← Book details Aisha Siddiqa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 27

Sashe 4

Aisha Siddiqa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

mara lafiya ce kuma ‘yar kauye”. Aisha-Siddiqah taji hawaye ya surnano a idonta, tace a ranta “Oh ni Siddiqah! Umma ta san gidan Yarbawa ta turo ni? Ina zaune suna zazzagina da Yarbancinsu…… Wallahi bazan zauna ba sai an maida ni gida.” Sai hawaye data keta rikewa ya digo, dis-dis a saman kundukukinta tayi kasa da kai tana tsanewa da gefen mayafinta. Kyawun gidan, da alatun data gani cikinsa, da irin daular dake cikin sa wanda ko a talbijin bata taba gani balle a zahiri bai ko dadata da kasa ba, hasalima bata lura da komai ba hankalin ta yayi mugun tashi ya tattara ya koma gidansu a Jeka da Fari. Damuwarta yafi karkata ga yaren yarbanci da taji a bakin jama’ar gidan ba babba ba yaro, kowa da kowa, har ma'aikatan gidan, wanda tun farko ba shi ta ji a bakin mahaifiyarsu Haj. Sappa ba ai da kome Umma zatayi mata da bata yarda ta biyo Nenne Sappa ba Ga Siddiqah da dan banzan kabilanci a zuci. Ko bahaushen mutum bai cika mutum a idanun ta ba, balle Bayerabe, in dai kai ba bafullatani bane Siddiqah wani ganin daban take maka. Tun suna yara da ta ji ana waka ana cewa “Yarbawa masu kashi a kwano" to fa tun daga lokacin Siddiqah tasa a ranta duk Bayeraben mutum kazami ne. Ita a duniyarta da zuciyarta tana da kabilanci, data dade da gina zuciyar ta akai, na jin cewa kabilarta ta Fulani tafi kowacce kabila, tana ganin Bayeraben mutum kamar wani ‘alien’ ko wani na daban a cikin mutane sabida yarensa. Princess Firdausi ce ta lura da tsurewa da tsoron da ya samu Aisha a idanunta, amma bata san me ya kawo shi a tareda Siddiqa ba, sai taga jikinta na 'yar kyarma wanda bata ga dalilin sa ba. Ita kam Aisha-Siddiqah kawai yaren da suke yarawa ne ya tayar da hankalinta ya dugunzuma ta don ta gama sawa a ranta zaginta suke faman yi da yarbanci suna mata kallon raini wanda a zahiri ba haka bane yanayin kallon Firdausi da Fatima ne haka kaga suna kallonka daga kasan ido kamar suna harararka kasancewar sunada dara-daran idanu. Inda Allah ya taimaketa kafin su sake yin yarbancin dake barazanar saka ta ciwon kai, sai ga Nenne ta shigo tareda Babansu Taiwo wato da Dade Engnr. biye a bayanta. Nan Siddiqa ta ga ‘yan matannan biyu duk sun nutsu matuka, itama sai ta fara kokarin nutsar da kanta daga firgicewar ta. Amma idonta yayi kozai-kozai. Nenne da murmushin kaunar ta da Siddiqa tace “Aishan Nenne mutanen Lagos, yaya bakunta? Ga Babanku yazo don ya ganki”. Hawayen sabon tashin hankali ya kara digowa daga idon Siddiqah data gane Bayerabe ne mijin Hajiya Sappah shima. Kenan ita Nenne din kadai ce ba bayerabiyar ba a gidan? Haka zata zauna cikin Yarbawa kwana da kwanaki? Sai ta cije lebenta kamar 'yar goye, tana binsu da Ido ta kasa cewa komai. Amma tayi tunanin yakamata ta gaida Dade ko da ba zai gane nata yaren ba. Ta duka tana gaisheshi cikin Fulatanci, da matukar girmamawa cikin dari-dari don ta dauka baya jin ko alif a nata yaren, kamar yadda itama bata jin nasa ba kuma ta fatan ta koya. 'Yar dariya ta kama Engnr. Akanni. Kasancewar yana jin fulatanci suwayya-suwayya (kadan-kadan), ya kuma gane yanayin data ke ciki na kin sakin jiki dasu kamar ace kyat! Ta zuria da gudu zuwa Gombe, suka yi mata dariya gabadayansu ganin irin tsugunon data yi a gaban Dade ta kasa dagowa, dariyar su ta kara dugunzumata, don dai ita bata ga me ta fada abun dariya ba bayan gaisuwa. Ga mamakin Siddiqah sai taji Engnr. Idris Akanni yace “Calm down Aishah, feel at home kinji, zan hana su yin yare in kina zaune, ya kika sauka a Ikko kuma ya kika baro mutanen gida a Gombe?” Ya Karasa da Hausa. Wata wawuyar ajiyar zuciya Siddiqah ta ajiye, at least Uwar da Uban su sun iya Hausa. Kuma zasu hana a yi mata yaren oduduwa a kunne. Ta sakko daga gefen gadon tana gaida Baba da ‘yar karamar muryarta. Gaisuwa irin ta al'adar mutanen Gombe. Nenne ta dago ta daga gaisuwar “ina wuni?” Don ba haka ake gaisuwar al’adar Ilorin a gidan ba. tace a ranta coaching na musamman zata soma yiwa Siddiqah akan ala’adun gidan. Baba Engnr. na observing komai na Aisha a fakaice, sai ya tuna da sanda aka kawo masa Nenne Sappa gidan sa a matsayin matarsa, haka take ‘yar tsurut kamar Aishah duk ta rikice a cikin danginsa Yarbawa, lokacin itama bata wuce girman Aisha din ba sai tsantsar kyau irin wanda mazan Yarbawa ke matukar so daga matan Fulani (kyau da farar fata). Dade ya tambayeta makaranta, ajinta nawa? A hankali cikin nutsuwa da sanyin murya Siddiqah ta gaya masa aji shidda wato ajin karshe zata shiga da zarar an koma hutun nan. Dade bai jima tare dasu ba yayi musu sallama cewa zai fita kuma zai kai dare bai dawo ba kada su jira shi cin abincin dare. Waziri Idrisu ya fita da gamsuwa sosai da zabin da Nenne Sappa ta yiwa Prince Abdulrasheed. Zai iya cewa shigen nasa zabin ne da mahaifinsa Sarki Abdulrasheed yayi masa. Banbancin shine Siddiqa ba ‘yar sarauta bace ba ‘yar kowa ba. Bai san yaya akayi ba zuciyarsa dari bisa dari tayi na’am da zabin matarsa “Aishah-Siddiqah Yunus”, ta zamo musu suruka, mata ga tauraron zuciyar zuri’ar Akanni’s kuma tilon Dan sa namiji a duniya Prince Abdulrasheed (Kehinde). Firdausi ce tayi waya kitchen wa Femi, shugabar kukun gidan bakidaya, inda ta ce mata maza a shirya abinci yanzu, Nenne nada bakuwa daga Gombe tun zuwansu bata ci abinci ba, Nenne ta raka Dade har ma’adanar motocinsa ya fita, sannan ta dawo ta tarar Firdausi ta saka an shirya musu abincin rana a dining. Don haka ta hutar da ita wucewa kitchen wajen su Femi, ta dawo ta samesu a ‘dining area’. Princess Firdausi ita ta jagoranci Siddiqa zuwa ‘dining room’ dinsu. Bayan ta fito daga wankan data sata tayi. Ta bata sabuwar doguwar riga cikin kayan da niece dinsu Kiki ta bari a gidan tace ta saka kafin a wanko nata, ganin cewa Siddiqah bata fice sa'ar Kikin ba, tsayinsu ma zai zo daya da Kiki, kiba kawai Kiki Ruqayyat ta fita. A idon Firdaus sai taga kamar duk kayan Siddiqa masu datti ne. Don haka ta hada duk kayan da Siddiqah ta zo dasu tace Femi ta tafi dasu BQ ta wanke ta goge mata kayan bakidaya sannan ta dawo dasu, tace da ita da fulatanci “duka kayan naki ba guga ba saiti”. Wannan abu bai yiwa Aisha-Siddiqa dadi ba, don harda kayan sallahnta na bana a ciki, sauran kuwa duk kure adakarta ne atamfofine masu kyau da daraja daidai karfin Ummanta, cote d’voire ce da glitter da kuma atamfa ‘yar Ghana, amma sarkin fi'ilin gidan wato Princess Firdausi tace basu da saiti ba karin guga bayan sunfi wata uku a wanke a goge a kasan akwatinta na gida, tana makaranta shiyasa ba wani sawa take yi ba. Amma maganar da Firdausi tayi da fulatanci maimakon Yarbanci yasa taji dadi bat ace komai ba tunda Dade ya hana Firdausi da Fatima yin Yarbanci a gaban Siddiqah ganin yadda take muzanta in ana yi, sai suke yin turanci ko fulatanci, don da gaske Hausa bata wani zauna a bakinsu ba, don haka taji sanda Firdausi ta ce da Femi a kaisu BQ a wanke a goge, sai akayi sa'a ‘yan maganar Siddiqah basa kusa bata ce abar mata kayanta ba yadda taso fada tayi shiru, suka wuce zuwa dining tana bin bayan Firdausi. Nenne ta nuna mata kujerar gefen damanta tace ta zauna, haka ta zauna a dofane, ta ga ma’aikatan kitchen din wadanda duk mata ne dake kai kawo a gabansu suna aje akusan abinci duk tumatuman yarbawan Lagos ne, suna aje abubuwa suna juyawa suna kada bombom suna badeta da warin jikin yarbawa. Ko motsi wannan da kyar Aishah ke yinsa a ‘dining room’ din, don ita kam tasha jin ance jikin yarbawa body odour dinsu daban ne dana hausawa ba tun yau ba, ga Nenne ta cika gida dasu sune duka hadimanta ba bahaushe ko bafillace ko daya, ta riga ta saka ma ranta duk Bayerabe nada warin jiki daya banbanta dana hausawa da fulani, shiyasa har zuwa lokacin a darare take dasu kuma a kyankyame, ita dai a ranta kawai so take ta bude ido ta ganta a dakin Ummanta a lungun Jeka da fari, amma abu ya gagara, don haka ta zama rakumi da akala sai yadda Princess Firdausi tace tayi kawai take yi bata umh bata umh umh. Duk bakin nan na Aisha ya kama kansa a gidan Engnr. Idris Akanni musamman data lura babu hayaniya a gidan sam. Wannan abincin dai da aka zauna cinsa tare da Siddiqah, wadda a rashin saninta ta zauna ne a kujerar da Prince Abdulrasheed ke zama gefen a Nenne, kasancewar kujerun dining din a kirge suke iya jama’ar gidan kacal, sai ko ta Hakeem da Kiki ‘ya’yan Taiwo, wadanda suna cikin iyalin gidan, ko kwakkwarar loma uku Siddiqah bata yi ba, ta fada a ranta ita bazata iya cin abincin da tumatuman Yarbawan nan suka girka ba. dama dai Nenne ce tayi shine zata ci. Ta san yarbawa suna cin dodon Kodi da Qaguwa (shrimps). Duk yunwar data ke ji haka ta hadiye abarta, data tuno Dodon kodi da Qaguwar da yarbawa ke ci a cikin abincinsu, ta na juyawa kuwa ta yi ido biyu da Fatima ta cako katuwar shrimp da fork ta kai bakinta, tana shirin kurbar ruwa a tambulan don toshe yunwar dake addabarta wanda ba abinda yake mata sai kara kulle mata ciki, duk idanunta sun fada cikin lungu, Fatima na tauna ‘shrimps’ dinnan cikin taunarta ta gayu da yanga Siddiqah ta ji ta kware jikake “kat!” Da ruwan data ke sha, amai kuma ya zo mata gabagadi. Da sauri ta kai tafin hannunta ta toshe bakinta, idanunta fal! Kwallah! Dukkansu ba wanda ya lura cewa bata cin komai sai Nenne, ba kuma kowa ya lura da halin takura data ke ciki a a baka da zuci ba sai Nenne, wadda duk wani motsinta tana ankare ta gefen idonta har aman
Chapter 4 · 0% Book details