Sashe 16
Aisha Siddiqa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kanta zata sanar dashi ta hanyar da zai fahimceta, don yanzu makaranta ma zata mayar da Aisha abin bana gaggawa bane, zata ta zana WAEC da NECO kafin lokacin da yaga damar zuwa don radin kansa. Taiwo was speechless. Har suka gama magana da Nenne, bata yarda ta ce uffan ba don bacin rai, ita bata yarda bama ba’a mafarki taji zancennan ba. Wasa kawai ake yi hakan ba mai yuwuwa bane Haseenah da Kehinde zasu komawa juna da taimakonta. Don a halin yanzu ma suna tare da Haseenah a UK, wadda tayi tattaki ta sameta har gidanta a Lancashire ta gaya mata komai na hanyoyin da Tokumbo yabi ya yaudareta ya rabata da Prince. Ita kuma kamar wata Rakumi da Akala duk tabi ta hau kai ta zauna. Ita ta san zuciyar Prince har gobe Haseenah take so, don soyayyar da yayi mata irinta ce ake kira soyayya ta gaskiya da babu material attachement, tunda kuwa a kanta ne ya guji dukkan ‘ya’ya mata. Haseenah ta gaya mata cewa ta dade da barin kasar Japan, wato bayan kammala karatun digirinta, tana aiki da bankin Barclays a yanzu haka a garin Leicester. Har gobe aure ya gagareta, ba don batada masoya ba, a cewarta sai don Prince kadai take jira ya huce. Yadda Nenne ta sanar da Taiwo haka ta gayawa Firdausi da Fatima, cewa kada su sake su sanar da shi sai ya zo don gigin kansa. Taiwo ta rasa me yasa ta yarda da duk abinda Haseenah ta gaya mata, har hakan yasa kwanannan take jin kewar rashin Haseenah cikinsu a ranta, ji take babu macen da ta kwanta mata a matsayin partner ga dan uwan nata irin rainonta HASEENAH AMBURSA! Yo waye yake sama da aikata kuskure ma? Haseenah ‘yar adam ce kamar kowa, mai sexual feeling at her very age a lokacin, Nenne kuma ta hanasu aure itada Prince, don haka ta dauko uzuri saba’in ta yiwa Haseenah tun sanda ta sanar da ita asalin komai da ya faru ta daina tsangwamarta a ranta. Sai ma ta koma ganin beken dan uwanta kan ya fiya kullata. Abu baya taba barin zuciyarsa ya wuce. Shi Kehinde din zai ce a tsayin rayuwarsa bai taba kusantar kowacce mace bane? Musamman in akayi la’akari da inda yake zaune, a matsayinsa na namiji mai cikakkiyar lafiya da arzikin rayuwa mai albarka irin wannan?? Saidai idan da gaske ne da ake kishin – kishin din cewa, bashi da lafiya ta auratayya ko aljana ta shafeshi. A ganinta Haseenah ce kadai ta dace da bukatun Prince, ita kadai zata iya baiwa Prince kulawar aure da ya dade yana bukata daga mace, ba wannan yarinyar kamar ‘yan tallan nono ba. Fatima ta tura mata hoton Aisha Siddiqah ta waya ba tareda Aisha ta san lokacin data dauketa ba, tun ranar da sukayi discussion a kanta, kyau kam akwai shi tareda Aisha-Siddiqah Yunus itama ta shaida, ko makiyin Aisha zai shaida wannan farat daya, gashinan har neman zuba yake inji zuciyar Aunty Murjanatu, ga cikar sumar kai, ta gira data ido masha Allah, amma kuma nakasunta shine ba exposure (ba wayayyen kai) da zata jera da Prince matsayin matarsa. Har ila yau kamannin Siddiqah sun nuna innocent looks dinta, babu sanin me duniya take ciki ko dabarun zama da namijin duniya irin Prince Kehinde. Uwa Uba babu dressing a tareda Aisha-Siddiqah irin wanda zai dauki hankalinsa a matsayinsa na celebrity, ba cikar kirji balle na mazauna kamar ma yanzu ne ta soma balaga, Ya Ilahi ga mazansu na Yoruba da son mata masu manyan abubuwa, gatanan dai a hoton irin (typical Fulani girls) na garin Gombe. Wadda babu abinda take da shi da zai dauki hankalin namiji irin dan uwanta (Prince). Wannan din dai tunaninta ne amma, bata ce lallai kowa ya yarda da ita ba. Yanzun damuwarta shine ya zatayi da Haseenah in taji Prince yayi aure? **** **** **** Yau kwanan Siddiqah uku kenan a gidan iyayen mijinta. Mijin da ko a hoto bata taba ganinsa ba, ko a sauti, bata ji muryarsa ba. haka ko a mafarkai bata taba yin na ta ga kamanninsa ba. Saidai kuma karamcin iyayensa ya danne komai. Tsakanin Nenne Sappa da magidanta Dade wato Engnr. Idris Akanni, sai ka rasa waya fi damuwa da son a kyautatawa Siddiqah a cikin gidan. Suna kula da ita su duka biyun daidai gwargwadon iyawarsu. Duk abinda aka san zai kwantar mata da hankali shi ake mata. Ba’a yare a gabanta tunda Dade ya hana, don muzanta take sosai in ana yin yarbanci ana kallonta. Iyayen Abdulrasheed mutane ne maso son ‘ya’yan su kamar larabawa suke wurin son ‘ya’ya shiyasa soyayyar su da Abdulrasheed duk ta dawo kan Siddiqah ganinta suke kamar Prince da kansa a gefensu, ko wani bangare na jikinsa. Don ya jima rabonsa da gida, shi da kowa nasa yanzu sai dai waya. Don haka zamu iya cewa matsayin kaunar Prince a zuciyarsu ya shafi kaunarsu da Aisha-Siddiqah. Duk yadda zuciyarta ta kai da kin auren, da kuma kabilancinta garesu, wanda har kawo lokacin yake kwance lambam a kasan ranta wanda zuwa yanzu zaka iya fahimtar cewa kabilancin Siddiqah ga yare (in born character) dinta ne, wato kabilanci a jininta yake ba ga kabilar Yoruba kadai ba har ma ga Inyamurai, ‘yan Kudu da duk ma wata bakuwar kabila da ba tata ba kuma suna yin yare, in dai ba Hausa ba ko Fulani, ba wai da gangan take yinsa ba, a’ah, da gaske zuciyarta ta raina Yarbawa, ta riga tayi underestimating dinsu a ranta. Saidai kuma zuwa yanzu ta gane cewa kabilar yarbawan ma wajen tsafta akwai (exception). In general ma ai Yarbawa yanzu sun fi gaban irin kallon data ke musu. Wannan din da ya samu muhalli a tareda Siddiqah wani abu ne da ke faruwa tun zamanin iyayenmu da Kakanninmu akan Yorubawa amma ba a wannan zamanin ba. Sannan kuma rainin da zuciyarta ke musu a yanzu baida alaqa da rashin tsafta, ko warin jiki (kamar yadda take fadi) ko makamancinsu, kawai dai perception dinta ya riga ya ginu akan cewa Bayerabe bai kai malam bahaushe ko bafullace daraja da martaba ba a duniya. Don haka har zuwa lokacin kabilancin Siddiqah yana nan a ranta ba tafiya yayi ba, tana jin kiyayya da kyamar aurenta a ranta, musamman in ta tuno maiyuwuwa mijin nata ma Bayerabe ne, abin ba wai ya bar ranta bane gabadaya amma ya ragu kadan data gane cewa Yorubas ba yadda take jinsu (in theory) suke (in practice) ba. Zamu iya cewa kaso hamsin cikin dari ya russuna ne sabida abinda take ta cin karo da shi akan yarbawa ya saba da tunaninta. Yawanci duka mockery ne na hausawa sabida kabilancinsu garesu Adadin yawan kyautatawar iyayen Prince a gareta, wato kulawar da (Nenne da Dade) suke mata yasa dole zuciyarta ta sanyaya da zaman gidan, ta ragewa kanta damuwa da takurar zuciya ta ragewa kanta kewar Ummanta. Ta dauko ‘yar walwala dai – dai misali ta sakawa fuskarta a gidan, in ka ganta kadaran-kadahan bata fushi kuma bata far’a, ko don Nenne ta san cewa tana appreciating kyautatawar da suke yi mata taga ya kamata ta saki ranta. Ina laifinsu don sun kawota don ta zauna a cikin family dinsu? Ai ba mai kawo ka cikin iyalinsa a wannan zamanin sai mai kaunar ka da gaskiya duba da ajin rayuwarta dana iyayenta akan nasu. Yau Nenne taje ta ga Likitanta na Lagos ta dawo, jikin nata dai da sauki, ta samu Siddiqah da Firdausi suna shirya abincin rana, maimakon abincin da Nenne ta bada order ayi a gidan wato (Oka/Amala and Ewedu Soup) sai ta samu suna shirya shinkafa da wake da salad da mai da yaji (daga gani ta gane bisa zabin Aisha ne) Firdausi kuma ta biye mata aka yi. Ire-iren abubuwanda ke bata ran Princess Fatima kenan, don haka bata ce musu don me ba kada Siddiqah taji ba dadi, amma sai tasa Femi ta dafa mata indomie da sardines ta jajjaga mata attaruhu da albasa a ciki, ba zata iya cin wannnan abincin na hausawa mara ban sha’awa ba. Firdausi ta yarda ayi wake da shinkafa dinne matsayin abincin gida duka, duk don tasa Siddiqa ta yi (feeling at home) daga yadda ta kasa far’a a gidan tun dawowarta, zuwa yanzu ita Firdausi da yake psychology ta karanta, ta fahimci Siddiqah sosai har fiyeda kowa a gidan, duk da ba janta a jiki take ba, ba kuma daki daya suke kwana ba, ta gane ba da gangan Aisha-Siddiqah take yin kabilancin da take yi musu ba, tsakaninta da Allah da ya halicceta bata taba samun kanta a wata kabila daban ko shiga wata al’ada ba bayan tata, kuma bata taba jin wani abu ‘positive’ akan kabilar Yoruba ba sai ‘negative’, so adopting komai nasu gareta farat daya a matsayin sabuwar al’ada zai mata matukar wahala, saidai ace zata iya with time, idan sun jata a jiki su basa nuna mata kabilancin, gradually (a hankali) nata ma zai tafi, musamman in tana tare da Hammansu Prince. A wurin Firdausi ba mutum mai kirki irinsa a duniya. Sannan shi baida al’adunsu sosai a tare dashi, yawanci dabi’unsa na western societies ne, wato inda ya rayu tun haihuwarsa ya kuma girma cikinsu. Nenne ta isa dining tana duba abincin cikin a manyan food warmers na alfarma da suka shirya shi ciki, sai ta zauna a kujerar dining daya a gajiye, ta ce su zuba mata taci ta kwaso yunwa da gajiya, amma kada su saka mata barkono (yaji), ta tambayesu ko ina Princess Fatima? Bata jin dadin yadda Fatima bata zama tare dasu. Firdausi ta gayawa Nenne cewa Fatima ta fita tareda Seun (Direba) yanzunnan bayan taci abincin rana, wai zai kaita wankin kafa, daga nan zata kitso amma tace bazata jima ba. Aisha-Siddiqa ta ga Nenne ta rame mata a idonta, amma ko ya akayi ‘ya’yanta basu kula da cewa a kwanakin nan karfin hali kawai take yi ba amma cikin ciwo take? Siddiqah ta samu kanta da jin tausayin Nenne, ta dauko gorar ruwan swan mara sanyi ta kawowa Nenne ba tareda ta bukace shi ba, bayan Firdausi ta cika mata abincin a plate, Nenne ta karba da murmushin godiya ga dukkansu, har tana tsokanar Aisha duk