Sashe 14
Aisha Siddiqa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A can gidan Sarkin Gombe kuma su Nani Oummana abin nema ya samu, shirin biki ya kacame ka’in da na’in, bikin jikan da aka jima ana jiran zuwan ranar aurensa a zuri’arsu Nenne Sappa, duk da Nenne tace bata son biki, sabida bata jin dadin jikinta. Uban kasa yaki amincewa, yace ta kwanta a daki ta huta ta barsu suyi. Abdulrasheed ne, dole su yi biki kona kwana uku ne, tunda dangin ubansa ma zasu yi irin nasu a Ilorin. Yayinda can gidansu amarya hankula ba’a kwance suke ba suna asibiti tun faduwar Aisha suke asibitin a hannun likita Umar. Ko a lokacin Haj. Zainab sunyi waya da Nenne ta gaya mata ga akori-kurar kayan abinci nan an taho saukewa sabida bakin da suka zo biki, komai na al’adar bikin gidan Sarkin gombe an hado musu dashi rankatakaf. Hajiya Zainab bata gaya mata Petel dinma tana asibiti ta rikice musu da sambatu ba. Don kada hankalinta ya rabu biyu, ko daga jin muryarta ta fahimci Nenne bata da lafiya, sai Haj Zainab ta roki alfaramar Nenne, tunda itama bata jin dadi kan cewa suna so a daga daukar amarya zuwa kwana uku don a samu a sanar da ita ko me ake ciki a kuma samu a lallasheta. Nenne ta amince da hakan inda ta sanar da ita matan ‘yan uwan mijinta masu daukar amarya zasu zo daga Ilorin, zasu hadu da nata ‘yan uwan su dauki amarya. Likita Umar shine likitan asmar da Petel take gani tuntuni shi suka samu nasarar gani a hannunsa Siddiqah take, kuma yana kula da ita yadda ya dace don dama sun saba sosai shi da ita, yace ba asma ce ta tashi ba, suma tayi dan firgici, ya bata (bed-rest) na kwana daya don yanaso yayi counseling dinta tunda Haj. Zainab ta gaya masa aure ne aka yi mata bagatatan. Koda ta farfado ma bin su Ummanta take da ido ta dauka asma ce ta kawo ta asibiti ta manta shaf da abinda ya faru din. Duk yadda Likitan ya iya lallashin Siddiqa don ta gaya masa abinda ya firgitata da bakinta yau Siddiqah shiru tayi masa, tace ya tambayi Umma don ita ta manta. Umma dake gefe tace. “Likita ba abinda aka yi mata rigima ce irin tata daga dawowarta bata ko ganmu ba, ta tsinci magana a wajen ‘yan uwanta shikenan ta fadi ta sume min. Umma ta kara da cewa “Petel dina, ai kinsan daga ni har Abbanki masu son farin cikinki ne, ba abinda zai daga miki hankali ba”. Sai a lokacin Siddiqah ta tuno exactly me ya faru daga shigowarta gidansu daga Lagos. Da sauri Siddiqa ta katse Umma hawaye nan da nan ya cika idonta. “Umma! Kuna son farin ciki na shine kuma aka aura min Bayerabe da ban ma san shi ba? Umma kinfi kowa sanin yadda bana son yarbawa”. Dr. Umar wanda mahaifiyarsa ‘yar kabilar Yoruba ce, bai san sanda ya kufula yace da Siddiqah. “shi Bayerabe ba mutum bane Aisha?” Ta yi maza ta sunkuyar da kai, hawaye ya zubo mata tace “amma ai inada miji, kuma ban gama makaranta ba”. Abban Siddiqah da Baba Barau tare suka shigo lokacin, suka ja kujera suka zauna ta gaban gadon Siddiqah aka cigaba da lallashin tare dasu. Muryar Abbanta abin tausayi yace “Aishah-Indo Siddiqah, to uban Ishaq din yace bazasu aureki ba tunda kinada cutar numfashi”. Aisha ta zaro ido daga kwance, Baba Barau ya gyada kai ya gyada mata kai cikin tabbatarwa, yace “to su kuma wadanda kikewa kabilancin son ki suke da asmar taki, da dukkan zuciyarsu sun karbeki cikinzuri’arsu, Ubanki kin ganshi sabida ya faranta miki ya kuma fita hakkinku don yasan kinason yaron nan shima yana sonki da gaske sai da ya yi tattaki ya isa ga mahaifin Ishaqa, amma bawan Alllahn nan ya wulakanta mu, don haka ya rage naki ki nemawa kanki mutunci kije inda ake son ki ko ki tsaya shirmen banza a inda ba’ayi dake saboda lalurarki. Hajiya Sappa Uwa ce da kowane Da zai so ta za uwarsa. Ke ya kamata ki bada wannan shaidar, kowadanne iyaye zasu so hada zurri’a da ita saboda karamcinta da girmama dana dam da halin tawali’u, ai dai kin dan zauna da su zuwa yanzu ya ci ace kin san ko su su waye. Inna kara jin Kalmar “Bayerabe” ta fito a bakin ki wallahi sai na kumbura miki shi, don dama yayi miki kadan”. Suka taru su duka har likita Umar suna tausarta, likita yace “Aisha kibi zabin mahaifinki nina gaya miki in sha Allah bazaki nadama ba, a cikin biyayyar iyaye babu nadama kin ji? I am a Yoruba man by maternal tribe, ina tabbatar miki mun iya rikon aure mun iya tattalin matanmu da girmama su”. Umma tace “wallahi wallahi bamu yi miki zaben tumun dare ba duk da ban san shi ba ban kuma ganshi ba ko a hoto, zuri’ar Hajiyar Lagos ba yarbawa ba ko inyamurai ne zan basu ke albarkacin ta da addu’ar da naji tana yi a filin Arfah, tunda dai kalmar shahada ta hada mu bakidaya. Ni bansan ina kika koyo wannan kabilancin naki ba, ni dai baki taba jin na ce wani da ba bahaushe ko bafillace ba daban yake da sauran mutane ba”. Ko ta ina sun rufu a kanta basa ko bari ta ce uffan, wannan ya koro nashi wannan ya cafe. Baba Barau yafi kowa zafi, shi baya hadawa da lallashin ma. Cewa yake ta kara fadin Kalmar yarbawa ko bayerabe yanzu ya kumbura mata baki. Malam Yunus shi ke lallashinta, yana gaya mata kaddadar kenan data hado Hajiya Zainab da Hajiya Sappa a aikin Hajji, wato kaddarar aure a tsakanin ‘ya’yansu. Kaddara mai kyau, wadda aka kullata a gaban Ubangiji a dakin Allah kan dutsen Arfah mai alfarma. Domin Umma ta gaya musu addu’ar data ji Haj. Sappa nayi a kan dutsen arfah. Ta ce tun a lokacin ta fada a ranta baiwar Allah inama zai amince da Petel dina! Ko ba komi addu’arta da tsarkin zuciya tayi ta, kuma sai ta riga ni furtawa kafin ni in furta nawa fatan. Ina kara fada miki cewa ban ganshi ba, ban taba ganinsa ba ko a hoto ban kuma taba jin muryarsa ba, amma shi na zaba miki a matsayin miji Petel”. Aisha ta saka kuka tana cewa “Umma karatuna, Umma makarantata shikenan bazan gama aji shidda ba?” Malam Yunus yace “Aishatu ni malamin makaranta ne kin fi kowa sani, na san muhimmancin ilmin diya mace, ko bana raye bazan bari a aurar dake a inda za’a tauye ki ta fannin ilmi ba. Ki bari ki samu lafiya ki barwa Allah komai, shi zai iya miki kinji ko?” Har dare suna kanta, kuka da sheshsheka har da jijjiga don kuka. Hawaye ya hade da majina. Saida likita Umar yayi mata allurar barci suka samu lafiyarta. Washegari da safe data tashi nurses suka bata maganin ciwon jiki da Panadol ta sha. Umma ta hada mata tea mai zafi da kauri shima ta sha. Wajejem karfe sha biyu na rana yace zasu iya tafiya gida sannan yace da Siddiqah ita kadai. “Babanki ya bani tausayi Aisha, ki duba yadda ya damu da halin da kike ciki, jiya ya sameni a ofis ya gayamin yafiso yayimiki abinda kikeso amma yana ganin kimar wannan baiwar Allah, kiyi hakuri kiyi masa biyayya kinji bazaki tabe ba”. Ya kara da cewa “one more albishir, Yarbawa fa sun fi Fulani iya soyayya Siddiqah”. Siddiqah ta harareshi sannan ta gyada kai, tana tsane hawayen idonta, Umma kuma na can tana tattara ‘yan kayansu batasan me Dr. Umar ke fadawa Siddiqah ba wanda shi fisabilillahi an yi masa riga malam masallaci ne tuntuni yana matukar son Siddiqah, amma da yaji ko sakandire bata gama ba shiyasa ya dakata, don shi kadai take gani a matsayin likita duk sanda tazo FMC. Umma tazo inda suke sukayi sallama da likita ta kamata ta sakko daga gadon suka wuce zuwa mota inda malam Yunus ke zaune cikin motar shi Toyota Corolla yana jiransu. Ko kafin su iso gida, an sauke buhunhuna da katon katon na kayan abinci daga gidan Sarkin Gombe. Siddiqah ta wuce uwar dakin Ummanta ta kule a karshen gadon Umma bata ko kula kannen iyayenta dake tsokanarta ba, wai ciwon aure take yi ai normal ne. Addar Kumo da yake mijinta bai jima da rasuwa ba, tabi Siddiqah har dakin Umma tace da ita, “to ni ki bar min Bayeraben mana? Shashasha jikan uban kasar Gombe ne ta fannin uwa, ni inasonsa tunda ba wani tsufa nayi ba”. ta kara da cewa (cikin jin takaicinta) “Su Indo! An tako arziki ana kokarin fatali da shi da gangan”. Siddiqah kasa shiru tayi tace “Adda wallahi Allah na bar miki bayeraben dari bisa dari kuma da zuciya daya, koda Ishaq ba zai aureni ba ai na fi karfin auren bayerabe jikan oduduwa”. Sai jikake gab! Umma data shigo ta gabje bakin nata. “Inace dazunnan Babanki Barau yace kada a kara jin kalmar nan ta kabilanci daga bakinki?” Siddiqah kuka ya koma sabo, bazata iya tuna (when last) Umma ta kai hannu jikinta ba sai yau. Itace ta fari itace auta tsakanin ta da Umma sai soyayya. Sai yau akan Bayerabe dan kawarta. Tayi kuka-tayi kuka ta gode Allah bata kara tankawa kowa a gidan ba. Daga bisani kuma barci ya dauketa. Data farka da la’asar da kyar Addar Kumo tasa ta tayi wanka shima duk rabi ita ta cuda mata baya Siddiqah na rufe kirjinta wai kada Adda ta gani. Wannan abu ya kara kular da Siddiqah don tayi tayi Addar ta fita ta bata wuri tayi wankan da kanta taki, tace na san biji-biji zaki yi, gara in cuda ki da kaina, da aka haife ki ma ni dinnan nina cude ki, har yaushe kika yi girman? Ina abin yake da zan gani wai maye ya ci jinjiri kirji kamar ‘ya’yan goriba? Haka in kin haifo mana jikan Uban Kasa ni zani har kasar Yarbawa in sake wanke ki fes da runhu da ganyen darbejiya”. Kabakin abinci iri-iri aka dinga fiddawa daga gidan su Siddiqah da soyayyen naman Sa zuqu-zuqu akai, wanda aka saka cikin abincin ya wadata. Lemuka (soft drinks) kamar a wanke tsakar gidansu Aisha dasu. Surutu