← Book details Aisha Siddiqa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 27

Sashe 21

Aisha Siddiqa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Itama Siddiqah ta tsorata sosai da jin halin da Nenne ke ciki. Tuni ta fara mata addu’ar duk da tazo bakinta. Sanda suka isa asibitin Nenne ta sha allurai ta samu barci mai nauyi amma bata san wanda ke kanta ba, motsin da bakinta ke yi ya nuna salati take yi da hailala wanda daman baya rabo da bakinta koyaushe. Gari na kara wayewa likitoci sun gama shirinsu na shigar da Nenne tiyata. Dade yayi shahada kan ba yadda zai yi yasa hannu, aka wuce da ita dakin tiyata. Shi da Siddiqah suka koma suka zauna a dakin da aka bata, kowannensu yayi tagumi da hannu bibbiyu yana kissima irin girman rashin da zaiyi, it will be (irreplaceable loss) rashin Nenne a tare dasu. Idan Nenne bata fito da rai ba, dukkansu rayuwarsu ta durkushe suna addu’a suna kuma hawaye, Siddiqah har da kuka wiwi amma Dade ko umh bai iya yace mat aba balle ya lallasheta shima fama yake da kansa, da zai iya shima fashewa da nasa kukan zaiyi yadda ta yi ba kananan hawaye ba amma dai ya jure yanata hailala da carbinsa yana tsane ruwan ido. **** **** **** Koda Dade ya kashe masa waya. The Prince was shocked, hankali a tashe ya zubar da komai da yake yi a lokacin, yanada tournament din da zai halarta swannan satin a Argentina amma ya kansile shi nan take, haka yayi ta kansile duka scheules dinsa na sati yana bada excuse, ya soma neman jirgin da zai kawo shi Lagos ido rufe. **** **** **** Sosai Siddiqah kewa Nenne addu’a kafin fitowarta dakin tiyata da carbin da da Dade ya ciro a aljihunsa ya mika mata, yace tayi masa shiru haka, kafin isowar Femi da kayan karin kumallon su. Amma ko kallon kwandon abincin babu wanda ya iya yi a cikinsu, kuma Dade ya ki kiran kowa nashi daga Ilorin ko nata daga Gombe don ya sanar da su, don yasan da ya fada za azo a cika asibitin. Ya dai kira Fatima da Firdausi yace su bar bikin su dawo gida maza-maza. Bai kuma basu damar tambayar ba’asi ba ya kashe wayarsa amma sun tsinkayi damuwa a muryarsa. Wajen karfe sha biyu na rana aka fito da Nenne daga theatre room. Cikin ikon Allah an yi aikin lafiya, an cire stones and cyst, aka kawo abubuwanda aka ciro din aka nuna wa Dade, Dade sai hamdala yake yana godewa Allah, Siddiqah ta rungume hannu a gefe tana hamdallah, aka fito da ita tana barci akan gado aka gungurata zuwa dakin hutu. Sai lokacin Dade ya samu ya fita ya tafi gida don ya dan kintsa, ya bar Siddiqah tana jiran farkawar Nenne. Ta sakata a gaba, motsi kadan ta gyara mata rufa. Amma an tabbatar musu komai lafiya lau, nan da mintuna talatin zata iya farkawa. Kona minti daya Siddiqah bata dauke ido akan Nenne, fatanta dai Nenne Sappa uwar alkhairi ga al’umma ta farka cikin koshin lafiya don ita tafi yarda zaman Nenne take a gidan, ba zaman kowa ba. Wato ta fi yarda cewa ta zowa Nenne hutu ne gidan ta a Lagos, kamar yadda aka fara tun farko. Ita kadai ta sani, da ita kadai ta saba a cikinsu. Bata san wani Hamma, bata addu’ar ta san shi nan gaba. Ta kuma yarda cewa Nenne Sappa mai kaunarta ce, ba saboda dan ta ba sai saboda amincinta da mahaifiyarta. Ita da Haj. Zainab Allah ne kawai yaga dama ya hadasu zumunci a dakinsa mai alfarma, don su abokantaki juna ba don ajin rayuwarsu ya zo day aba, sai don halayensu da suke kusan daya, na kaskantar da kai, tsoron Allah da yawan tawali’u (down to earthiness). Don haka lokaci-lokaci inta kalli Nenne ta tuno abubuwanda aka ciro a cikinta wadanda aka ce sun dade suna wahalar da ita har share hawaye take sake yi da gefen hijabinta. Aka turo kofar cikin wata irin nutsuwa kamar ansan mara lafiyar barcin allurar anaesthesia take yi. Wani dogon ingarman mutum ya bayyana a gaban Siddiqah. Shi ba fari bane ba kuma za’a kira shi baki ba. In fact, kalar fatar jikinsa rarely kaga mai irinta a kusa, domin mai wuyar samu ce a cikin al’ummar Afrika ta yamma. Gashinan dai ingarman gaske, ma’abocin fadin kirji da kasaitar tafiya. Sannan akwai kamala da nutuwa ta ban mamaki. Sallamarsa cikin wani accent mai dadin ji da zakin sauraro. Kai tsaye bazaka iya gane ko wane yare ne hakikanin harshensa ba. Domin accent din sallamar yafi kama dana Fulanin da basu kware da Hausa ba tsantsa. Yana sanye da ‘casual wears’ na wani tsadadden yadin Filtex ruwan makuba, wadanda da gani babu tambaya zaka fahimci masu matukar daraja ne a inda ake amfani dasu. A kafarsa bakin takalmi ne sau ciki samfurin Raul Burgundy (Black Italian Leather Loafers). Idan kana neman perfection na rayuwa to ka gama samunsa a wannan mutum mai shigowa, dauke da sassanyar sallama a siririyar fatar bakinshi, wadda gashin bakin nan na (man’s pride) yabi ya zagaye har kasan habarsa inda ya kwanta sosai akan habarsa. **** **** **** Siddiqah bata dauke ido a kansa ba har ya zo daidai kan Nenne ya tsaya, hancin ta ya shako mata wani ni'imtaccen turaren maza na “Boss Intense” har bata san lokacin da ta ja numfashi ta aje ba. Ko lura da ita bai yi ba, don gabadaya hankalinsa yana kan Mamansa. “Here comes THE PRINCE!” Zuciyar Siddiqah ta ta gaya mata cikin whisper. Alhalin har yatsun kafarta kakkauran takalminsa ya dan taka mata kuma ta ji zafi da radadi, amma da yake hankalinsa baya jikinsa bai lura ba, kacokam hankalinsa ya dauku kan mahaifiyarsa dake kwance saman gado, baima kula da ya dan taka yatsun mutum ba, yama dauka inuwar daya cikin twins ce a zaune gaban Nenne. Sai ga Nenne ta bude ido a hankali bayan ta shaki turarensa, kamar tana jiran isowarsa kafin ta bude ido, sai idanunta cikin na Abdulrasheed. Prince yasa tausasan yatsunshi ya damke hannun Nennensa sosai, yana fadin "Nenne please don’t leave us..... gani nazo. My Nenne get well soon I beg you, duk abinda kikeso zan yi, koda barin Polo ne dungurungum, na rantse in har yanzu ba kya so daga yau na daina! Na kuma dawo gida kenan!!". Nenne ta lumshe ido ta bude, ta tabbatar Abdulrasheed ne a gabanta, ba cikin mafarkinsa take ba, yadda yayi ya zo haka cikin gaggawa shikadai ya sani. Ta damke hannunsa itama cikin nata, ta nemi ciwon da take ji ta rasa, tana kokarin juyawa idanunta suka fada kan Aisha-Siddiqah. Wadda ta ja can gefe ta tsaya duk ta sha jinin jikinta cewa Prince Abdulrasheed ne. Siddiqah ta sunkuyar da kai, lokacin da Nenne ke yafitota da hannunta da Prince bai rike ba, ko dagowa kasa yi tayi, don jikinta ya gama bata. Hamman gidan ne ya iso. In ka lura zaka ga yadda jikin Aisha ya dan dauki rawa da ‘yar karkarwa. Nenne ta juyo saitin da take tace Siddiqah matso nan kusa dani. Ga Hammanku kingan shi ya zo!" Da hanzari Siddiqah ta dago, anyi sa’a shima Prince ya dan cira ido ya dubeta. Suka hada ido. Siddiqah taji gabanta ya fadi, shima kuma Prince haka yaji. Saboda nauyin igiyar aure ba wasa bane. Amma dai Prince ya dake ya cije faduwar gaban data sameshi a lokacin tunda baima santa ba. Da kailula Siddiqah ta iya cira kafa ta isa ga Nenne, ta tsaya a gefen Prince suka jeru gaban Nenne, jikinta har lokacin bai daina bari ba. Abdulrasheed ya juyo gefensa a hankali yana kallon bakuwar fuskar mai jinyar mahaifiyarsa wadda Nenne ta kira da suna Siddiqah. Wadda da farko sabida rudun da yazo a ciki, tun dazu ya dauka Firdausi ce a zaune a gefensa. Sai ya juyo gareta sosai, ya bude manyan maganansa masu salki da haske da wani irin sheki na musamman a cikinsu, yana kallon bafullatanar yarinyar. A idonsa bata fice sa'ar Kiki ba. Idonsa ya gano masa tarin kuruciya da innocent looks irinna Kiki a fuskarta. Amma cikin dangin Nenne kaf bai santa ba. Nenne bata bashi damar gama tunanin inda ta samo yarinyar ba ta soma shaquwar dake bukatar ruwan Sha, irin na wadanda aka yiwa CS. Don haka da hanzari da zafin nama Prince ya durfafi firjin dakin da saurinsa. Amma ko kafin ya juyo... Siddiqa sarkin zafin nama ta rigashi da nata irin zafin naman, ta dauko robar ruwan Faro akan lokar gado ta bude ta kafa ma Nennne a baki. Saida ta sha sosai ta koshi shakuwar ta lafa mata sannan ta dauke robar daga bakinta, Nenne ta koma ta kwanta ta rufe idanunta a hankali ta barsu. Dade ya murdo kofa ya shigo dakin. Ya tadda Prince da Aisha sun kafa ma Nenne ido, kowanne da gorar ruwan Faro a hannu. Siddiqah ta manta yadda ake gaisuwa sakamakon nauyin igiyar aure na wannan bafillacen sardidin bayerabe dake tsaye gefenta da yazo nan take yayi mata dabaibayi, ta san dai ana gaida babba a ko’ina aka ganshi, Ummanta tayi mata wannan tarbiyyar, amma ta rasa dalilinta na kasa gaida Hamma Prince. Shigowar Dade dakin ne ya ceceta domin ya bata damar shaqar numfashin da ya kasa ratsa huhunta yadda ya kamata tun dazu, sakamakon inner feelings na wanzuwar Prince a wurin da take ji a ilahirin jikinta. Aisha tayi ta maza ta amsa sallamar Dade idonta a kasa, muryarta na dan shakewa. Sai taga kawai bari tayi amfani da wannan damar ta fice daga dakin, zai fi mata sauki fiyeda cigaba da tsayuwar rashin sakewa kusa da Prince, ta kama tafiya ta nufi kofa da zummar fita reception na asibitin ta zauna, ko ta samu damar jan numfashi ta koshi, kuma ta basu dama su gaisa sosai shi da mahaifansa. Amma sai Dade yace “yaki Aisha, zo nan ki gaida Yayanku Abdulrasheed kinji, sai kije Seun yana waje ya kaiki gida ki yi wanka da sallah ki huta, ki ci abinci don nasan rabonki da abinci tun jiya, tunda ga Abdulrasheed ya zo, shi sai ya karbe ki jinyar. Zuwa dare sai Seun ya dawo dake ki kwana shi ya koma. In kuma su Fatima ma sun iso kan magariba kina iya zamanki a gida sai gobe da safe kya
Chapter 21 · 0% Book details