← Book details A Gidan Haya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 30

Sashe 15

A Gidan Haya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zatayi magana Fadila ta katseta ta cigaba da cewa."A she yaya Fadil bai da arzikin da zaici darajar Umma ki aminta da Soyayyarshi ba, tabbas Rumaisa baki yi mana adalci ba, kuma banji dadin jin haka daga bakin ki ba gaskiya."saurin rufe mata baki Rumaisa tayi sannan tace."Fadila dan Allah kiyi hakuri, wallahi banyi tunanin rainki zai baci har haka ba, nima na baku matsayi mai girma a rayuwa, har abada ba zan manta da hallacin ku daga gare ni ba, kawai dai sai naga kamar banga dacewar mu ba da yaya Fadil."kallonta Fadila tayi sannan tace."Mungode da matsayin da muka samu, Rumaisa kinga na tsuguna giwowi na duka biyu in ma kina so zan dafa kafafunki ki taimaka ki Aminci ce Yayana."
ago ta tayi tana cewa."Subuhanalillah, Fadila dan Allah ki mike tsayi, wallahi kin fi garfin komai a wajena, ai bun kunya ne naki dan uwanki, naso wani, Amman ina san ki bani dama nayi shawara da su Mama."murmushi Fadila tayi sannan tace."To shikenan Rumaisar Mama, Allah yasa muje alkhari, Amman dan Allah ki tausayama Yayana."tashi tayi tana cewa."to ni Fadila na wuce gida sai gobe." tashi Fadila tayi, ta tafi wajen Umma tana cewa."Umma albishirinki."?

Kallonta tayi sannan tace."Goro."cewa tayi."fari ko ja."?

Cewa Umma tayi."Fari tas da shi ma."dariya tayi sannan tace."to Umma yau dai yaya Fadil yace ma Rumaisa yana sonta."murmushi Umma tayi sannan tace."Alhmdulh Allah nagode maka, gaskiya na baki kyautar MOTA cikin new motors din da aka kawo jiya, amman ita Rumaisa mai tace mashi."?cewa."nagode Umma, ita bata ce komai ba, wai sai tayi shawara da Mama."cewa Umma tayi."Da kyau bani son ta bashi ansa dan yanzun har sai na ida tabbatarwa da kallar son da yake mata, dan ni na haifi Fadil na san waye shi, shi mutun ne mai wuyar fahimta."dariya Fadila tayi, sannan tace."To shikenan Umma, haka za'ayi, zan sa ta gara shi yanda ya dace, shima ya san yanda ake san wuya wajen neman aure."cewa Umma tayi."yauwa albarka haka nike son ji da man."
Tunda Rumaisa ta koma gida, ta kasa yanda zatayi, daurewa tayi sannnan tace."Mama da man ina son na gaya maki wata magana."kallonta Mama tayi sannan tace."wace magana ce haka Rumaisa?

Fadi inajinki." kallok Mama Rumaisa tayi sannan tace."da man Fadil ne."kallonta Mama tayi sannan tace."Fadil ne mai wani abu ya sa mai shi."?cewa tayi."Aa da man ce wa yayi yana sona."tashi Mama tayi sannnam tace."Yana sonki fa Rumaisa."?

Kallon Mama tayi sannnan tace."Eh Mama."zaunawa Mama tayi sannan tace."Rumaisa kiyi hakuri da Fadil, dan Fadil ba sa'an aurenki bane, ko ke baki lura ba."?cewa tayi."Mama ni ma haka nace ma Fadila, amman sai ta nuna bacin ranta, wai ashe ban dauki matsayin da suka bani ba, har da tsugun nawa tayi kasa tana neman alfarman na so Yayanta."shiru Mama tayi, dan itama ta hango hallacin mutanan gidan, take jikinta yayi sanyi sannnan tace."To shikenan Allah yayi maki albarka, Allah yasa shine alkharinki."cewa tayi."Amin Mama, ni zan kwanta sai da safe....
*Yar'mutan kankia ce
Share
Comment
Vote
Like
A GIDAN HAYA
_STORY AND WRITING_ _BY_
_Jameelah jameey_
*Yar'mutan kankia ce
MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION
*M.

W.

A*
'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________________
*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Page_37&38
Yau Rumaisa tana gama aiki, ta wuce gidan aiki, bayan ta gama duk aikin da take Hajiya Maryam ta kirata ta fara yi mata magana.

"Rumaisa."sai da ta kalli Umma sannna tace."Naam Umma." Murmushi Haji ya Maryam tayi sannna tace."da man ina san nayi wata magan dake."cewa tayi.

"to Umma."cewa Hajiya Maryam tayi."Rumaisa, naji Fadil yace yana sonki, amman sai naji wata magana wanda kwata kwata bata yi man dadi ba."numfasawa tayi, sannan ta cigaba da cewa."Yanzun Rumaisa da man baki dauke ni a matsayin uwa ba."?

Sauri dago kanta Rumaisa tayi sannan tace."Yi hakuri Umma, amman ba haka nike nufi ba."murmushi yayi sannan tace."to shikenan Rumaisa bakomai,Ki dauke ni a matsayin uwa, yanda nike daukar Fadila, haka ke ma nike daukarki, zan baki shawara tsakani na da Allah."
Cigaba da cewa tayi."Rumaisa, na san Fadil na san halinshi duk da baka yabon dan yanzun, Fadil yana da wuyar sha'ani, na san kin san da haka, Fadil wani kallar murderden mutun ne baka gane gaban shi balle bayan shi."
Murmushi ta sake yi, sannan ta sha tea sannan ta cigaba da cewa."To ke taya zaki gane gaban shi?

Shin taya zaki iya fahimtar halinshi?

Taya zaki gane kallar son da yake maki?

Dan haka Rumaisa kina da aiki sosai a gaban ki, amman kafin nan indai har baki son Fadil ki fidda kunya ki gaya man, domin mai iya zama da Fadil sai ya shirya."
Kallon Umma tayi sannan tace."Umma
ina son yaya Fadil, sai dai nima ina tsoron kalar zaman da zamu yi da shi a matsayin ma'aurata, duk da akwai shakuwa tsakanin mu ni da shi yaya Fadil din."shiru Umma tayi sannan tace."Tabbas haka ne naji dadin wanann maganar Rumaisa, yanzun zan gaya maki yanda zaki fahimci komai na Fadil, da yanda zaki ci ribar zama da shi a matsayin miji in Allah ya yarda."
Cewa tayi."Rumaisa Fadil mutun ne mai bala'in son kwaliya da tsafa, Fadil yana da musulkilanci sosai, amman kin san mai Rumaisa."?

Girgiza kai tayi sannan tace."Aah Umma."..."to Rumaisa zama da miskillin mutun dadi ke gare shi amman in kin bi abunda yake so, to ba abunda ya fi zaman kalar masu halin Fadil dadin zama,sannan ban yarda ki gaya ma Fadil kina son shi ba dan yanzun, har sai kin tabbatar da ya wahalu sannan ki bashi ansar kin yarda da Soyayyarshi, shi kuma wannan wahalar da ya sha zai sa ya rike soyayarki riko na gaskiya da Amana."kallonta Hajiya Maryam tayi sannan tace."Karki yarda ki nuna mashi tausiyi a lokacin da kike ba shi gashi a hannu dan wannan zai sa ki gane ina matsayinki ya kai a cikin zuciyarashi, sannan Rumaisa, daga yau duk wata hanyar da zaki san zata hadaki da Fadil ki kiyaye ta, wannan ma wani shirine babba, ta yanda zaka gane matsayinka wajen mutum,sannan duk lokacin da kika amince da Soyayyarshi, karki yarda dai-dai da yatsan hannunki ya taba, dan duk budurwar da ta yarda saurayi ya kama mata hannu nan gaba NONONTA zai ce zai taba, tunda ya ga hanya,yanzun soyayyar da rabin da kwatan yan-matan yanzun suke wato soyayyar MINTI, ke kin saki jiki kin barmai yana ta tabawa a banza babu sisin kabo, sai ya gama bata maki rayuwa ya gudu ya barki da citson yatsa, Allah ya sa mu dace."
Dukar da kanta tayi sannan tace."Amin Umma."sake cewa Hajiya Maryam tayi."sannan Rumaisa ina san ki kara zage danke wajen iya abinci sosai, domin Fadil yana son mace wanda ta iya abinci dan shi baya cin abincin waje,Ke koda shi mutum ne mai cin abincin waje, ai ke macece sai ki bi hanyar da zaki bi kiga kin hana shi wannan hali, shin Rumaisa wace hanya ce wannan?

Hanya daya to shine kisa mu ki koyi iya abinci kala kala, tun daga kan na zamini har zuwa na gargajiya,dan haka daga yau keda Fadila ku zaku ringa yi mana girki a cikin gidan nan, dan ban sake shiga kitchen daga yau."murmushi tayi sannan tace."To shikenan Umma insha Allah, zanyi ko kari
na bi shawarar da kika bani da yarda Allah."
Murmushi Umma tayi sannan tace."To Rumaisa, Allah yasa."..."Amin Umma, ni Umma zan cigaba da yin aiki kafin lokacin Isilamiya yayi, dan yau muna da Isilamiya."..."to Rumaisa Allah ya taimaka."...

"Amin ya Allah."
Fadil ne zaune a office yana tunani duk abun duniya yayi mashi yawa, Abdullah ne ya shigo, tun dazun yana ma Fadil magana, amman bai jishi ba, bugasshi yake yana cewa."Fadil!

Fadil."firgigi ya dawo cikin haiyacin shi
yana cewa.

"Naam Abdullah."kallon shi Abdullah yayi yana cewa."lafiyarka kalau kuwa."?
aro murmushi yayi sannnan yace."Maika gani, ko nima baristancin za'ayi man."!?

Dariya Abdullah yayi sannan yace."haba Fadil ai da an kalleka ansan baka cikin natsuwarka, Lafia mike damunka."?

Shiru yayi sannna kuma yace."Abdullah, Ruma ce."nazari Abdullah yayi sannna yace."mai ita Rumaisar tayi maka, har haka."?shafe zufar da ta fito mashi a goshi yayi, yana murza koshin shi sannnan yace."Abdullah ina son Ruma, akan Ruma ba abunda ba zanyi ba."ajiyar zuciya Abdullah yayi sannnan yace."To kaje ka gaya mata mana, sai kabar abu yana ci maka rai."Murmushi mai ciwo Fadil yayi sannan yace."Abdullah baka fahimceni ba, tun jiya na gaya mata, tun daga jiya ban sake ganin ta, ta tafi ta barni cikin zullumi da tunani, wallahi jiya sai dai bacci barawo ya kwasheni."shiru Abdullah yayi sannan yace."To may be, sai yau zata zo kunyi magana inta gama aiki ko."!?

Shiru yayi sannan yace."Nima haka nasa rai, shiyasa nike son nayi sauri na koma gida nasan yanzun sun kusa gama aiki." dariya yayi yace."Kai Fadil kai kana da abun haushi wallahi."cewa Fadil yayi."ni din ko"?.."Eh mana, ai nasa wani abu ne daban, da na ganka cikin damuwa, sai nayi tunanin cewa tayi bata sonka."
Dariya yayi sannan yace."Aah ko daya, kawai nidai banson ko second nayi ba tare da na waiga na ganta kusa dani ba, yanzun ma hakuri nike har kake jin magana ta."
"To ai sai ka tafi gida tunda da man time din tashi yayi."..."aiko yanzun shirin da nike yi kenan,
byeee."
Nan fadil ya dauki hanyar gida yana addu'a Allah yasa Ruma ta Amince da Soyayyarshi, inko taki amincewa da shi, shi kawai mutuwa zai yi, dan ba ya iya ganin wani ya auri Ruma in ba shi ba...

"Ina ai nasan Ruma itama tana sona, ba zata kini ba, ta na sona, ai in nasara Ruma kawai nasan ni Fadil tawa tazo karshe, dan banson wani kallar sone nike yi ma Ruma ba."
Haka dai Fadil ya kama tunanin shi ya na drive har ya samu ya isa gida, nan zuwa part din shi ya shiga yayi wanka ya shirya sannan ya tafi part din Umma dan suyi magana da Rumaisa, amman ya na shiga ya tadda Umma da Fadila suna yin lunch nan ya zauna suka yi sai dan dube-dube yake ta inda zai hango Ruma, kallon Fadila yayi sannan yace."Fadila."kallon shi tayi sannna tace.
Chapter 15 · 0% Book details