← Book details A Gidan Haya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 30

Sashe 9

A Gidan Haya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cewa yayi."Lafiya lau ya jikin."?cewa tayi."Da sauki Baba."dafa koshinta yayi sannan yace."Allah ya baki lafiya."kallon Mama yayi sannan yace."Maman Rumaisa gobe Insha Allah ki kai ta chemist din Bala ko allura yayi mata muga yanda hali zaiyi."cewa Mama tayi."to shikenan Allah ya kaimu goben Lafiya." "Amin ya Allah."
*********************
Fadil ne ya shigo part din Hajiya maryam, zaunawa yayi ya fara gaida Mahaifiyar ta shi sannan yace."Umma." kallon shi Umma tayi sannan tace."ina jinka, lafiya."?Sosa
eya yayi sannan yace."Eh to Umma, amman kinga duk yau Rumaisa bata zo ba, Allah yasa lafiya."Murmushi tayi sannan tace."Amin ya Allah, nima abunda nike tunani kenan, abunda Rumaisa bata taba yi ba, in bata zo yau ba,
gobe sai muje muga ko lafiya."cewa yayi."To shikenan Allah yasa dai lafiya."cewa tayi."Amin tashi kije ki kwanta dare yayi, nima sai da safe."
Cewa yayi."ok Umma byeee tooo."
_*Ina masoyana suke
masoyan yar'mutan kankia, wanda suke fadin yar'mutan kankia itace tauraruwa a social media, nice dai yar'mutan kankia wanda ta kawo maku NANA JAWAHEER, karku manta irin soyayyar da aka sha da Sadiq da Nana, sannan kuma ta sake kawo maku shahararrin litafin nan nata wato GIMBIYA HAKIMA inda aka zuba soyayya Hakima da Hakim, sannan kuma ta kowo maku SANADIN LINK, inda Sofy ta canca
a soyayya da Aliyunta, ba tayi
asa a gwiwa ba tazo ta kawo kamu IZZAH KO MULKI, inda kukaga yanda ake mulkin zalinci, sannan kuma kuka ga yanda ake makirci iri iri, ga ban tausayi dai dau abubuwa a cikin Izzah ko mulki.*_
_*Yanzun kuma take kawo maku A GIDAN HAYA, wanda A GIDAN HAYA aka fara wasan dan ko ba'ayi komai a cikin shi ba
, uwa uba kuma ga SADAUKIN BURHAAN, wowowoho!!!!

SADAUKIN BURHAAN kenan karku manta cigaban Izzah ko mulki ne, inda zakuji ina Sadauki yaje?

Wata kallar fansa Sadauki zai dauka?

Abubuwa da dama fa
, To Masoyana anan zaku nuna man soyayyar da kuke cewa kuna yi man, domin ku masoyana, zan baku GARA
ASA!

GARA
ASA!!

GARA
ASA!!!

Daga yau 10/9/2020 zan sakar maku da Sadaukin Burhaan akan naira 200kacal, karku manta naira 300 nasa shi to duk domin ku masoyana mai doshi 200 daga yau tara ga wata zuwa ashirin da
aya ga wannan watan na satuba 31/9/2020 an single kenan, yan vips kuma nai maido maku shi akan naira 400,karku manta daga yau 9 ga zuwa 31 ga watan September din nan insha Allah.*_
_Wata GARA
ASAR kuma masu bukatar karanta Izzah ko Mulki yanda zasu ji dadin karanta Sadaukin burhaan su fahimci ida labarin ya dosa zaku bada naira 100 kacal ba baku document din sa, kunga kenan idan single ki saya Sadaukin burhaan zaku bada naira 300 duk da Izza ko mulki, idan kuma sadauki kawai kike bukata zaki bada dari 200 kawai, idan kuma vips ne zaku bada naira dari 450 duka biyun kenan sadauki da izzah ko mulki idan kuma sadauki kawai kike bukata zaki bada naira 400 kawai
Masoyana karku manta tana nan ne kawia zaku nuna man kaunar da kuk cewa kuna ma NOVELS dina, sannan kuma Hausawa sunce sayan na gari mai da kudi gida
, ina maraba daku MY GUYS
*Yar'mutan kankia ce
Share
Comment
Vote
And
Like
A GIDAN HAYA
_STORY AND WRITING_ _BY_
_Jameelah jameey_
*yar'mutan kankia ce
MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION
*M.

W.

A*
'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar
da masoyan ta.
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________________
*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*wannnan page din naki ne Auntyna, Wato BINTA UMAR ABBALE, Allah yabar kaunar da zuminci, Allah ya kara nisan kwana Aunty Bintu
Page_21&22
Har yanzun jikin Rumaisa sai dai addu'a dan tana dan jin jiki ba laifi, kwance take sai ga Mama ta shigo tace."Tashi mu tafi Rumaisa, ayi maki wannan allura ko mun dawo."kallon Mama tayi sannan tace."Wayyo Mama wallahi ban son wannan allura nike ba, dan Allah kayi hakuri kice ma Baba anyi mani kawai kinga daman ai naji sauki sosai."wani kallon banza Mama tayi mata, tana mamakin yanda Rumaisa bata san allura da magani cewa Mama tay."To bada ni za'ayi wannan rashin hankalin ba, inke baki da hankali ni inada hankali, a haka zamu sama maki ido baki lafiya amman muki baki magani, ai duk da sauki na gun Allah, amman Allah yace in baku lafiya kunsha maganin."sannan cigaba da cewa mama tayi."Dan haka tashi mu tafi tun muna mu biyu, kafin raina ya baci, Allah sai na bata maki rai."cikin irin tausayin nan Rumaisa tayi duk dan Mama taji tausayinta tace."Yi hakuri Mama yanzun zan tashi mu tafi, amman nidai tsoro nike ji sosai, bani son
wannan allura ko kadan Allah."hijab dinta Mama ta dauka ta bata sannan itama tasa tata hijab tana cema Rumaisa." Kinji dashi yar'nema, ke dai Rumaisa mijinki zai sa fama, ace mutum bai shan kagani kuma bai son allura, sai dai kawai aka ce mashi sannu ya ansawa, to ni Hadiza ba haka nike ba, dan haka tashi maza mu tafi wallahi na kusa sa maki bulala Rumaisa."tashi Rumaisa tayi tana cewa."yi hakuri na tashi mu tafi Mama."nan suka fito a tsakar gida, nan Mama tace ma yan mutan gida."To
mutan gidan nan mun tafi chemist sai mun dawo, za'ayi ma Rumaisa allura bata jin dadin jikin ta."cewa Mama A'I tayi."Ayyya Rumaisa Allah ya baki lafiya."cewa Mama tayi tana murmusi."Amin ya Allah Maman A'I."cigaba da cewa Maman A'I tayi."To Maman Rumaisa, adawo lfy."cewa Mama tayi."Allah yasa Maman A'i, A'i abincin ake ci ba'a bani, mun wuce."
Shewa Halimai tayi tana dariya tace."Allah yasa dai ba abun kunya aka dauko mana a cikin gida ba."dariya Lami tayi sannan tace." Amin Halimai nima abunda nike
tunani kenan, dan jiya cikin kunnena naji tana amai da dare, Allah ya kara ma."Hindatu ta bushe da dariya sannan tace."sai ku gaya man, bari mu fara tara kudin raggon suna, da kayan mai jego."kallon su Maman A'I tayi tana mamakin mugun hali iri na su Halimai sannan tace masu."Yanzun ku wai maiyasa baku gyale Yaya Hadiza ita da Rumaisa su sha numfashi a gabanku?Ace mutun shi kullun ba alkwari a cikin zuciyarshi sai Shari, ku baku yi mata ya mai jiki ba, amman kun sama mata ido cikin gida, kuma baku hada komai dasu ba *GIDAN* *HAYA NE* ya hadu amman kuna kishi da baiwar Allah."wata rin ashar Halimai tayi sanna tace."Wai Maman A'i maiyasa kike shiga abunda bai shafeki ba."?Lami ce ta ansa maganar tana cewa."Ke dai kyaleta Halimai, abun nan yana bani haushi sosai, ke dai bamu Sanyo ki ba cikin hidamarmu ba,amman kin sama ido a gida, wallahi ki fita a harkarmu Maman A'i muna ganin girman ki."Hindatu tace."kin dai gaya nata Lami, na lura Maman A'i tana son shiga hancinmu da gudundune, dan haka kiyi harkarki muma muyi tamu cikin gidan tunda nagadai gida ba na mijin kowa bane a cikin mu, gida dai naga *GIDAN* *HAYA NE*."kallon su Maman A'i tayi, taga yanda duk suka tadda jijiyojin wuya cewa tayi."Allah ya baku hakuri, bansan zaiyi maku zafi har haka ba da bansa maku baki ba, amman insha Allah daga yau na daina, kuma Insha Allah watarana zaku daina."cewa Halimai tayi."Wannan kuma ke kika san shi, hakuri ba, baki san mu ba mu san wata kalma wai ita hakuri ba, yau muka fara jin ta kuma daga cikin bakin ki muka ji ta, mudai kawai zaman lafiya a gidan nan shine ki fita a idonmu mu kulle."tashi Maman A'i tayi bata ce masu komai ba ta wuce dakinta,suko Rumaisa tunda suka tafi take hawaye dan tana tsoran Allura sosai, koda akayi mata allurar kuka ta tashe dashi sosai Mama ce tace."Rauguwar banza, ke da kike mace, watarana haihuwa zaki yi fa Rumaisa, amman kike yi ma allura wannan ihun sai kace wanda aka cika ma wuka a wuya, Allah ya kiyaye dan wannan rauganci ba Kara in mamaki kika bani ba."cewa tayi tana goge hawaye."Allah Mama baki ji yanda nike ji ba, gashi allurar shegin zafi ne da ita, ni nasa ma na mutu."tsaki Mama tayi sannan tace."Eh kin mutu dawowa kika yi yar'nema, yanzun allurar ita ake cema wa kamar an mutu, duka minti nawa ne akeyi, Allah dai ya sawaka maki."cewa tayi." Amin Mama ni nama samu sauki, gobe zani koma bakin aiki
na, dan nagaji da kwanciya har jikinka yayi ciwo."kallon Mama tayi sannan tace."Allah ya kaimu lafiya, amman dan kar a kuma yi maki allura shiyasa zaki koma aiki." Cewa tayi."Amin Mama, kinsan nayi missing din Fadila sosai, itama tana can tana missing dinna."cewa Mama tayi."kudai keda Fadila Allah ne ya hada ku."murmushi Rumaisa tayi sannan tace."hakane ko Mama."haka suka kama labari har suka iso gida suka shige room din su.
***********************
"Fadila!

Fadila!!

Fadila!!!

Wai wannan wani kallar shiri ne kike kin barni tsaye, kamar wata dogarin sarki?

Kin fito ko sai mun tafiyarmu, ga Fadil can ya fara dan na mana uban horn shima marar hakuri kawai."Umma ce ke cema Fadila haka dan tun dazun take jiran Fadila ta fito su tafi, amman ta tsaya kwaliya, Fadila ce tace."Umma gani nan, hijab na dauko shiyasa."cewa Umma tayi."kedai kika sani, shiga kitchen ki dauko cooler abincin na nan da zamu tafi da ita."ta fitowa tayi ta wuce kitchen sanna tace."to Umma, mu tafi na dauko." Suma fitowa Fadil ya wurga ma Fadila wata uwar harara sannan yace."Fadila daga yau karki sake ki
ara
ata ma mutane lokaci in zamu yi tafiya, inba haka ba wallahi sai dai ki hau motarki ki iske mu, ba wanda zai tsaya bata lokaci gun jiranki, fatan dai kinji ni."?

Lura da yanda ranshi ya
aci Fadila tayi sumi sumi tace mashi."Naji yi hakuri Yaya Fadil, da gyale na dauko sai naga ya dace ace hijab nasa shiyasa na koma na nemo wanda zata hau da kayana."cewa Umma tayi."Allah dai ya sawaka, yanzun ace Fadila ku yanmatan zamani komai zakusa sai kunyi tomarch da komai naku."cewa Fadila tayi."Ai Umma mun fi kyau in munyi tomarch."shi dai Fadil bai ce masu komai ya cigaba da driving din shi,cikin natsuwa da kwanciyar hankali.
*********************
"Rumaisa tashi ki shiga wanka ko."?
Chapter 9 · 0% Book details