani kalas! Yaje ya auri Haseenan dama duk matan gidan marayun Ambursa masu wayewar kai da iya rangwada in har yanada lafiya, don yanzu ita uwarsa ma tana tababa akan ingancin lafiyarsa. Sai suyi mai fishshesu ta maida Siddiqah ga iyayenta ko ba takardar saki, don bazata iya cewa ayi abinda Allah ya halatta amma baya so ba (saki). Dama Siddiqah din ba kwantai tayi ba kuma ba wani girma tayi da iyayenta suka gaji dashi ba. Mutunci ne da sanin yakamata da alkhairi yasa aka bashi ita. To amma ina mafita? Aisha zata dauwama ne da auren Kehinde da bashi da gurbin ajiyeta cikin rayuwarsa ko lafiyar da zai iya ijjema bukatar aurenta. A rayuwarta kuma bata ko son jin kalmar “saki” balle gittawarsa a aure, watakila ko don babu ita a kamus din gidan sarauta gabadaya daga nasu gidan sarautar har na mijinta. Sai taji ta kasa ce da Kiki Aisha matar Uncle dinta ce, in tayi hakan tamkar ta cusa Aisha ne a inda bata da kwarjini, tace da Kiki Aisha diyar kawarta ne kawai ta zo mata hutu daga Gombe. Ai kuwa tashin farko Kiki ta makalewa Siddiqah tana rokon itama tayi mata lallen, Firdausi tace “na kudi ne malama?” Kiki tace “Ke kudin kika biya Aunty Feedy? Imma na kudin ne kinsan Uncle dina zai biya mun ayi mun” Ta fada cikin tsananin shagwaba irin tata, Aisha na dariyar shagwabar Kiki katuwa da ita sai sokonci, tace. “Wasa Anti Feedy take miki kinji Kiki, zan miki lalle wanda yafi na Aunty kyau kin ji?” Kiki ta hau murna tace “kuma zaki na koya min hausa?” (kasancewar maganar Kiki duk rabi yarbanci ne sai kuma turanci da yafi yawa), Siddiqah ta ce “zan koya miki hausa har sai kin ce ta isheki”. To dama a dakin Kikin Aisha Siddiqah take zaune, sai ga Kiki na shigo da jakunkunanta jikake keeeyyy! Tana jansu a kasa cikin dakin cikin dokin zama tareda Aisha. “Pretty, tare zamu dinga kwana har in koma gida, yaushe zaki koma Gombe zan biki in ga gidanku?” Aisha ta rasa me zata cewa kiki, ita kanta batasan sunan zamanta a gidan Engnr. Idris Akanni ba, haka bata san matsayinta ba. Don haka a karshe sai tayi kundumbala kamar tasan shirin da Nenne ke yi tace, “Sai na gama WAEC zan koma gida”. A daren Kiki bata bar Aisha tayi barci da wuri ba sabida hira, Nenne taji dadin irin reception din da Aisha ta samu a gurin Kiki, ko dama bata jin ta, indai wajen son mutane ne