← Book details Aisha Siddiqa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 27

Sashe 3

Aisha Siddiqa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

R anar da Nenne Sappa ta koma Lagos tareda Aisha ta sauka a gidanta a Banana Island da tsakiyar marece, Aisha rike da ‘Handbag’ din Nenne tun daga Gombe ta riko mata, duk da bata son tafiyar kuma hakan ya kasa boyuwa a fuskarta duk yadda Nenne ta dinga kokarin daukar hakalinta da hira cikin fulatanci don dai ta saki jiki da ita, amma har suka sauka a Lagos kalaman Aisha a matsayin amsa basu fi biyar ga Nenne ba, haushin ta rabo ta da Ummanta ya ki barin ranta, tana dai kula ma Nenne da jakar hannunta da kan wayoyinta uku bata bari ta yi dakonsu ba, yadda take Ummanta in zasu unguwa ko ta rakata asibiti, suna isa gida ko hutawa Nenne bata yi ba ta kama hannun Siddiqa zuwa cikin gidan, babu kowa zaune a babban falon kasa sai talbijin dake ta aiki ita kadai cikin tashar kasar Yemen, barorin gidan dake giftawa kowa naaikinsa sunata russunawa sunama Nenne barka da sauka, tun daga fitowarsu a mota (Venza) da direba ya dauko su daga filin jirgin Murtala Mohammed har shigarsu ainahin kwaryar cikin gidan Engnr. Idris Akanni Aisha taga ma’aikata sun kawo gaisuwa sun kai su biyar, kai tsaye Nenne ta wuce rike da hannun Aisha-Siddiqah har dakin “Princesses” yadda take kiran (Firdausi da Fatima). Princess Fatima na kishingide a gado rike da wayar ta tana Magana da fiancé dinta Abdulganiyu Dasuki, yayinda Firdausi ke stretching gashin kanta da na’urar tazar gashi Nenne ta tayi sallama a kansu, Siddiqah na biye bayanta, Fatima ta kashe wayarta da sauri cikin murnar dawowar Nenne lafiya, Firdausi ta dago kai da murmushi suna amsa sallamar mahaifiyarsu da murna fal a fuskokinsu kafin su kula ba ita kadai bace, wata siririyar kyakkyawar yarinya mai ruwan ‘yan Gombe biye a bayanta, Nenne tace “shiga daga ciki ki huta kinji ko Siddiqah, Fatima a hada mata ruwan wanka, diyata ce na taho da ita daga gida (Gombe), ku kula min da ita da kyau, kamar yadda kuke kula da Ruqayyat (tana nufin Kiki), kafin a gyara dakin da zata sauka, zan shiga inga Dade, ina fitowa zuwa anjima”. Princess Firdausi da Princess Fatima suka dubi juna fuskar kowacce fal curiousity, sun sha mamakin inda Nenne ta samo ‘yar kyakkyawar bafullatanar yarinya haka. Kodayake tace daga gida Gombe take. Saidai basu santa cikin dangin Nenne ba kaf. Bata sauraresu ba da tarin tambayoyin data gani fal fuskokinsu ta wuce turakar mijin ta tana gaya musu cikin harhen yarbanci “su tabbatar Aisha-Siddiqah (feel at home) wato su tabbata ta saki jikinta dasu. Baba na faman aikin nasa na karatun jarida wanda ya zame masa lazim kullum tun bayan ritayarsa, Nenne ta zauna a kusa da shi cikin gajiyar tafiya bayan ya amsa sallamar ta ya kum a ajiye jaridarsa a gefe. Kallo daya Baba Engnr. Idris Akanni ya yi mata ya ga farin cikin da bai taba hangowa cikin idanunta ba. Tun kafin yaci abincin data shigo masa da shi ko suyi doguwar gaisuwa yadda suke yi idan dayansu yayi tafiya Nenne ta kasa jinkirta abinda ke bakinta. Ta gayawa Baba, ta samowa AbdulRasheed aure a Gombe. Engnr. Idris Akanni ya dago manyan idanunsa daga kan jaridar dake hannunsa yana duban matarsa Hajiya Sappa a hankali cikin nutsuwa, wato yana mata irin kallon nan na kodai tayi gamo ne? prince din zata ganowa mace? Shi baida idon gano matar data dace dashi a shekaru irin nasa sai an gano masa? Shi Engnr. Idris Akanni Waziri of Ilorin ya riga ya sakawa ransa Prince baida ra’ayin aure ne kawai shiyasa baya shiga sha’anin maganar auren da kowa ke yi a kansa kamar shikadai suka haifa, afterall sunada ‘ya’ya masu yawa a family dinsu da suka tara musu jikoki fal, maiyasa kowa zai damu kansa da Abdulrasheed shikadai? a rayuwar Idris Akanni shi bature ne baya shiga rayuwar kowa hatta ‘ya’yansa ya basu dama suyi abinda suka tsarawa kansu da wuya kaga ya shiga rayuwarsu daga lokacin da suka haura shekaru sha takwas. Don haka cikin yanayi na I don’t care attitude dinsa na halitta yace da Nenne “diyar wanene kika samo masa din? ‘Yar wace masarauta ce? Kinada tabbacin Abdulrasheed zai karbi zabin ki tunda ba wai mata ne baya gani ba a duniya? Me kika gano haka har ke da kanki yau kika zabi ki tafi nemo masa aure alhalin ina raye haka kannena maza? Amsar da Nenne ta bashi yai matukar saka shi bude ido sosai yana kallonta da mamaki don tace yarinyar bata da alaqa da sarauta. Har ila yau ya dauka ne zata ce a cikin danginta ta samowa Prince mata, tunda an zaga ta bayan fagge ance dashi Nenne ce ta daure gindin kada Abdulrasheed ya karbi mace a ‘ya’yan ‘yan uwansa wato jikokin Emir. Lokacin da akayi wancan zaman dashi yayi kuskuren cewa zai fadawa Nenne amsa ta zo ta fada musu. Daga lokacin ya gudu Qatar bai kara zuwa gida ba, sunata jira Nenne ta zo musu da gamsashshen bayani daga bakin Abdulrasheed akan zabin da suka bashi har gobe shiru. Baiwar Allah Nenne, bata ma san Abdulrasheed ya saka sunanta cikin maganarsa da kannen mahaifinsa ba a lokacin ta tafi aikin Hajji. Nenne ta kwantar da kai da murya a gaban Dade, ganin kamar cikin gatse yake mata magana. Mai bi masa wato Turaki ya masa famfo ba jimawa cewa Nenne ce ta hana danta Abdulrasheed karbar ‘ya’yansu. Sabida ta fi so ya auro daga nata dangin. Nenne bata san an yi haka ba. Tana zaune daidai kafafun maigidanta shikuma yana bisa kujera. Ta tankwashe kafafunta ta duka a gabansa (yadda take yi masa in zata yi masa magana mai muhimmanci), cikin girmamawa ta ce da shi. “Ba komai na gano ba Your Highness, ban ga sarauta ba, kuma ban ga tarin arziki ba. Na gano ma Abdulrasheed mace daya cikin dubu da na dade ina roka masa wurin Allah, irin wadda ta dace dashi ne, wadda zai matukar so fiye da komai na jin dadin rayuwarsa duk da gudun matan da yake yi. Yarinya karama wadda ta fito daga tsatson mutanen kwarai masu tarin halin kirki da nagarta. Na samo masa mace wadda ta samu tarbiyyar Uwa da Uba a tare, kwarai da gaske mai tarbiyya ce, wadda nake da yaqinin zata zauna da shi da zuciya daya ta taiamaka masa wajen gyara duniyarsa da lahirar sa. Zai zama cewa ta raba gardandamin auren zumunci da aketa so yayi daga kowanne bangare nawa da naka. Inada tabbacin Aisha Siddiqah ce kadai ta dace da zama (first wife) kuma uwar iyali ga Abdulrasheed ba tareda yawan shekarunsa ya dameta ko yayi sanadin kawo mishkila a aurensu ba. Sannan in akayi duba da kankantar nata shekarun sai naga cewa zata iya da halinsa da yi masa kowacce irin biyayya. Iyayen Siddiqah mutane ne dana dade banga irinsu ba, warin gudun duniya da tsoron Allah da tsayawa a matsayinsu. A takaice Dade naga duk abinda nake nema a suruka da surukai daga Siddiqah da iyayen da suka haifeta wanda shi yasanya ni kwadaitarwa Abdulrasheed aurenta, da fatan Barewa bazatayi gudu dan ta yayi rarrafe ba”. Nan ta kwashe komai na haduwarta da Haj. Zainab a filin Munna, da yadda ta tsinci Dollars din guzurinta ta kuma maido mata su cas a yadda ta tsince su, tace wanna shine babban abinda ya burge ni da mahaifiyarta, sannan kamanni na halitta da halayyar Siddiqah bakidaya yayi mata irin na mahaifiyarta, tana kwadaitarwa Prince samun wannan tsatson mai albarka. Sannan a surar Aisha ma bata jin AbdulRasheed zai kushe ta matsayin matarsa, tace saboda Aisha kyakkyawace shikuma aduniya yana son abu mai kyau. Duk da ake masa kallon wanda baya son mata tace zata gwada sa’arta akan Siddiqah. Tace saidai idan dansu Prince Abdulrasheed ba namiji banemai cikakkiyar lafiya. Nenne tace daga ganinta na farko da Siddiqah taji a jikinta ga matar Prince Abdulrasheed Allah ya nuna mata yau a zahiri, tace komai na yarinyar yayi mata shige dana yarinyar datake gani a istikhararta ta koyaushe, fuskar Siddiqah ta dade tana gani a cikin mafarkin ta, a matsayin matar Prince AbdulRasheed. Diyar dattaku da mutunci”. Haka dai Nenne tabi ko ta ina ta daddaure Babansu Taiwo, ya ji shi da kan shi yana son ahalin Haj. Zainab dinnan, wannan halin amana data nuna wa matarsa a wannan zamanin da muke ciki yayi matukar impressing dinsa. Ya dade bai ji hakan a kan mutanen arewa ba, kowa dai yaki halak-yaki haram saboda talauci. Dade Engnr. duk da haka bai amsa mata dari bisa dari ba, yace ne ta bashi lokaci yayi nazari sannan yayi shawara da Emir da sauran ‘yan uwansa. Ita kanta ta san Dade shikadai bai isa ya zartar da komai akan auren AbdulRasheed ba tareda amincewar Sarki da sauran ‘yan uwansa ba. ta gaya masa ta taho da yarinyar zata yi mata hutun sati daya, sai Dade yace da Nenne ta raka shi ya ga yarinyar da kansa. Baba da Nenne suka taho dakin Princess Fatima, inda Nenne ta baro Aisha-Siddiqah tun shigowarsu gidan. Siddiqah tayi tagumi a gefen gadon Princess Fatima (looking uneasy), cikin damuwa take sosai jin ‘yammatan gidan na Yarbanci, wani yare data tsana kuma bata son ji ko a makaranta, Yarbanci shine yaren data tsana fiyeda kowanne yaren al’ummar Najeriya sabida jinsa take a kunnenta kamar fada, ita kuma bata son fada da hayaniya ko kadan. Ko Ummanta ta sani Siddiqah bata shiri da bayeraben mutum a duk inda ta ganshi. Kai ita ko a makaranta bata kawance da ‘ya’yan yarbawa. A yau sai ta tuno da BISOLA! Akan kunnenta Princess Firdausi tace da Princess Fatima “Mi o mo ibi ti Nenne ti ri omo Fulani to rewa bayi. O ma’n fi oju kekere wo eyan”. (I don’t know where Nenne got this beautiful Fulani girl, she keeps looking at people with her small eyes - ma’ana; bansan ina Nenne ta samo wannan ‘yar kykkyawar bafulatanar ba, sai kallon mutane take da kananan idanunta masu kyau kamar almond)”. Princess Fatima ta dan saci kallon Siddiqah daga kwance, cikin ginshira irin ta ‘ya’yan sarakuna tana daga kwance akan gado tace “O jo ora oko ti ko ri itoju gidi (she looks local and unhealthy) wato da ganin ta
Chapter 3 · 0% Book details