Sashe 10
Aisha Siddiqa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
why zata taho da Siddiqah? Taiwo tace “ha’an, na tuna zancenta”. Sun hada baki itada Fatima kan cewa duk yadda zasuyi su sa Nenne ta maida yarinyar Gombe zasu yi, a bisa dalilinsu na rashin son bare a cikin gidansu. Sun gama magana akan cewa su Taiwo zasu taho Lagos dinma in Toufeeq ya koma don ta kwana biyu bata zo ba, zata jira har ya koma, inyaso lokacin Kiki ta dawo daga Los-Angeles sai su taho gabadayansu (Kiki ta tafi yin wani gajeren kwas na ilmin na’ura mai kwakwalwa na watanni shidda a wata shahararriyar Institute dake Los Angeles) bayan kammala karatun sakandirenta a wannan shekarar. Ta shiga Institute dinne kafin ta fara jami’a. A lokacin Taiwo tana gidanta na Ilorin, an maida ta aiki asibitin koyarwa na jihar Kwara/Ilorin daga Lagos State Teaching Hospital da jimawa. A halin yanzu Taiwo Murjantu na matsayin Consultant a gyanaecology Kiki-Ruqayyat a lokacin ta gama sakandire ta nada shekaru goma sha takwas. Zamu iya kiran Kiki sa’ar Siddiqah amma ta bata wajen watanni tara, saidai Kiki tayi biyun Siddiqah a girman jiki. Ko don yadda Abdulrasheed ke sakar ma Kiki kudi tana wadaqa yasa ta zama irin (first class ‘yammatan nan), kaunar Kiki da Uncle dinta Prince har girmanta bata canza ba. Dade ya kira Nenne a daren ranar da suka sauka a Gombe yace da ita suna Gombe shi da ‘yan uwansa su Dan Iyan, Malami Uban Doma da Turaki da Mutawalli, gobe Juma’ah zasu daura auren Abdulrasheed da Aisha a garinsu mahaifinta wato (Kumo) in Allah yaso ya kuma yarda, bayan masallaci. Ya tabbatar mata komai na neman auren ya kankama Emir bai sa wasa cikin lamarin ba ranar da yaje masa da zancen, a take ya bada sadaki da dukiyar aure yace suje suyi komai da ya dace, ya gaya mata Baban Aisha-Siddiqah wato Malam Yunus da dan uwansa basu kawo kowanne uzuri ba don sun riga sun warware maganar aurenta da yaron da yake neman nata. Ya roketa kada ta gayawa su Taiwo komai don zata bata musu shiri. “Lets’ take all of them by surprise”. Inji Dade. Kunnen Taiwo na Abdulrasheed ne, baya so Abdulraheed ya kawo musu kowanne cikas ko da kuwa na cewa a dakata ne sai yazo ko makamancin haka, yace duk wata dama sun gama bashi ita yanzun hukunci yana hannunsu, don haka sai an daura ya ji daga baya, ya gaya mata cewa Emir yace kada a sanar dashi sai ranar da yazo gida dan kansa don a lokacin ma baya Qatar, ya halarci wani shahararren ‘tournament’ a yankin kasar Rasha. Nenne a wurin da take zaune ta fadi tayi sujjadah da wayar a kunnuwanta. Albishir ne irin wanda Dade bai taba yi mata mai dadinsa ba. Alas! Burinta yau ya cika, akan damuwarta ta rashin auren Prince Abdulrasheed (Kehinde), ko yau rayuwarta ta kare (wadda take da tabbacin ba mai tsayi bace) ta tafi cike da farin cikin cikar buri, ta tabbatar Aisha-Siddiqah data zaba masa bata yi masa zaben tumun dare ba, tana fatan ta zame masa matar rufin asiri kuma uwar ‘ya’yansa kamar ita da Dade, Nenne tace a fili “ko yau Allah ya katse tafiyar, ta gode masa. Don ta san Kehinde zai rike Siddiqah muddin ta bashi hujjarta ta hada su aure haka da gaggawa, zai riketa albarkacinta, koda baya son ta. Ita bata aura masa Siddiqah don ya so ta ba, ta aura masa ita ne don ya cika mutum! Mai kamala. Rayuwarsa ta zama cikakka kuma mai ma’ana kamar ta kowa, kuma ya samu zuri’a shima. Tana cikin damuwa da bakin cikin rayuwar da yake yi shikadai. duk da a yanzu bata zarginsa da rayuwar ashararanci face rashin auren wata jarrabawa ce a gareshi. Tana da yaqinin AbdulRasheed zai rike Aisha-Siddiqah a gidansa irin rikon da Dade yake mata don barewa bata gudu danta yayi rarrafe, zai shiga da ita duk inda ya shiga cikin duniya albarkacin cewa ita Nenne ce ta aura masa ita, ba don kasancewarta ‘yar wasu masu mulji ko dukiya ba sai don kasancewarta zabin Nennensa. Nenne ta kwana da sanin cewa babu gurbin soyayya a zuciyarAbdulrasheed dinta, ya dade da konewa kurmus daga kowanne sako na zuciyarsa, akan dalilin da har gobe ita bata sani ba. Amma ta shinshini cewa koma dai menene kin auren Kehinde yanada dalili in tayi la’akari da irin kalaman dake fita bakinsa akan mata. Koyaushe tayi masa maganar aure cewa yake “Nenne…they are nothing but gold-diggers… true love does naver exist. I am a hopeless romantic… And I want true love!” A ganin Nenne Sappa shi aure ba a yadda Abdulrasheed yake kallonsa yake ba a zahiri. Abdulrasheed yana kallon aure ne a matsayin wani abu mai girma wanda sai da sahihiyar soyayya yake yiwuwa (sai zukata biyu sun hadu akan son juna, sai yana son mace zai aure ta, itama sai tana matukar sonsa zai yarda da ita, alhalin kuma ya kasa son kowacce din balle ya bata dama) har gashi yayi sallama da shekarun kuruciya. Bai kamata yayiwa matan duniya duka hukunci akan laifin mace daya ba. Ita Nenne ta yarda cewa ba lallai sai da soyayya ake yin aure ba; circumstances yana kawota (along the way) ga ma’aurata. Nenne tafi yarda da cewa ana yin aure ne don dalilai masu karfi na addini dana al’ada, muhimmi shine don raya sunnahr Annabi SAW da cikar kamala da addinin mutum, da neman zurri’a saliha. A al’adance kuma sai dashi kake cika mutum, kima da martabarka ke cika a idon al’ummar da kake tare dasu. Amma ba don soyayyahr da yake ikirarin shi bashi da ita akan diya mace ba. Nenne bata san cewa abinda ya hana shi sake soyayya tun daga incidence dinsa da Ex dinsa Haseenah ne, ya zama cewa he lacked his trust and feelings on women akan Haseenah Ambursa, al’amarin daya kwashe shekaru kusan goma sha biyu yana dawainiya da shi yana haunting dinsa, yana lalata yardarsa da bukatuwarshi akan mata bakidayansu. Shikuma ba aboki na jiki gareshi ba, tunda ya rasa Bello Birnin Kebbi, wanda zai zaunar da shi ya gaya masa gaskiyar cewa ba’a yiwa duka mata hukunci da laifin mutum daya. **** **** **** WAIWAYE “ Nenne Sappa has been battling with kidney stones for some years, ba tareda ita kanta ko wani cikin ‘ya’yanta ko mijinta Dade ya sani ba. Tana dai ‘yan ciwuwwukanta a tsaitsaye wadanda basu kwantar da ita ko sau daya ba, har zuwa shekarun baya da ya fara nuna alamu har ta kwanta a asibiti a Morocco. A shekarun baya tana yawan tafiya kasar Morocco da sunan ziyartar kaninta da iyalansa a rashin sanin kowa medical check-up take zuwa akan treatment din da ake mata don a lokacin kanana ne stones din likita na tunanin zai iya treatment dinsu ba tareda surgery ba. Daga baya ta manta da zancen don bata fama da kowanne ciwo ga yawan sabgogin iyali dana al’umma dake kanta. A check-up na karshe da Hajiya Sappa ta je Morocco aka tabbatar stones tana bukatar surgery don a ciresu gabadaya ta huta. Kaninta Abdulmajid baisa was aba yajaddada mata cewa da zarar ta dawo ta yi shiri ta sake dawowa ayi aikin. Amma Nenne tunda ta dawo kuma tanacikin koshi lafiyarta sai bata sake bi ta kan lalurarta ba. Daga ita sai Dr. Abdulmajeed Ahmadu Jalloh Omar, suka rike da wannan zancen na kidney stones dinta a tsakanin junansu, wato kaninta mai binta a haihuwa wanda likitan Koda ne dake aiki a babban asibitin Koda na kasar Morocco, su biyu kadai suka san da wannan al’amarin. A can baya da take yawan zuwa Morocco da sunan ziyarar Abdulmajid da iyalinsa a rashin sanin Dade da yaranta ana treating dinta ne, don samun lafiyarta. Daidai lokacin data dago daga sujjadarta, jikinta ya soma dan bari da karkarwa na shigar zazzafan zazzabi, bata taba jin zazzabi irin na wannan lokacin ba tun saninta da ciwon nata. Zafin jikin Nenne ya karu, har ta kai ga ta bar abinda take yi a kitchen ta koma dakin mijinta ta kwanta a gadon su na alfarma. Nenne ta dauki waya ta kira Abdulmajid, yana jin muryarta sanda suke gaisawa ya san jikin ya tashi sosai, yace “Adda kiyiwa Allah ki yarda ayi miki aikinnan kowa ya huta, ina amfanin zama da ciwo? Kuma kin hanai fadawa kowannensu har yau” Nenne tace “Abdul tsoron aikin nake ji, gara idan tafiya ce in tafi salin alin ba tare da an farke ni ba, ina rokon ka kara rike min sirri na, ban yarda Dade da Hammansu da Nani Oummana su ji wannan maganar ba…”. Abdulmajeed ya katseta cikin damuwa “Adda na gaji! Na gaji da wannan boye-boyen da muke yi, mara amfani, Adda boyewar nan bata da wani amfani, su dinnan duka musulmi ne Adda, musamman miji da mahaifiyarki, koba komai zasu yi miki addu’a ayi aikin nan a sa’a. shikuwa Abdul ai namiji ne shi yafi kowa dacewa ya san halin da kike ciki, ki sanar da ko Abdulrasheed da Murjanatu ne kadai su rako ki ayi aikin, in har bazaki bari Dade dinsu ya sani ba saboda hawan jininsa, su ya kamata su sani”. Nenne tace “ko zan sanar dasu ba yanzu ba sai na shirya, akwai abinda ke gabana yanzu, zan cigaba da shan magungunana da na bar sha kwana biyu. Tunda na samu cikar burina da raina akan Hammansu (Abdulrasheed) to Alhamdulillah!” Abdulmajeed Yace cikin damuwa da hukuncin ganganci na ‘yar uwarsa, “amma Adda idan kika mutu kina musu wannan boye-boyen ba tareda sun san jinyar da kika dade kina yi ba, suka kuma ji da hadin bakina, na rantse daga ni har ke bazasu taba yafe mana ba!”. Nenne tace “bazan taba saka sunanka cikin maganar nan ba Abdulmajeed, amma zan duba yuwuwar na sanar da Abdulrasheed shikadai, amma dai don Allah ka kara min lokaci Abdul, har Abdulrasheed ya karbi matar dana aura masa daga hannuna”. Abdulmajeed ya rasa me zai ce mata da zai sa ta dauki al’amarin lafiyarta da muhimmanci sama da zancen auren danta. Yace a hankali “Adda!” Nenne Sappa ta katse kanin nata cikin kulawa. “Abdul, Ko Allah hoddiri fe’an be tagu fe’an!”. (Abinda Allah ya riga ya rubuta zai faru ga bawa ba makawa sai ya