← Book details A Gidan Haya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 30

Sashe 3

A Gidan Haya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin shagwa
a tace."haba Yaya
Fadil maiyasa zaka ce haka, bayan ni na gurza kubewar da akayi miya."murmushi yayi ma kanwar tashi sannan yace."to naji duk ba wannann na tambayeki ba wace ke yin wannan abun mai kamshi har haka."?

Cikin jindadi Fadila tace tana kama hannunshi tace."Eh Rumaisa ce."zaro ido yayi gami da fisge hannunshi daga nata yana cewa."What?

Wacece Rumaisa kuma."?cikin mamaki Fadila tace."haba Yaya Fadil kina nufin baka san Rumaisa ba sabuwar yar aikin gidan."?
aga mata hannu yayi yana mai wurga mata harara yace."Hey yaushe na zamo abokin wasan ki?

Ya ina yi maki question kema kina yi man naki Fadila?
in nasan ta na tambayeki."?

Ta tsora da yanda ya chanza mata lokaci guda cewa tayi."Aah hakane kuma Ya
2 Fadil, to Rumaisa yar'aikin gidan nan ce, kuma kawata ce."kallonta yayi yana mata kallon taji kunya bata iya girki ba yace."ita Umma tana ina."?cikin gajiya da question din Yayan nata tace."ai kasan ta hospital dinta ko? ko kamanta yau Monday?

Tana zuwa taga patient dinta na musaman."cewa yayi "ok I forget about it , Allah abincin yayi dadi, ita Umma tasan ba ko wane abinci nike ci ba, shine taba yar yarinya tayi, salan tayi mana jaqwalgwalo."ya fadi yana ma Fadila kallon banza, dan yaji haushi sosai da ya tadda Umma bata nan.

Rumaisa ce ta fara gwalama Fadila kira."Fadila!

Fadila
2,wai ina kika shigeni kin barni da aiki ni daya?

To sai ki taho na gama, har kitchen din ya gyara."sosai gaban Fadil ya fa
i dan tunda
yake bai taba jin voice mai dadi kallar wannan ba, sai da yace." masha Allah." cikin zuciyarshi,kuma yace."wannan wata aljannace su Umma suka kwaso mna cikin gida"?

Yana cikin tunina yaji tana cewa."To nidai na wuce gida zani Isilamiya."
Fadila ce tace.

"haba Rumaisar Mama, ai kin tsaya ki gaida Ya
2Fadil ko?

Sannan kuma na zuba maki naki abincin."
Cewa tay."au Fadilar ya
2Fadil, ai ban lura da shi ba shiyasa na wuce da yake ina sauri karda na makara, abinci kuma kibarshi nagode, Ina wuni?

Ina wuni."?

Sai da ta gaishe shi har sau biyu amman Fadil yayi banza, Fadila ce tace.

"Ya
2 Fadil ana gaidaka fa."wani kallo ya watsa mata sannan yace."naji ai ba dole sai na ansa ba, ke dai baki san kiga bakin mutum yana hutawa ko."?

Cewa Fadila tayi."shikenan Ya
2 Fadil, kawata muje nasa maki abinci."Rumaisa bata ji dadin abunda Fadil yayi mata ba cewa tayi.

"Aah wallahi Kawata nagode, ni daga nan Isilamiya nayi ba gida ba."cewa Fadila tayi."to shikenan sai gobe."cewa Rumaisa tayi.

"Allah
kaimu Lafiya."
Nan fa Fadila ta jera tuwo a dining area, ta wuce ta shirya kafin Umma ta dawo tana cikin shiryawa Umma ta shigo, bayan sun gama shirya wa suka hadu a gun abinci zasuyi dinner saboda sun makara ba suyi lunch ba, sai dinner, nan Fadila tayi saven din kowa itama tayi saven din nata ta zauna ta fara ci..

Fadil yana ya tsina fuska yace."haba Umma yanzun wannan bakin tuwan yaranan zasu yi mana?
kuma gashi ni bakar yunwa nike ji."
Kallonshi Umma tayi sannan tace."yanzun Fadil ka daure kaci ko kadan ne, in na gama cin nawa sai na tashi na soya maka wararka ko?

Ohk shikenan, ai Fadil yana yin spoon daya sai da ya lunshe ido, su Umma suna kallon shi sai kayi kamar basu ganshi ba, daya fahimta basu ganin shi sai da yayi ma cikin tab, sannan ya tashi yana cewa yayi hakuri ya daure ya cin ba dan dadi ba, ita dai Umma bata ce mai komai ba..

Nan Rumaisa ta kama gabanta, ta wuce Isilamiya,ana taso wa ta wuce gida, tana shiga gida ta iske ana fada dasu Hindatu da Maman A'i, wai jiya suna jinta tana zaginsu, wai har tana cewa mazajensu matsiyata ne.

"Ke Lami sauraren ni jini da kyau, daga yau na sake jin kunyi fada da Matata wallahi sai hukuma ta shiga tsakaninmu da ku, in ba rashin san gaskiya kallar taku ba ya zaku biyo ta har dakinta kuce zaku ci mata mutunci, bama ku tashi zuwa ba, sai da kuka ga na shigo gidan sannan zaku kwaso kafafu kuce zaku yi mana rashin kunya."?

"Da kata Abdul, karda ka kurkura kace zaka yi ma matata tsawa, akan Lami ba abunda ba zanyi ba, kuma ni nasa ta tayi ma matarka rashin mutunci tunda tace man matsiyaci bayan kuma ni nasan ba matsiyaci bane."
"Ashe kasan kai ba matsiyaci bane, kazo kana tada jijiyoyin wuya, ai nasa ko kallon Hafsat ba za kuyi ba dan tace maku matsiyaci, tunda kunsan ku ba haka kuke ba, amman saboda rashi tunani kunzo har gaban dakin matar aure kuna zaginta, kuma a gaban mijinta, to nima akan Hafsat ba abunda ba zani yi ba a cikin gidan nan."
Itadai Rumaisa ta gefen su tabi ta wuce bata cema kowa ci kanka ba, amman dan bala'i irin na Halimai sai da tayi jacking din hijab din Rumaisa wai tayi mata kallon banza, bayan harta Baban Rumaisa ya ga yanda abun ya kasance, ita dai Rumaisa cire mata hijab din tayi ta shigewarta daki ta barnan tsaye da kunfar baki yanda kasan karya sabon haihuwa ba.. ..
*Yar'mutan kankia ce
Share
Comment
Vote
And
Like
A GIDAN HAYA
_STORY AND WRITING_ _BY_
_Jameelah jameey_
*Yar'mutan kankia ce
MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION
*M.

W.

A*
'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________________
*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*Wannan page din naku ne Sansanin yar'mutan kankia fan's group da Real Jameey Fan's one and two kuyi yanda kuke so dashi, dan naji dadin comments dinku sosai, much love
Page _7-8
"Mama sannu da hutawa."..."yauwa Rumaisa sannu Andawo lfy."?

Sai da ta zauna sannan tace."Lafiya lau, Mama , gaskiya Mama na fara gajiya da abunda su Halimai ke yi man a gidan, yanzun fa daga shigowa ta wai nayi mata kallon banza."ji tayi Babanta yace."Rumaisa."waigowa tayi dan bata lura da Baban mata ba tace."Naam Baba"cikin fushi da bacin rai yace."daga yanzun duk wanda ya sake yi maki a cikin gidan nan bance ki raga mashi ba, ko wanene ni na baki dama."cewa Mama tayi."haba Babanta, ai bai ka mata kace mata haka ba, hakuri zamu cigaba yi mana."wani irin kallo Baban Rumaisa yayi ma Mama sannna yace."wani hakuri? na lura mutanan gidan nan basu san hakuri ba, ko daya dan haka duk wanda yayi maki ki rama ni na saki, tashi kije kici abincin ki kwanta bacci kinji yar albarka."cewa Rumaisa tayi."To Baba." bayan ta gama cin wata shinkaface yau Mama ta dafa masu, jollof din shinkafa da wake tayi masu, tana gama ci ta tashi tayi sallah sannan tayi karatu ta kwanta bacci, itace bata tashi ba sai 3:00am, tayi sallah,
asuba nayi tashi tayi asuba, sannan ta cigaba da yin azakar, tana gama azakar ta tashi ta shiga wanka, bayan ta fito wanka suka yi breakfast, kosai ne da koko, tana gama yin breakfast ta tafi gidan aiki.

"Aunty ina kwana."..

"Lafia
lau,ya gajiyar jiya da kuma."?

Murmushi tayi sannan tace."Aa Aunty ai ba wani aiki bane mai wahala ba, Fadila fa."Hajiya Maryama tana jindadin zama da Rumaisa dan tarbiyar Rumaisa tayi mata cewa tayi.

"tana dakinta tana baccin da ta saba."tashi Rumaisa tayi sannnan tace."to shikenan bari na fara aikin kafin ta tashi nagama, dan yau tace zanyi mata karin quri'an."cewa Umma tayi"To Rumaisa a gama lafiya."
Bayan Rumaisa ta gama yin aiki, tayi komai harta mopping duk tayi ta gama, nan ta shiga kitchen ta taya Hajiya Maryam aikin abinci, coconut rice su kayi da miyar kwai, bayan sun gama yin abinci ta wanke duk abunda suka bata, sannan tayi mopping din kitchen din again sannnan taje room din Fadila, dan zata yi mata karin karatun alqurani mai girma.

"Kawata, ai nasa har yanzun baki tashi bacci ba."?

Cewa Fadila tayi."Rufaman asiri kawata, tun dazun na tashi, kawai na tsaya karatun wani novel mai suna *SANADIN LINK* , wanda *jameelah jameey* *Yar'mutan kankia* tayi shi, gaskiya *NOVEL* din akwai shi da Ilimantarwa, dan gaskiya naji tsoro, dan novel din ya Nishad'antar sosai, kuma ta farka da mata daga dogon baccin da suke yi especially mata masu bala'in bin *LINK* din tsiya."Numafasawa Rumaisa tayi sannna tace."Ohni kawata dama ace ina da waya da kin turoman wannan *NOVEL* na karanta, daman naji ana maganar *NOVEL* din *jameelah jameey* *yar'mutan kankia*, na karanta novel dinta daya, da wayar wata kawata a Isilamiya *NANA* *JAWAHEER* , shima yayi man dadi."Fadila tace."eh nima na karanta *NANA* *JAWAHEER* harda ma *GIMBIYA HAKIMA da IZZA KO MULKI* dan ko shi Izza ko Mulki na kudi ne tayi haka, dadin da yayi man nasa kudina na saya, ai ni gaskiya duk *NOVEL* din da *jameelah jameey* *Yar'mutan kankia* za tayi bani yarda ya wuce ni gaskiya, saboda duk novel dinta suna da ma'ana, yanzun in mun gama Karin karatun, zan baki ki karanta tunda ba wani yawa ne da shi ba *SHORT STORY* ne."cikin jindadi Rumaisa tace."to shikenan ngd."dan taji dadi sosai da Fadila zata bata ta karanta Sanadin link, dan taji ana labarinshi a isilamiyarsu.

Bayan sun gama yin karatun suka je yin lunch harda Rumaisa, domin Hajiya Maryam ta dauki Rumaisa kamar diyarta Fadila, sunyi lunch kowa ya kama gabansa, nan Rumaisa ta ansa wayar Fadila ta karanta *SANADIN LINK,* sannan ta ansa abinci ta wuce gida.

Tafiya Halimai take cikin san
a, samu tayi ta shiga kitchen ta bude tukunyar sauwar Lami ta fara ebar mata abinci, tana cikin haka sai ji tayi ana salati."Innalillahi, mai zan gani haka ni Hindatu?
Chapter 3 · 0% Book details