← Book details A Gidan Haya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 30

Sashe 25

A Gidan Haya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Woow, wasu yan-mata biyu na hango a hall din dinner, ko wace tana tare da saurayin ta suna ta zuba soyayya, yan matan nan anko din wani materials suka yi, Army green, su duka material din nan yayi masu kyau duk da ba hasken su daya ba, dan Fadila fara ce sosai, ita kuma Rumaisa ruwan tarwadace, Amman colour din tayi bala'in yi masu kyau, su Fadil ne suka tashi suka barsu, ai suna tashi wani handsome guy ya taso yazo wajen ssu Rumaisa ya zauna, kallon su Rumaisa yayi sannan yace."Yan mata sannu fa, Am Nasir Abu-turab, dan Allah ki bini lokaci na gaya maki abunda nazo dashi izuwa gareki." ita dai Rumaisa bata ce mai komai ba, yayin da Fadil ji yake kamar ya shake wuyan Nasir da man tunda suka zo wajen nan yaji guy din bai yi mashi ba, dan da man ya lura yanda ya nuna maitarshi a fili a kan princess din shi...

Nan take Fadil ya isge hannun Rumaisa yana janta, tana cewa."princes ka matse man
hannu fa, da zafi sosai fa." yana jinta amman yayi banza ya kyale ta, sai kara ma matsa hannun da yayi sosai, ba ajeta ko ina sai cikin mota, ya shiga ya ma motar da gudun bala'i nan take Rumaisa ta fara kuka, ba tayi tunanin zasu iso gida lafiya ba, koda su iso gida, bude motar yayi ya wucewarshi cikin part din shi, dan haushin Rumaisa yake ji sosai, biyo shi tayi tana kuka, tana shigowa ta kara rushewa da kuka tana cewa."Prince dan Allah kayi hakuri, wallahi ban san shi ba, hushinka zai iya haifaman da matsala babba, kayi man ko wani hukunci amman banda kalar wanann, amman kasani ni ban sanshi ba, ban ma taba ganinshi ba." kallonta yayi yana cewa."eh na san baki san shi ba, amman mai yasa kika sakar mashi fuskar har yazo wajenki, da kinji yanda naji da ko kallon fuskar shi baki balle har yazo wajenki."
Kuka take sanann tace."bai dace kayi man haka ba, amman kayi hakuri bazan sake ba." matsowa yayi kusa da ita yana share mata hawaye sannan yace." komai ya wuce princess, amman ki sani komai kika nayi duk sonki ne sila." dariya tayi mai hada da kuka sannan tace." nagode da kayafeman, nima sonki ba zai bar ni na kula wani ba inba kai ba."
An kawo lefen Fadila akwati
18 da gana biyu, an ma dangin Abdullah tarba ta mutuncin, sun koma gida suna yabon tarbiyar gidan su Fadila, dan gaskiya Abdullah yayi dacen mata.

Washe gari jirgin su Rumaisa ya tashi zuwa England, sun yi abunda ya akaisu, dan itama Rumaisa akwati 18 aka yi mata da gana biyu, sannan furnitures da komai iri daya aka yi masu set daya duka white in colour, sai set daya kuma brown and milk, ko wane set biyu aka yi mashi, sun dawo gida Nigeria lafiya, sunyi fresh sun kara kyau sosai da ka gansu ka ga amare,
bayan sun dawo su duka suka koma part din Inna da zama nan ake yi masu gyaran jikin,
dan har wani glowing suke dan tsananin gilka da halawa da suke sha.

Yau biki saura kwana uku, kuma yau, za'ayi diner, sun dauko makeover zata yi masu kwaliya da gyaran gashi, masha Allah, gaskiya duka
Amayarnan biyu ba karamin kyau suka yi ba, sunsa gown brown and white, an daura masu head sunyi bala'in kyau, nan aka saka kowa motar da angonta ke ciki yana jiran ta, domin suje meenet event.

"Princess, kinyi kyau sosai." waigowa tayi yana murmushi sannan tace.

"kayi kyau sosai prince." kamo hannunta yayi yana cewa." flower din nan tayi man kyau gaskiya princess, princess wannan wani turarene kika shafa."!? nan ya janyo ta jikanshi yana sunsunan kamshin jikinta, itako sai tureshi take, da taga abun ya fi karfin ta ta sa mashi ido
, tana cikin tureshi taji ya hada bakinsu waje daya yana kissing dinta, shiru tayi ta kwantar da kanta a kafadunshi, dan ta da yanda zatayi dashi lumshe idanu kawai tayi yana jin yanda Fadil yake tsotsar mata harshe kamar ya samu sweet, ba su san an iso meenet event ba, sai
dai Mubarak yace suyi hakuri, hakanan mai suke ci na baka na zuba
Itama Fadila, tunda ta shiga mota, Abdullah ya matsa mata da ya mitsa, shine ya taba can ya lasa can sai da yaga zata yi mai kuka sannan ya daga mata, suna iso suka jera bakin dayansu suka shiga, anyi diner yanda ya dace amare sun yanka cake, an tashe kowa ya koma gida...

Washe gari, aka yi bridel shower, tsaya wa gaya maku kyau da Amare suka yi bata lokacine, amma kyau ko anyi masha Allah...

Sai Washe gari a kayi wa'azi, Malama juwairiya tazo tayi wa'azi a kan yin biyeyya ga miji da kuma shi auren mai ye shi, tayi wa'azi mai shiga jiki, dan su Rumaisa sun sha kuka...

Yau ta kama daurin aure....
*Yar'mutan kankia ce
Share
Comment
Vote
Like
A GIDAN HAYA
_STORY AND WRITING BY_
_Jameelah jameey_
*Yar'mutan kankia
MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION
*M.

W.

A*
'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar
da masoyan ta.
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
______________________
*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Page_57&58
Yau da misalin karfe 2pm aka daura auren FADIL KHAMIS
MUHAMMAD da Amaryarsa RUMAISA FADIL MUHAMMAD a kan sadaki naira dubu Dari, sannan aka daura auren ADBULLAHI ABUBAKAR SULE da Amaryarsa FADILA KHAMIS MUHAMMAD akan sadaki naira dubu Dari, bayan an gama daura auren aka wuce reception aka ci aka sha..

Bayan nan sun Fadil suka yi pictures da abokanansu, sanann ya samu ya turama Rumaisa message..

Gidan cike yake da yan'uwa da abokan arziki, su Rumaisa suna part din Inna ta shirya su, dan har anzo daukar Fadila, tana basu wani jiko da ta anso masu,kallon Rumaisa Inna tayi sannan tace."wai Rumaisa zaki ansa ki sha ko sai muyi ta dake cikin gidan nan."turo baki tayi tana cewa.

"Inna wallahi na gaji da shan wannan abubuwan naki, su ba wani dadin kirkiba." Cikin fada Inna tace."ai da yake bani zan ji dadin abun ba keda mijinki zaku ji dadin abun ku, lokacin ni banma san inda kaina yake ba,ku kuwa kina can kuna murzar juna, dan dagake har shi Fadil din ba hak'uri gareku, yanda kuke rawar kan nan ai dole sai da gyara." Rufe fuska Rumaisa tayi, tana cewa."ni dai Inna bani na sha yanzun zaki fara kallar wanann maganar taki ba dadin ji,ki tasa mutun yana jin kunya." ai Rumaisa tana cikin sha taji message ya shigo wayar ta nan ta fara karantawa..
_Yau din na kin zama tawa halak malak, inyi yanda nike so da yarinya ba mai ce man dan mi, congrats Rumaisa Fadil, yau kin zama matar Aure.._
Nan take Rumaisa ta fasa ihu, da man mai neman kuka, an gaya mashi mutuwa
,kallonta Inna tayi sannan tace.

"ooo ni Fadila yau ina ganin zamani, shine kika kama kuka, daga anshi kisha?

To ajiye ki tashi mujo gun iyayenku su yi maku fada, tunda ba ku za'a tsaya jira ba." Ida shanyewa Rumaisa tayi, ta cigaba da kukan ta itadai bata ce ma Inna komai ba.

Nan aka kaisu part din Abba yayi masu fada, da fatan alkhari, sannan Baba, shima yayi masu fada, yi nayi bari na bari subi mazajensu, banda biyema shawarar kawaye...

Dan ga nan kuma suka wuce part din Umma, Umma tayi masu fatan alkhari, sai Mama itama ta fadi ta bakinta...

Nan aka fito da Fadila za'a tafi da ita, nan suka rungumi junansu suna kukan rabuwa, sai da Fadil ya shiga tsakaninsu yana ma Rumaisa magana a hankali yanda ba mai jinsu sai ita daya, yace."Haba princess, kukan ya isa haka mana, sai kace gidan makiyanku za'a kai ku, ai kyau kuyi murna ma, zaku zama cikakiyar mace."
(team Rumaisa kunji abunda Fadil yace
Haka aka tafi da Fadila tana kuka, Umma na kuka, Rumaisa na kuka, Mama ce kawai tayi karfin halin basu hakuri..

Bayan sun isa unguwar da za'a kai Fadila a kano..

A parking space duk aka tsaya su Hajiya Zainab (yayar Umma ce) ne suka fito da amarya daga cikin motar Saif fuskarta na rufe suka ka mata aka nufi cikin gidan inda sauran mutanen suka take masu baya a dai dai bakin k'ofar da zata sadaka da cikin gidan aka ja aka tsaya inda amarya tayi addu'a sannan aka ida shiga Masha Allah tun daga nan aka fara santin gidan amarya saida aka shiga part d'in da yake mallakinta inda aka zuba mata kaya abun sai wanda ya gani ana shigowa parlour ne da yasha tank'ama tankaman kujeru royal brown and milk color sai faskekiyar plasma da aka yi ma gefenta decoration din well stickers, daga chan gefen haggu kuma wani dining area ne da ya sha ado masha Allah,
inda suka nufi wata k'ofa dake gefen dama ana bud'ewa wani parlourn ne maroon color aka zuba leaders cunshen masu bala'in kyau,
mai d'auke da room uku d'aya daga cikin room d'in aka shiga da ita nan ma komai na ciki royal ne Ash and black Color an tsara mata bedroom d'inta sosai abun sai wanda yagani haka jama'a suka dinga bin gidan suna tofa albarkacin bakinsu itadai amarya kuka kawai takeyi har aka zaunar da ita saman gado, sannan yan kawo Amarya suka fita gani gidan..
______________________________
Tunda aka tafi da Fadila, Rumaisa ke aikin kuka, sai da su Abba suka gama yi ma Fadil fada,kallonshi Abba yayi sannan yace."inka rigeta da Amana yar'uwarkace, in kayi akasin haka ma yar'uwarka, dan haka kaji tsoron ka daura turbar adalci a gidan ka, ku tashi ku tafi Allah yayi maku albarka." "Amin ya Allah, Abba insha Allah ba zakuji Abu marar kyau ba a rayuwar auren mu." Fadil yace haka yana mikewa sai fita, kamo hannun Rumaisa yayi ya bude mata nota ya shigar da ita, sannan shima ya shiga, daga ma su Mama hannu yayi sannan suka wuce gidansu suma.
Chapter 25 · 0% Book details