Sashe 23
A Gidan Haya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Rumaisa.".."Naam Baba." Murmushi yayi sannan yace."naji komai daga bakin Maman ki, a kan maganar yaron nan Fadil, ta gaya man yanda suka yi da Mamanshi yaron, naji dadin haka sosai, amman dan Allah Rumaisa ki kula da mutuncin ki kinji."? cewa tayi."Eh Baba nagode sosai."
'''Wayyo Allah, Wallahi na gaji sosai
, typing ba sauki, gashi kunce dole sai anyi maku read more
, ni kuma wallahi ban son ya wan typing sosai
, amman ai bakomai book ya zo karshe dan bai fi sauran yan pages ba, ya kare baki da'ya
'''Ina yinku my fans I love you wujiga-wujiga, dan comment din ku shi ke sa man kwarin giwar yi maku yanda kuke so
'''
*Yar'mutan kankia ce
Share
Comment
Vote
Like
A GIDAN HAYA
_STORY AND WRITING_ _BY_
_Jameelah jameey_
*Yar'mutan kankia ce
MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION
*M.
W.
A*
'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________________
*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Page_53&54
A haka rayuwa, ta cigaba da tafiya, soyayya mai karfi ta kunnu tsakanin FADIL DA RUMAISA, da kuma FADILA DA ABDULLAH..
Soyayya wanann masoya suke babu kama hannun yaro, zumincin tsakanin Umma da Mama, suma abun sai gaba yake, wannan dalilin yasa Umma ta ba su Rumaisa wani part a cikin gidan.
Kallon Mama Rumaisa tayi sannan tace."Mama wai yaushe zamu koma gidansu Yaya Fadil da zamane?
Kinga Umma batajin dadi ace ta bamu wani bangare mu zauna a gidansu amman har yanzun bamu koma ba."
Kallon Rumaisa Mama tayi sannan tace."ba haka bane Rumaisa, nidai sai naga kamar bai dace ba, ace mun tare a gidan surukanki muna zama." Kamo hannun Mama Rumaisa tayi sannan tace." Mama su Umma ba irin wannan mutanan bane, su zasuyi ma mutun abu kuma ba gori har abada, amman yanda kika gani Mama." Suna cikin maganar Baban Rumaisa yadawo, yaji komai suka tautauna akai, zaunawa yayi,sanna yace." Hadiza kuyi sallama da mutanan gidan nan, yau da dare zamu koma gidansu Hajiya Maryam da zama, tunda ba tambayarsu muka yi ba." Murmushin murna Rumaisa tayi da Baba ya amince, itama Mama taji dadi cewa tayi." Shikenan insha Allah zaniyi duk yanda kace." Tashi yayi ya dauko abunda ya maido shi gida dauka sannan yace masu." Ni zan koma." A tare suka ce." Allah ya taimaka ya kawo kasuwa." "Amin." Yace sannan ya fita, fitowa Mama tayi tsakar gida, taddasu Halimai tayi zaune sun hada kai waje daya sai magana suke a hankali ga dukan alamun gulma suke, kallon banza sukayi mata a tare sanann suka kauda kai, bata damu da kallon da sukayi mata ba murmushi tayi sanann tace." Sannunku da hutawa ina kwanan mu."!?
Tsaki Halimai tayi sannan tace." Ke hutu ya gani, kuma da bamu kwana ba da kin ganmu."?
Dariya Mama tayi sannan tace." Hakane kuma Halimai, daman zuwa nayi muyi sallama yau zamu tashi daga gidan nan zamu koma gidan Hajiya Maryam da zama." Take fuskokinsu ta chanza, bakin cikine kwance kan fuskokinsu, tsaki Hindatu tayi sannan tace." Andai ji kunya wallahi, kinsan Allah Lami da nayi roko da bara kwara na mutun cikin gidan haya, amman da yake wasu ba su da zuciya anje anyi fadanci an samu anba miji aikin gadi,har ana shirin kome." itadai Lami cewa tayi." aiko dai Hindatu, ni banga amfanin zuwa wani yi mana sallama ba, mu daman anzo anyi mana bakebake cikin gida, ai mu dadi mukaji za'a tafi a barmana gida." itako Halimai bakin ciki yasa ta kasa magana, sai ma kallon Mama da tayi tace." munji dan Allah wuce ki bamu waje Allah ya raka taki gona." itadai Mama murmushi tayi sanann ta koma suka cigaba da hada kayansu, daman Rumaisa ta gaya ma Fadil dawowar tasu yau, aiko suma sukaje suka gyara masu part din da zasu zauna, Baba na dawowa suka kwanshe kayansu nasawa kawai kujerun dakin da gado harma wasu kayan sawar da kwanonin cin abinci, Mama su Halimai taba tace su raba,haka suka tafi suka barsu da kayan bakin ciki, kuma bayan tafiyarsu, harda fada akayi tsakanin Hindatu da Halimai akan kayan da Maman Rumaisa ta bar masu, dan ita Lami cewa tayi ta barmasu su raba, dan taga sun fita bukata tunda ita mijinta ba abunda baya sayar mata.
Su Mama sun dawo gidan su Fadil, da zama suna zaman su hankili kwance, amman duk da haka Baban Rumaisa ya na zuwa neman kudin shi, dan yace shi dai a barshi ya nema na kanshi, ba dan Hajiya Maryam taso ba ta barshi.
Yau ta kama ranar da Alhaji Khamis zai dawo cikin iyalenshi, dan haka kowa ya tashi da shirin tarbarshi....
__________________________________
*WUDIL-KANO*
"Malama." Wanda aka kira da Malama naga ta dago tsuhuwar fuskarta, dan da alamu ta tsufa sosai, dan dai bafulatace kuma tana da jiki mai kyau shys ba'a cika gane tsohanta ba sosai, cewa tayi."Naam Malan, ya na ganka haka?
Kamar wani marar lafiya."! ?
Numfasawa tsohon yayi, dan da alama da kaganshi kasan mijinta ne, cewa yayi."Lafiya lau, sai dai kwana biyu hankalina ya tafi wajen Fadil, ban san yanzun ko yana wani hali ba." Shiru Malama Fadila tayi, dan mijin nata ya soso mata inda yake mata kaikayi, amman bata zabi daurewa tayi sannan tace."Hakane Malan, shiyasa nike nuna maka, rashin dacewar hukuncin da ka dauka, ai in Khamis ya gudu ya barmu, bai ka mata ace muma mun tafi
mun bar dan karamin yaro, saboda san zuciya Irin tamu, mun tafi mubar yaro wanda bai wuce shekara goma ba a duniya, yanzun ko Yana wani hali?
Allah kadai ya sani." Cewa Muhammad yayi."Tabbas Malama, mun tabka baban kuskure, wanda in bamu gyara shi ba, mu ka bar duniya, gaskiya sai mun hadu da hushi ubangiji,
ya bamu amana mun watsar mun tafi mun barta." Girgiza kai tayi sannan
tace."Yanzun mai abun yi Malan."!?
Tashi yayi yana cewa."Abun yi shine yanzun ki tashi, ki hada kayan ki, dan yau insha Allah a Kano zamu kwana." Itama tashi tayi tana cewa."to shikenan Malan."
_____________________________
*KANO*
Alhaji Khamis ne ya shigo compound din gidan shi, parking yayi yana murmushi yanajin farin cikin dawowarshi cikin iyalanshi, duk da
abunda yaje nema bai samu, hawaye ne suka fara zubo mashi, dan da ya tuna tarin dukiyar da yake da ita, kuma ya tuna daginshi basu tare dashi, baisan a wani hali suke ba, baisan suna da rai a halin yanzun ba ko kuma basu da shi, yana cikin wanann hali , yaji an rungume shi ana cewa."Oyoyo, Abba sannu da zuwa." saurin goge hawayenshi yayi sannan ya jiyo yana murmushi, yace."Yauwa Fadila, ya na samai ku Auta."?
Cikin Murna tace."Lafiya lau Abba, sai dai munyi missing dinka sosai." lakutar hancinta yayi sannan yace."Nima nayi missing dinku." Fadil ne ya taho yana cewa."Abba sannu da zuwa ya hanya."!?
Rungumo Fadil Alhaji Khamis yayi, sannnan yace."Lafiya lau, Son, fatan kana cikin koshin lafiya."?
Shima kara rungumar Abbanshin yayi yaga cewa.
"Lafiya lau Alhmdulh, sai dai missing dinka da nayi sosai."shafa kanshi yayi sannan yace."Allah sarki barisster, Nima nayi missing dinka sosai." Hajiya Maryam ce tsaye tana kallonsu cikin farin ciki, cewa tayi."To masu uba, ai kun kyale man miji haka ko?
Ku barshi ya huta, kun hana
ko gani na yayi." Sakin yaran nashi yayi yana dariya sannan yace."oyoyo da girman kujeranki, uwargida ga Khamis Muhammad Dako." Murguda baki tayi sannan tace."uwargida kawai."!?
Dariya sukayi tare sannan yace.
"Aah Amarya ga Khamis Muhammad Dako."
nan Umma ta shige jikin mijin nata tana yi mai sannu da zuwa, tana sheda mai yanda tayi missing din shi, nan suka kwasa suka shiga ciki, sai da Alhaji Khamis, ya gama cin abinci yayi wanka ya huta, sannan Haji ya Maryam ta fara magana...
"Abban Fadil." Kallonta yayi sannan yace."Naam Umman Fadila, lafiya na ga tun dazun, kamar da akwai magana a wannan bakin naki." Kamo hannunshi tayi tana murzawa sannan tace."eh ina san na gaya maka da man, na taimaka wasu suna zauna cikin gidan nan, basu da gidan zama shine nace su dawo nan ita da mijinta." Kallonta yayi, yana mamaki sannan yace." Kina gani ba matsala Hajiya."!?
Kwantowa tayi jikinsa sannan tace."Eh ba matsala, ai yarinyarsu ma Fadil zai aura, da man jira nike ka dawo, sai a sa bikin nasu baki daya harda Fadila." Dariya yayi yana shafa jikinta yace."To To, masha Allah gaskiya naji dadin wannan labarin, insha Allah gobe zan gaisa da shi mahaifin yarinyar, sai musan yanda za'ayi komai, daman inasan naga Fadil yayi aure." Cewa tayi."To Allah ya kaimu goben Amin ya Allah."
_____________________________
*WUDIL KANO*
Malan Muhammad ne tsaye yana jiran Malama Fadila yana cewa."Shin Malama fito mu wuce ko."fitowa tayi tana cewa."to gani nan fito Malan, wai na tsaya yin sallama da Mutane ko."?
Cewa yayi.
"To kinyi kokari mu tafi, kin san garin mu da dan-nisa kadan." nan suka
je tasha suka hau motar Kano..
________________________________
*KANO*
Bayan mota ta sauke
su, suka tafi bakin titi domin tsada nape, suna tsaye Baban Rumaisa yaga iyayen nashi,
nan ya tsada napen , ya fito ya rungume Malan Muhammad yana kuka yana cewa...
"Maiyasa!
Maiyasa!!
Maiyasa?
Mai nayi maku har haka?
Kuka yanke man wanann hukuncin, kuka tafi kuka barni ni daya."!?
Kallon Baban Rumaisa, Malama Fadila tayi sannan tace."FadiiiiL, kaine dana."!?
Cewa yayi.
"Eh nine Inna." Sake cewa Baban Rumaisa yayi."maiyasa kuka tafi kuka barni."!?
Dafashi Malan Muhammad yayi sannan yace."yanzun fadil, labarin nan ka bari sai mun zauna, zamu gaya maka dalilin tafiyarmu muka barka.
Nan fa Baban Rumaisa, yasa ma iyayen nashi kaya cikin napen, sannan suka shiga suka kama hanyar gida.
Alhaji Khamis ne yace ma Hajiya Maryam."Hajiya, je kiyi man magana da Baban yarinyarnan Rumaisa." Cewa Umma tayi."Haba Alhaji, ai ka matayayi ka tashi mu tafi tare ka gaisa da shi." Cewa yayi."To shikenan,tashi mu tafi." Fadila tace."Abba nima zani." Kamo hannunta yayi yana cewa.