← Book details Aisha Siddiqa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 27

Sashe 6

Aisha Siddiqa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kai bawa baka da ikon banbance kabilar da zata shiga karkashin wannan inuwar a cikin musulman duniya”. Haka Nenne tayi ta yiwa Siddiqah nasiha mai shiga jiki akan ta daina wariyar launin fata akankabilun da ba na arewa ba, tace ba Yarbawa kadai ba, dama kowanne yare in dai musulmi ne, har a karshe tacema Aisha cikin zolaya ganin ta kasa sakin ranta. “baki sani ba ko akansu ranar ki zata fadi Siddiqah?” Ta karasa da dariyar tsokanar Siddiqah, Aishah-Siddiqah ta sunkuyar da kai ta nutsu tana sauraren wa’azin Nenne kamar da gaske nasihar da take matan na shigarta. Sai tace a ranta ai tunda Babansu Firdausi Bayerabe ne, ko meye ma Nenne zata ce akan yarbawa din, dole kuma ta so su tunda har zuri’a mai yawa ta shiga tsakani amma ita meye nata, ita bata ga dalilin da zata yarda bayerabe da bafillace abune iri daya ba. A zuciyar Siddiqah tace “in Allah ya yarda a Nafada rana ta zata fadi, Ishaq Hassan Nafada, mijin da Allah ya zabar min tuni, baida alaqa da Yarbawa ko any yare, ta kowanne bangare shi hausa/Fulani ne ziryan”. Kenan nasihar Nenne ta shiga ta hagu, ta fita ta dama a kunnen Siddiqa, nan kusa bata ga me zai sa ta yarda bafullatani/bahaushe daya yake da bayerabe ba. Watakila dai Umman Siddiqah wato Haj. Zainab ta manta da halin Petel dinta ne na rashin wayewa da shiga jama’a da irin wautar ta na diyan fari ne ko auta za’a ce, wanda ta kan taba lokaci-lokaci, gashi ita ba ‘yar fari ba ita baza’a kirata auta ba. Aisha-Siddiqah a dabi’arta bata iya boye abinda ke ranta ga wanda ya girmeta musamman Ummanta da tafi kowa kula da abinda zai dameta, kuma kallon kawar Umma take kamar tata uwar. Shiyasa kai tsaye ta zayyano mata abinda ke ranta babu kwane-kwane, watakila Ummanta ta manta da hakan wato rashin sakaya damuwa irinna Siddiqah, da maiyuwuwa bata barta ta biyo Nenne Sappa ba, ba tare data sanar da ita Aisha nada tarin rashin wayewa ba. A rayuwar Aisha Siddiqah Yunus, ita batasan wani abu kara ba, ko fuska biyu, sannan bata san boye abinda bai yi mata daidai da ra’ayin taba, komai girmansa kiri-kiri zata nuna maka abin nan bai mata ba. Ita ’yar keke-da-keke ce. Ba sakayawa. Da kyar Nenne ta samu ta yarda ta sha fresh milk din data kawo mata, don tace mata a firjinta ta dauko, amma sam ta ki cin shawarmar. Tace a ranta mai yuwuwa da naman dodon kodi akayi shawarmar ma. Princess Fatima ta koma da baya zuwa dakinta da bacin ran maganganun Siddiqah fal ranta, taji bata son zaman Siddiqah a gidansu, nan da nan ta dauki waya ta dokawa aunty Taiwo, a mamakance tana labarta mata irin yarinyar da Nenne ta kawo musu gida daga Gombe wai kyamar Yoruba food take and Yoruba people. Taiwo tace “'yar waye haka?” Fatima ta labarta mata daga haduwa da uwarta a Saudiyya Nenne ta makale musu harda dauko 'yarta wai zata kaita asibiti”. Taiwo da yake ta san halin karamcin mahaifiyarsu sai bata yi mamaki ba, cewa Firdausi tayi “in kin bibiya hausawa ne, sune most attimes masu raina kabilar Yoruba. They are more ethnocentric. Kuyi hakuri ita da kanta zata maida ita inda ta daukota”. Princess Fatima har lokacin ranta bai gamsu ba, haka curiosity na son sanin dalilin Siddiqah na kyamarsu wai har abincinsu duk tsaftarsa ya ki ya barta. Sai ta kira Hamma (Prince). Tana so a bata karin bayani akan me Siddiqa ke nufi da hakan? She was like irin me aka fi su? Taiwo kuma kashe wayarta tayi bata yarda sun tattauna maganar ba don tana tareda Toufeeq a lokacin ya zo musu annual leave. "Hamma!" Daga daya bangaren, Prince ne ya amsa, a lokacin yana tsaye kan Pareto ana yiwa Dawakansa wanka, yaja gefe yana amsa wayar Fatima. "Bongel!” (Sunan da Prince yake kiran kanwarsa Fatima) wanda kalma ce ta harshen Fulatanci mai nufin “mai kyau”, ya kara da cewa “Bongel, yaya akayi ne?" A fusace Princess Fatima tace "Ka roki Nenne ta sallami yarinyar data kawo mana gida daga Gombe, kafin na yi mata ‘Ai lojuti’". Ta bashi dariya sosai don tana nufin (kafin tayi mata rashin mutunci) da harshensu na Yoruba. Da muryarshi ta girma da kasaita mai tafe da lallashi ga kanwar tasa Prince yace. "Wace yarinya ce haka? Bansan Bongel na da rashin mutunci ba". Nan Fatima ta gaya masa wata yarinya ce Nenne ta kawo bata fice sa'ar Kiki ba, sai mulki da fi’ili take zuba musu a gida da shan kamshi da kyankyami sabida taga Nenne na nan-nan da ita, wai bata iya cin abincin su sabida su Yarbawa ne". Abin ya bashi dariya sosai yace "Bongel, haka Hausa-Fulani ke ma Yoruba people kabilanci ai, tun iyaye da kakanninmu, tun muna yara munsan wannan irin kabilancin da hausawa ke mana, muma kuma Yoruba kada ki manta haka muke musu kallon wadanda basu waye ba, kauyawa, dakikai, muna ganinsu marasa ilmin boko da ko turanci basa ji duk ilminsu, kema ba sai ki rama ba? Hausawan da asalinsu maguzawa ne? Kice mata jikokin barbushe da tsimbirbira ‘yan kan dutse, in kuma bafullatana ce bakida halin ramawa fa Bongel, for Nenne’s sake, for Nani’s sake ki yafe mata. Saboda kema rabi itace, fullata, saidai kawai in kinje gidansu kema kada ki sha fura da nono kada ki ci tuwo da miyar kuka, inace shikenan kin rama?". Kasancewar da yarbanci suke maganar harshen da Princess Fatima tafi jin shi sosai fiyeda kowanne harshe da suke yi a junansu. Ganin Hamma yaki daukan zancen da muhimmanci ya kara tunzura Fatima. Gabadaya Hamma ya maida zancen wasa. Tace "Hamma I am serious, Nenne ta dauki yarinyar nan da muhimmanci wallahi, I am jealous of her, wata 'yar firit da ita, sai shegen kyau irin na aljannu". Wanna karon Hamman, couldn’t control his laughter akan wautar kanwar tasa, wadda daga murmushin kasaita da yake yi yanzu ta zarce zuwa dariya mai kima, yace "kada kice min kishin kyawun nata kuma kike yi Bongel? Shin Bongel akwai wanda ya kai tagwayen Nenne (Fatima da Firdausi) kyau ne a Najeriya? Kada ki manta sau biyu kuna dauko ‘beauty contest’ a makaranta in kin manta ni ban manta ba”. Fatima taji dadi, ta saki kasaitaccen murmushi (from ear to ear), ko ba komai Hamma Prince yasa kanta ya kumbura, ta rage jin haushin Siddiqah, amma ta rasa ta yaya zatayi dashi ya yarda bata son zaman Aisha-Siddiqah a gidansu, ganin ta kawai fadar mata da gaba yake yi, don jinta take kamar (part of the family), alhalin ba abinda ya hada su. Sai ta nisa tace "Hamma! Ni bana son zamanta damu kawai, Hamma bana son bare agidanmu, kai kadai zaka iya yiwa Nenne magana ta ji, to take her back to her home, har akwai wata kabila da zata aibata Yoruba a idanuna in so ta?" Yace "in kuma bafullata ce fa, tunda kince daga Gombe ta dauko ta? Ai kema Fulani ce idan anbi salsala, jinin Uwa ma da kaurinsa, don haka taci albarkacin ta fito daga tsatson kabilar Nenne, keda ita duk abu daya ne, kinji Bongel?!" Da haka Prince ya kashe bakinta ya lallasheta suka yi sallama a wayar, ko dama can haka yake da son kannensa da kula da al’amarinsu, kome yake ciki in suka kira zai tsaya ya sauraresu ya basu attention dinsa, amma duk da haka da Firdausi ta dawo saida ta gaya mata komai data ji tsakanin Nenne da Aisha-Siddiqah, don abin ya kasa barin ranta, da abinda Hamma Prince yace na hakan ba abunda zata damu bane, in dai akan hausawa da Fulani ne. Princess Firdausi tace “I once heard something like that fah, Hausawa na da kabilanci akan Yoruba food and Yoruba people in general, ba tun yau ba na sha jin wannan kisser ba, so ki manta da yarinyar nan har nawa take, kin faya mita da kambama karamin abu Fatima”. Nan suka hadu suna tattaunawa akan kabilancin da hausawa ke yi akan duk wani yare na cewa ko kai musulmi ne in dai wani yare ne kai ba hausa Fulani ba kallon wani arne-arne suke yi maka, basa maka kallon cikakken musulmi, meyasa? Kuma me ya janyo? Sannan saboda me hausawa ke yiwa yare haka? Haka Suka maida abin ‘topic of discussion’ dinsu na ranar, kamar masu yiwa juna (tutorial class). Su lallai suna son gano dalilin afkuwar hakan tun tali-tali. Fatima har da hada ‘Imo’ ta kira Yayarsu Taiwo. Suna shiga tattauna maganar tareda Aunty Taiwo dake Ilorin a lokacin. Amma Firdausi kare Aisha take tayi, tana cewa ai yarinya ce da bata wuce sa’ar Kiki ba, kuma bata da wayewar kan da har zata san sauran kabilu sun wuce haka yanzu a hannun hausa-fulani, tace ba wani exposure keda yarinyar ba tunda daga cikin Gombe take, su yi mata uzuri. Allah kadai yasan dalilin Nenne na son yarinyar alhalin bata da alaqa da su, kuma basu kai matsayin da Nenne zata yi alaqa ta jiki dasu ba irin haka a matsayin su na talakawan gari. Lafiyayyen dakin da aka baima Siddiqah ita kadai shimfide yake da sabon lafiyayyen zanin gado hade da duvet mahadinsa, amma Aisha-Siddiqah tasa hannu ta cire zanin gadon nan ta aje a gefe, ta yi kwanciyarta akan zanin atamfarta wai bata sani ba ko Yarbawa sun kwana a kanshi, ita bata son jin warin jikin Yarbawa. Duk fadan da Umma tayi mata kafin su taho na shan magungunanta, ta bayan kunnenta yabi ya fice. Tun saukarsu a Lagos bata kara shan maganinta ba, ta yi masa maboya cikin lokar jikin gado ta manta dashi. Dama dai Siddiqah ba dai kin kwayar magani ba. Cikin dare kuwa Asma ta tashi, sosai sosai, ita kadai tayi ta fama da inhaler ba wanda ya san me take ciki, ga yunwar data dorawa kanta don haka kafin garin Allah ya waye Aisha-Siddiqah ta ji jiki, tayi zuru-zuru a garin Ikko kamar ba gidan daula tazo ba. A tsarin rayuwa irin na Fatima da Firdausi, ba Siddiqah kadai ba ko wani wanda ya hada jini dasu ne ya zo gidansu da sunan kwana, misali daga Ilorin cikin dangin Dade, kota fannin dangin Nenne daga
Chapter 6 · 0% Book details