← Book details Aisha Siddiqa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 27

Sashe 2

Aisha Siddiqa Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

AISHA-INDO-SIDDIQAH 2
B
ada jimawa ba binciken Malam Yunus da Yayansa Malam Barau ya bayyanar musu da duk abinda suke son sani game da ko waye Engnr. AbdulRasheed Idrees Akanni, ba kowa bane sai Polo Legend “The Latest Yoruba Demon” (inji abokin aikin Malam Yunus, wani bayerabe mai suna Abdulganiy musulmi da suke aiki tare a hukumar alhazai ta jihar Gombe wanda ya san zuri’ar Sarki Akanni kakaf sani na sosai da sosai, farin sani, kasancewar mahaifiyarsa ‘yar Ilorin ce kuma acan ya girma), mutuminnan ya gaya musu nasabar AbdulRasheed da iyayensa kaf dinta, a karshe ya gaya musu Prince din babban jikan Sarki AbdulRasheed Abdullateef ne (Emir of Ilorin) na yanzu, shine na fari cikin jikoki, sannan kuma jikan Sarkin Gombe ne na baya Sarki Ahmadu Jalloh Umar.
Har ila yau, an tabbatar musu da cewa Prince din baida wani aibi takamaimi da za’a ce shi ya hanashi aure akan lokaci, maiyuwuwa shahararsa a wasan Polo ce da arzikin da yake samu a jikinta suka kwashe lokacin sa da sha’awarsa daga yin aure a sanda ya dace,Abdulganiy yace don 'Polo Celebrities' na duniya irinsa aure akan lokaci na musu wahala matuka, musamman da basa zama a wuri guda kullum a tafe suke, a takaice a bakin Abdulganiy suka ji kusan komai da ya shafi Prince, suka ji cewa duka lokutan rayuwarsa na wasan tseren Doki ne a kasar Polo ta Argentina, sannan ya kan fita tournaments a sauran kasashen da ake Polo a duniya.
“Babu wanda yasan hakikanin abinda ya hanashi yin aure har tsayin wannan lokacin da yake cikin shekaru na 42”.
Amma koma meye, a cewar mutumin mai bada shaida bazai zama hujja na a hanashi aure ba a wannan zamanin da masu auren wurin ma ba duka ne nagari ba, don iyayensa malamai ne, mutanen kwarai, kuma sarakuna nagari.
Baban Aisha ya tsorata bayan jin wannan bayanin da kuma jin su waye Akanni’s, da matsayin ita kanta Haj. Nenne Sappa a Gombe, don haka ya tuntubi iyayen Ishaq akaro na uku kenan cewa Ishaq ya kawo sadaki ya aura masa Aisha a wuce wannan gabar don ya tsorata sosai. Domin koda suka yi tsammanin Nenne Sappa a matar mai kudi kawai suka tsammaceta, ba’a diyar sarkin Gombe, matar dan sarkin Ilorin, kuma uwar dan sarki mafi soyuwa a ran Kakansa ba.
Ya tuna dadewar da Ishaq yayi tareda Aisha-Siddiqah, da karfin shakuwa da soyayyar dake tsakaninsu tun farkon balagar kowannensu, don haka ya yankewa kansa cewa Ishaq shi yafi kowa cancantar aurenta, yaro matashi kamarta, wanda zai rike masa ita da daraja da kima, kada ya kaita inda bazata yi daraja ba, shi baya son auren hadin iyaye irin wannan, yafi yarda da aure na na gani inaso daga namijin kansa ba daga iyayensa ko wani nasa ba.
Ishaq kadai zai iya baiwa Aisha hakalinsa ya kwanta, don shi ya san asalinta ya san halinta ya san komai na iyayenta da ciwon asmarta mai dan tashi lokaci-lokaci.
Malam Yunus mutum ne marar kwadayin abin duniya kamar matarsa Zaynaba. Tabbas duniya tayi musu wannan kyakkyawar shaidar akwai wadatar zuci. Shiyasa hankalinsu ya zo daya suke zaune lafiya shekaru aru-aru ba mai jin kansu. Hankalinsa a kwance ya kira dan uwansa Malam Barau ya gaya masa komai ya yanke, sai Barau yace su wuce gidan Malam Hassan din kawai a yi komai yau a gama wato mahaifin Ishaq a yita ta kare su aurar da Aisha su huta.
Shima Baba Barau ya dade da sanin duk duniya ba mai son Aisha irin Ishaq Hassan, yaron ya jima yana hidimarta da dakon soyayyarta tun shigarta sakandire, ba wani mai mulki ko mai kudi da zai rude su su yi wa Aisha auren cushe. Auren da bazata yi daraja ba ko a maidata sadaka.
Nan suka mike suka je har zauren gidan su Ishaq suka tadda mahaifinsa Malam Hassan kuma makwabcinsu, suka share wuri suka zauna suka gaya masa duk abinda ake ciki, a karshe Malam Yunus yace yana son aurar da Aisha a wannan gabar, yana tsoron al’amarinta, rana daya ne ba’a zuwa a sameshi akan maganarta da manyan mutane, Aisha manema gareta bila adadin ba tun yau ba, mafi yawansu kuma ‘ya’yan manya, sannan ‘ya’yan mutunci da iyayensu ke takowa da kansu har gidansa nema musu aurenta, wadanda mutuncinsu yake sawa bazai iya tula musu kasa a ido ba saidai yayi ta togaciya da Ishaq.
Yace yau gashi ‘ya’yan Sarakuna sun fara zuwa neman aurenta. Gaba kadan bai san su waye kuma zasu zo neman auren Aishar da ya dade da ajiyewa Ishaq ba. Malam Yunus din yace farin jininta yana bashi tsoro a shekarar nan data shiga ajin karshe na sakandire.
Budar bakin Malam Hassan kasancewarsa irin mutanen nan da basa tauna magana ko kadan kuma basu da kawaici akan ‘ya’yansu musamman in suka lura yaran nama mace mugun so, sai yace da Malam Yunus da dan uwansa Kawu Barau.
“ku gafarce ni Barau da Yunusa, domin dai ni na dade da yiwa Ishaq mata a cikin dangin mahaifina dake kauyen Nafada, maganar gaskiya kawai kallonsu muke yi tuntuni (Aisha da Ishaq din) nida mahaifiyarsa, shiyasa tun da farko da ka tuntubeni watannin baya kan batun aurar da Aisha nayi shiru ban baka cikakkiyar amsa ba.
Amma zuwa yanzu ba zan boye maka ba Ishaq ya jima da samun mata daidai da ra’ayinmu”.
A karshe yace “bazai aura ma Ishaq (mai ciwon numfashi) ba, kamar aka ce mata sun kare a duniya, don Asthma ana gado, kuma (allergy) ne a cewarsa. Yace kuma shi za’ayiwa barazana da sarakuna da masu kudi don a takura shi tashi tsaye yin aure bai shirya ba dansa ma bai shirya ba sabida ka gaji da sayen inhaler da maganin Asma da yawon kwanciya a asibiti?
Yace to ba sarakuna ba Barau da Yunusa, ko dan shugaban kasar Najeriya ne yazo neman aurenta na lamunce ka aurawa diyarka damuwarku ce.
Ishaq yanzu yake kokarin hada hidimar kasa, baida halin aure a yanzu. Shiyasa na nema masa yarinya ‘yar shekara goma sha daya wadda zata yi daidai da zabinsa da namu”.
Wannan magana ta fusata Malam Yunus da dan uwansa Kawu Barau, ta kuma bakanta ma Barau rai ba kadan ba, kasancewarsa mai saurin fushi da yawan harzukar zuciya a kusa, sukayi shiru shi da kaninsa Yunusa zaune akan tabarma a zaurensu Aisha. Barau tun fil azal mutum ne mai saurin daukar zafi akan ‘ya’yansu, sabida ko a cikin ‘ya’ya takwas maza da mata da shi yake dasu a gidansa manya da yara, tofa yana ji da Aisha-Siddiqa a cikin yaransa, kasancewarta daya tilo da Allah ya barwa dan uwansa, kuma duk rashin kwaramniyarta da kazarniyarta irin na sauran ‘yammata yana son dabi’unta.
Bayan sun baro soron Malam Hassan Kawu Barau ya samu wuri ya zauna a zauren gidan su Aisha, ya dubi dan uwan nasa Yunusa da idonsa ya kada, yace “bayerabe ne kace dan ita Hajiyar Lagos din ko me? Kuma ya jima bai yi auren fari ba? Sannan ba’a kasar nan yake rayuwa ba gabadaya kuma dan wasan Polo ne shiyasa kake tababar bashi auren Indo ko?”
Malam Yunusa ya gyada kai. Sai Kawu Barau yayi kuta yace. “To gara shi sau dubu akan zuri’ar wannan marar karar makwabcin naka daka kwallafawa rai, da bai san mutunci da kara ba, kamar ba bafullatanin mutum ba, na bi kabilanci da gudu na kamo shi na kawo cikin zuri’ata”.
Nan take Kawu Barau ya shiga cikin gidan ya gayawa Haj. Zainab ta gayawa kawarta Haj. Sappa take ko Safiya? Duk sanda suka shirya su turo an basu auren “Aishatu-Siddiqah Yunus”.
Kawu Barau yace cikin bacin rai, “ba Bayerabe ba ko dan sarkin Nufawa da Agalawa ne Dan nata, a gaya musu ya bashi Aisha. Tunda har uwarsa da kanta tazo ta durkusa a gabanka har da hawayenta tana rokon a basu auren Aisha sabida kauna, cikin darajawa da mutumtawa irin haka ba tareda la’akari da matsayinmu ba, alhalin ita ta san da Asmar Aisha, don haka shi ya basu Aisha-Siddiqah ko dan nata yayi saba’in a duniya ba arba’in da ‘yan kai ba, koda kansa fari fat ne yana dogara sanda don tsufa an bashi, in yaso Aisha ta yi zaman zuba ruwa a buta da kai masa ruwan wanka bayan gida, wato (tayi zaman kula da tsufansa ba zaman soyayyar miji da mata ba)”.
**** **** ****
Chapter 2 · 0% Book details