← Book details Aisha Siddiqa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 27

Sashe 17

Aisha Siddiqa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da muryarta ba karsashi. “ka ga min Indo amaren Lagos! Kaga min amaren bana masu abin mamaki sai kyallin goshi suke amma ba tsoka”. Siddiqah ta kyalkyale da dariya, itama ta san bata da tsoka irin ta jama’ar gidan, dukkasu bulbul suke, Nenne ce kawai har yau jikinta na Fulani bai canza ba, kamar bata haife su ba dika-dika dasu. Ganin yau ta sake tana dariya sai Nenne taji dadi, ta kara da cewa. “Yo daman kina faman cin abinci da mai da yaji kullum Aisha ina zakiyi wani kumari? Bari dai insa Femi ta barzamin garin gero dana farar shinkafa, sai a hada da garin Aya na dabino da na cukui, in samu lokaci daga gobe in fara hada miki abinda zai sa ki murmure nan da nan”. Dariya Siddiqa ta kara yi, zata so kwarai taga ta murmure din itama, ta zama cif-cif kamar Aunty Princess Firdausi, wajen kwalliya kuwa da iya taku na class Princess Fatima wadda kullum cikin kalkale jikin ta take a shagunan beauty make up, saidai ina! Tasan ita bazata taba iyawa ba don bata taso cikin hakan ba. Nenne ta shagala cikin kallon Aisha-Siddiqah tana dariyar, tayi mata kyau sosai a idonta, sai tayi kama da furen fulawar nan rose don kyau. Dariyar data keyi har ranta, ta kawata ‘yar karamar kyakkyawar fuskarta sosai. Nenne ta soma tunanin ko yaay Prince zai karbi zancensa da Siddiqah ranar da ya ganta? Ta sani ba komai ke burgeshi ba, amma ko hasidin iza hassada bazai kushe Siddiqah ba sai don kawai ace bata da wayewa irin tasu, Nenne ta kara cewa cikin mamakinta, “anya Indo! Ba kya ko tambayar wani cikinmu wanene angonki? Yau kwananki uku gidannan babu shi babu alamarsa, amma ko a jikinki, sai cin wakenki da shinkafa kike hankalin ki kwance, kamar ba aure aka yi miki ba, ya dai kamata zuwa yanzu ki kauda kawaicin kice “Nenne, ku nuna min shi haka mana?” Kunya sosai ta kama Siddiqah. Da sauri ta bar wurin zuwa dakinta cikin sassarfa, don ji tayi kamar ta nitse a gun don kunyar da Nenne ta bata, ba tareda ta cewa Nenne komai ba ta gudu dakinta. A ranta ta san idan tana marmarin ganin mijin nan nata, kada Allah ya bata abinda take so. Bata san shi ba, bata fatan tasan shi ko a hoto ko a mafarki. Namiji daya take so har gobe a ranta da ruhinta, wato Ishaq Hassan Nafada, wani kwayan mutum guda daya da ya nuna mata yadda zata so shi tun bata balaga ba, kuma tunda ta rasa shi shikenan. Ita kawai gata nan ne a gidannan bata san me tazo yi ba. an dai yi mata yankan kauna an rabota da Umma. Amma Nenne da Dade na kokari matuka a kanta, bazata taba kushe kulawarsu da soyayyarsu gareta ba. Ko don hakan zata cigaba da zama a gidan Engnr. Idris Akanni, har Allah yayi hukuncin da ya dace akanta. Ita dai ta san tayi biyayya kuma falalar biyayyar take jira. Princess Firdausi na dariya tace ma Nenne. “Har fa album na hotunan Hamma na dauko mata fa, tuna yana yaro dana dokunansa, na ce ta ganshi takuma ga SAHEEB dinsa kafin yazo, amma kememe Siddiqah ta ki yarda ta kalla sai ma ta tashi ta bar min wurin”. Zuwa yanzu Aisha- Siddiqah ta kara fahimtar cewa, shi din, wato mijin nata da bata sani ba wato Hamma Prince AbdulRasheed, dan gata ne a wajen mahaifiyarsa da ‘yan uwansa mata, haka a wajen mahaifinsa Dade bashi da na biyu, ko don shikadai ne namji a cikinsu? Ko daga yadda take yawan jin zancensa a bakin su kowa “HAMMAH”. Komai zasu yi sai sun tuno shi “HAMMAH” dai. Akalla sai tace babu ranar Allah da bata ji sun ambace shi ba tun dawowarsu daga Ilorin. Haka shiga goma fita goma kowaccen su sai ta ambaci Hamma yayi kaza ko yana son kaza, ko tana kewarsa, Siddiqah uma ta sha jin Ummanta na cewa yawana adadin ambaton ka da mutum yawan adadin kaunarka gareshi, hakan kuma ya nuna mata cewa akwai kyakkyawar alaqa tsakaninsa da twin sisters din shi Princess Fatima da Princess Firdausi. Itama mahaifiyarsu Nenne a cikin gidan nan kullum sai ta ambace shi cikin hira. Sannan ko cikin maganar wasa sai ta tunawa Siddiqah cewa zaman shi take yi bana kowa ba, sannan ta kan ce yana gab da zuwa Lagos, nan bada jimawa ba. Amma har sati biyu da tarewar Aisha Siddiqah wato har ya koma Qatar daga aikin da yaje yi babu Hamma Prince ba labarin zuwansa. **** **** **** Jikin Nenne kwana biyunnan da sauki sosai, don an hadata da wasu magunguna masu tsada da zasu taimaka wurin kwantar da ciwon nata har zuwa lokacin da zata bukaci a yi mata surgery din. Nenne ko magungunanta zata sha bata sha a gaban su, tana dai yawan ce musu bata jin dadi zata shiga daga ciki ta kwanta. Sai ta shige uwardakinta, ta rufo ta barsu tayi ta murkususun ciwon cikinta har ta samu ya lafa. Idan kuma tana jin kwarin jikin to koyaushe zaka samesu a kitchen itada Siddiqah, suna hada girkin Dade tare. Siddiqah ta like ma Nenne a gidan don ita kadai take gani a matsayin yarenta (Bafullatana) suyi fulatanci tare taji dadi. Saddiqah ga makon Uwa, ko Ummanta haka take like mata a kitchen in tana girki, koda kuwa bazata tayata da komai ba to zata zauna a gefenta tana girkin ita kuma tana cika ta da dumin zance. Ta kan manta cewa Nenne uwar mijinta ce sam ko don babu mijin tare dasu ne? Nenne sai tayi amfani da wannan damar ta like mata da Siddiqah keyi a kitchen ta soma koyawa Siddiqa ‘Traditional Yoruba Dishes’ musamman wadanda ta san AbdulRasheed naso. Tana yawan gaya mata Hamman nasu Firdausi nada son cin abincin gargajiyarsu, in yazo ba abinda yake so irin ayi ta jere masa su, ‘traditional Yoruba food’ kala-kala, yana diban wanda ransa yake so da kansa, saboda baya samun irinsu a can inda yake rayuwarsa, Nenne tace “his best friend is food”. Abin nufi. “Abinci shine babban abokinsa (tana nufin Prince nada yawan cin abinci mai maida ruwan jiki). “Don haka Siddiqah ki dage ki koyi wadannan girke-girken na Veggies dana ke yiwa Dade dinku kullum. Su Abdulrasheed ke ci. Saboda yana yawan kona ruwan jikinsa ta hanyar exercise mai matukar wahala kullum safe da yamma. Ta fada mata yanada son cin “WARA” wani abincinsu ne na Yoruba da ake yi da nono, mostly Yarbawa ke yin shi da kansu (deep fry na Nono). Sannan Nenne ta kan ce mata “Abdulrasheed yana da son neatness na muhallinsa, musamman toilet, in kina so ku haura, to ki bata masa toilet, ko ki hargitsa masa daki, ko ki bar masa shirgi akan gadonsa, yanzunnan zaku bata dashi a jiku duk shirin da kuke yi. Ta kara da ce mata kuma shi mahayin Doki ne. A bakin Nenne taji cewa Hamma din, Polo Legend ne, a tsakanin kasashen Africa dana Turai. Tace "yana da Dawakai, yana son Dawakan shi yana kula da su matuka, kada kiyi mamaki innace miki kamar yadda mutum ke kula da ‘ya’yan da ya haifa. Kullum cikin dawainiyarsu da hidimarsu yake rayuwa. Ki taya shi son su, musamman wani tsohon dokinshi Saheeb, sai ki ribaci zuciyarsa da wurwuri. Nenne kan samu lokaci again tana koyawa Siddiqah yadda ake hosting baki a family dinsu. Hatta dressing dinta na yanzu bata barta da irin wanda take yi a Gombe ba, ta kan gyara mata kadan-kadan. Misali ta kan ce ta rage jambaki yayi yawa, ta rage kaurin gazal, ko tace tasa mascara a girarta maimakon jagira, tace powder mai duhu ya dace da ita ba mai haske ba tunda ita mai hasken fata ce, don haka powders mai duhu ta saya mata cikin sayayyar data yi mata tunda su basa lefe. A satinnan an dinka mata sittiru iri-iri sun kai hamsin daidai jikinta, sittiru masu daraja da zata dade tana mora. Firdausi kuma tana tare da Aisha koyaushe tana kara koyar da ita tsaftar jiki yadda ya kamata da matar aure, don ta raina tsaftar Aisha. A gidan Nenne ne Siddiqah ta san cewa in za’a kwanta sai an yi wanka da brush na barci. Don a Gombe bata yinsu take barcinta abinta. Princess Firdausi Ta koyar da ita yin shaving akai-akai. Tace duk sati biyu ya kamat tayi ba sai gashi ya taru ba. Hatta manner din cin abinci tareda jama’ar gida bisa tebir, Nenne bata yin shiru in ta ga Aisha tayi wani abu ba daidai da su ba, wanda a wurinsu kauyanci ne ko Arewanci, sai ta gyara mata (in a nice way) yadda bazata ji ta muzanta ba, mostly in suna girki a kitchen suna hira, bata yimata gyara a gaban su Firdausi. Ta wannan hanyar tunani na farko da ya dade da samun muhalli a tareda Siddiqa ya goge na cewa duka Yarbawa kazamai ne. Ya Ilahy, ashe a rashin saninta, wasu yarbawan dai har sun fi wasu hausawa da Fulanin tsafta, kudin goro hausawa ke musu na isgilanci da iya shege da suke kiransu masu kashi a kwano ko masu tukin tuwo da Duwawu. A hutun karshen makonnan baki suke tayi a gidan yawanci danginsu ne dake zaune a Lagos da family friends, masu zuwa ganin amaryar Prince, manyan mutane sosai ke zuwa suna tafiya, ‘yan kasuwa, ‘yan siyasa da ‘yan sarauta da manyan ma’aikatan gwamnati dake da alaqa dasu Nenne. A zahiri suna mamaki in suka ga ‘yar ficikar yarinyar da aka aurawa Prince Abdulrasheed da bata ko kai shekaru ashirin ba, in suka fita sai sun gulmanta, Bayerabe da son tsegumi, kuma babu wayewa irinta kabilu ko ‘yan bokon arewa a tareda ita, (typical Gombe Fulani girl). Wasu basa iya shiru ko a gaban Nenne sai sun tanka, cewa “Prince shi ya zabi little fulani girl haka?” Nenne saidai tayi murmushi tayi shiru bata cewa komai. Jikin Aisha da ake yawan yiwa ba’ar siranta a wurinta harda sakacin Haj. Zainab ga irin abincin da ta bar Siddiqah tana ci. Ire-iren abincin da Aisha ke ci duk na kwalam ne, tafi ganewa mai da yaji da kayan kwalam su agwaluma, dinya, kanya, magarya wanda babu
Chapter 17 · 0% Book details