← Book details Aisha Siddiqa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 27

Sashe 26

Aisha Siddiqa Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

cikin kwantar da murya. “Kiki ki dinga addu’ar neman zabin Allah kin ji? Don’t be obsessed with him, ki bi mahaifiyarki akan duk abinda takeso wallahi zaki ga alfanu a gaba. Kuma ko a kan son da kika ce min Uncle dinki na yi miki zaki iya yi masa solidarity ki jikirta baiwa zuciyarki abinda take so kamar yadda Mum take so sabida shi, da gaske baza taso ki yi aure ki haihu alhalin shi bai yi ba, baki son soyayyar twins ga junansu bane musamman in opposite sex ne (mace da namiji). Nima bana son zaman gidannan, bana son zaman Lagos at all, amma yana iya? Dole na yiwa iyayena biyayya kuma ina kan yi. Na san ko bajima ko ba dade zan tsinci wannan biyayyar dana yi musu a gaba ko a kan ‘ya’yana ne. Ke kinji dadi ma kina tare da ita har gobe (mahaifiyarki) an kuma barki kin gama karatu kafin ayi miki aure kuma ga dukkan alamu wanda kikeso za’a barki ki aura …..”. Sai bayan ta fadi hakan ta tuno cewa ta saki layi. Kiki bata san wacece itaba har yau a gidannan. Bai kamata Kiki taji daga gareta cewa tana da auren Uncle dinta daga bakin ta ba, idan har Nenne da Aunties dinta babu wanda ya ga dacewar ta sani din ita akan me zata fada? Amma ina! Aka ce magana zarar bunu ce ta riga ta fita, ta kuma shiga kunnen Kiki-Ruqayyat. Kiki tayi dan jim, kafin tace. “Kina nufin kina da aure? Ko kin taba yi kenan sister Aisha?” Ta girgiza kai da sauri tana cewa “Kiki chapter closed, kiyi ta istikhara kina addu’a idan Tosin rabonki ne, kuma akwai alkhairi a tarayyarku, Allah ya kawo auren Uncle dinki kurkusa kamar yadda Mum keso, idan hakan ne kwanciyar hankalinta. Kada kimanta kullum tafi Tosin muhimmanci agareki”. Kiki ta ja numfashi tace “Sister Aisha, my Mum is annoying, wadda take so Uncle ya aura fa ba wata bace Aunty Haseenah ce, his ex Haseenah Ambursa, koda yake ya so ta acan baya, amma wallahi yanzu baya sonta, ban dai san abinda ya raba su ba amma anfi ten years da rabuwarsu, rana daya naga ta dawo jikin Mum dina sun koma shiri, ni nafi Mum sanin Uncle dina, bakina da nasa yace min shi matansa Hurul eeni ne suna aljannah, me Uncle zai yi da Haseenah yanzu? Don kawai ya taimaketa? Tsintacciya ce fa as in ‘yar gidan marayu bata da iyaye shiyasa Nenne bata so. “Ho Kiki! Shafa labari Shuni!” Duk da Kiki bata san me kalmar shafa labari shuni ke nufi ba, ta san yana nufin dai kamar ta faye surutu ko fadi ba’a tambayeki ba. Ta hau dariya tana cewa “da gaske nake duk abinda na gaya miki ni bana karya, ke nafi ganin dacewar Uncle ya aura kuma zan je har Qatar in sameshi akan hakan”. Siddiqah tace da karfi “Kiki! Ni nace miki banida wanda nake so toh? Ba kyau cin naman mutane ki daina zancen wata budurwarsu. Is better you mind your business Kiki, ki rabu da sa damuwar kowa a ranki. In Allah yayi matarsa ce tunda Mum naso, sai kiga anyi”. Kiki tayi maza tace “ba amin ba! Because my Uncle has a pure heart, I assure you he’s pure and clean, with a golden heart! Allah bazai bashi mace wadda ba mai tsarkin nasaba ba. Bazai taba auren mara asali ko lalatacciya ba in sha Allah”. Amma ko bayan gama wayar su da Kiki, Aisha sai tayi jimm! Tana jin maganganun a ranta. Ashe shiyasa bata samu reception a wurin Aunty Taiwo ba, akwai wadda ta dade da yiwa dan uwanta tanadi. Banda haka bata ga me tayi mata ba da ko gaisuwarta sama-sama ta amsa kuma a shaqare. “Umh! Su suka sani” inji Aisha. Babu wani Bayerabe data saka a ranta balle damuwarsu ta dameta. Sati biyu bayan nan su Aisha suka fara zana WAEC, wadda zata dauke su tsayi sati hudu suna zanawa. Watarana Siddiqah ta fito dakin jarrabawa ta tadda Seun yana jiranta zai dauketa zuwa gida, suka kamo hanyar gida, sai taga Seun ya karkace kan motarsa ya tafi wani wurin da ita. Saida suka isa wurin ta fahimci ko’ina ne, wata ma’aikata ce ta shige da fice a jihar Lagos (immigration office). Da ta tambayeshi ko’ina zasu je yace “tayi hakuri Dade zai dauka. Suna isa ta hango dade a nesa yana jiransu, sai ya karaso jikin motar tana kokarin fitowa cikin girmamawa don ta gayar dashi, yace ta biyoshi zuwa ciki. Tare suka shiga ciki yasa aka mata hoto da finger-print. Seun ya dauko su zuwa gida gabadaya. A kan hanya Dade na tambayarta yaya jarrabawar tana gaya masa ita bata da matsala har suka iso gida. **** **** ****
Chapter 26 · 0% Book details