← Book details A Gidan Haya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 30

Sashe 19

A Gidan Haya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A*
'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________________
*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Page_45&46
*Iye iye nanaye
, inji mawa
a, haka maganar take, idan Allah ya nufa zaka cigaba, zaka zama wani tam ba wanda ya isa ya hana, duk ko bakin cikin mutun da hassadarshi
, dan haka nidai Jameey yar'mutan kankia sai dai a ganni a kyale nan gani nan bari, idan ko aka shigoman gonata zan shafa ma
kwali nayi ma mutun abunda baya tunani, dan haka sai a kiyaye
_Masoyana kuna raina, kamar yanda nima nike ranku, inayinku over and over, soyayyar da kuke nunaman tana sani farinciki sosai
Kallon Fadila Rumaisa tayi yana girgiza kai sannan tace."Fadila taya zanyi shiru, bayan kinsan ina cikin matsala, masoyina baya lafiya,
amman fa Fadila Yaya Fadil Aman jini fa yake, ni ya zanyi da raina, nasan ban kyauta ma kaina ba."
Tashi Fadila tayi tana lailashin Rumaisa sannan tace."to yanda zaki yi da rainki, shine kiyi addu'a, kuma insha Allah ba wani abu ki ringa yimai hasashen alkhari, mana Rumaisar Yaya Fadil."zaunawa Rumaisa tayi tana cewa."To Fadila nagode sosai."murmushin karfin hali Fadila tayi sannan tace ma Rumaisa."yanzun tashi mu tafi mu daho mashi abincin kafin a fito dashi."girgiza kai Rumaisa tayi tana cewa."Aah Fadila kedai ki tafi ki daho mashi, nidai ina nan har sai naga an fito dashi."shiru Fadila tayi tana dan tunani na wani lokaci sannan tace."To Rumaisa, tunda baki zuwa, bari na kira Dear
yazo ya dauke ni, sai na hado mashi."cewa tayi."ki hado mashi harda tea please."harararta tayi sannan tace."shi da yace ban iya hada tea ba sai dai ke, amman zanyi dai dan baya lafiya,
bari na kira shi, mu tafi."
Dauko wayarta tayi, tana kiran Abdullah."Hello Dear, kana jina."daga can bangaren Abdullah yace."yes Sweety am hearing you, what wrong."?

Murmushi tayi sannan tace."Da man yaya Fadil yana hospital."tashi Abdullah yayi daga zaune sannan yace."what?

Kina nufin Fadil baya lafiya."?

Cewa Fadila tayi."Eh Dear
yanzun haka ina hospital, kazo ka dauke ni naje gida na hado mashi abinci."tashi Abdullah yayi yana cewa."ok wait for me am coming now." Cewa tayi."ok safe trip."waigowa Fadila, taga Rumaisa tana kuka,matsowa tayi kusa da ita tana cewa."Yanzun tsakani da Allah Rumaisar Mama, har yanzun baki daina kukan ba?

Shi yaya Fadil ba mutuwa yayi ba."
"Hmm
Fadila kenan baki san yanda nike ji ba shiyasa kike cewa haka."kallon Fadila tayi sannan tace.

"Uhmmm nidai na tafi kinga dear har ya iso." Cewa tayi."to Fadila ki gaida da man da Abdullah.".."to zai ji."
e hannuwanta tayi waje
aya, ta langwa
ar da kanta gefe tace."Dear sorry na barka tsaye." murmushi yayi, dan yanda tayi sosai tayi mashi kyau, cewa yayi."bakomai Sweety,shigo mu tafi ko."?

Shigiwa tayi tana cewa."ok, ya gida."?..."lafiya lau."..."ya Adda ta take."?..."tana lafiya lau,wai Sweety da yaushe aka kawo Fadil hospital?

Daga gidan mu yake,ya anshi motana zai je wajen Rumaisa." numfasawa Fadila tayi sannan tace."to wallahi ,muma anyi mana waya ance muzo yana asibiti,abun da mamaki da muka tadda Rumaisa tana kuka."murmushin ta
aici Abdullah yayi sannan yace."To may be ,itace tayi causing din matsalar ko."?

Shiru Fadila tayi na wani lokaci sannan tace."nima haka naki tunani,to ka bani some minute, yanzun zan fito." fitowa tayi zata shiga gida, dan har sun iso, cewa yayi yana murmushi."to a fito lafiya."
Fitowar Umma kenan, daga wajen Fadil, da sauri Rumaisa tazo wajen Umma tana cewa."Umma ya jikin yaya Fadil."?

Dafa mata kafa
a Umma tayi, kallonta tayi sosai taga duk ta rame rana daya kawai duk ta fita haiyacinta, girgiza kai tayi tana murmushi sannan tace."da sauki,yanzun za'a fito da shi a kanshi resting room." sauke naunauyar ajiyar zuciya Rumaisa tayi sannan tace."wash Alhmdulh,har naji sauki Umma." Umma Soyayyar dasu Rumaisa suke ma juna tayi, dan basujin kunya a gaban kowa suke nuna son junansu, cewa tayi.yanzun ina Fadila take."?

Cewa Rumaisa tayi."ta tafi ta hado mashi abinci,yanzun Umma ina iya zuwa na ganshi."?

Dakuwa Umma tayi mata sannan tace."Aah bacci yake, yana bukatar hutu,yanzun
biyo ni office zamu yi magana."
Fitowa Fadila tayi tana cewa."Dear har na gama,mu wuce ko."?ansar coolers din hannunta yayi yana cewa.Tom Sweety ,mu wuce." Sun fara tafiya Abdullah ya waigo ya kalli Fadila sannan yace."sweety." Cewa tayi."Naam Dear." Cigaba da driving dinshi yayi, sai da ya dauki lokaci sannan yace."ina son na tambaye ki."?

Shiru tayi sannan kuma tace."to ina jinka."cewa yayi."OK kinsan Fadil ya na son Rumaisa."?...."Eh na sani." Kallon Mamaki Abdullah yayi ma Fadil sannan yace."tun yaushe kika san Yayanki yana son kawarki."?

Murmushi Fadila tayi, dan taga yanda Abdullah yake mamaki dan tace tasan Fadil yana son Rumaisa, cewa tayi."ba tun yau ba na fahimci Yaya Fadil yana son Rumaisa." Murmushi shima Abdullah, yayi sannan yace."Tom bayan nan fa."? cewa tayi."Eh naso na fahimtar da ita Rumaisa, Amman sai tace ita mutuncine tsakaninta da Fadil,da naga bata yarda sai na kyaleta." Cewa Abdullah yayi."Uhmmm Sweety,to kin san Fadil ya gaya ma Rumaisa yana son ta."?

Cewa tayi."Eh to daga baya naji a bakin Yaya Fadil,a jiya kenan, Amman da man kwanakin baya Rumaisa bata zuwa aiki da wuri kuma da wuri take koma wa gida."
Kallonta Abdullah kawai, dan bai gamsu da maganar Sweetyn tashi ba,dan yasan Rumaisa ta gaya mata Fadil yana son ta, kin gaya mashi gaskiya kawai tayi, kuma ta manta shi Barrister ne, yana gane maganar gaskiya da karya, cewa yayi."OK nagode Sweety, mun iso ,ki gaida man da Umma, anjima zan dawo dan nasan yanzun Fadil bai farka ba.".."to dear byeee."
"Rumaisa, ya jikin Yaya."? kallon Fadila tayi sannan tace."da sauki sosai, yanzun aka kai shi resting room, muje ki raka ni office din Umma."cewa Fadila tayi." To bari na ajiye abincin ko."..."ok ina jiranki."..."mu tafi to." cewa Rumaisa tayi."Fadila yau naga bala'in karki so kiji yau yanda naji, ashe
haka SO yake." dariya Fadila tayi sannan tace." sai yau kika gane kenan yar nema."?

Shiru Rumaisa tayi, dan ta lura yanzun Fadila zata kama tsokanarta, shiga sukayi office din Umma, sallama sukayi.

"Sallama Alaikum." dago kanta Umma tayi sannan tace."Amin wa'alaikumus sallama, ku shigo, sai yanzun kike zuwa ko."?

Kasa da kai Rumaisa tayi sannan tace.

"Aa Umma na jira Fadila ne."harararta Umma tayi sannan tace."ai da yake keda Fadila nike nema."cewa Fadila tayi."Umma ba'ason muji mai zaku ce kenan."?

Harararta Umma tayi sannan tace."Ban sani ba, yanzun ku zauna."
zaunawa sukayi, kallon Rumaisa Umma tayi sannan tace."Yauwa
Rumaisa, kina jina ko."?

A sanyaye ta dago kanta tana kalllon Umma, dan rainta ya bata Fadil ba lafiya, cewa tayi.

"Eh Umma." kallonta sosai Umma tayi sannan tace."Fadil ya kusa ka muwa da heart attack."hawaye ne masu zafi suka zuboma Rumaisa kas tsadasu tayi, cikin inda indar kuka tace."heart attack Umma."?

Cewa Umma tayi."Eh ai ba wani abun tashin hankali bane, in dai mun bi hanyar da ya kama ta, dan yanzun aiki ya ganmu, mu duka baki dayanmu, dan yanzun ya zama dole mu guji abunda zai batama Fadil rai ko ya yake." cire glass din fuskarta Umma tayi, tana goge zufa sannan tace."Ya zama dole, ke Rumaisa daga yau ki fara nuna ma Fadil kalar son da kike yi mashi, dan shine zai sa ya samu saukin ciwon shi,dan haka daga yau sai ki fara naki aikin, muma zamu yi namu aikin, shi heart attack ba wani ciwon tashin hankali ba ne kin gane ko Rumaisa, kawai mubi abunda ya kama ta, abunda ya kamata shine mu kiyaye duk abunda zai
ata ma Fadil rai, kamar yanda na gaya maki a farko."
Cewa Rumaisa tayi."to shikenan Umma, insha Allah zani kiyaye." cewa Umma tayi."yanzun ku tashi muje na san ya tashi baccin yanzun, sai yaci abinci, anjima in nagama aiki mu tafi gida.".."to Umma." nan suka tashi suka tafi wajen Fadil, zaunawa sukayi sannan Fadila tace."Yaya Fadil, ya jikin."?

Cewa yayi."Da sauki Fadila, ina Umma."?

Cewa tayi."Ga ta nan shigowa ta biya ta fara ganin wani patient."cewa yayi.""ok shikenan." Kallonshi Rumaisa tayi sannan tace."Yaya Fadil, sannu ya jikin."kallonta yayi sannna yace.

"Alhmdulh Ruma, mai kika zo yi nan?

Mai zaki yi gun makiyin ki?bayan kince baki sona, wuce kibar wajenan kafin raina ya baci." Nan take Rumaisa ta fara kuka, ita kuma Fadila ta fita ta bar masu dakin, kuka take tana cewa."Haba Yaya Fadil, dan Allah kabar cewa haka."cewa yayi."taya zan bar cewa hak? bayan da bakinki kika ce baki Sona."cewa tayi cikin shagwa
e."to ai sharin she
en ne, wallahi INASONKA."tashi yayi zaune yana cewa."Ruma da gaske kina SONA."?

Cewa yayi."Eh Yaya Fadil."
aga hannuwanshi sama yayi sannan yace."Alhmdulh Allah na gode maka, ni nama samu sauki, suzo su sallamaini." cewa tayi tana murmushi."To ai baka ci abincin ba."kallonta yayi sannan yace."ai naji na koshi tunda kince kina sona,yanzun ba abunda ke damuna Ruma." cewa tayi.

"Nidai kaci kona yi maka kuka."ta fada tana harfa hannu tana bunbuga kafafu, ita a dole kuka zata yi..

Dafe kirji Fadil yayi, yana lumshe ido, sannan yace."Asssh Ruma, karki kasheni da Salonki, bani zanci, ai shikenan ko."?

Cewa tayi cikin salon kissa tace."Eh Ehmna." nan Rumaisa ta ba Fadil abinci da kanta har sai da ya koshi sannan ta barshi haka, Umma ce ta shigo tana kallon Fadil tana cewa."Aah patient din ne haka, kamar bashi bane yake rai hannu ga Allah ba." kallon Umma yayi sannan yace."ni Umma na samu sauki, da man lafiyata lau ai."dariya Fadila tayi tana cewa."laaa kaji Yaya Fadil, kai dai kace kai da Rumaisa kun dai-daita kanku." Kallonta yayi sannan yace."ke yaushe na fara wasa dake."?

Tareshi Umma tayi tana cewa."Aa kyale man Autata ta shana,
ka bari anjima sai mu wuce gida tare ni na wuce wajen Dr.

Musa."tafiya Umma tayi, ta barsu suna ta hirarsu cikin natsadi, Abdullah ne ya shigo sallama yayi.

"Assalama Alaikum."..."Amin wa'alaikumus sallama." suka ansa a tare, cewa Abdullah yayi."to wai patient din na mu ne haka."kallon Abdullah yayi yana cewa."hmm na samu sauki ai, kuma sai yanzun ka gadamar zuwa ko."?

Cewa Abdullah yayi."Aa nazo dazun lokacin kana duniya duniya lahira lahira."dariya yayi sannan yace."Aa sai dai lahirar baki daya."cewa Abdullah yayi."to dan lahira, yanzun Sweet sai ku tafi gida keda Rumaisa, ni sai nayi jinya ko."?
Chapter 19 · 0% Book details