Sashe 22
Aisha Siddiqa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
dawo”. Daga bakin kofar da take tsaye ta russuna da irin durkuson yarbawa ga manya ta soma gaisheshi, wani irin innocently bewildered, ba tareda ta dawo cikin dakin ba, muryarta na fita a nitse, a ladabce, tana kuma dan shaking haka, cikin fadin, “Barka da zuwa HAMMA ABDUL. Yaya hanya? Allah ya huta gajiya ya baima Nenne lafiya”. Prince AbdulRasheed dai ya rasa a yanayin da gaisuwar tata ta riskeshi, yana cikin wani hali ne na juyayin halin da mahaifiyarsa ke ciki, tunanin halin da Nenne ke ciki yasa baya fahimtar komai sosai yanzu. A halin da yake ciki yanzu bashi dako muhallin da zai iya amsa wata gaisuwa daga kowa in har ba ya ga Nenne ta mike akan kafafunta ba. Don haka bai amsawa Aisha ba. Ya bita da kallo kawai da manyan maganansa da suka dan kada. Sai Aisha tayi amfani da shirun nasa tayi ficewarta. Kallon idanun Prince kadai ya nuna mata bai santa ba sai yau, kamar yadda itama yau ne ta ganshi gani na farko, bayan auren watanni akalla hudu, kuma ganin nasa ya hargitsa nutsuwarta da tunaninta, don yadda ta zace shi ba haka ta ganshi ba. Tayi tsammanin ganin irin katon bakin bayerabe. Sai taga ba haka ba, wani sardidin matashi ta gani tsaye a gabanta mai wadatar lafiyar jinin jiki da koshin lafiya da kuzari, ingarman jiki gareshi irin dai na ‘ya’yan sarakunan Najeriya. Amma me? Bata ga wani gurbi a fuskarshi na ya santa a matsayin matar shi ba. Gashinan dai emotionless. Ba wani reaction da ya nuna mai nuna ya santa ko sanayyar miji zuwa ga matarsa, wani abu data dade tana tambayar kanta “anya Hamma dinma ya santa?” yau dai ta yarda ko a fuska bai santa ba shima. Itama bata ji komai game dashi a ranta ba bayan ‘yar faduwar gaban data samu daga ganinsa na farko yana shigowa, Hamma ya bayyana sabani ga tunaninta. Fuskarsa kadaran – kadahan, wato ba yabo ba fallasa a lokacin da suka hada ido, wato dai kallon da kake yiwa wani da ka fara gani yau aka nuna maka ya sanka kafin ka ganshi, amma bayan wannan babu abinda Siddiqah ta iya ta fahimta a tare da facial expression dinsa. Dade kuwa binsu yayi da kallo a sace su duka biyun yana kokarin karantarsu, har Aisha ta fice daga dakin asibitin da ‘yar sassarfa, dogon maroon kala hijabinta, yana binta yana jan kasa. Seun, ya daukota sai gida. Ta bude ta shige dakinta har da tuntube, ta kulle kanta ta fada toilet ta sakarwa kanta shawa mai dumi tayi wanka sosai, daga bisani ta daura alwallah ta dauro towel a kirjinta wanda ya sauko har saman cinyoyinta ta fito. Tana idar da sallah Princess Fatima da Princess Firdausi suka shigo dakinta a tare, suna tambayarta ina Nenne. Saukarsu kenan daga filin jirgi suka biyo taxi suka iso gida. Siddiqah ta gaya musu Nenne na asibiti babu lafiya yanzu ta dawo daga can, Seun yana waje ai, shi ya dawo da ita, tace su je ya kai su ya san dakin da Nenne take. Don ita Dade yace ta dawo gida tayi wanka sai dare zata koma in ta girka abincin Nenne. A firgice Fatima ta dubi ‘yar uwarta Firdausi, itama ta dubeta, sai suka juya da gudu cikin razani, da sauri suka fice. Saddiqah ta cewa ranta tunda dai duk ‘ya’yan Nenne sun hallara akanta, to komawarta asibitin a daren yau bashi da amfani kada ta takura musu, musamman zasu so su sake da Yayansu da ya jima baya nan, a ganinta presence dinta a wurin zai iya rage musu jin dadin haduwa da juna ko ta hanasu sakewa yadda suka saba. Don haka bata koma asibitin a daren ba. Seun ta shiryawa abinda Nenne zata iya ci ya tafi dashi, faten dankalin turawa ne tayi mata mara yawa da yaji ganyen alayyahu da hanta da koda. Sai washegari da safe ta sake shirya karin kumallon mara lafiya, ta yi wanka ta shirya tsaf cikin ruwan goron atamfa mai glitter din silver da ratsin baki ta dauki abincin a Kwando ta tafiwa da Nenne. Seun ya dauketa sai asibitin. Lokacin Fatima da Firdausi kadai ta tarar a dakin. Prince ya je gida yin wanka shima don anan asibitin ya kwana. Don haka sosai ta sake cikinsu Fatima suka gaisa ta tambayi mai jikin da gajiyarsu ta biki a Ilorin, daga nan ta karbi komai a hannunta na kula da Nenne. Su kuma suka sakar mata suka fara shirin tahowa gida, dama Nenne tafison Aisha tayi mata komai, ta kan ce ai ta fisu zafin nama. Aunty Murjanatu ma daren ranar ta baro UK zuwa Lagos don duba jikin Nanne. Ko don taron dangin da iyalin Engnr. sukayi a asibitin yasa dole likita ya baiwa Nenne sallama a washegari, musamman da ya kasance surgery din da aka yi mata na zamani ne kuma yayi kyau sosai baya bukatar doguwar jinya, in yaso ta cigaba da shan magani da ganin likitanta a gida. Sun dawo gidan dukkansu a tare, a mota guda, in ka cire Prince da ya biyo motar Dade. Nan gida ya kacame da hidima, masu aiki sai shige da fice suke yi suna kaiwa da komowa don wadata al’ummar gidan da abinci da abubuwan bukata da tsaftace shi. Prince tun daren jiya ya zama curious sosai akan bafullatanar yarinyar dake jinyar Nenne a asibiti, yana hankalce da duk irin kyakkyawar kulawar da take baima Nennensa da dukkan nutsuwarta da attention dinta in tana gaban Nenne itace kawai a gabanta, ko uwarta ce sai haka, kuma yaji dadi sosai a ransa. Ya cika da son sanin ko wacece yarinyar. Kwana biyu kacal da dawowarsu Nenne ta kara warwarewa, duk da bata bar gado ba amma tana iya cin komai da Siddiqah ta sarrafa musamman don ita. Yau da kansa ya tambayi Nenne bayan fitar Aisha daga dakinta, bayan ta gama bata maganin safe. Tana kokarin fitowa shikuma yana shigowa. Sai ta rabe cikin ladabi ta bashi hanya ya wuce ciki, ta gaisheshi a gajarce yana amsawa yana karasawa ciki. Prince ya zauna a gefen kafafun Nenne, suka gaisa yadda suka saba, ya tambayeta ina ke mata ciwo yanzu Nenne tace babu sai bayanta, shima din saboda yawan kwanciya ne. Yau dai Prince ya kasa shiru har ta kai da ya tambayeta. “Ni Nenne ‘yar waye wannan kika samu haka mai kokari a kanki da nutsuwa, sannan ga hankali da ladabi haka?” Nenne taji dadin furucinsa, a lokaci taga ya kamata tayi masa bayanin kome ke akwai, don a yanzu taji karfin jikinta zata iya daukar reaction dinsa. Tayi sassanyar ajiyar zuciya tace. "Abdulrasheed Aisha matar ka ce fa. Itace matar dana zabar maka a duniya da lahira. Cikakken sunanta “Aishah-Siddiqah Yunus”. Ita muka zaba maka nida mahaifinka da albarkar Kakanka Emir. Itace matar da muka aura maka baka nan, kusan watanni hudu kenan tana tare dani tana jiran zuwanka. Kayi min biyayya yadda Aisha-Siddiqa ta yiwa iyayenta, ka zauna da ita cikin kauna da amana ko bayan raina". Nan Nenne ta koro masa labarin asalin haduwarta da Haj Zainab da yadda komai ya wakana. Abdulrasheed ya rasa tsakanin mafarki da ido biyu wanne yake ciki. Don jin abinda Nenne ke fadi yake kamar almara mara yuwuwa. Prince Abdulrashheed ya yi shiru yana jin bugun zuciya na wani lokaci kamar ruwa ya cinyeshi. “Aure? Aure? Aure? Mata? Gareshi shi Abdulrasheed Idris Akanni Kehinde din? Ko kuwa dai wani ne daban da ya sani mai irin sunansa Nenne ke nufi?” amma a yadda tayi maganar nan she seriously mean it. Ba shiri ya yiwa Nenne sallama yace zai je yayi sallahr walha, ba tareda ya tofa komai akan muhimmin zancen Aisha data gama yi masa yanzu ba. Ai kuwa tun daga lokacin Prince ya daukewa Aisha wuta, 'yar gaisuwar ta da yake amsawa a mutumce da karsashi in ya zo ya tadda ta tare da Nenne ya koma baya amsawa ma. A kwanaki biyun nan kullum zaka samu ‘ya’yanta sun zagayeta amma Siddiqah taki zama a cikinsu musamman bayan zuwan Aunty Murjanatu (Taiwo), da irin tarbar data samu a wurin ta, sannan da dauke mata wuta da Hamma yayi lokaci guda, ba tare data san ba’asin abin ba. Don wani sabon daure fuska ya koma yi mata. in kuwa ta shigo dakin Nenne yana ciki to zai fita yace ma Nenne yana zuwa. Hakan yasa duk ta takura, ta fara killace kanta a dakin ta zuciya babu dadi. Amma hakan baisa ta fasa zuwa ta yiwa Nenne hidimar data saba yi mata ba, ta bata magungunan ta, ta gyara mata gado ta bata abinci ta killace mata daki. In ta gama sai ta bar musu dakin, ta daina zama sam a dakin ko a falo ta koma nata dakin kawai, ko ka sameta a kitchen tana taya Femi da sauran masu girkin gidan shirya abinci. Nenne ta fiso Siddiqa ta dinga zama a cikinsu, bata son ware kanta dinnan data soma yi wanda ta lura saboda Prince ne, amma taga yaran nata kamar sunfi gamsuwa da hakan da take yi musamman Aunty Taiwo wadda ko bude ido bata son yi taga Aisha a cikinsu, ba kuma ta son yiwa kowannensu korafi akan Aisha don tserar da martabar Aisha din a idanun su kada su rainata, amma dai ta gane babu wanda ya damu da zamanta cikin gidan banda Firdausi, musamman bayan zuwan Aunty Murja duk sun kara ja baya da Aisha. Kannenta sunata murnar zuwanta kamar me don Aunty Murjanatu ta dade batazo Lagos ba. AbdulRasheed, Murjanatu, Fatima da Firdausi sun hadu yau sun saka Nenne a tsakiya kowa na bata labaran da suka shafe shi da harshen da yafi so, masu yarbanci na yi haka masu turanci, amma Nenne da fulatanci take mayar musu. Can na hango Prince AbdulRasheed a gefe yana cin “WARA” akan wani ‘royal plate’ mai ruwan gold, wadda yasa Femi tayi masa, ya takaitawa kansa yawan magana a cikinsu yanzu, ba don komai ba sai don tunanin yarinyar da aka kira matarsa ko tana inama? Baya son wani dan adam ya shiga takura saboda shi, ya kuma lura zamansa a gidan ya takura Siddiqah din, don haka ya sakawa ransa komawa da gaggawa ba tareda ya batawa kowa