← Book details A Gidan Haya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 30

Sashe 29

A Gidan Haya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Shiru yayi ya fara inda inda, dan yasan sun saba wanann case din da Umminshi, mudun ya samu kudin registration tom ta dinga yi mashi tambaya kenan, dan tana tsoran kar yan iska suyi amfani da dama dan sunga baida kudi su bashi kudi suyi iskanci dashi, abunda take tsoro kenan, cewa yayi."Na manta jiya ban gaya maki ba, da man inasan na gaya maki wallahi jiya mantawa nayi sai da akayi Ihu gidan Alhaji Nura na tuna kuma dare yayi lokacin ga hankalinki duk a tashe yake shiyasa nace yau da safe na gaya maki."
cewa tayi."Mustapha ba wannan na tambayeka ba,
ina kasamu kudi har Naira dubu Tamanin."?
*nan fa akeyinta
ARAWO NE kenan, wanda zaizo maku
13 ga wannan watan insha Allah, nan ne zakuji ansar da yake ba Ummi idan ya samu kudin, amman fa naga ruwan comment sannan zan fara posting
*Sai kuma kadan daga cikin* *~BAYI MA YA'YANE~*
kuma ba yanzun zai zo maku ba
Masarautar Daborah masarauta ce dake can cikin kasar Gambia,
yankin Afrika ta gabas masarautar ta shahara a fagen Sarauta wadda ta share sama da shekara Dubu Ukku da kafuwa a cikin duniya ba inda ba'asan labarin Masarautar ba, a cikin kasar Gambia harma da kewayenta.

Masarautar kwata kwata basu san kima ko darajar bayin su ba sun maidasu kamar wasu dabbobi wani bima har kwara dabbobi sun fisu
ima a cikin masarautar Daborah, kuma sunyi suna wajen tarar abokan gaba daga ko ina a cikin sassan duniya, wanda suke da tarin makayaka masu karfin gaske, labarin su ya karade kaf nahiyar wannan dalilin yasa ake shayin haye masu, wannan kenan.

Duke take tanata famar nakuda kamar zata mutu duk tagama fita hayyacin ta duk yan uwanta sun zagaye kofar saboda gudun kar labarin nakudar Binta tafita a cikin masarautar, kowa ajinin shi akan hakaifa sai uban zufa suke ketawa karma ace mijin Abdulmajid hakan bakaramin tada mashi hankali yakeba, itako Binta baiwar Allah sai addu'a su Jummai ke mata ciki ikon Allah ta surbudo kyakkyawar yarta santaleliya jajir da ita gwanin ban shi'awa, godiya taima Allah duk da tasha wahala hakan baisa hankalin ta ya gushe yabar jikin taba, kukan da jaririyar keya hakan yasa ya fita har waje da sauri Abdulmajid ta shigo ya dauke diyar ya boyeta, sannan yasa su Jummai suka shirya su, duk baki daya hankalin su yaki kwanciya.

Ladidi ce ta shigo sai haki take a cikin Turakar bayi ta shigo dakin su Binta duk sun raina gaskiar su, kowa yabita da kallan tuhuma ko lfy?

Bude baki tayi tafara magana cike da tsoro duk ya mamaye ta."kin bani Binta wayace ki haihu a cikin wannan Masarautar?

Ko kinsan kalar hadarin da kika jefa kanki?Kin manta da matsayinki a cikin wannan masarautar?Amman kikayi wannan gangancin."?

Maida kallonta tayi ga mijin ta fara cewa."yanzun kai Abdulmajid a matsayinka na uban bayi yaza kayi da wannan matsalar."?

Kowa ya kasa magana danko su jummai kuka kawai sukeyi sunajin tausayin Binta, karma ace yar jinjirar da batasan komai ba,
zuwan ta kenan a cikin duniyar ga baki dayanta ma, kukan da yar tasu takeyi shi yakara jefasu cikin tashin hankali hakan yasa Binta daukar diyarta tafara feeding dinta kila tasamu kodan jinkai ne a wajen yarta bayan rasa su, magana Abdulmajid yafara yace."Ladidi ko kinsan me kike fada, taya zamu kawar da abinda Allah ya kaddara mana, karfa kimanta munkai sama da shekaru Arba'in da aure muna neman haihuwar nan amman bamu samuba sai yanzun Allah yajikan mu yabamu sai mu yarda muce bamu so mukasan ko wacece wannan yarinyar nan gaba, kisani ni Abdulmajid koda za'a sare kaina bazan taba wofintar da kyautar da ubangijina yaimani ba,
bayan na bata sama da shekaru masu yawa ina nema kawai dan ina bawa sai in wulakanta wannan ni'imar mai girman gaske, amm...."Aa uban bayi ba nufina kenan ba nidai fatana Allah ya tsaremu daga sharrin makiya kuma yakare mana yar'mu." Ladidi ta katse Abdulmajid tana cewa haka, cewa sukayi."Ameen."itadai Binta ita kadai tasan halin da take ciki sai kuka takeyi tana addu'a Allah ya tsaremata yar'ta koda ace ba tare zasu rayuwa ba.

FA'DA, zaune take a saman karagar mulkin ta alfarma wadda tasha ado da ruwan gwal da arzurfa ta hakince sai takama takeyi da gadara sai fiffita ake mata cikeda izzah take kada yan yatsunta wa'anda suka sha gwala gwala saman kyakkyawn wuyanta shima yasha ado mai ban mamaki ta gyara gashin kanta da aka daura mashi crown sai shaining takeyi taji gwal baki daya farfajiyar fadar fadawa ne zaune a saman kujeran su a suka kewaye fa'dar sai tsakiyar fa'dar katon kafat ne wanda ya gaji da tsaruwa kujerar Sarauniyar ce a tsakiya sai sauran yan fa'da suka kewayeta inda akabari in anzo kowa zai duka saman kafat dinnan yakai gaisuwa wajen Sarauniya inta zauna sannan kowa zai zauna.

Ba abinda yaimata zafi ko magana ba tayi sai ka
a kafar ta takeyi a hankali cikeda kasaita, jin Sarkin kofar shiga cikin fa'da yana dakatar da wata baiwa a cikin amintattun bayin ta, hakan yasa ta kalli wani dogari dake gefenta kallan sa kawai da tayi yasa shi tafiya da sauri yacema Sarkin kofa da ya budema wannan baiwar gate din shigowa cikin fa'da jikin shi na rawa ya bude mata ta shigo faduwa tayi saman tsakiyar kafat din fa'da takai gaisuwa wajen Sarauniya takai wajen minti biyar sannan Sarkin Zagi yace mata." Sarauniya ta amsa." kanta a kasa a jin maganar Sarkin Zagi yabata ikon dagowa ta kalli Sarauniya tace."Allah yataimaki inaneman izinin zanyi wata muhimmiyar magana mai mahimmanci aimin a fuwa tuba nike Allah yakara girma." a dakile ta daga mata hannu." Sarkin Zagi yace."angai sheki Mero Sarauniya tabaki damar magana." Cewa Mero tayi."Godiya nike Allah yataimaki Sarauniyar Daborah ina tafe da wani labari mai girman gaske lallai yau antashi da alhini a
cikin wannan Masarautar mai tarin albarka, yau a cikin Turakar bayi antashi da firgicin gaske yau dinnan Uwar bayi Binta ta haifi kyakkyawar yar'ta mace hakan yasa nace bari in hanzarta fada maki,
Allah ya huci zuciyar ki yakara daukaka."
Mikewa tayi cikeda gadara tana ka
a kai cikin izzah da isa sannan ta bude baki tafara magana."Sarkin fa'da kaida Sarkin horo ku hanzarta zuwa ku kamomin dasu baki dayan su harda yar da iyayen baki daya kuma nabaku nan da minti ukku." tashi sukayi suna cewa."Allah yakara nisan kwana angama yanzun nan kuwa." fita sukayi da sauri duk cikin su ya duri ruwa, itako sai kai lawo takeyi cikeda da kasaita.

Dauke suke dashi a saman wani gado daya gaji da kayatuwa bayine guda hudu suke dauke da wannan gadon mai dauke da kayan ado na jauhar da lu'u lu'u, sai daukar ido yakeyi ga dogarawa sai dukan wadannan bayin sukeyi hakan yasa wani matashin Saurayi yayi magana
a hankali yana saman gadon duk da bazai wuce shekara goma sha biyar ba a duniya ba karamin bacin rai bane ya kama shi ba, suko wadannan dogarawan sai ahi sukeyi suna neman tuba cewa yayi."daga yau karku sake ku kara dukan su me sukai maku?
da zaku dinga zalintar su, ga aiki sunayi ga duka dame kuke son suji."!?
cewa sukayi."Allah yahuci magajin gobe tuba mukeyi Allah yakara maka lfy." haka sukaci gaba da tafiya dashi sai a lokacin bayin nan suka samu sukuni ba inda suka isa sai bakin kofar shiga fa'da, da sauri Sarkin kofa yafara koda wannan kyakkyawan Saurayin mai farin jini ga alumma Masarautar, a hankali yake tafiya har ya isa wajen zaman shi, nan ya gaishe da Sarauniya sannan ya zauna a gefen ta saman tashi kujerar duk danya fahimci ran ta a bace yake sai dai baiyi magana ba, ba dan yana san zuwa fa'da ba yasan ba yanda zaiyi dole yazo, gani yayi dogarawa nata dukan wasu bayi, kamar zasu kashe su ga jinjira a hannun su bakaramin taba ransa hakan yai ba, ba inda suka gurfana sai gaban Sarauniya
kowa yakawo gaisuwa jikin su sai uban
ari yakeyi duk sungama tsorata,cewa Abdulmalik yayi.

"Allah yataimakeki kiranki ya samemu kimana aikin rai."
tahowa tayi kusa dashi ta wasga mashi wani kalar masifaffan mari mai rudarwa, cewa yayi."tuba mukeyi Allah ya kara girma." Cikin Izza ta fara cewa."Uban me yasa kuna bayina zaku sake jiki har ku haihu a cikin masarauta ta?Har yaushe kukeda wannan yanci?Ku kuka kafara karyaman dokata kuma manyan bayi lallai kun raina dokar Sarauniya Zulai
ha kenan."?

Cikin tsoro sukace."kiyi mana aikin rai haka Allah ya kaddara." wani kalar wawan kallo ta aika masu dashi, wanda yasa kowa yayi kasa da kanshi cikeda tsoro.
Chapter 29 · 0% Book details