Sashe 5
Aisha Siddiqa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
data kunso ta cika bakinta dashi. Kasancewarta Uwa mai tsananin kula da mood din ‘ya’yanta. Abincin da Siddiqah ta tsana a duniya (bakar Amala) ne aka yi da kuma lafiyayyar sakwara dakan hannu (pounded yam) da taji kirbin tabaryar Femi tayi laushi lubus da miyar ganyen Ugu da taji kaguwa da ganda zuqu-zuqu da naman Tolo-tolo wannan shine (favourite food din Dade) kuma don shi aka yi, in har yana gida to abincinsa kenan, duk da yace ba zai dawo da wuri ba a fitar da ya dan yi sun zuba a ma’adanan abinci (food warmers) sun ajiye masa nasa. Amma Siddiqah ko loma uku kwarara ta kasa, kuma ko sha'awa abincin bai bata ba, duk haduwar abincin da bajintar Femi wajen iya abincin yarbawa na alfarma, itafa komai na bayerabe bai burgeta, a wani bangarenma kyankyami abincin ya bata. Ba dadewa tun ba’aje ko’ina ba Nenne ta gama karanto matsalar Aisha-Siddiqah da zaman gidan (kabilanci) ne da ita, da belief din cewa kabilarta sama take data kowa, abinda masana zamantakewar dan adam ke kira ethnocentrism (feeling na cewa kabilarka tafi ta kowa daraja) irin wanda itama tayi fama da shi a farkon zuwanta cikin zuri'ar Emir Abdulrasheed Akanni, wato royal family na masarautar Ilorin. Banbancinta da Aisha-Siddiqah ita ko a lokacin data zo bata kyamaci abincin Yoruba ba, dagewa tayi ta koyi ci, kai komai nasu ma kokari take tayi adopting cikin dan lokaci with great passion, saboda soyayyar mijinta Engnr. Idris Akanni data yi wuf da ita lokaci daya, sabida karamcinsa da bala’in iya tattalin mace da nuna soyayyarsa karara gareta. Murmushi Nenne ta yi. Zuciyarta tayi tsalle ta tafi ga hasko mata ranar da za’a kai Siddiqah gidan Prince Abdulrasheed a matsayin matarsa. Ashe kuwa kallo na gaba, in dai haka Siddiqah ta dorawa kanta kabilancin kabilar Yoruba babu gaira babu dalili. Ko yaya Siddiqah zata ji ranar da aka sanar da ita Bayerabe dinne abokin rayuwarta na har abada toh? Bayeraben ma jikan sarkin Yarbawa, shi ne zai mallaki komai nata da take tinkaho na Fulani ne? Murmushi sosai Nenne tayi a lokacin, tana hangowa idanunta Siddiqah da Abdulrasheed a matsayin mata da miji. A cikin ranta tace “Aishatu-Indo Siddiqah! Ina jiye miki ranar karyata kai. Ai saidai Allah ya taroki tunda kin fado komar auren Bayeraben mutum. Tuni zaki mance da shirmenki da ethonocentrism dinki, domin su din maza ne na daban da suka fi kowacce kabilar Najeriya son matansu, iya soyayya da iya kula da bukatunsu da tattalin macen da suke aure. Ba jimawa na tabbata zaki manta da kabilancin, da zarar kin fada hannun Bayeraben miji. Nayi fin wanda kikayi a baya, kuma gashi na cika masa gida da zaratan ‘ya’ya na soyayya. Ta san dai nan bada jimawa ba komai zai kasance tsakaninsu cikin yardar Ubangiji wato tsakanin Prince da Aisha tunda har Dade yayi na’am da Siddiqah. Dama shikadai take fargabar amincewarsa. As long as ana tare da ita kuma, yau da gobe, koda bayan auren ta da Prince da kadan zai goge mata hadda, Siddiqa zata kai ga fahimtar babu mutane masu dadin mu’amalar aure da tsafta da gayu da son uniqueness da iya tafiyar da mace irin Bayeraben Najeriya! Don haka koda ta tsame hannu tace ta koshi, Nenne bata ce komai ba, ta tashi a hanzarce ta koma dakin da aka sauketa duk suka bita da kallo, kai tsaye toilet ta nufa ta tofar da aman da ya cika mata baki ta wanko bakinta ta fito, nan ta tarar an kawo mata kayanta da aka wanko aka gogo dukkansu, da wasu ma da a saninta ba nata bane, a rashin saninta dakin hutun Kiki ne dake daura dana su Fatima aka gyara mata. Nenne ko ta ji ba dadi da abinda Sidiqah take yi bazaka gane hakan a fuskarta ba, kasancewarta mai iya zama da mutum da duk wani halinsa da tafiyar dashi da halinsa, bin bayanta tayi bayan ta dauki madarar shanu (fresh milk) mai sanyi a firji da sinkin shawarma mai zafi da aka gama gasawa yanzu-yanzu ta bita dasu har dakin Kikin. Tun daga bakin kofa Nenne ta hangota ta shige cikin bargo ta takure ta kudundune, ta san yunwa take ji, yarinya sai kafirin kabilanci. Watakila kuma AC da aka kunna ce ta matsa mata ba kadan ba, don haka sai jijjiga take yi a ita kadai cikin bargo. Nenne ta tsorata, data tuna Siddiqah nada (Mild Asthma), da sauri ta karasa ta kashe iya kwandishin din, tana yi tana fada “wa ya ce a kunnama Indo AC?” Ta zauna a daidai kanta ta dora hannun ta saman goshin Aisha da har ya soma daukar zafi. Cikin dabara irin ta iuyaye da son nuna bata san halin da take ciki ba take magana. “Aisha lafiya kuwa? Meyasa baki ci abinci ba? Ina kula fa tun isowarmu baki ci komai ba sai ruwa, so kike in maida ke gida da ulcer kuma nida na dauko ki neman lafiya daga wata cutar?” Kasancewar Siddiqah frank, irin yarannan ne dasu ba za'a kirasu 'yan fari ba don wauta, sannan su ba auta ba sabida rashin iya rufe maganar dake cin ransu, a zahiri Siddiqa bata iya boyewa Ummanta abinda ke damunta komai girmansa, sai ta ke ma Nenne kyakkyawan zato na cewa in taji damuwarta zata fahimce ta, zata yi mata uzuri tunda ita `babba ce kuma bafullatana ‘yar uwarta, ta kuma lura Nenne nada kulawa a kanta, ga yunwa ta gama jigata ta don hanjin cikinta rawa yake amma bazata iya cin abinci mai qaguwa ba, don haka tsakaninta da Allah tace. “Umman Lagos wallahi bana iya cin abincin Yarbawa. Inada kyankyami, nayi kokari inci na kasa”. Wannan magana sai ta sauka a kunnen Princess Fatima data doso dakin neman Nenne, abin ya daure mata kai ya kuma bata mamaki sai ta dakata kadan don son ta fahimci me Aisha ke nufi, duk da ba halinsu bane labe, amma maganar ta doketa, me yarinyar ke nufi da abincin kabilar yarbawa din? Ita bata taba jin maganar da bata yi mata dadi makamanciyar wannan ba. Nenne tayi murmushi mai tafe da dariya tace “Siddiqah ho!” Duk da taji ba dadi a ranta musamman da burinta akan Siddiqah din na ta tallafi rayuwar Prince ya fado mata a rai, da irin alherin data keson kullawa a tsakaninsu, sai kuma gashi Siddiqah data zaba masa matsayin mata ta nuna kiri-kiri a matsayinta na Hausa-fulani kyamar kabilarsa take yi gabadaya, (which means) har shima bazai tsira ba daga wannan kyamar da kyankyamin ba kenan. Ta tuna yadda akayi ta kace-nace a danginsu lokacin da marigayi mahaifinta Sarki Ahmadu Umar Jalloh ya kawo batun aurar da ita ga Dan sarkin Ilorin, ba karamin opposition aka samu ba a lokacin don dai Sarki mai magana daya ne kuma ya isa da kowa dake karkashinsa amma hatta mahaifiyarta Nani Oummana bata so, bazata manta da statement din Oummana a lokacin ba “ka rasa wanda zaka baiwa Sappa sai Bayerabe?” ta rasa wane irin kabilanci bahaushe/bafullace ke da shi akan Yarbawa. Wanda su yarbawan a garesu ba haka bane suna girmama kabilar Hausa-fulani. Nenne sai ta wayance cikin lallashi da tsokanar Siddiqah tace, “Ha’an, kamar yaya ba kya iya cin abincin Yarbawa Aisha-Siddiqah?!” cikin hawaye dake tsatstsafowa tace “saboda qaguwa (shrimps) da aka zuba a miyar” “haka ya kamata kice, ba kya iya cin shrimps, amma ba bakya iya cin abincin yarbawa ba, this is sheer discrimination! Shin Siddiqah Bayerabe ba musulmi bane? To idan Allah yayi ikonsa kika auri Bayeraben mutum fa, kamar yadda nima na aura tun ina kankanuwa ba tare dana shirya kona zaba ba? Yaya zakiyi idan hakan ta faru dake tunda aure babu inda baya kai mace?” Saddiqah ta zaro ido cikin tsoro da firgicin maganar Nenne abin gwanin ban dariya ga wanda ya gani, sannan ta saki hawayen data ke maqalewa suka dirgo akan kuncinta tace “kuma kika yarda kina bafullata aka aura miki Bayerabe?” Wannan Magana ta kara rikita Princess Fatima dake tsaye tana jinsu. Aisha bata yi shiru daga wannan ba ta kara da cewa “Ni dai Umman Lagos ki tofar da miyaun bakinki, Umman Lagos kada kiyi min baki, indai akaina ne kinyi babban sabo kada Allah ya hada ni da miji bayerabe….. (iya abinda Princess Fatima ta iya jure ji kenan ta juya da sauri zuwa dakinta. Tun daga wannan ranar kiyayyar Siddiqah ta fara darsuwa a ran Fatimah. Aisha ta cigaba da gayawa Nenne cikin rufe ido da bayan hannnunta tana ‘yar dariya “Umman Lagos kada kice nayi rashin kunya. Allah ya riga ya bani miji bafulatani dan uwana fa ba tun yanzu ba, ki tambayi Ummana zata gaya miki Ishaq dan Gombe ne, haihuwar Nafada, tun ina karama muke tare yake riko na Umma tun ban san wani Kalmar so ba”. Nenne Sappa taji wani iri a ranta, Aisha wace irin yarinya ce haka mara kara da sakayawa akan abinda ta yardarwa kanta bata so? Ta dan yi murmushi cikin rashin jin dadi, sannan ta gyada kai tace. “naji Siddiqah, kuma Abbanki ma ya gaya min zancensa. Amma Siddiqah mace budurwa a addinance da al'adarmu ta Fulani musamman a zamaninmu na baya bata zabarwa kanta mijin aure, biyayya muke yi ga duk abinda iyayen mu suka zartar akanmu, sai muga alheri mai dimbin yawa ya biyo bayan hakan, ni da aka aura min Babansu Fatima ban ma ganshi ba har saida aka kaini Ilorin. Kuma a haka nayi biyayya yau na tashi da alkhairi da riba mai yawa. Ki dinga neman zabin Allah akan aurenki kin ji ko Aisha-Siddiqah? Ki yi kokari ki cire kabilanci daga ranki don bashi da kyau ga zuciyar mumini, shi din lahani ne ga Imani, tunda Allah da kansa yace “Innna akramakum indallahi atqakum”. Don haka (ethnocentrism) abu ne da bashi da amfani ko kadan a addinance, tunda dukkanninmu addinin musulunci muke bi, kuma mun yarda da Allah da Manzonsa to mun zama daya, dukkanmu musulmai ne da muka hadu akan kalmar LA’ILAHA ILLAH-MUHAMMADUR-RASULULLAH, wannan ce tsintsiyar data hada mu ta daure duka kabilun duniya ta mayar abu guda, ba iya ‘yan Najeriya kadai ba, mu duka al’ummar Annabi Muhammad SAW ne, dake kwadayin tashi karkashin inuwarsa ranar da babu inuwa sai tasa. In hakane kuwa ai