Sashe 28
A Gidan Haya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kwanaki sun sude, shakaru su sude, abubuwa da dama sun faru mai dadi da marar dadi, dan Allah ya anshi rain Inna Fadila, dan Fadil da Khamis sunyi rashin mahaifiya, sai dai muce Allah ya basu hakuri...
Bayan rasuwar da wata shidda Rumaisa ta sake haihuwar yan biyu duk mata yara sunci sunan Hadiza da Fadila...
Itama Fadila ta sake haihuwar mace ansa mata suna Rumaisa, suna kiran yarinyar da suna Ruma...
Su halimai, duniya ta juya mata baya, dan yanzun Halimai bata da hannu daya, dalilin ciwon cancer da tayi shine aka cire mata hannu, Rumaisa ta biya kudin aiki.
Bayan sakinta da mijinta yayi, tayi kukan nadama, sannan Rumaisa ta saya gida taba Halimai take zaune, tabbs Halimai tayi nadama tagane HASSADA ba abu bane mai-kyau.
______
Ita ko Lami tabi gaskiya, dan ta gane *HASSADA* ba abu bane mai kyau, ita duniyar duka nawa take da zaka tsaya kana yima wani *HASSADA* , ta nemi yafiyar Rumaisa, akan abunda suka kama yi mata ita da su Halimai.
Kuma tana kaima Halimai ziyara, idan ta samu dama, itama Mijinta Allah ya hore mashi yayi gidan kanshi.
_________
Ita ko Hindatu, mijinta ya kamata da karto har cikin daki suna lalata, yayi masu mugun bugu sannan ya saketa saki uku, yanzun haka Hindatu bara take a kan titi ga tana fama da cutarb HIV.
Watarana Rumaisa tana cikin driver taga Hindatu tana bara, parking din motar tayi., aiko da gudu masu bara suka doso wajen Hindatu ce ja gaba, zuge glass din Rumaisa tayi, sannan tace."Hindatu kece nike gani ko kuma mai kama dake ne."!?
Sai da Rumaisa tayi magana sannan ta gane Hindatu ta ganeta, kuka Hindatu ta fashe dashi tana cewa."Rumaisa yanzun kice kika zama Hajiya?
Kaicona ni Hindatu kaico mai hali irin nawa, tabbs na biyema shirin zuciya da kuma zaga ta Halimai mukai ta wulakantaku muna binki da shirin zina, sai ga shi sheri ya fada mana, kinga yanda Allah yayi dani Rumaisa, na tabbata alhakinki ne ke binmu, dan Allah Rumaisa karki duba abunda mukayi maki, dan ko munsan mun cutar dake, ki yafemana saboda da Allah."
Kallonta Rumaisa tayi, sannan ta bude mata mota ta shigo suka tafi gida tare, ruwan wanka
ta hada ma Hindatu bayan Hindatu ta fito wanka kaya ta bata tasa Sannan Suka ci abinci tare, kuma tace ta yafe mata, gidan Halimai ta Ka
ita tace su su zauna tare, sannan tace ma Hindatu ta ringa zuwa tana ansar magani kuma duk wata tana aiko masu da abinci da kuma kudi.
______
Rumaisa ce kwance bisa cinyar Fadil, kallonshi tayi sannan tace."Prince." cewa yayi.
" Naam princess." cigaba da cewa tayi "ya shara'ar Allah yasa ku kayi winner."?
Murmushi yayi sannan yace."Eh Alhmdulh princess, mun gama cases
munyi winner, da man muke da gaskiya, ake ta bata lokaci ga gaskiya suna gani, amman su kulle ido su tsaya suna kare marar gaskiya a kan karya." cikin jindadi tace."hakane gaskiya, Allah ya kara taimakawa.".."Amin, gobe ne fa ake yinkarin girman nan." cewa tayi."eh duk mun shirya, Allah ya kaimu goben Allah."
Washe gari duka ahalin Mai *DAKO* suka hallara gun da ake ma *BARISSTER FADIL KHAMIS MUHAMMAD* *DAKO*
arin girma,
taro ya ansa taro manya barissters na Nigeria sun zo inda aka nada barisster Fadil *CHIEF OF JUSTICE*
na *KANO STATE*,
baki daya...
Nan fa Fadil ya tashi yayi speak inda yake godiya da matarshi Hajiya *RUMAISA FADIL MUHAMMAD DAKO* , sanann ya maika godiyarshi ga iyayenshi da yan'uwa da abokan arziki..
Anyi walima, anci ansha, anyi hanikan,Fadil ne ya shigo cikin room din da Rumaisa suke ita da Fadila, Cewa yayi."princess zo kiga wani abu, kema Maman Deejat taso mu tafi." wani dakine ya kaisu nan suka tadda *SADIQ* yazo shida *NANA* *JAWAHEER* , sai *KHALID* da *ZAINAB* , sai *LUKMAN* shida *SALMA,na* *NANA* *JAWAHEER*
suna cikin murnar ganisu tana waigawa ta hango *GIMBIYA HAKIMA DA SARKI HAKIMA NA CIKIN GIMBIYA HAKIMA* suna cikin murna sukaji anyi gyran murya waigawar da zasuji sukaga
*SOFY* itada *ALIYU* Na *SANADIN LINK*
, abun dai ba'a magana dan harda *SADAUKIN BURHAAN* yazo shida *HUSNARSHI* DA *ZUBAINA* suma sunzo taya Fadil murna Karin girma da ya samu, nan su matan suka tafi bedroom din Rumaisa suka zauna suna labari da ba juna shawarwari, suma haka su Fadil suna labari da yanda zasu kugadanar da wani kasuwanci baki dayan su Anan kano, nan suka fito cin abincin rana, sun ci abinci cikin farin ciki da annashuwa...
*ALHMDULILLAH RABBIL* *ALAMIN*
Anan na kawo karshen wannan littafi mai suna *A GIDAN HAYA* ,kuskuren dake ciki Allah ka yafemin,abinda na rubuta daidai kuma Allah kabani ladan,nagode nice taku har kullum
Jameey yar'mutan kankia
semun hadu cikin sabon book dina me suna
ARAWO NE*
'''Ai da kunji ance
ARAWO NE kun san akwai cakwakiya da sirkarkiya a cikin book din kudai ku biyo ni,
karki sake a baki labari
*~KADAN DAGA CIKIN
ARAWO NE~*
Karfe Uku na dare, gari yayi shiru bakajin motsin komai, sai kukan karnuka da mujijo, wani mutun ne na ga ya haura wani gida ya shiga, shigar shi keda wuya naji ana."Ihu barawo!
Ihu barawo!!
Ihu barawo."abunda ake cewa kenan, sai zunduma abun wannan ihun ake, suna neman taimakon mutanan unguwa Amman shiru kake ji ba wani motsi, jin shiru yasa nayi saurin shiga dan na kwaso maku rohoton abunda ke faruwa, ina shiga naji ana cewa."Kai Alhaji zaka yi man shiru ko sai na fasa maka kai da wanann bundugar?
Na tarwatsa maka gwakwalwa." cikin karma da tsoro gami da firgici wanda aka kira da Alhaji yace." Nayi shiru, Amman Dan Allah mai nayi maka bawan Allah?
Mai kake nema wajena." murmushin gefen baki wannan
arawo yayi sanann yace."Kudi!
Kudi nazo ansa a wajenka, idan ka bani kudi shikenan zan tafi ba ruwana da kai." kallon bindigar da
arawo yasamashi bisa kai kawai yake, cikin tsoro yace."To!
To!!
To!!!
Naji Dan Allah karda ka harbai ni da wanann bungugar, indai kudine ga su'nan." Allah Sarki, nan Alhaji Nura ya kwaso kudi masu yawa ya ba wannnan
arawo, Wanda ya boye fuskarshi da facemask shiyasa baiga kwayar idonshi ba.
Yana amsar kudin ya Kama gabanshi da sauri ya fita gidan Alhaji Nura, yana fita ya cire mask din fuskarshi.
Sannan ya shiga gidansu, wani gidane yanda kukasan kango dan baida banbanci da akirashi da suna kango.
Yana shiga, yaga mahaifiyarshi a tsakar gida, nan ya fara tambayarta cikin tashin hankali, dan baiyi tunanin zai taddata ido biyu ba, kuma yasan mudun ta ganshi waje zata tuhumaishi abunda ya fiddashi waje, cewa yayi."UmmiYa akayi naga kintada hankalinki?
Ai nasa tuni bacci kike." cikin tsoro da firgici tace ma mashi."Mustapha Ina'ni ina bacci, ko bakaji anyi ihu
arawo ba a gidan Alhaji Nura."!?
Tayi mashi tambayar cikin tsoro dan tunda taji anyi ihun farko a cikin kunnanta akayi shi, shiyasa ta tada hankalinta, kallon Ummin tashi yayi, sannan ya kamo hannunta ya zaunar da ita cikin dakinta sannan yace."naji wallahi Ummi, ai shiyasa na fita Amman banga
arawon ba, dan da alamu ya Samu ya gudu." numfasawa Ummi tayi sannan tace."Kash!!
Allah dai ya shiga tsakanin na gari da mugu, suma wannan
arayin Allah ya shiryasu, su gane hanyar gaskiya." kallonta Mustapha yayi sannan yace."Amin ya Allah Ummi, yanzun dai Ummi ki
kwanciyarki kinga dare yayi sosai." cewa tayi."To shikenan, kaima kaje ka kwanta, kafin Allah ya kaimu gobe musan yanda zamuyi akan wannan kudin na registration dinka Mustapha, abun yana damuna amman insha Allah zan fita na samo koda bashi ne." tashi yayi yana cewa."To ummi sai da safe." kwantawa tayi tana cewa.
"Allah ya kaimu."
Bayan Mustapha ya shiga dakinshi da bakomai a cikinshi sai wata tsohuwar tabarma wanda da ita gwanma babu, ya zauna ya fara aikin kuka yana fadin..
"Na shiga ukuna ni Mustapha wanna wata kallar rayuwace na daukarma kaina?
Wai ni Mustapha yanzun ni akeyi ma ihu barawo kaicona da wannan bakar rayuwa."
Yana cikin wannnan hali wata zuciya tace mashi inbaiyi sata ba ai da yanzun bai kai 600level ba, tunda baida kudin da zaiyi registration.
Haka Mustapha yai ta tunani yana tur'da hali irin nashi, domin shi ya san halinshi ba hali bane mai kyau..
Nan ya dauko kudin da ya sato wajen Alhaji Nura ya lissafasu yaga dubu dari da hamsin ne, nan yaji wani kallar dadi ya mamaye mai zuciya, dan sunkai yanda yake bukata harma sun wuce.
Dan haka shima gobe zaije yayi registration,
dan yaji ance sun kusa closing din portal dinsu.
Bayan Mustapha ya gama lissafa kudin registration ya tashi yayo alwallah ya fara sallah, yana kuka ya neman gafara wajen Allah, ya roki Allah ya kawo mashi karshen wanann wahalar da yake ciki.
Sanann ya kawo mashi mafita a cikin rayuwarshi, shine bai kwanta bacci ba sai da ya dawo daga sallahr asuba, sannan ya kwanta bacci bayan ya gama azkar din safe.
Shine bai tashi ba sai karfe goma na safe sanann ya tashi yayi wanka ya wuce wajen Ummi, zaunawa yayi sannan yace."Ummi ina kwana."?
Kallonshi Ummi tayi tana murmushi sannan tace."lafiya lau Mustapha ga tuwanka can na ajiye maka tashi ka dauko ka ci." girgiza kai yayi sannan yace."Ayyya Ummi na koshi kedai ki dauka kici, dan nasan baki ciba kika ajiyeman." kallon
a'n nata tayi tana jin sonshi yana kara shigarta, domin yanason farincikinta cewa tayi."Kai dai kaci Mustapha waya gaya maka ban ci ba?
Dan haka kayi maza kaci ni yanzun gidan Alhaji Nura zani nayi masu jajen wannan abun da ya samaisu jiya." murmushi yayi mata, sannan yace."Dan Allah Ummi ki tsaya kici , ni yanzun zan tafi wajen Kamal nasan zansamu abunda naci, sanann kuma daga nan zan wuce makaranta nayi registration na samu kudin." kallon mamaki tayi mashi, tana mamakin ina ya samu kudin registration, cewa tayi fuskarta babu wasa."Kudi Mustapha ina kasamu kudin registration."?