← Book details Aisha Siddiqa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 27

Sashe 18

Aisha Siddiqa Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

wani sinadarin gina jiki a cikinsu. In kuma abinci zata ci sai ta shirbineshi da barkono yayi jajir Nenne kan ce Allah ya so ta bata da ulcer, suma Yoruba na son yaji amma na Aisha is over ace ko abinci aka yi da miya da nama ita sai ta dibi fara ta sa mata mai da yaji zata ci. Duk wannan enne na kokarin rabata dasu yanzu. Kai hatta yadda zata dinga dukawa ta gaida Emir da sauran Baffanninsa in taje Ilorin ko sun hadu Nenne bata barta haka ba sai da ta koya mata dukawar gaisuwarsu ta al’ada, ta maida kanta TUTOR ga Siddiqah ba Uwar miji ba. Duk da dai Siddiqah bata nuna wani interest akan abubuwan al’adar Yoruba da Nenne kullum ke kokarin dorata a kai. A wurin Nenne aure abu ne mai broad perspectives, wanda cikinsu ya hada da rungumar al’adun juna (embracing each others’ cultures and traditions) don samun karuwar soyayyar juna, wanda ita Siddiqa a tunaninta bai zame mata dole ba ai, since she has her own culture data riga ta girma cikinta. Nenne kuwa ta yarda da cewa in ka auri mutum ka aure shi ne da shi da danginsa da kabilarsa da iyayensa da dabi’unsa bakidaya, wato dai ba shikadai ka aura ba. shiyasa ta dage wajen koyar da ita abubuwanda watarana su zasu taimaketa a zama da Prince da danginsa. Duk da haka Aisha na jin dadin girke-girkennan data ke koyo daga Nenne, don wani ilmi ne na daban yazo mata, sannan yana keeping dinta busy a gidan har bata zama tunanin gida. Nenne ta gaya mata in zata maida kai ta dinga cin abincinsu ta maida, shine zai gina mata jiki ta zama mace. Ta gaya mata cewa Yoruba na amfani da komai na abincinsu (fresh veggies) ne masu kara lafiya, duka abincinsu kyakkyawan vegetables ne da protein, basa cin abinci saida isashshen nama da kifi da korran ganyayyaki iri-iri, shiyasa take ganinsu healthy cike da kuzari, ga su Firdausi nan masha Allah dasu, bul-bul, cif-cif, kamar ka taba jini yayi tsartuwa. Siddiqa gani take jikinsu Fatima kamar da an soka tsinke zai bule don laushi da kyau. Kirjinsu tantsan da dukiyar Fulani, bayansu cike da mazauna kamar balan-balan, har bata son kallon kanta a mudubi a gidan don sai taga kanta kamar kwancen yunwa, har bata son duba mudubi. Ta maida hankali ga cin ire-iren girke-girken da Nenne yiwa Dade kullum, musamman da yake tare suke yi ba Femi ke yi ba. Nenne tace mata Hammansu Fatima ma abinda yake ci kenan mostly wato Brown Amala da Ewedu Soup. Ta taba gaya mata Hamma baya cin Igbin saboda snails da ake sakawa a ciki. Inda abincin Yoruba guda daya da baya so a duniya to Igbin ne, don baya cin snails tun yana yaro. Amma Gbegiri ma yana sonta sosai. Ta gaya mata shi din ne ma’abocin cin korran ganyayyaki ne a cikin abinci, sannan yana matukar son WARA. In ka gansu a kitchen sun hada kai itada Nenne suna hada girke-girke akan cooker kamar kanwarta dake mata zaman daki, don jikin Nenne baya nuna shekarunta sam. Kullum tana nan fit and healthy don akan ce jikinta na Fulani Prince ya samu mai boye shekaru da rashin mummunar kiba. Bata da kiba, kuma sannan bata da rama sam. Jikinta daidai ita kamar ita ta zabawa kanta. Da farkon zuwanta tana dan jin kunyar Nenne, daga baya da taga bata da wadda ta fita a gidan ga sakewar fuska irin na Nenne Sappa sai ta ware ta maida ita kamar Yayarta. Kai bazaka ce wai danta ne aka aura mata ba kwanaki kadan da suka gabata, ko watakila don ita kanta Siddiqar bata shaida hakan bane a zahiri, wato bata yarda tana auren dan Nenne ba, tunda kuwa da idonta bata ganshi ba, sannan da kunnenta bata taba jin muryarsa ba ko inuwarsa bata sani ba. Don har gayawa Nenne take tanaso tayi kiba da cika irinna su Firdausi. Nenne tace “good, ai siranta ba abin so bace, haka itama kiba, amma taki kam akwai rashin ‘good nutrition’, to daga yau sai ki cire kabilancinki ki dage da cin su Gbegiri, Oka/Amala, yam flour/ponded yam, da miyar Ewedu. Ga kuma kunun farar shinkafa, garin gero, cukwi da aya da dabino dana sa aka niko, zan ke dama miki kullum kiyi ta sha. Nina gaya miki har sai kinfi Firdausi cikar ido da cikar kirji, wadannan ‘yan kirgen dangin naki da aka rasa size din braziyar da zata yi musu daidai, suma su cicciko suyi gwanin ban sha’awa, gasu dama ‘yan kanana da basa bukatar rigar mama”. Kunya sosai ta kama Aisha ta kare fuska da tafukan hannunta tana dariya, hakan da Nenne ta fada ya tuna mata wani abu da ya faru da jimawa sanda Ummanta ta sa muciya ta buge kirgen dangin data soma, wato ta mayar da nonon, lokacin da ya fara fitowa cikin wata hikima ta iyayen da. Nan ta hau dariya ita kadai, tace. “Nenne, ni fa na san dalilin da yasa har gobe ni banida manyan nono, zan baki labari, amma kada ki gayawa Ummana na gaya miki”. Nenne tace “umh, I am all ears, amma ‘yar shekaru kusan sha takwas haka bata saka ‘bra’ ai da mamaki, to ina jinki” ta dakata da abinda take yi ta bada hankalinta tana sauraron Aisha. Rufe ido Siddiqah tayi da fararen tafin hannunta tana kyalkyala dariyar maganar da Nenne ta gama yanzunnan, kafin tace. “Ai wato Nenne sun fito fa da farko, tun ina 13 years, Ummace ta bige su da muciya, lokacin da suka fara fitowa ta samu muciya ta karanta addu’ar da bansan me ta karanta ba tace "Ya Allah ba yanzu ba, sai ta kara girma", sai ta buge su da bakin muciyar, daga lokacin suka koma”. Nenne ta kasa rike dariyarta, don ita bata taba jin inda akai haka ba, kai Hajiya Zainab sai a barta, saida ta gama dariya mai isarta kafin tace. “to ita kuwa Umma meyasa tayi hakan ai girma dole ne ga diya mace, fatan dai shine Allah ya taya mu akan tarbiyyarku, har mu mika ku gidan mazajenku. Fara kirgen dangi da wuri ba abinda zaisa ba abinda zai hana in lokacin aure ya zo wa mace. Sabida shi aure lokaci ne dashi ga kowacce mace ba sai sanda ta shirya ba”. Siddiqah tace “ai Ummana bata so ayi min aure da wuri, ga Babana yayi alkawarin da wuri zai min aure, saboda ya samu jikoki da wuri tuda shi bashi da’ya’ya da yawa, ita kuma Umma tunda nikadai ke gareta, sai bata son auren wuri gareni, shine dalilin data komar da kirgen dangin lokacin da ya soma fitowa, tace itama Goggonta Allah ya jikan rai haka tayi mata kuma suka koma, don in Abbana ya gani zai ce ai kawai na isa aure”. Kai yau cikin Nenne har kullewa yayi don dariyar da Aisha ke bata, tace “kuma sai gashi hakan bai hana auren yazo miki da wuri ba, Allah kenan! Mai yin yadda yaso a lokacin da yaso”. Ita kuwa Siddiqah sai yanzu take jin takaicin abinnan da Umma tayi mata, da yanzu tana cancada gayu kamar su Fatima, don gani take ko kwalliya tayi bata kyau kamar yadda su Firdausi ke cika idon mai kallonsu, suna juya jikinsu yadda ransu yake so. Tun daga ranar Siddiqah ta cire kyankyamin abincin yarbawa, ta bude ciki tana cin ire-iren abincin da akeyi a gidan, irinsu ‘Afang Soup’ da ‘Ewedu Soup’ da ‘Oka (brown amala), ga Iyan (yam flour/pounded yam) da 'ékuru' da akeyi da wake’. Duka abinciccika ne masu gina jiki da kara kuzari. A gefe kuma ga kamun da Nenne ke yi mata da kanta kullum da yamma bata mantawa har cikin dan lokaci ya fara bin jikin Siddiqah. **** ***** ****
Chapter 18 · 0% Book details