← Book details Aisha Siddiqa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 27

Sashe 15

Aisha Siddiqa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

iri-iri a Jeka da fari, don basu bayyana neman auren ba sai bayan daurin auren aka bayyana kowa yaji. Wasu ma sun ce Uban kasa ne da kansa wato Yayan Nenne Sarki mai ci a yanzu Abdul Yasar Jalloh Umar ya auri Aisha-Siddiqah. Duk kuwa da cewa ana kishin-kishin wai sarkin Ilorin ne da kansa ko babban dansa. Shaci fadi iri iri musamman daga gidansu Ishaq. A lokacin shi Ishaq yana can Abia state yana bautar kasa babu wanda ya sanar dashi daga gidan su. A kwana biyun Aisha ta dan kwantar da hankalinta, amma bata fitowa daga daki. Adda tayi mata kwalliya amma iyakata uwar dakin Umma. Ko falo bata zama. Musamman da Malam Yunus jiya da daddare yazo har dakin Umma ya sameta, ya bata kunshin balangun da ya shigo mata dashi mai zafi da ruwa-ruwa, don yasan ko abinci ba sosai take iya ci ba, sai Umma ta zauna ta bata a baki, shima loma uku take yi tace ta ko shi. Malam Yunus ya zauna a gefen gadon da Aishah take kwance, yace da ita “kwantar da hankankalin ki kin ji Indo? Dazu nayi Magana da Hajiya Sappa kan makarantarki, ko zasu mana alfarma su bari ki karasa kafin ki tare, tunda term biyu kadai ya rage miki? Tace kada in damu, gtana sane da wannan, zasu wuce dake gidanta a Lagos ne daga Ilorin, in an kai ki kin ga dangin mahaifinsa, Kakansa ya ganki yasa albarka, amma a gidanta zaki zauna har sai kin zana WAEC da NECO zaki bari ki tare a gidan mijinki”. Wannan albishir ya dan faranta ran Siddiqah. Ba’a tashi drama da Siddiqah ba sai a washegari da ‘yan daukar amarya suka iso da hantsi ido na ganin ido daga masarautar Gombe, tareda hamshakan dangin Abdulrasheed mata daga Ilorin. Matan Baffanninsa ne su duka tara da dangin marigayiya kakarsa Olori Murjanatu, wadda ta haifi Waziri Idrisu, su uku suka zo daban, suka hade da mutanen Ilorin suka taho Jeka da fari a manyan motoci Hummer Jeep bakake wuluk masu tinted. Raba Aisha da Ummanta kadai abin kallo ne domin wani ‘show’ ya koma, don saida aka boye Umman aka iya fitarda Aisha daga gidansu zuwa fadar Gombe, tare da Goggonninta su Addar Kumo, da Baba Barau da kansa a gidan gaban motar a matsayin uban aurenta kamar yadda yake a al’adar su dole a yi mata uban aure. Nasiha iri iri babu wadda iyaye da ‘yan uwa da baba Barau basu yiwa Aisha-Siddiqah tun daren jiya ba. ko ta dauka ko bata dauka ba dai ta ji su. A gidan Sarkin Gombe a dakin Nani Ummana wato Kakar Abdulrasheed data haifi Nenne Sappa aka kai amarya da iyayenta, Nani duk da ta tsufa sosai amma kasancewar 'ya'ya na kula da ita ga rike ibadah tsufa baisa ta rikice ba, tsaf take, cikin nutsuwarta, ita ta amshi amarya da iyayenta inda aka wadatasu da nau’I nau’I na kayan abinci na alfarma da abin sha gwargwado. Daga bangaren matan Sarki na yanzu wato Yayan Nenne Uban Kasa Abdulyassar wanda shi ya gaji mahaifinsu duk an kawo kabakin abinci iri-iri na sarauta. Da daddare ne aka kai Aisha har turakar uban kasa yayi musu addu’a mai tsayi, inda yace da ita suna mata maraba da shigowa masarautar Gombe. Suna mata fatan alkhairi mai yawa da fatan bada jimawa ba ta cika musu gida da 'ya'ya. Sun kwana a gidan Sarki karkashin kulawar Nani Ummana da hadimanta sai washegari Nenne da wasu daga ‘yan uwanta da iyayen Abdulrasheed mata da suka zo daga ilorin suka dauki amarya suka wuce Ilorin da ita ta jirgin sama, don a kaita ga Emir, da kuma dangin mahaifin sa da da yawa basu ma san da zancen auren ba. Abinda zai baka mamaki hatta Taiwo bata san komai ba. Nenne da Dade suna ta boyewa, Taiwo itace kunnen Abdulrasheed shiyasa suka boye mata kada su bata musu shiri, kuma cikin ikon Allah babu wanda ya kira ta a kan maganar don ta tafi UK tare da mijinta bayan y agama hutunsa. Da yawa cikin family din su ma basu sani ba, banda matan baffaninnsu da suka je Gombe dauko amarya. Princess Fatima da Princess Firdausi kuwa suna can gida Lagos, basu san meke gudana ba, sun dauka Nenne ta tafi mayar da Aisha wajen iyayenta ne kawai, daga nan zata ga gida ta dawo, basu san ana can ana bidirin auren Hamma (Prince) da Aisha a Gombe ba tare dasu ba. Duk abubuwa na al’adar su na karbar amarya an yi wa Aisha-Siddiqah a Ilorin, aka kuma kaita ga Emir. Sarki Abdulrasheed dan Abdullataeef Akanni, ya dade yana musu addu’a itada Kehinde ya kuma baiwa Aisha kyautar zoben zinare mai daraja a cikin battarsa, kyauta ce ta bajinta da sarki ya dade baiyiwa kowa ba. domin kuwa zoben na marigayiya Olori Murjanatu ne da ya gada. A kofar fitowarsu daga turakar Emir ne mayafin Siddiqah ya dan zame, fuskarta ta bayyana sai a idon Bisola. Bisola ta cika da mamaki, wannan kamar abokiyar fadanta Siddiqah Yunus. Ta tambayi ta kusa da ita aka tabbatar mata daga Gombe aka aurota. Bisola sai da ta san yadda tayi ta kutsa cikin mutane ta isa har jikin Siddiqah wadda ke rike cikin hannun Adda Magajiya, ta sunkuya daidai kunnenta ta ce “an fadi ba nauyi. Aisha Sadiqqah! Kece kuma kika bige da auren dan sarkin yarabawa?” A firgice Siddiqah ta dago sai taga Bisola Akanbi. Bisola ta kyabe baki ta ce “dama an ce mutum bai san inda ranarsa zata fadi ba. Sai a koyi kiyaye harshe acan gaba”. Ta murguda baki ta kada ido ta wuce cikin ‘yan kallo. Kafin su wuce Lagos kusan duk masarautar Ilorin sun samu labarin auren. Masu mamaki nayi masu jin haushi da takaicin an rasa wadda za’a baiwa Prince duk cika da batsewar masarautarsu sai diyar fulanin arewa na yi, kuma wai ba ‘yar sarauta bace diyar malamin sakandire ce, ko daga nan Aisha Siddiqah bata samu wani maraba sosai daga dangin mahaifin Prince ba. Musamman da ba wani shahararren biki aka yi mata ba irin wanda aka saba yi a gidan, ba kuma angon, kuma babu danginta masu yawa da suka nuna ita mai yawan dangi ce, sannan kowa ya tabbata Prince Kehinde, bai san ma ana yi ba. Rabonshi da kasar shi an doshi watanni uku kwarara yanzu. Sai bayan sun koma gida Lagos ne an kai Aisha dakinta na da, an kai mata duk abinda zata bukata sannan Nenne ta samu nutsuwar zama ta kira babbar diyarta Taiwo a waya, dake Lancashire a lokacin tare da maigidanta. Bata san cewa kafin ta kira ta tuni Fatima ta kira Aunty Taiwo din cikin tsegumi da mamaki, wai Anti Bisi (matar Uncle dinsu Malami Uban Doma) ta gaya mata sunje Gombe dauko amaryar Hamma Prince, amma meyasa Nenne bata saka su a ciki ba. Me hakan ke nufi?” Taiwo (was like) irin bata yard aba wasa ake yi, hakan ba mai yuwuwa bane a yiwa Kehinde dinta aure babu saninta. Wane irin aure ga Prince haka bagatatan kamar wasan yara? Ita din ai daga mahaifiyarsu wato Nenne, sai ita a mutane masu matsayi cikin rayuwar Prince, kuma ta ya za’ayi masa aure babu sani da amincewarsa sai kace wai saurayi ko karamin yaro? Don ko jiya sunyi waya dashi lafiya-lafiyar Allah sukayi sallama bai ce mata komai ba, mai nuna ya san zancen. Tana kashe wayar Fatima don tsananin haushi ta kasa cewa komai, sai ga kiran Nenne na shigowa, kamar jira take Fatima ta gama tseguminta sannan ita kuma ta kira. Taiwo ta amsa wayar mahaifiyarsu ba tareda ta nuna jin haushinta na tsameta da tayi daga al’amarin ba. Nenne ta kwashe komai ta gayawa Taiwo, tun haduwarta da Hajiya Zainab a tafiyar filin Munna, da yadda taji sha’awar karbawa Abulrasheed auren diyarta bai ko sani ba, ba don komai ba sai don ita kadai taga ta dace dashi. Yarinya ‘yar masu mutunci sannan mai addini da tsarkin nasaba. Amma ina! Hankalin Taiwo yana kan Haseenah da labarin data zo har UK ta bata akan abinda ya faru tsakanin ta da Tokumbo, cewa daga baya ta gane magani Tokumbo yasa mata a lemo a gidan Prince, yayi raping dinta a dakinsa shine har Prince ya zo ya gansu basu sani ba. Da sauran maganganu very sensitive na kare kai, da yasa ta daina ganin laifin Haseenah kwatakwata. Ai daga jin Nenne tace daga Gombe ne ta karbawa Hamma aure, nan take Taiwo ta tuna da zancen yarinyar nan ‘yar siririya da Fatima ke bata labari kullum, wadda tace Nenne ta dauko a Jeka da fari tana zuba musu fi’ili a gida har da kyamar abincinsu. Babban abinda ya bata ran Taiwo da aka yi abinnan babu sanin ta, ba kuma ita ta tsara komai ba. ba karamin buri ta ciwa auren Kehinde dinta ba duk ranar da yazo. Amma wai an yi an gama babu ko saninta. Taiwo nada son girma, wannan halin a ciki jininta ne, wanda ta tashi dashi a matsayinta na babbar Yayarsu tun suna yara tanada son seniority. Hakannan tanada son duk wani sha’ani in dai ya shafi Prince Kehinde ya kasance kacokam a hannunta. Kuma wai yarinyar da aka ce kyamar kabilarshi ma take yi, koba itace akace wai bata iya cin abincin gidansu ba. Me Kehinde zai yi da karamar yarinya haka (teen) mara exposure? Ai ko Haseenah da ya so ta baiwa shekaru 22 baya a lokacin, kuma tana ajina uku a jami’a a turai, duk da shi ya saka ta. Ta tabbata Prince ba zai taba yarda da wannan zabin ba ita kuma har kullum tana bayan abinda yake so ne. Ita a wurinta Prince har gobe yana son Haseena bacin rai ne da kishi, wanda tayi alkawarin sulhunta su. Nenne bata taba yin wani hukunci da ya bata ran Taiwo irin na wannan lokacin ba. Don ta katse duk wani hanzarinta na shirin sulhunta Haseenah da Kehinde. Kafin Taiwo tace komai, Nenne ta soma gargadinta kan cewa bata yarda Hammansu Fatima ya ji komai akan maganar auren shi daga bakinta ba, ta kyaleshi har zuwa ranar da yayi niyyar zuwa don kansa, bata yi mishi aure don ta takura shi ba, ita da
Chapter 15 · 0% Book details