← Book details A Gidan Haya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 30

Sashe 11

A Gidan Haya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallonta tayi tace."Da sauki kawata, nayi missing dinki sosai."murmushi Fadila tayi sannan tace."nima haka kawata,yaya Fadil yana waje muje mu gaisa tunda jikin naga da sauki sosai."cewa Rumaisa tayi."To shikenan, amman ki bari na shirya sai mu tafi, ki shigo daga ciki mana."cewa Fadila tayi."Aa ki barni nan gun su Umma, zaki yi saurin shirya wa in baki gani na."cewa tayi."ok na wuce na shirya."bayan Rumaisa ta shiga mai ta shafa da farar hoda da man baki ta zunbula hijab, sannnan ta fito tace ma Fadila."To tashi mu tafi na fito, Mama mun tafi gun Yaya Fadil kofar gida."cewa Mama tayi."to shikenan Rumaisa ki gaida shi kice muna godia."..."to Mama."tunda suka fito Fadil ta saki baki yana kallon Rumarshi dan tayi mashi kyau sosai, duk ta dan rame, amman hakan ma kara yi mata kyau yayi,
bai san da isowarsu ba sai dai yaji Fadila na cewa."Yaya Fadil ga Rumaisa nan na kowa maka ku gaisa."murmushi yayi wanda ya kara fiddo mashi da kyanshi yace ma Fadila."aiko kin kyauta kanwata, nasan ba dan ke ba,
da bata fitowa mu gaisa."dariya Fadila tayi sannan tace."Ni zan shiga ciki yaya Fadil."da sauri Rumaisa tace."Aah kawata ki tsaya gaisawa kawai za muyi sai mu shiga ciki tare."dariya ciki ciki Fadila tayi, dan tasan halin Fadil baisan ana dariya sosai, cewa tayi."Aah kawata niko kinga tafiya ta sai kin shigo."kallonta Rumaisa tayi tana girgiza kai,
sannan tace."amman kawata....

"Amman mai sai kin shigo."Fadila ta tari numfashinta tana shigewarta cikin gida.

Kallonta Fadil yayi sannan yace."Shine dan ta tafi kika wani shiga damuwa."?

Murmushi tayi tace."Yaya Fadil ai banga dalilin tafiyar ta ba."sake kallonta yayi sannan yace."Ke ce baki ga dalilin ta fiyarta ba, amman ita tasan ya dace ta shiga ciki kin shigo daga baya, ke idan mun gama gaisawa."ta
e fuska tayi sannan tace."amman yaya Fadil..

"Amman mai Ruma, kinsan bani son aita magana daya ko."?

Cewa tayi."To shikenan, ina wuni."..."lafiya lau, ya jikin naki."?..."Da sauki Alhmdulh."...

"Allah ya Kara baki lafiya."..."am
in ya Allah."cewa yayi yana kallonta." Ruma nayi missing din ki sosai,
sannnan nayi missing din kallan wannan beautiful face din taki, kuma, tunda kika tafi ban sake shan tea ba."cewa tayi."Ayya yaya Fadil, ba sai kasa Fadila ta hada maka tea din ba."?

Girgiza kai yayi sanann yace."Aah ni in ba naki ba bani shan kowane tea yanzun, dan haka yanzun dai yaushe zaki dawo."?

Cewa tayi."Gobe insha Allah."cikin jindadi yace."to Allah ya kaimu lafiya Ruma, dan baki daya gidan
yayi missing dinki sosai."cewa tayi."nima nayi missing dinku sosai,to yaya Fadil ni zan shiga ciki."ba dan yaso ba ta tafi ba yace."to Ruma, sai goben ko."?..."Eh Allah ya kaimu lafiya Amin."nan ta wuto gida, Fadil ji yake kamar ya riketa karta tafi, amman bashi da za
i, tana shiga taga Fadila, kallon banza tayi mata, dariya Fadila tayi sannan tace.""Kawata sai yanzun kike dawowa, da kina wani yi man efizi hahahahaha."kallonta Rumaisa tayi sannan tace."Haba kawata maiyasa zaki tafi ki barni ni daya."?

Cewa Fadila tayi tana dariya."Saboda na ba masoya wuri su gaisa sosai ko Rumaisar Yaya Fadil."?

Cewa Rumaisa tayi."Wai masoya?

Ku mutane kuna bani mamaki, mutun bai da ikon ya yi mutunci da mutun sai ku kama Cewa wai soyayya mtsssss.....
*Yar'mutan kankia ce
Share
Comments
Vote
Like
A GIDAN HAYA
_STORY AND WRITING_ _BY_
_Jameelah jameey_
*Yar'mutan kankia ce
MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION
*M.

W.

A*
'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________________
*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Page_25&26
Dariya Fadila tayi sannan tace."Eh munji haka muke, mu mutane, ai daman ita soyayya a cikin ido ake ganin ta, kuma wallahi keda yaya Fadil ana kallon idanunku za'aga son jununku, amman nan gaba zaki fahimta."tsaki Rumaisa tayi sannan tace Fadila."ke dai kika sani, amman kisa nidai ba wani wata fahimtar haka wai ana ganin soyayya a idanu, kuma ni nasan Yaya Fadil ba sona yake ba tausayina ne kawai yake, nima haka ba sonshi nike ba, ina mashi kallon Yayana,dan haka Fadilar yaya Fadil wallahi
kibar yi man haka."
e baki Fadila tayi sannan tace."To shikenan Rumaisar Mama zamu gani nan gaba."shiru kawai Rumaisa tayi mata, dan taga komai zata ce ma Fadila ba yarda zatayi ba, kawaai tana
ata lokacin ta ne wajen yi mata bayani, ji sukayi Umma na cewa."Fadila fito mu wuce dare ya fara yi."cewa tayi."to Umma, kawata sai kin shigo goben,amman ki sani ina kan bakana, Yaya Fadil yana sonki, kuma nan gaba zaki ce ni Fadila ni na gaya maki, na barki lafiya."cewa Rumaisa tayi."to kawata, Amman kisani Yaya Fadil baya sona, kumaa kema nan gaba zaki sani."dariya Fadila tayi sannan tace."haka zaki ce daman, amman mu dukanmu mu bari idan muna da rabon ganin gaba duk zamu gani."suna maganarsu har suka iso parlour Rumaisa tace."Aunty mungode sosai, Allah ya bar zuminci."cewa Umma tayi."Amin Rumaisa, yauwa zo ki ansa wani sako Rumaisa."cewa tayi."to Aunty."Mama ce ta tashi yana cewa."Hajiya mungode sosai, gashi mai gidan baya nan bai Kai da dawowa ba, da kun gaisa."cewa Umma tayi."bakomai Maman Rumaisa in ya dawo kin gaisheshi."haka Mama ta rakosu har kofar gida, sannan ta juya, ita kuma Rumaisa har bakin mota taje, nan Umma tace."Rumaisa anshi wannann, kin gaida Babanki in ya dawo kinji."?

Ansa tayi tana cewa." to insha Allah Aunty, nagode sosai."cewa Umma tayi."bakomai Allah ya kara baki lafiya."..."Amin ya Allah,
awata sai goben ko."?

Murmushi Fadila tayi sannan tace."eh
awata Allah ya kaimu."...."Amin ya Allah, Yaya Fadil nagode sosai."Rumaisa tace tana shigewa gida, suma suka kama hanyar gida, koda ta shiga gida, dakinsu ta shiga sannan tace."Mama kinga abunda Aunty ta kawo man, ga kuma abinci nan duk sun kawo, Allah ya saka masu da alkhari."cewa Mama tayi."Amin Rumaisa, gaskiya Hajiya Maryam tana da mutunci sosai, Rumaisa ji yanda ta saki jiki ta zauna muke ta labari bata jin komai ba."cewa Rumaisa tayi."ai haka take Mama."Mama cewa tayi."gaskiya taji dadin halin ta."haka sukai ta labarin su har Baban Rumaisa ya dawo, aka gayamashi.

Washe gari, tunda safe Rumaisa ta tashi ta shirya, tayi wanka da aikin da take yi ma Mama, sannan wa wuce gidan aiki...

Bayan taje ta gaida da Hajiya Maryam, sannan ta fara yin aikin gida sai da tagama yin komai a part din Hajiya sannan ta shiga dakin Fadila...

"Kawata tashi hakanan mana."Fadila ta tashi tana cewa."oyoyo ga kawata, wallahi nayi missing dinki sosai."itama Rumaisa cewa tayi."nima haka kawata, kiji dadi sai bacci kike."cewa Fadila tayi."wani bacci yanzun na samu na kwanta kika
shigo kuma."kallonta Rumaisa tayi sannan tace."Ikon Allah, hala waya kika tsaya yi da Abdullah ko."?
ara kwanciya Fadila tayi ta rungume pillow sannan tace."Eh mana wai bacci yake so ya koma ya kasa shine ya kira ni na sashi baccin."dariya Rumaisa tayi sannan tace."eyyye ha haha kawata masoya,anyi nisa ba'ajin kira."cewa Fadila tayi."eh bakomai, ai mu mun bai yana tamu soyayyar ba kamar ta wasu ba da suke cutatar kansu."shiru Rumaisa tayi sanna kuma tace."Ke dai kika sani Fadila,
ni na wuce gun yaya Fadil na fara yin aiki karda na makara wajen tsayawa jin shirman ki."dariya Fadila tayi sannan tace."Ba wani nan kedai kice kin tafi kiga sinadarin rayuwarki."tafiya Rumaisa tayi tana cewa."ke dai kika sani Fadilar yaya Fadil."dariya Fadila tayi sannan tace."muka dai sani baki dayan mu Rumaisar Mama."ita Rumaisa tana mamakin yanda Fadila take ha
ata da yayanta, bayan ita tasan ba abunda ke tsakaninsu sai dai mutunci, da tausayinta da Yaya Fadil yake, haka tai ta tunanin ta har ta shigo part din shi, tana cewa."Hello, yaya Fadil, sannu da hutawa."waigowa yayi yana cewa."oyoyo ga Ruma welcome back, gaskiya munyi missing din ki sosai."murmushi tayi tana cewa." nima haka yaya Fadil,gaskiya yaya Fadil kuna da mutuncin sosai, baku da wulakanta tallkawa."kallonta yayi sannan yace."haba Ruma maiyasa kike kallar wannan magana?

Ai ke kin zama yar gida kuma yar uwa."murmushi tayi tana cewa."To nagode sosai."nan Rumaisa ta fara yin aiki bayan ta gama ta zauna sunata labari ita da Fadil, suna kallon wani film a MBC BOLLYWOOD, ko wannan su film din yayi mashi kyau saboda soyayyar da ake yi cikin film din, sai da suka gama kallon film din baki daya sannan tace."yaya
Fadil ni zan tafi."cewa yayi."ok Ruma sai gobe ko."!?

Cewa tayi."insha Allah byee."
A kwana a tashi, shakuwa mai tsanani ta shiga tsakanin Rumaisa da Fadil , wanda takai da bamai sun yaga dan uwanshi cikin bacin rai, ko wani hali na daban...

Fadil ya saya ma Rumaisa waya, in ba gidan su, to suna tare da waya, sai sunyi wayar awa biyu, ammn duk a cewar Rumaisa haduwar jini ce ita da Fadil."
Rumaisa tana zaune ita da Fadila suna labari sai kawai Fadila ta hau cewa."Rumaisa!

Rumaisa!!

Rumaisa!!!

Wallahi soyayya kike da yaya Fadil, in kuma ba soyayya bace mai ce?
kagaya man."kallonta Rumaisa tayi sannan tace."wallahi kin tada man hankali irin wanann kiran dakika yi man, kuma gani gaki, nasan wani abu kika gani ma."cewa Fadila tayi."nidai ba wannan na tambayeki ba, soyayya kuke da Yaya Fadil, idan kuma na soyayya bace mainene."?

Tsaki tayi sannan tace."Ni fa ba wata soyayyar da muke na ce maki haduwar jini ce da kuma tausayi haba."cewa Fadila tayi."to shikenan na yarda haduwar jinice."
Ita ko Hajiya Maryam tuni ta gama gane takun Fadil, tana mamakin yanda Fadil
ya fada kogin son RUMAISA ita abun yayi mata dadi sosae.

Dan ko idan har abunda take tunani ya tabbata sai tafi kowa farin ciki, dan dama tuni take ma Fadil shi'awar auren Rumaisa..."Mama ni zan tafi, insha Allah daga nan zamu wuce kitso nida Fadila."Rumaisa ke cema Mama tana sa hijab zata wuto gidan aiki, cewa Mama tayi."to shikenan Rumaisa adawo lfy.".."Allah yasa."
"uhmmm ta bizaro,,an tafi yawau ta zibar da aka saba, yo ni Halimai Allah ya sawaka ina anfani
wa."?
Chapter 11 · 0% Book details