← Book details A Gidan Haya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 30

Sashe 2

A Gidan Haya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kin gani yau Kuma sai yanzun."cewa Hajiya Maryam tayi."aiko dai yanzun Fadila ta gama tambayar ki, zaki raka ta wai kunshi, ta gaji da jiranki, sai Yayansu yayi dropping din ta ya wuce wajen aiki."cewa tayi."ayya banji dadi ba, ai da na raka ko mike kafafu nayi tunda yau babu Isilamiya yau, ai shiyasa ban zo da wuri ba."
"Nikom nace Rumaisa yaushe zan baki waka kiyi man awara, kinsan Fadil yana bala'in san awara, gashi yau na ida soya mashi ta cikin freeze, nasan gobe dan Ubanshi sai munyi fada da Shi in yaji babu awarar."..

Murmushi tayi sannan tace."Shi dai Yaya Fadil yana son awara naga Alama, bakomai Aunty bari na ida aiki yanzun naje nayi maki ita zuwa anjima nagama insha Allah."
"Bani takura maki ba dai ko Rumaisa."?...cewa tayi."haba Aunty wata kallar takura, ai kifi karfin komai a guna."..

"To nagode Rumaisa, bari na tashi ya dibo wankan kafin ki gama."cewa tayi."To Aunty a fito lafiya."..

"Allah yasa."
Bayan Rumaisa ta gama yin aikin gida, ta ansa waken ta wuce gida, tana mamakin yanda Fadil yake da halinshi, shide haka Allah yayo Shi cewa tayi."ni Rumaisa ai tunda nike ban taba ganin dariyarshi ba, gaskiya Fadila tana hakuri da Allah ya hada ta da Yaya mai halin Fadil ace mutum baya dariya kullum fuskar shi tamau sai kace an aiko mashi da sakon mutuwa."haka ta kama maganar ta cikin zuciya har ta isa gida, dan tayi alkwarin baza ta sake yi masu sallama ba, in ba dai su Maman A'i ta iske ba a tsakar gidan wannan zata yi mata sallama har ta gaidata domin Maman A'i mace mai hankali da wayau...

Dawowar Rumaisa gida kenan tace."Mama ga aiki awara nan zamu sake yi ma Aunty Maryam." murmushi Mama tayi tace."A'a to bari na fito daman zaman banza nike yi bani da abun yi."nan fa Mama ta fito cikin some minute suka tsinke wankan, nan Rumaisa tasa hijab takai markade, tana dawowa suka daura sanwar awararsu, suna fira da Maman A'i, nan Hindatu ta fito tana yi masu wannan kallo sanann tace."Allah ka rabamu da matatsiyar zuciya, in ba rashin zuciya ba, mutane sai dan banzar kwakwa, in ba kwakwa ba ace duk sanda za'ayi awara kuke yinta dan ku samu na dare."
Maman A'i tace."Ai Hindatu kasan ance *NEMAN NA KAI,*
*HALAK NE,* dan haka ba ruwanki da lamarinsu, ya ka mata ku chanza hali, haba Hindatu mutanan nan basu tsarema ku komai ba amman duk kunbi ku sa masu ido, Kuma ku ke da abun da ido."
aga ma Maman A'i hannu Hindatu tayi tana cewa."dakata malama, au ashe yar iya Andawo?
yanzun za'a fara yin shigar sugula, inba shigar sugula ba wa ya saki cikin wannan maganar yar'nema."?

Cewa Maman A'i tayi."Ban sani ba sai naji bugu sannan."Maman Rumaisa ce ta fara ba Maman A'i hakuri dan taga ranta ya fara
aci yanzun zata biye masu suyi fada cewa tayi."Dan Allah Maman A'i kiyi hakuri, karda ki biye mata, duka duka maiye duniyar, da za'abiye Anita bata lokaci gurin fada, kinga ma awarar ta kusa yi muna gama soyawa sai mu shiga daki ba shikenan ba." cikin raina da jin zafi da hassada Hindatu tace."da ya fi maku ma kwakwata banza da ku."Maman A'i tace."ke dai kije ji da shi, mundai yi gaba sai dai a bimu da ido."
"Maman A'i dan Allah kibar biye masu, mutanan nan ba hankali ne dasu ba." Cewa Maman A'i tayi."wallahi Maman Rumaisa, indai su kayi bisa idona sai na yi magana, yo ina dalili mutane ba ku hada miji ba, amman sunbi sun sa maka ido suna kishi dakai, ai wannan kishi ne da hassada, haka zasu kare a wulakance, mu Kuma insha Allah yanzun muka fara yin gaba, dan munyi masu nisa fidtinkau, dan ba yabon kai ba baki daya gidan nan mazajenmu sunfi sauran nasu, ai Alhmdulh ko nan aka tsaya."cewa Maman Rumaisa tayi."Allah yasa dai mu dace, "Amin Maman Rumaisa...

Bayan sun gama yin awarar, Rumaisa taje ta kaima Hajiya Maryam, nan suka dan yi hira sannan tayi mata sallama ta dawo gida direct dakinsu ta wuce, daman tsakar gidan su Lami ya iske suna zaman banza, zaman gulma...

"Rumaisa har kin dawo?

"Eh Mama wallahi yau duk na gaji sosai, "ai dole, tashi kici abinci ba sai kin tsaya jiran Babanki ba, "To Mama." bayan ta gama cin abinci ta samu ta kwanta cikin bacci taji ana fada da mijin Halimai da na Lami, suna ta fada sai kace yara kanana,
wai abunda ya hada su, shi mijin Lami yace ma mijin Halimai yayi ma Halimai tsakani da matarshi dan ya lura ita take koya ma Lami zaman gulma da kirbibi, shi kuma mijin Halimai yace suna koya ma juna dai, dan matarshi ba ma gulmaciya bace, da kyal da jibin koshi su Baban Rumaisa suka raba wanann bala'i...

"Na boni ni Rumaisa, wai har sai yaushe mutanan gidan zasuyi hankali."Rumaisa tace tana mamaki dan
tunda suka zaune a gidan nan bata taba ganin rana ta zo ta koma ba, ba'ayi fada a cikin gidan ba sai kace antara karnika a cikin gida, haba Allah ya sawaka ya yaye masu wannan masifar da ke damunsu....
*Tabbas naga ruwan comments dinku sosai, sai kash abunda baiyi man dadi ba
, sansanin yar'mutan kankia, bakuyi comments ba, haka real jameey fans
one and two comments dinku yayi man kadan gsky
, Mudun baku gyara ba zan daina yi maku posting
*Yar'mutan kankia ce
Share
Comment
Vote
And
Like
A GIDAN HAYA
_STORY AND WRITING_ _BY_
_Jameelah jameey_
*Yar'mutan kankia ce
MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION
*M.

W.

A*
'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
___________________________________
*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Page_5-6
Washe gari, bayan su Rumaisa da Mama sun gama wakansu da wanke
2,suka dumama tuwan da ya rage masu sukayi kalaci bayan sun gama yin kalacin, Rumaisa taje dakin Maman A'i tayi mata karin karatu ita da A'i, bayan ta gama yi masu ta wuce gidan aiki..

"Sallama Alaikum, "Amin w'alaikumus sallam, Rumaisar Mama har anshigo kenan."?..."Eh wallahi Fadila Allah ya yarda, jiya Aunty ta
ce man kin jirani zani raka ki gun kunshi."cewa Fadila tayi."Eh wallahi, ashe ma mota ta bata da mai, sai da na shiga na kuna tace bata san wannnan ba sai dai Yaya Fadil yayi drooping din na, karki so kiga kallar wulakacin da nasha jiya kawata, Allah yaso ki ba baki biyo ni ba inajin yanda kike da saurin fushi sai kinyi kuka."cewa Rumaisa tayi cikin mamaki."Ke ko wannan wani irin wulakanci ne?da har zaisa mutum kuka?

"wai zan shigar mai da datti cikin mota, duk kuwa wankan da nayi amman Yayi Fadil cewa yayi datti ke gareni kiji fa kallar wannan wulakancin da cin fuska?
kuma ba'a fita motar sai yayi 15min ta kashe ta, sannan zaka bude ka fita, ai na gaya maki na manta shap da wannan roles din nashi yana tsaya wa na kama marfin mota zani fita, kinga wata kallar tsawa da ya maka mani, wallahi bansan Lokacin da nayi Ihu ba, kuma dan nayi Ihu wai nasa mashi ciwon kai, ke dai wallahi ina tausayin matar Yaya Fadil."cewa Rumaisa tayi."Ha haha haha!
gaskiya Fadila sannu kiyi kokari, ai in nice da tuni munyi ta ba dadi, kin san Allah ni bani san tsawa ko ya take, ni fa lokacin damuna bani yin motsin kirki saboda bala'in tsoran tsawa nike, balle wannan Yayan naki ni ko dariya ban taba ganin yayi ba, maganar fatar baki bani fatan ta hadani da shi, shiyasa nagode ma Allah banda dakinshi nike gyarawa."cewa Fadila tayi."To ai shi Yaya Fadil koni baya cika san ina shigar mai room ba, balle yan aiki."...

"To ai muma yan aiki an hutar damu ko Fadila."?

Cewar Rumaisa tana murmushi, itama Fadila cewa tayi."Aiko dai, shiyasa yake gyara wajen shi, in kinga part din Yaya Fadil sai ki rantsa kice dakin amarya ne, saboda tsatarshi."Cewa Rumaisa tayi."yajii dadi, niko inason mutun mai tsata sosai."Umma tace ta fito zata wajen aiki ta gansu suna ta aikin surutu tace."Kuna nan kunata abun surutun naku ko."?

"Aah Umma, kawai dai ina gaisawa da kawata."cewa tayi."ai Fadila kinsan nasan gaisawarku ke da Rumaisa sai kuyi awa daya kuna ta zuba, da anyi maku magana sai kuce wai gaisawa kuke."Rumaisa tace tana murmushi.

"Aunty ayi hakuri yanzun zamu tashi insha Allah."Umma tace."Allah yasa, ni na wuce office Fadila keda Rumaisa kuyi mana lunch."...

"To Umma mai zamu dafa."?

Umma tace."Ku yi komai yayi, amman ku san kunyi abunda Fadil yake ci karda kuyi abunda baya ci, yazo yaita yima mutane bakin rai."..

"to shikenan Aunty,
insha Allah."
"Kawata, bari nayi sauri na ida wanann moping din sai mu daura sauwar ko."?

Fadila tace."Eh Rumaisar Mama, amman bari na taya ki ko munyi sauri mu gama, kafin Yaya Fadil ya shigo."
Kallon ta Rumaisa tayi sannan tace.

"Fadilar Yaya Fadil, godia nike yar'umma.".... bayan sun gama yin aikin gidan baki daya nan fa suka shiga kitchen suka fara tunanin mai zasu dafa at the end Rumaisa tace tunda suna da garin dawa mai zai hana suyi tuwan dawa miyar danyar kubewa taji Nama da manya shanu, nan fa Fadila ta Amince, daya ke ita manyar tuwo ce, shap ta manta da Yaya Fadil dinta baya son tuwo, balle ma tuwan dawa..

Nan ko Rumaisa ta zage tayi tuwan dawa mai kyau, wanda kallo daya zaka yi mashi sai ka sake kallon shi tsabar kyaun da yayi, nan suka kulleshi a leda, sannan Fadila ta gurza kubewa ita kuma Rumaisa ta hada miya bayan ta gama hada miya nan take gidan ya gauraye da kamshi take yawun Fadila ya fara tsinkewa, tana ta yaba Rumaisa wurin iya gorki, ai suna cikin magana suka ji ana cewa."Ummana yau mai kike dafa mana cikin gidan nan mai dadi kamshi haka."?

Fadila ce tace."Laaaa ga Yaya Fadil, oyoyo Yaya Fadil, ai ba Umma bace take yin girki yau ba."wani kallo yayi mata sannan yace."wacece take yin girkin nasan dai ke ba iya girki kika yi mai kamshi har haka ba."?
Chapter 2 · 0% Book details