Sashe 7
Aisha Siddiqa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
masarautar Gombe yarannan sam basa shiga sabgar bako, wasu irin ‘yammata ne masu halin ‘ya’yan sarakuna na halin girman kai da da wanda hali ne da ya sha bambam dana mahaifiyarsu da mahaifinsu kansa, balle Siddiqa da tazo musu da wani al'amari da ya bata ran su, wai kyamar Yorubawa take, Firdausi kadai ke mata uzuri, don haka Siddiqa da Nenne ta kawo gidan Engnr. Idris Akanni don ta nema mata magani ita kuma tana rarraba musu ido a tsorace wai tazo gidan Yarbawa in suna yarbanci, ita Siddiqah tsakaninta da Allah da gaske ko yarbanci ake yi bata son ji a kunnenta, damunta yake yi, don jin yaren take kamar fada-fada, ita kuma bata son fada da hayaniya, ta kuma kasa boyewa a ranta har ta kai ga Fatima ta fahimta, itama kuma ta kasa boye jin haushin hakan har ta fahimtar da sauran ‘yan uwanta, sai hakan yasa suka fara tsanar bakuntar Siddiqah, suka nesanta kansu da shiga sabgar ta, suka barta da Nennen data kawo ta kadai kuma basu nunawa Nenne hakan ba. Ga hudubar Aunty Taiwo na kada su sakar mata fuska ta samu damar zama dindindin a gidansu, ita bata son jaye-jayennan na Nenne, ko na ‘ya’yan yan uwanta da take kawowa hutu gidan Taiwo na yawan hanawa, musamman daga bangaren Gombe, Taiwo tafi son dangin Babanta ba tun yau ba don a cikinsu take rayuwa jefi jefi take zuwa Gombe, Oummana kanta ta sani Taiwo tafi son dangin Babansu, a cewar Taiwo bahaushe bashi da amana, gashi da butulci da rama khairan da sharran. Firdausi dai bata tsananta ba, cikin mu’amalarta da bakuwar Nenne Aishatu-Siddiqah, a kiyayyar da suka kafawa Siddiqah, ita tana yiwa Siddiqah uzuri da kuruciya da rashin wayewar kai. Fatima kuwa ta daina zaman gidan sabida Aisha-Siddiqah, ganinta kullum tareda Nenne cikin gidan yana bata mata rai, in ta fita tun safe sai yamma, dama service (NYSC) suke yi a wurare mabanbanta itada Firdausi. Don haka a kwana biyunnan asabar da Lahadi ba karamin shiga takura Siddiqa tayi a gidan Engnr. Idrees Akanni ba, na farko babu kawayenta na makaranta su Amintako, da Ramatu da sauran ‘yan gang dinta masu kara mata karsashi, ba Ummanta data ke zubawa shawagwaba kullum a gefe, sannan babu Babanta mai biyewa rikicinta sannan ba Ishaq masoyi mai sa ta dariya da murmushi sabida iya soyayyarsa, a wurin Aisha-Siddiqah duk wani farin cikinta yana tattare da kasantuwar wadannan mutanen data zayyano a sama a tare da ita. Don haka cikin kwana biyunnan Aishah duk ta birkice da dacin rai, duk kokarin Nenne nata saki jiki tayi feeling at home abun ya ci tura, Allah-Allah kawai take safiyar Litinin tazo, a kaita asibitin da aka ce don shi aka kawota Ikko, a gama a maida ita gidan su a Jeka da Fari. Don Nenne tace sai litinin zata kaita taga likitan Firdausi. Yau Lahadi da Nenne ta ga taki cin dinner ta kuwa ce mata komawa Gombe ba rana tazo gidan yarbawa kenan har abada. Musamman data lura da dabi’un Siddiqah na kabilanci basu canza ba, duk da nasihar data bata lokaci tayi mata, shiyasa take so ta saba dasu tun yanzu, tunda kuwa she is going to be part of them nan bada jimawa ba idan Allah ya so ya amince kuma ya yarda, tanaso ta cirewa Siddiqah ethnocentrism din data likawa zuciyarta akan kabilar Yarbawa. Don haka cikin serious ta gaya mata yau cewa komawarta Gombe fa ba rana in zata bude ciki taci abinci ta ci, ko ta dinga dafawa da kanta. Duk girman kulawar da Nenne ke baima Aishah-Siddiqah a gidanta, duk sonda take kokarin gwada mata, da daular da ta tsinci kanta ciki rana daya, sama A/C kasa A/C kai har a kitchen A/C ce da fitilu masu haske wadanda da dare sai ka dauka kamar rana ce a gidan Engnr. Idris Akanni, ga cima ta alfarma wadda bata ko taba gani ko mafarkin ci ba, ga motoci na zamani kullum a jere a parking lot suna jiran mai fita a gidan da direba, rayuwa ce irin wadda Siddiqah bata taba ji ko gani ko a mafarki ba a gidan Haj. Sappa dake a Banana Island, Lagos, amma duk wannan sabida kulafucin uwa irin na Siddiqah hankalinta bai taba kaiwa kansu ba balle tayi appreciating. Kacokam! hankalinta yana gidan su a Jeka da fari. A weekend dinnan kafin zuwan Litinin da zasu ganin likita, sau uku Aishah tana shiga toilet ta kulle tayi kukan makon uwarta da kewar Gang members dinta na Billiri, a karshe ta goge hawayenta ta fito, ita ba waya ba balle ta kira Umma ko Ishaq ta gaya musu kurkukun Yarbawa Umma ta kawo ta. Ishaq ya sha gaya mata cewa sabon data yi dashi yafi son da take masa yawa, yau ta yarda da cewar nan tasa it aba wani soyayyar namiji a ranta sai kauna da sabo na ‘yan uwantaka da shakuwa tsakaninta dashi, don a baya in ya fadi irin hakan fushi take yi sosai, ta ce ya raina son da take masa, ita ba wani sabo a ranta sai SO. Yau dai ta yarda Ishaq ya fita gaskiya ta saba da shine kamar Yayan da suka fito ciki daya shima wani irin kewarsa da take daban ce. Haka a daddafe Aisha Siddiqa Yunus ta kai safiyar Litinin a gidan Engnr. Idris Akanni, kafin kwana biyun nan duk ta kara ramewa kamar kudin guzurin da ake diba kullum, Umman Siddiqah ma tana can a Gombe amma hanakalinta yana Lagos, tana kewar Petel dinta duk da ta saba da hakan in ta tafi makarantar kwana amma wannan kewar bata san meyasa ba ta dabam ce, tasan dai Hajiya Sappa zata kula da ita har fiyeda kulawar da zata bata, don taga tsantsar kaunar Siddiqah cikin idanun ta rana ta farko data fara ganinta a kwance a jikin gado a asibitin FMC Gombe. Komai na gidan a darare Aishah-Siddiqah take dashi, ta sanyawa ranta son komawa Gombe a matsayin abinda zai bata kwanciyar hankali kadai. Nenne kuma tace ba rana. Ko jiya data baiwa Nenne tausayi ganin yadda ta maida kanta daddawar daka, saida tace da direban su Fatima in ya kaisu wajen saloon ya dawo ya dauki Siddiqah ya kaita yawo ta ga garin Lagos, ta bata kudi tace ta sayi duk abinda take so in sun fita, madadin zaman daki data ke tayi ta dankare a kuryar gado tun safe har yamma in har ba Nenne ta kirata falo ba. Amma Siddiqah taki, harda rokon Femi da Nenne ta aiko kiran nata. “Don Allah don Annabi a kyaleni kallo nake yi”. A ganinta gara ta zauna a gida tayi kallon talbijin da bata san ma me ake yi a ciki ba sabida hankalinta da baya jikinta yana Gombe ya fiye mata shiga cikin garin yarabawa, a ranta tace ta san duk garin Legas dinma Yarbawa ne, don haka ita bata ga abun kallo a garin Lagos ba. Nenne dai tana ta kara fahimtar (negative attitude) din Siddiqah akan kabilar da ba tata ba, duk wani motsinta a daki ne ko a falo akan idonta ne ba tareda Siddiqah ta sani ba, ta fahimci irin kallon da Siddiqah ta ke yi jama’ar gidan bakidaya kallon (yare) bama musulmai ba, musamman kabilar yarbawa da sukayi kaurin suna (ridiculously) a idanun hausawa wanda a zahiri yake bukatar gyara, ta fahimci har zuwa lokacin Siddiqah ta kasa karbarsu a ranta. Nenne ta gama sawa a ranta ita kuma sai ta goge wannan negative perception din daga kwakwalwar Siddiqah koda ba a lokaci daya ba. Tace “Siddiqah na bukatar thearapy, counseling kai har da rehabilitation akan shin su waye kabilun Najeriya wadanda ba Hausa-Fulani ba??? Me yasa aka sanya mu karkashin tuta daya (gabas da yamma, kudu da arewa) muka amsa GREEN WHITE GREEN??? A ganin Hajiya Sappa kabilancin dake zuciyar Siddiqah da idanunta ya wuce kima ya kintace har ya zarce na musulunci ya zame mata wani abu daban kuma, domin kuwa yafi nata na can baya tsanani, a lokacin da take da shekaru irin na Siddiqa sanda ta tsinci kanta a gidan aure dumu-dumu a tsakiyar masarautar Ilorin, lokacin da aka kawota cikin dangin mijinta da babu bahaushe ko daya a matsayin mata ga daya daga cikin zuri’ar Emir Abdulrasheed Akanni. Siddiqah ta yi wa kabilanci da banbancin yare da al’ada tsakanin ta da da kabilar da ba tata ba mummunar fassara wanda Nanne Sappa ke son ta rage ko bata yi nasarar cire mata shi duka ba. **** **** **** Ranar litinin da safe Nenne ta shirya tsaf cikin koriyar laffaya tayi sharr sai tashin sassanyar kamshin turarukan “Naseem” take, kyakkyawar bafullatana wadda bata kwalliyar fuska sam, amma fatarta sumul-sumul kamar ta shiga injin wankan fata, daka ganta ka ga daya daga irin matan manyan sarakuna ko masu arziki wanke hannu ka taba, kalarta harda jaja-jaja na samun kula da samun daular rayuwar da kowanne dan adam ke buri, hannunta cike da bangles na zinare hagu da dama ko yaya ta motsa sai sun motsa tamkar ba’indiya. Haka tasa Siddiqa a gaban motarta ita kuma tana hakimce a gidan baya direbanta Ojotu ya ja mota zuwa asibitin da zasu je. Tuntuni dama tayi (booking appointment) na ganin likitan nasu, tafiyar mintuna kalilan a manyan titunan garin Lagos daga Banana Island ta kawo su asibitin (Lagoon Hospital), da kanta ta kai Aisha har gaban likita Ayoade wanda shine likitan Firdausi, Dr. Ayoade Khalil. Dr Ayoade yayi mata kyakkyawan (check up) ya dorata akan sabon treatment da yafi wanda take kai a FMC Gombe, ya kuma canza mata magani mai kyau, da ya auna jininta yace sai yaga yadan hau, ga rashin nutsuwa a tare da ita da alamun akwana bukunnan data yi a Lagos ko sau daya bata ci abinci cikin nutsuwa ta koshi ba, likitan yace da Nenne zai riketa two days bed rest don ya ga jininta ya hau. Zai kuma sa mata drip. Nenne ta damu kwarai, yau tana ganin ikon Allah a gun Siddiqah wannan makon gida nata har ina! Ta ce ma Aisha bayan kaucewar likitan daga kusa dasu. “Yanzu saboda Allah Siddiqah me na raga miki? Me Umman take baki wanda bana baki? Na tabbata sabida baki son zama damu ne kika