← Book details Aisha Siddiqa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 27

Sashe 20

Aisha Siddiqa Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

wani iyawa tayi can acan ba, tana dai ji in an yi mai sauki amma ko na su Fatima ba duka take ganewa ba. Da wannan damuwar Aisha-Siddiqa ta kwana yau, wadda ta saka mata kewar FGC Billiri, ta hadu da kewar Umma data gang members dinta su Amintako, Ramatu da sauransu. Ga Ishaq dinta masoyi na hakika data kwallafawa burin rayuwa tare dashi ya mata nisa yanzu, ta tambayi kanta ko zuwa yanzu Ishaq ya gama NYSC? Rabon ta dashi har ta manta. Kowa nada wayar hannu a gidan nan banda ita, don Nenne tace makaranta zata fara, nan kuwa bata so Siddiqah ta dinga yiwa Ummanta kuka a waya ne, don kusan kullum ta hada su waya a gabanta sai Siddiqah tayi kuka da ta ji muryar Umma, saidai ta kai yanzu Nenne ta dade bata hadasu gaisawa da Haj. Zainab ba. Yau kam da yake cikin tension da takurar zuciya take, saita nutsu, tana sauraron zuciyarta, shiga tunane-tunanen abubuwan da suka dace suka kuma shafeta, ciki har da tunanin wai shin ma wanene shi wannan Hammansu Firdausi din da ake kira Hamma Prince??? Ko meye matching dinta dashi da har yasa iyayensa suka ga kamatar su katse mata rayuwa a kansa, ta hanyar hadasu wannan makalallen aure haka bagatatan bata shirya ba, kawai daga haduwar Umma da Nenne a hanyar Munna, alhalin sun san ba sonta yake yi ba shanyata zai yi a garin yarbawa? Ai ko ba'a fada ba zuwa yanzu ta gane kamar ma baisan da auren ba, don kusan duk wayarshi da Nenne dasu Firdausi ta kan ji jefi-jefi, bata taba jin wani cikinsu yayi masa zancenta koda da subutar baki ne ba. Kamar ma boye masa suke, me hakan ke nufi? Anya Umma ta san zaman kashe wando da take yi a Lagos ba a gidan Prince din takde ba? Haka kawai an raba ta da mai sonta bayan shi ba son ta yake ba baima da lokacin zuwa kasar Nigeria, me yasa iyayenta zasu takurata a yi aurennan don kawai su farantawa Nenne dake cikin damuwa akan danta. Ita ba'a damu da nata feeling din akan kabilar yarbawa ba. da gaske take tanada kabilanci da ethnocentrism ba da gangan gtake yi ba. amma aka tashi aka aura mata Bayerabe da bata ko taba gai ba shima kuma baya sonta. Ta tabbata da yana son ta, da tuni ya zo, ko bai zo ba, da wani cikinsu ya gaya masa batun auren su da zaman jiransa data ke yi. Gashi har ana neman fita watanni uku. Shi wanda aka ce zaman shi take yi a gidannan bai zo ba, bazai wuce shima bakin bayerabe bane kamar kowanne bayeraben mutum data sani, kuma irin katoto dinnan ya tsa tsagu ba kamar Ishaq ba. Kodayake taga cewa Dade baida tsagu, kuma indai irin kalar su Fatima ne kuma Nenne ce ta haife shi da gaske to ba lallai yayi muni ba. Ai kawai data rasa takamaimai tunanin daya dace tayi, ta kuma ga cewa tunaninta ya fara fita daga saiti, sannan ta kuma ji ta na dokin ganin Prince Abdulrasheed (just to quench her curiousity about him) sai ta karkace ta cusa kai a kasan pillow ta tsinke da kuka ita kadai, irin kukannan na banida tsumi bani da dabara. Ba tareda ta san mawuyacin halin da al’ummar gidan suka kwana a ciki ba. Ashe ita kukan samun wuri takeyi. Kwana sukayi Nenne na suma tana farfadowa cikin murmukususu na azabar ciwon ciki. Don haka cikin daren akayi asibiti da ita. Sai da asubahi taji ana buga mata kofa, dama barcin nata ba wani nisa yayi ba, ba kuma dadinsa take ji bat un bayan daya sureta, tana dai kwance ne kawai, nan da nan ta bude ido tana mutstsika shi sai taji ya kumbure suntum. Ta mike ta bude, sai taga Femi tsaye cikin damuwa. “Aisha ki sauko falo Dade na kiranki”. Gabanta saida ya tsinke ya fadi, amma bata tambayi Femi komai ba ta dauko hijab ta dora akan kayan barcin ta cikin kidimewa tabi bayanta zuwa downstairs. A falon kasa ta tadda Dade a tsaye yana jiranta, Fatima da Firdausi basa gidan suna Ilorin bikin cousin sister dinsu ‘yar wajen Malami Uban Doma. Da girmamawa ta hau kokarin gaisar da shi, amma ko daga fuskarsa ta ga damuwa, Dade yace mata cikin Hausa “Aisha biyoni, Nennenku ce babu lafiya tun cikin dare muna asibiti, and she’s calling you”. Iyakar firgita da rudewa Siddiqa ta shigesu. Ta bi bayan Dade zuwa mota a sukwane, Seun direba ya ja suka tafi asibitin da Nenne ke zuwa wato Lagoon. Suna tafe a hanya Siddiqah na jan hasbunallahu wani’imal wakeel saboda ko daga damuwar da Dade ya nuna a fuskarsa ka san jikin na Nnnne ya matsa, ta na jin sa yana waya da Hammansu Firdausi, akan hanyarsu ta isa Lagoon Hospital. Dade na magana kamar cikin hassala yana cewa. “Kehinde na rantse maka zaka hadu da fushi na, na ga alama baka san zuru ba, na rantse in ban ganka gobe ko jibi ba zaka sha mamaki na, aiki da hawa doki yafi ahalinka ko? Yau watan ka nawa rabon ka da gida saboda Baffanninka? To in kaga dama yanzu ai ka zo, in kana da rabon ganawa da mahaifiyarka dake kwance rai kwakwai, mutu kwakwai tun jiya. Gata nan kwance rai a hannun Allah amma da yake har kullum kana ranta bata fasa kiran sunanka ba. Ka tabbatar ka bar duk abinda kake yi ka nemi jirgi mafi kusa ka taho Lagos”. Ya danyi shiru, da alama rokonsa Prince yake ta daya bangaren, kan ya fadi masa ko me ya faru da mahaifiyarsu Nenne? Dade sai da ya nisa kafin yace. “Wai ashe Hajiya Sappa ta jima da 'renal stones' har 'cyst' ya fito a ‘kidney’ dinta, tana treating ni ban taba sani ba saboda zurfin ciki irinnata?” Da haka Dade ya kashe wayarsa, ba tareda ya jira amsar Hamma Abdulrasheed Prince ba, ya koma ya jingina da allon kujerar motar, ya lumshe ido yana maida numfashi a hankali yana kiran sunan Allah As-Sattaru, yana rokonsa ya tashi kafadar matarsa abar son sa uwar ‘ya’yansa Nenne Sappa.
Chapter 20 · 0% Book details