← Book details Aisha Siddiqa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 27

Sashe 12

Aisha Siddiqa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ROUQAYYAT-KIKI
K
iki (Ruqayyat) zuwa yanzu an zama manyan ‘yanmata, shekafun ta zasu kai sha bakwai da watanni tara. A bana ne ta kammala karatun sakandire. Can na hangota cikin shiga ta alfarma ta ‘ya’yan gayu amma kuma wadda bata nuna tsiraici a tare da itaba, irin dai shiga ta yaran musulman Yoruba, rashin saka lullubi ko a kafada aka ya nuna ita din ba cikakkiyar bahaushiya bace, cikin wani hamshakin supermarket take shawagi a (Santa Monica) din birnin Los Angeles.
Dana leka kwandon da Kiki take sayayya a ciki sai na ga cewa kanta take zabar ma ‘brazier’ da ‘panties’ da ‘undies’ da kuma ‘nighties’ ‘yan ubansu-ubansu, kasancewar a gobe ne zata koma hutu na farko gida Ilorin, tun bayan zuwanta kwas din Computing a Los- Angeles, sai wani tunani ya fado mata, kasancewar kome take yi Uncle AK baya barin ranta.
Mai zai hana tayiwa Kawunnata gudunmuwa dasu shima idan aurensa ya tashi ya baiwa matarsa? Sabida a idanunta nighties dinnan da undies din duka unique ne, da kyawunsu da tsadarsu ya kai ya kawo. Kiki na nan ‘yar lukuta haka duma-duma kamar buloras, doguwa mai garin jiki kamar na mahaifiyarta, Taiwo.
Da ‘yan yatsunta da suka sha adon bangles da zobban zinare ta latsa tsadaddiyar wayar hannunta wadda Uncle AK dinne ya mallaka mata (yadda take kiran Prince har inda yau ke motsi watau Uncle Abdulrasheed Kehinde) a ranar da yazo bikin graduation dinta na sakandire daga ‘Greensprings School’ dake jihar Lagos, alkawari ne da ya dade da yi mata cewa sai ta kammala secondary school da kyakkyawan sakamako sannan zai mallaka mata wayar hannu kuma a ranar ya samu ta cika shi. Musamman kasancewar Kiki tayi kokari sosai a jarrabawarta.
Yana kwance cikin ‘sofa’ a ranch house dinsa atsakiyar babban birnin kasar Argentina, a jiya yazo kasar daga Qatar wani babban tournament.
Dawowarsa kenan a matukar gajiye ko Polo Helmet din kansa da chukka boots din kafarsa da socks bai samu ya cire ba. Da chukka boots da safa da komai dake jikinsa ya fada akan Sofa-bed din, yana matukar son zuwan su Nenne a satinnan kafin lokacin tafiyarta aikin Hajjin bana yayi, don ya jima shi bai je ba. Idan kuwa har yayi irin wannan jimawar bai je gida ba irin haka Nenne kan tarkato kan kannensa Princess Fatima da Princess Firdausi, da ‘ya’yansa Hakeem da Kiki su zo su yi masa sati.
Daidai lokacin yana tunanin mikewa don wucewa bedroom dinsa yayi sallah, ko ya samu yayi barci sosai, ya huta gajiya don rabonsa da barci tun daren shekaranjiya wato kafin su fara tournament din da ya kawo shi, wayar ‘yar rigimarsa Kiki ta shigo masa.
Da kyar ya mika hannu ya daga idanunsa a lumshe saboda gajiya. Amsawar kawai yayi cikin dushewar murya ba tareda yace mata komai ba.
Tace “Uncle AK size nawa zan daukar mata na backward da frontward?”
Abdulrasheed ya yunkura ya mike zaune cikin yamutsa fuska yace “Kiki! Where are you now? What sheet are you talking about?”
Kiki ta rangwadar da kai gefe irin na yaran da ke jin duniya akan tafin hannunsu tace “Uncle AK, lefe zan fara hada maka, in duba wata hadaddiyar Baby haka anan ajinmu in yi mata tallanka, Uncle nagaji da ganin ka kai kadai a gida, Uncle nagaji da ganin ka a cikin Dawakai ba ‘ya’yan ka ba”.
Idanun Abdulrasheed suka dan bude kadan don mamaki, har an kawo wannan lokacin da ‘yar cikinsa ma ta damu da rayuwarsa har haka, da kyar ya iya ya hadiyi miyau, yace.
“Kiki are you alright? Ko kin fara shaye-shayen zamani ne?”
“Allah ya sani ban sha komai ba. Mamana ta hanani sauraron samari saboda kai, ina dalili? Akwai BF dina dana ke matukar so Mama ta hana ni ko magana dashi wai sai kayi aure, rannan fa cewa tayi wai bana jin kunya in shige gidan miji in barka a zaure?” Kiki ta karasa harda kirkiro ajiyar zuciyar damuwa, yadda take maganar kadai zaka san bilhaqqi take yinta cikin gabunta.
Wata ajiyar zuciyata subucewa Prince, shikansa bazai iya tuna rabonsa da yin irinta ba, in ba yana magana da Kiki ba baya tuna yawan shekarunsa. Ita kadai ke iya saka shi dariya a kowanne lokaci koda bai shirya ba.
“Idan na fahimceki daidai Kiki, kina so in yi aure ne don a baki dama kema kiyi aure?”
Kiki tasa hannu daya ta rufe ido daya tana dariya don kunya, kamar Abdulrasheed na ganinta, shikuwa kallon mamaki yakewa kan wayarsa, har yaushe ‘yar cikinsa Kikin da yake sawa ‘diaper’ ta girma haka?
“Alright Kiki, nina tsufa da aure, zan wa Taiwo magana kada ta kara fadin haka gareki. Ta baiwa mai kaunarki dama ya iso gida. Kiki har kayan dakinki na gama hadawa suna nan kulle a gidana na Qatar.
Kuma ni zaki fara kawowa boyfriend dinki din kafin kowa. Sai nayi na’am dashi zaki kaishi ga Daddynki. Yaya sunanshi?”
Don farin ciki Kiki kamar bakinta ya yage don murmushi tace “You know I love ko Uncle AK? Nayi alkawarin bazan taba sauraron saurayi ba sai kayi aure? Sunansa “Abdul-Nasir Oluwatosin”.
A kwance Prince yake amma bai san yaushe ya tashi zaune ba. ya rike wayar hannunsa sosai yace “Tosin Abdulnasir, a footballer?”
Kiki ta gyada kai tana jin kunya, kamar Uncle AK yana kallon idonta. Shi kuma yace “Kiki iyayenmu bazasu taba bari ki auri footballer ba, sai dan sarauta, ni nasan iyayenmu sarai, ki cire ni a gefe kan batun aure. Maybe your Uncle is not destined to marry in his life. Amma akwai mata fal a aljannah ai kin sani ko Kiki? They are called hurul’eeni, who knows ko mata na hudu suna cikinsu?
Don haka ki daina damun kanki a kaina kinji. If you really-truly love this Guy, I will stand by you Kiki. AbdulNasir was a football celebrity. Me ya hada ki da dan ball? A ina kika hadu dashi?”
Kiki ta labarta masa haduwarta Tosin AbdulNasir sun je kallon wasan da Inter-Miami tayi da LA Galaxy a California itada kawarta Badriyya.
“Amma Kiki ban hanaki bin kawaye yawo ba? Ban ce daga makaranta sai makaranta ba? wato har kallon ball kike zuwa?”
“Kayi hakuri Uncle AK, wallahi ba inda nake zuwa banda shopping, ranar ma Badriyyah ta matsa muje ne don taga AbdulNasir a fili, tana matukar son wasansa, na gaya mata ka hanani zuwa ko’ina, tace daga ranar bazasu kara zuwa yin wasa Los-Angeles ba, and she don’t want to miss seeing her favourite footballer in reality (bataso ta rasa ganin dan ball din data fi so a fili), sai na yarda muka je, tun a ranar ya nuna kaunarshi gareni muke waya, ban taba gayawa kowa ba sai Mama, shine ta bani waccan amsar cewa bazan taba sauraron kowa ba sai kayi aure”.
Abdulrasheed yayi ajiyar zuciya ya ce “Kiki count me out kinji? Bani lambar yaron kuma ki bar ni da Taiwo”.
Kiki ta dage itafa bata so itama, in Abdulrasheed naso tayi aure ko ta saurari maso sonta to ya barta ta hada masa lefe.
Dariya yake yi a yanzu. Yace “Kiki! Daga hada lefe sai me? Na baki dama kiyi tayi. Kudi ne dake. Ki sayi kome kike son saya kiyita tarawa gaibu, amma bada kudina ba bana cikin shirme kinji?”
“Yo dama Uncle ai ban ce ka turomin ko sisin kwabonka ba. Zai zama cewa tawa gudunmuwar kenan ta aurenka, saya maka akwatin (undies and night wears) dinta. Kawai cewa nayi ka gayamin frontward and backward size din matar ka”. Kan Abdulrasheed ya shiga duhu da shirmen Kiki, yace “meye kuma front and back?” Kiki ta hau dariyar shakiyanci sabida yadda Uncle Prince yayi maganar cikin yamutsa fuska dole ya baka dariya tace “brazier da panty dinta nake nufi, gani gaban wasu masu azabar kyau, amma bansan size dinta ba”. Da karfi Prince yace “Kiki! If I don catch you….” tayi maza ta kashe wayar don kamar zai fasa kunnenta da ihu. Itama ta san da a kusa suke yau ko Taiwo bata isa kwatarta hannun Uncle ba, in ya murde kunnenta.
Ya kashe wayarsa yana fadin “Oh my God! Kiki ta girma, har ta fara raina shi, don ya maida kansa abokinta.
Ya koma ya kishingida, amma barcin da yake so yayi yaki zuwa sam. Sai juyi yake gefeda gefe akan sofa-bed, maganar Kiki ta jefashi cikin wani yanayi na begen yayi auren don yasan yana missing wata rayuwa da bait aba shiga ba har shekarun girma suka riskeshi, sai kuma bacin rai ya biyo baya da wani tsohon tunani y gilma masa…
A can baya shekaru masu dama da suka gabata ya taba sayawa Haseena brazier da Panty da hannunsa, itace da bakinta ta gaya masa size tace ya sayo mata, a lokacin ne ma ya taba sanin wani abu brazier, da wannan tunanin dana kadaitacciyar rayuwarsa wadda bai nemi komai ya rasa a cikinta ba sai macen aure kadai, alhalin yanada tabbacin cikakkiyar lafiya ta kowanne dan adam a tare dashi, idan kuma by now ya rasa mazantakarsa ne duk ba mamaki, watakila yawan shekarunsa yasa ya rasa feeling na manhood dinma gabadaya, har gashi ‘yar da ya haifa ta isa aure, da wannan tunanin mara dadi kuma mai sosa zuciya barci mai nauyi ya dauke shi.
Yana fadawa ransa da zuciyarsa cikin barcin da ya debe shi mara dadi, mai wani irin nauyi; hatta matan aljannah (hurul eeni) in aka bashi zai ce baya so! Ko kuwa yace ya yafe!! He is not destined to experience that kind of life!!
**** **** ****
Chapter 12 · 0% Book details