← Book details A Gidan Haya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 30

Sashe 4

A Gidan Haya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yanzun Halimai daman ke keyi mana satar Abinci a gidan nan."cikin tsorata Halimai ta juyo, ji tayi hankalinta ya kwanta tunda Hindatu ta ganta ba Lami ba, cewa ta fara yi."To ni yanzun ya zanyi Hindatu, kinsan idan Lami ta gane na dibarmata abincin
sai ta gayama wannan jarabanban mijin nata, ya zo ya wulakantani, kuma ni idan ban dibarma yarana ba bansan ya zanyi ba.", kallonta Hindatu tayi sannan tace."to nima Halimai bansan ya zaki yi ba, nidai ba ruwana, duk abu na da wulakanci na a cikin gidan nan to walllahi
bani yarda da yin sata ba, saboda ita sata bakin fantine, kuma kina yin sana'ar wankin ki, mai zai ja maki sata?
nida nike yin kitso da kunshi banyi sata ba sai ke Halimai."?cewa Halimai tayi."Ai Hindatu, ba laifi na bane."cewa Hindatu tayi."laifin waye."?kallon Hindatu Halimai tayi sannan tace."Laifin Barau ne, kinga idan Barau ya kama hanya tun safe ya fita ya wonshi, bai dawowa sai in zai kwanta bacci, shi bai barmana komai ba muda yara wanda zamu sumu muci abinci
yace baya da kudi, to ya ake so nayi Hindatu?

Kuma wankau yanzun ba kullum nike samu ba, bani samun kudi sosai ga yara sun damai ni da kukan yunwa, kinga ai dole na ringa dibarmaku abinci ina ba yarana."cewa Hindatu tayi."To kedai Halimai ki samu ki chanza hali dan Allah, dan sata ba hali bane mai kyau, kuma Tunda plate daya kika diba nasan Lami baza yi maki magana ba."
"Mama kina jin su Hindatu ko?

"Eh ina jinsu Rumaisa, Allah ya ra bamu da buduwar zuciya."Rumaisa tace."Amin Mama, yanzun shi Barau a haka yake so Allah ya bude mashi, bayan ya tauye hakin iyalinshi."?

Cikin jimami na rashin jindadi Mama tace.

"Kin dai gani Rumaisa, ita kuma mata zuciya ta mutu da bakin ciki da hassada, shiya basu ganin cigaba, saboda mutun bashi yaba kanshi rufun asiri ba, Allah ya bashi,Allah dai ya sa su gane."itama cewa tayi.

"Amin Mama, ni sai da safe."..

"Allah ya kaimu Lafiya.''
Kwantawa tayi, tana mamakin hali irin nasu Halimai, kuma ta wani wajen Halimai ta bata tausayi sosai, ba yanda za'ayi ace mijinta bai bata ko sisi, ga yara to taya zata cinyar dasu?
ai dole watarana tayi sata, dan Halimai sana'arta d'aya wato sana'ar Wanki, kuma ba kullun ake kawo mata wanki ba, ga Allah ya hada ta da dan iskan miji, wanda baisan darajar ta ba.

Ace mutum idan ya fita tun safe bai dawowa sai dare kuma bai bada kudin cefane, gaskiya Barau baida imani, ko daya, dan wannan
hali bana mutane masu imani bane.

Addu'ar
ta d'aya, Allah yasa gobe karda suyi fada da Lami, dan Lami watarana ba mutunci bane da ita, duk da tafi Halimai kyaun hali, komai take Halimai ke zugata.
*Ga fa dama ta samu masoyana ina masu bukatar karanta Izzah ko mulki complete, to nisa ta zo kusa dan yar'mutan kankia ta gama izza ko mulki
idan kina bukata, maza gwarzayo kiyi ma wannan numbers din magana 08160508316 ko 07034464517, sister karki sake abarki a baya fa
***************************
'''Niko nace Allah ya rabamu da miji mai hali irin na Barau, idan kuma Allah ya baki, tom Allah ya shirya maki shi, ya maidoshi hanya madaidaiciya, dan ko ana fuskantar wannan Marsalar, kaga mutun ya fita ya bar matarshi da yaranshi bai barmasu ko gishiri ba, kuma bai dawowa sai dare
, idan kace ya bada kudi ko gari a saya sai yace babu
, idan ta matsa da tambaya sai yace bari yaje ya saida shekaransa ya sawo gari
, babu ma magana maidadi da zata sa matar ta danji sanyi
, watan watarana ke uwa kina ji kina gani kike barin dan'ki yana bara gidan mutane
, ko kuma ya zama dan aikin unguwa dan kawai ya samo maku abunda zaku ci
, a haka kai kuma uba kake so Allah ya bude maka hanyar samu kana tauyema Iyalanka hakinsu
, wannan dai hali ni yar'mutan kankia nayi tir da shi wallahi
, Allah ya mudace dai
'''
*Yar'mutan kankia ce
Share
Comments
Vote
And
Like
A GIDAN HAYA
_STORY AND WRITING_ _BY_
_Jameelah jameey_
*Yar'mutan kankia ce
MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION
*M.

W.

A*
'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________________
*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*wannan page din naku ne Bilkisu D da Shuraihat da Mummy Musty kuyi yanda kuke so dashi*
Page_9-10
Bayan Rumaisa ta gama yin komai a gida, sannan tace."Mama ni zan wuce."kallonta Mamarta tayi yana murmushi tace."To Rumaisa kiyaye kinji."?

"Insha Allah Mama."Rumaisa tace nan
ta wuce warta gidan su Fadila, tana zuwa tayi aikin ta,
tayi komai da komai , sanann suka shiga kitchen itada Fadila da Umma sukayi masu Lunch, bayan sun gama aikin suka gyara ko'ina tsa suna cikin yin fira Fadil ya kira Umma waya ta turo mashi Rumaisa tayi mashi gyaran a part din shi, ce mashi Umma."kaga Fadil bani son shashanci kai har wani gyara za'ayi maka?

Kai ba halinka bane kiran yan'aiki, amman ya naji haka yau."?

Cewa yayi."Umma nasa kisan waye ni?to kawai ki turota please Umma, wallahi aiki zata yi man."numfasawa Umma tayi sannnan tace."shikenan gata nan zuwa."
Umma tace."Rumaisa tashi kije part din Fadil, yace kije zaki taya shi aiki."sosai gaban Rumaisa ya fara dukan uku uku, dan bata abunda zai ha
a ta da Fadil, dan ta lura ba mutunci ga gareshi, tana iya zuwa ya disgata yace ma mai ya kawota, nan take fuskarta tanuna bataso zuwa ba, abunda ba ta ta
a yima Hajiya Maryam ba, kuma ita Hajiya Maryam ta lura da haka, Rumaisa cewa tayi."To Aunty."girgiza kai Hajiya Maryam tayi tana murmushi, dan bata ga laifin Rumaisa ba dan taa nuna bata son zuwa apartment din Fadil, dan ko Fadila itama bata son zuwa wajen Yayan nata saboda mur
an halinshi, cewa Hajiya Maryam tayi tana murmushi."Amman Rumaisa kina ga mawa ki taho kinji yar albarka."? murmushin karfin hali Rumaisa tayi sannan tace."insha Allah Aunty."tafiya tayi
ta wuce part din Fadil jiki duk a sanyaye.

"Assalama Alaikum." Fadil ne yace.

"Amin wa'alaikumus sallam."tsaye Rumaisa tayi ta
i shigowa, cewa yayi."shigo mana kika yi man tsaye sai kace wani abu zanyi maki."?nan Rumaisa ta shigo, ta zauna kasa kan carpet din dakin, tunda ta shigo yake kallonta da gefen ido,ba tare da Rumaisa ta lura ba, sosai ya gama
are mata kallo sannan yace."Yauwa Rumaisa ko."?

Sosai
Rumaisa taji haushin yanda Fadil yayi mata question, amman cewa tayi."Eh Rumaisa."cewa yayi yajan latsa laptop gami da dan kallonta ka
an yace."Yauwa *RUMA* , da man gyara zaki yi man na duka apartment din nan, zan je na dawo na san kafin nadawo kin gama, inkin gama sai ki kai ma Umma keys din kinji."
aga mashi kai tayi sannan tace."eh naji."tashi yayi yana cewa."ok na tafi."
Nan Rumaisa, ta fara gyara parlourn kasa, parlour ne babba wanda yasha royal cunshen har guda uku, ga wani lafiyayen dining table nan wanda yasha ado da ruwan royals din, ga wata makekiyar plasma ta mamaye bango daya ga uban homethearters nan suma manya manya, sannnan ga uban Chinese carfect nan an baza a cikin parlon masha Allah...

Ash and black two set sunyi bala'in yi ma parlon sama kyau, shima ga wata yar medium din plasma taci kunsan rabin bangon, tana waigawa hannunta na dama ta hango wasu hotona guda hudu, daya nashine shi ya yana dariya yayi bala'in kyau, bata san lokacin da ta dauki hoton ba tana kallon nan ta kare man kallo..

Shidai Fadil farine kyaukyawan ajin farko, yana da hanci gashi da farfaden girji, ga idanu, idanun farare ne tas dasu, ga dan pink colour din lips dinshi dai-dai bakin shi, finally Fadil yana kama da *SIDAT* *KOKUREJA* , actor din *KING OF HEART* , dayan hoton kuma Shida Fadila ne su duka sunyi kyau suna dariya sun rungume juna, dayan kuma suda Umma ne sun sata tsakiya suna dariya sunyi bala'in kyau, na hudu kuma wani mutunine shima yana dariya, amman da alamun shi hoton wannan mutunin ba lokaci daya akayi shi ba, nan Rumaisa tace."ko waye ne wannan mutum shima yana kama da indiyawa."
Nan dai Rumaisa ta gama yin gyaran dakin, tana cikin yin gyaran dakin taga rappers din dollars baje saman bed dinshi, haka ta gyara bed din ta maida mai kudin shi inda ta gansu, ta fesa room freshener, ta dai gama komai sannan ta kaima Hajiya Maryam keys tayi masu sallama ta tahowarta gida..

Bayan Rumaisa ta dawo gida, ta iske Mamanta zaune ita
aya a
aki babu abokin fira, kallonta takr tana murmushi, sanann tace."Mama
Allah yayi nadawo."murmushi Mama tayi tana shafa gefen fuskar Rumaisa tace."to Alhmdulh
tunda an dawo lafiy , Yakika baro su Hajiya Maryam din."?cewa tayi tana mai kwacinya bisa cinyar Mamanta."Lafiya lau tana gaidaki ma Mama."cewa Mama tayi."ina ansawa, gaskiya Rumaisa Hajiya maryam tana da mutunci sosai, tana da tausayi da ina da abunda zansaka mata da na yi mata , amman ba hali sai dai na cigaba da yi mata fatan alkhari."cewa Rumaisa tayi."Haka ne ko Mama Aunty tana da mutunci ita da yaranta,kin san ko ina a gidan ta shiga nike, ga kuma ina
a ruwa da ita sosai, yanzun ba sanwar zamanin da bani iya ba, Mama kinsan yau har da bangaren baban danta na shiga ko ina a cikin part din, har da kudi masu yawa nagani.''zaro ido Mama tayi, tana mamakin irin yarda dasu Hajiya Maryam suka ba Rumaisa kuma tana jin dadin haka, cewa Mama tayi."Rumaisa dan Allah ki zamo mai rike Amana da alkhari dun idan kika samu kanki, karda ki kuskura ki zamo mutum mai son zuciya ta, har ta kaiki da kinci Amanar wanda ya yarda dake ya baki Amanar, ina neman wannan alfarmar a wajenki Rumaisa ko bayan rainane ki zamo mai rike Amana."cewa Rumaisa tayi."Insha Allah Mama, nayi maki alkhawarin zan zamo mai rike Amana da mutuncin kaina."cikin jindadi Mama tace."Allah yayi maki albarka kinji yarinya kirki."Rumaisa tana jindadin yanda Mama take sama ta albarka cewa tayi."Amin ya Allah Mamana ta kaina, uwar da tafi ta kowa, yauwa Mama
har yanzun Baba bai dawo ba ko lafiya."?
Chapter 4 · 0% Book details