← Book details Aisha Siddiqa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 27

Sashe 13

Aisha Siddiqa Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

1/RABI’UL THANI HIJRIYYAH
P
rince Abdurrasheed Idris Akanni, yana wannan barcin mara dadi agareshi kife da ciki (rub da ciki) akan ‘sofa-bed’, irin kwanciyar da bai san ma yayi ba don tun suna kanana Nenne ke gaya musu bata da kyau ga musulmi, mafarkai barkatai masu alaqa da aure da ‘ya’ya na ratsawa ta cikin barcin nasa mara dadi. Daidai lokacin da Turaki of Ilorin (mai bin mahaifinsa a haihuwa) ya mikawa Malam Barau Hamza (madaurin aure Aisha-Siddiqah) wato wan mahaifinta sadakin Abdurrasheed na dankwala-dankwalan sarkokin zinare a cikin battarsu, ga “Aisha-Siddiqah Yunus”.
Aka daura auren nan da nan, bisa tsari da koyarwa irin na addinin musulunci, bayan an shafa fatiha, kalilan din shaidu kuma sun shaidah, masarautar Gombe data Ilorin da dangin Uwa da na Uban Siddiqah duk sun shaida domin kowanne bangare ya bada wakilai da suka shaida, aka fara musabiha a tsakanin iyayen wadanda suka kasance Yoruba da fulanis, daga kowanne bangare na farin ciki bayan kam]mala daurin auren mai albarka.
Abinda zai baka mamaki shine ko a kafar sadarwa daya ba’a sanar da wannan daurin auren na Prince ba, wannan kuma ya faru ne bisa umarnin Emir, daga nan aka wuce fadar Uban kasar Gombe inda za’ayi reception na bayan daurin aure tsakanin dangin Siddiqah maza, dangin Nenne da kuma Akanni’s dake nan har lokacin.
Sun kwashe akalla sati guda kenan a garin Gombe suna gudanar da komai cikin nutsuwa har alkawarin Allah ya tabbata a yau Juma’ah daya ga watan Rabi’ul Thaani da Siddiqah ta tabbata matar Abdurrasheed.
**** **** ****

An daura!”.
Dade ya gayawa Nenne, fuskarsa fal murmushi kamar tana kallon shi, ya kara da cewa “sai ki daukota ki dawo da ita Gombe toh, kin kama musu ‘ya kin rike daga zuwa asibiti, at least tayi sallama da iyayenta ko, in yaso su kawo ta da kansu”.
“Alhamdulillah!
Alhamdulillah!
Alhamdulillah!
Kawai Nenne ke maimaitawa a fili.
Nenne ta shigo dakin da Siddiqah take da wani irin annuri a kyakkyawar fuskarta irin wanda Siddiqah ko wani dan adam ko ‘ya’yanta babu wanda ya taba gani a tare da ita, zuwa yanzu alamu na raunin ciwo sun dade da bayyana a tare da ita, tana dai daurewa ne tana kuma karfafa jikinta da son ayi biki a gama lafiya kafin ta tafi Morocco ayi mata surgery, sai ta tadda Siddiqah tana hada kayanta a trolley dinta hajaran majaran, fuskarta fal damuwa da ci da zuci.
“Siddiqan Nenne yaya dai? Kayan menene haka aka dannawa a jaka ba ko ninki? Ko mun miki laifi ne za’a yi mana kaura?”
Cikin damuwa Aisha-Siddiqah ta dago ta dubi Nenne tace “Gida nakeso zan tafi, baku yimin komai ba Nenne sai alkhairi, na duba date ne a kalanda naga gobe za’a koma makaranta shiyasa nake hada kaya na, kinga har na cinye hutun ma a nan, ban ma Ummana ko kadan ba”.
Nenne ta karaso cikin dakin ta dafa kanta cikin tausayi da wata sabuwar kaunarta, tace “babu laifi Siddiqah munyi waya da Umman naki ma, tace goben dama zaki koma saboda makaranta”. Siddiqah ta hau murna.
“Allah Nenne ba tsokanata kike ba gobe zan koma Gombe?”
Sai ga Siddiqa tana far’a tana dariya kamar ba itace yanzunnan cikin damuwar data sameta ciki ba.
Nenne tace “wannan ‘mood swing’ haka Aisha ai sai kisa inyi tunanin mu din ba kya jin dadin zama damu ne, ko nida ahalina bama kyautata miki a kan guiwa kike”. Siddiqah ta rufe ido tana jin kunya, sai ta kara fadada far’arta, tana “a’ah Nenne ba haka bane, nayi kewar Umma na ne da yawa, kin san ban taba zuwa ko’ina na kwana ba banda makaranta, sai nan, ko gidan ‘yan uwanmu na Kumo muka je da sallah bana yarda in kwana”.
A washegarin ranar Nenne da kanta ta maida Aisha Gombe. Kai tsaye suka zarce zuwa gidansu Aisha kafin ko’ina. Nenne bata ko jima ba tasha kunun zaqi da cincin da aka sauketa dashi don basu samu Umman Siddiqah a gida ba sun fita da Baba Yunusa sayayyar wasu daga kayan auren Siddiqah duk kuwa da Emir yace a gaya musu yarinya kadai zasu dauka zuwa Ilorin. Sai ‘yan uwan Ummanta fal gidan. Ganin suna neman fallasawa a gabanta ta hanyar kiran Siddiqah da “amarya oyoyo!” Da ake tayi don haka suna gaisawa aka sauke kayan Siddiqah Nenne da direbanta suka juya a gurguje zuwa gidan Sarkin Gombe, suna tafe suna waya itada Haj. Zainab. Inda Nenne tace da ita a shirya amarya gobe-gobe zasu dauketa su wuce Ilorin bisa umarnin Maimartaba. Haj. Zainab ta kawo uzurin cewa a kara musu kwanakin tarewa su gama shirinsu a nitse, Siddiqah tayi sallama da danginta su kuma samu su lallasheta akai, tayi mata shirin aure kuma da ya dace. Nenne tace.
“Kada ki damu da wannan Zaynaba nima Uwa ce, uwar kuma ta ‘yaya mata, nasan me kike nufi, in lokacin tarewar yayi zan yiwa Siddiqa abinda ko su Murjanatu ban yiwa lokacin aurar dasu ba.
Zuwa yanzu dai Ilorin za’a isa da ita ga Emir da dangin mahaifin su. Kin gama mana alfarma ai tunda kin bamu diya kun gama komai, ku dai yi kokarin sanar da ita da lallashinta daga yau zuwa gobe”.
Da haka sukayi sallama Haj. Zainab da Nenne, itada direba suka karasa fadar Gombe.
Umman Siddiqah kuma ta gayawa Malam Yunus isowarsu bayan sun gama waya da Nenne, don haka a gurguje suka karasa sayayyar abinda suke yi suka koma gida.
Kukan Petel tun daga soron farko shi ya fara bakuntar kunnuwansu.
Daidai lokacin da suka sawo kai tsakar gidan, sai suka ji muryar Addar Kumo, sarkin kankanba wato kanwar Malam Yunus Magajiya da tazo daga Kumo tana ce da ita.
“Shin wai laifi ne don su Hasssilo sun kira ki amarya? To ko kina nufin baki san an daura aurenki bane tun jiya, da Dan Sarkin Yarbawan Ilorin take ko Ibadan??”
“Sun jika mana aiki!” Inji Umma cikin bacin rai, tana karasawa cikin gidan da sauri har zanin ta na kuncewa. Siddiqah na ganin shigowar Ummanta ta hau ja da baya a firgice, idonta cikin na Umma tana tambaya.
“Umma wai da gaske ne?”
Umman ta mika hannu zata rikota sai ta goce. Ido fal hawaye tace “ki gayamin Umma da gaske suke? Wai an yimin aure bada Ishaq ba? Umma wai da Bayerabe? Shiyasa kika kaini gidan Yarbawa na zauna dama Umma?
To makarantata kuma fa Umma? Don Allah kada kuyi min haka!”
Umma na isowa don ta rike Siddiqa dake kuka tana mazari sai gani tayi yiiip! Aisha-Siddiqah ta fadi kasa ta mimmike mata.
Umma cewa take “ku bani inhaler”. Addar Kumo na fadin “ki nutsu Zaynaba, ki gane wannan ba tashin Asma bane, shidewa ce (suma) ne”. Malam Yunus na karasowa bai ce komai ba, sai kawai ya kinkimi Aisha a kafadarsa zuwa motarsa, sai asibitin da take da file wato FMC Gombe.
**** **** ****
Chapter 13 · 0% Book details