← Book details Aisha Siddiqa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 27

Sashe 23

Aisha Siddiqa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

rai ba. A rashin sanin dukkansu su suna hira ne, Prince kuwa yana danna waya yana yiwa kansa booking flight tunda dai jikin Nenne masha Allah Alhamdulillah, bai ga zaman me zai yi ba kuma. Kwatakwata saboda shaukin haduwa da juna sun manta da wata Aisha kamar ma babu ita in existence a gidansu, to basu saba da shigowar bare cikisu ba. Hatta Princess Firdausi mai dan damuwa da Siddiqah yau ta manta cewa tana gidan sabida murnar zuwan Aunty Murjanatu da tarin tsarabobin data kawo musu daga UK. Wannan abu ya damu Nenne, kuma ta lura itama Aisha din tafi son zaman dakinta yanzu ko meyasa? Ko dai Hamma yace mata wani abu ne? Bata yarda ta zauna a cikinsu in Hamma da Murja suna falo, tun dawowarsu gidan daga asibiti. Nenne ta kasa shiru ganin sun gama rabon tsaraba a junansu ba wanda yace ga ta Aisha-Siddiqah. Maganar Asoebi ma suka koma yi wanda zasu yi na bikin kawar Fatima yar Sarkin Ibadan, suna rokon Hamma ya kawo kudi masu kauri. Ko kula su bai yi ba domin hankalinsa ya dauku ga abinda yake yi a wayarsa yanata danne-dannen da basu san me yake yi ba a ciki, ya samu jirgi mai tashi zuwa Qatar a gobe, don haka yayi maza ya yi booking, ya san dai Nenne bazata hanashi komawa bakin aikinsa ba tunda ta san yanke komai yayi ya taho sabida lafiyarta ba don yana cikin hutu ba. Nenne ta juya tayiwa Murjanatu kallon disappointment, tace a sanyaye “Maman Kiki, ina tsarabar ‘yar uwarki kika baiwa kowa banda ita?”. Aunty Murja ta juyo tana kallon Nenne, idonta na bidar tambaya, Nenne tace cikin lallashi “Kada ku manta she is now part of the family, in zakuyi irin wannan zaman na zumunci a gabanmu da rabon kaya kona menene ku dinga hadawa da ita”. Har suna hada baki wajen cewa “toh Nenne ai bamu ce kada tazo nan ta zauna ba?” Nenne tace “kun kirata cikin sakewa ta ki zuwa? Aishatu-Siddiqah bata da saurin sabo sai a hankali nikaina ta saba dani, ita kadai ce ‘ya a gidansu da mahaifiyarta kadai ta saba, zata saba daku idan kuna janta a jiki!”. Ta fada a hankali cikin lallamin ‘ya’yan nata idonta na kallon reaction dinsa. Prince, wanda har lokacin fuskarsa take expressionless, kansa na bisa wayarsa. Mikewa ma yayi daga bisani fuskarsa a sake yana fadin “I booked my flight back tomorrow Nenne, Allah ya kara miki lafiya da nisan kwana mai albarka, ina son ganin ku hakannan complete family, I am missing this!”. Nenne ta bishi da ido tana mamaki, kamar bai yi noticing maganar aurensa ba? Kamar bata gaya masa zancen aurensa da Siddiqah ba? Ko kuwa iya shege ne abun irin na su na diyan yarbawa? Zai kuwa ga iya shege albarka Annabijo (da albarkar Annabi). Sai kawai ta bi shi da adduar data saba yi masa wato. “Allah hokku sa’a Hammansu ko a yahi dabuttugo albarka Annabijo”. Kuma ko a fuskarta babu bacin rai. Watakila Prince harda auren aljana a tare da shi ta ke gayawa kanta. Namijin da zai ga mace tamkar Aisha-Siddiqah a matsayin halalinsa amma zuciyarsa bata ko motsa ba, manhood bai motsa masa ba. Sannan bai yi wani action ko kankani da zai nuna cewa ya san da wanzuwarta ba, alhalin ko jiya tana jin yadda Dade ya zaunar da shi kusan awanni uku yana labarta masa yadda aurensa da Siddiqah ya wakana, tun daga haduwar Nenne da Hajiya Zainab a filin Munna ya dauko masa labarin har kawo zuwa yau. Har Dade yayi yagama tana jin su daga kwancen da take uffan wannan Prince Abdulrasheed Kehinde bai ce ba. Dade da saurin hassala a lokacin taji yace da shi “ka samu lalurar ji ne ko Kehinde?” Dan murmushi ya yi cikin kasaitarsa yace “Dade, kunnena ras suke. Banida abin cewa ne, banda Allah yasa hakan shi yafi alkhairi a gareni daku da yarinyar bakidaya”. Wannan ne yasa Nenne bata kara yi masa zancen Aisha ba ita, koba komai he is now aware of it. His I don’t care attitude ne ya bata mata rai ta fasa ce masa ya tafi tare da Aisha. Aisha tafi karfin ta cusa ta wajen namiji, ta barwa Allah wannan ikon nasa. Su dai sun sauke nauyin dake kansu da addini da al’ada suka dora musu sauran ya rage nasa. Yarinya dai data dauko daga gaban uwarta da ubanta zata kula da ita kamar koma fiyeda tana gabansu. Don haka bayan barin sa wurin Nenne ta cigaba da yiwa Aunty Taiwo ciwon bakin tayi rabon tsaraba ta manta da ‘yar uwarta. Murjanatu-Taiwo, nan ta hau babbaka dariyar shakiyanci nan ta maida Nenne Kakarta, tana cewa “Nenne mai ‘yar fingi-fingi, kamar kazar mayu, ina ganin sai kin hada da addu’a fa, naga Kehinde yarinyar nan bata masa ba”. Ta kara babbako dariya tace. “Allah na tuba Nenne, wadanne irin matane Kehinde bai gani a kasashen duniya? Wadanne irin mata ne basa bibiyarsa kamar su bashi ransu har gida da ofis, Kehinde da in mata dari yakeso a rana zai aura, sai kece mai idon gano masa macen aure Nennenmu? Nenne a shawarce ki maida yarinyar nan ga iyayenta, ki basu hakuri kawai. An daina irin wannan auren yanzu”. Nenne tace da kakkausan lafazi, “Murjanatu! Shin ke kika haifa min yaron nan ko ni na haife shi? To in har ba ke kika haife shi ba, baki kuma shayar dashi ba, sannan baki tayani jegonsa da rainon cikinsa ba daga yau na cire ki daga sha’anin auren sa. Shiyasa dama tun farko ni ban saka ki ba don nasan dama tunaninki akan Abdulrasheed ragagge ne sai abinda yakeso kike bi, ba abinda zaifi masa alkhairi ba. Shiyasa tun farko kika biye masa akan waccan yarinyar. Na yarda har yanzu da sauranki Murjanatu a sanin baiwar da Allah yayiwa 'ya'ya mata, yawan shekaru da zurfin ilmi ko cikar jiki basu ne ba. Haka naki shekarun basu yi miki amfani ba, tunda har kike tunani akwai namijin da yafi karfin wata bafullatar mace don kawai bata da wayewa irin ta kabilunku. Murjanatu ta rage dariya ganin Nenne ta hassala sosai, gashi bata da lafiya, tace “Nenne ni dai ba ruwana fa kiyi hakuri, I rest my case akan maganar nan, shawara ce dama na bayar sabida saninda na yiwa Kehinde, amma kiyi hakuri ga ku ga Kehinde”. Nenne tace "ki yi fatan alkhairi ko ki fita daga sabgar da ba'a saka ki ba tun farko". Ai kuwa a washegari tunda asubah Prince ya tashi zuwa Qatar ko Dade sai a masallaci sukayi sallama da shi. Dade yaso yace dashi Siddiqah fa? Yaga cewa wannan ba wurin da ya dace suyi maganarta bane, amma ya sha mamaki da cikin daren Nenne tace masa gobe AbdulRasheed zai koma har yayi mata Sallama, ta rokeshi kada ya takura masa kan tafiya da Aisha wato yace sai sun koma tare, ya zuba masa Ido, ita bazata cusa masa ita ba don saya mata martaba a wurinsa don ta lura kawai shida Taiwo basuyi na'am da zabinsu ba. Dama kullum bakinsu daya. Kasancewar bata da koshin lafiya sai bai cikata da magana ba kawai ya gyada kai. Sukayi sallama da Dan nasa yadda suka saba yasa masa albarka ya kuma yi masa addu’ar da ya saba yi masa. Seun, ya wuce dashi zuwa filin jirgi. Kwanansa daya da tafiya itama Murjanatu ta koma gidanta a Ilorin. Gidan ya koma yadda yake wato su ya su. Sai lokacin da Firdausi ta tabbatar mata Hamma ya koma, Auntynsu Murja ma ta wuce gidan mijinta, sannan Siddiqah ta soma fitowa falo cikin su yadda ta saba ta sake. Nenne ta yankewa kanta shawarar bazata sawa ranta damuwar komai ba, cututtukan nan na zamani na zuciya da hawan jini ba karya bane. Ta samu ta sha da kyar daga cyst and renal stones. Bari ta maida hakali kan abinda zai fishsheta da ibadarta ta gama da damuwar Abdulrasheed kuma. Ya rage nasa ya gama da yazo ya dauki matarsa a sanda ya shirya ko ya cigaba da rayuwarsa a jirkice yadda yake yinta. Ita dai ta san ba zata kwari yarinya ba idan ya shekara bai dauketa ba, zata mayarwa iyayenta dake ganin mutuncinta ta ce musu ta gane bashi da lafiyar iya yin aure, wanda mutuncin ne yasa aka bashi ba wani abu nasa ba. Bazata yi sanadin da zumuncin ta da Haj. Zainab wanda sun ginashi ne saboda Allah zai lalace akan ‘ya’ya ba. Allah ya gani wahalar da ta sha a baya akan damuwar rashin auren Abdulrasheed, bazata kara maimaitata a yanzu ba. Ta cimma shekaru na girma da take bukatar tattalin lafiyarta. Kehinde ba shikadai ta haifa ba. Amma shikadai matsalarsa ke wahalar da ita, bazata taba lafiyarta dake reto saboda shi ba, alhalin shi yana can cikin jin dadin rayuwarsa. Tunda ta wanke masa ‘labelling’ na rashin aure (tambari) wanda addini da al'ada ya dora musu sauran hukuncin na rayuwa da matar ko a'ah nasa ne ba nata ba. Nenne ta sha mamaki da Aisha Siddiqah ta koma rayuwar walwalarta cikin gidan bayan barin Taiwo da Kehinde gidan. Wato itama ta gane Taiwo bata yin ta kenan. Allah sarki! Yo aka ce shimfidar fuska tafi ta tabarma, sannan ido ba mudu ba amma ya san mai maraba dashi, kai tsaye Aunty Murjanatu bata boyewa kowa ba matar Kehinde bata yi mata ba, including iyayennasu da suka hada auren bata yi musu alkunya ko Karar ganin ido ba wajen nuna musu basu yi zabin da ya dace ba. A wurin Siddiqah gidan har wani fili ya kara da iska mai dadi da Hamman su Firdausi ya bar shi. Wanda iya hangenta na kushe dan adam ko kabilan da ba nata ba data saba kushewa ta kasa hango ta ina zata iya kushe Prince Abdulrasheed (Kehinde) Idris Akanni. He's perfect, duk da ana cewa duk mutum tara yake bai cika goma ba. Gani uku ko hudu ta yi masa cikin gidan kuma ba wai ta masa kallon kurilla bane ko a asibitin. Amma tashin farko ta gane shi din ko cikin mazan Yoruba kyakkyawa ne na gaske ashe. Classique. Jinin fulanin Gombe ya wanke shi tas! Akwai abinda ya burgeta guda daya a tare
Chapter 23 · 0% Book details