← Book details A Gidan Haya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 30

Sashe 13

A Gidan Haya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A*
'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________________
*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Page_29&30
Numfasawa Rumaisa tayi sannan ta cigabaa da cewa."Mahaifina, ya fara kama GIDAN HAYA, a nann rijiyar lemu, nan ne farkon fara zamanshi a gidan haya."
"Iyayena suna zaune cike da soyayyar juna, duk da Babana
ba wani mai hali bane, amman bai ta barin Mamana tayi kukan takauci ba, dan gidanshi ba'a kwana da yunwa, sannan duk satin duniya sai sunci NAMA ko KIFI, dan Babana mutun ne mai neman na kanshi bai dogara da wani ba, yasan dai Allah yana tare dashi."
"Haka suka zauna cikin Soyayya, Babana bai yarda wani abu ya samu Mamana ba, in ko tana bukatar wani abu sai inda karfin shi ya kare dan sai ya samarma ta, duk da na wata sana'a yake mai karfi ba, sana'ar ga ruwa yake a cikin garin Kano, amman bai yarda wani abu ya samu Mamana ba."
"A kwana a tashi babu wuya a gurin Allah, Allah yaba Mamana ciki, sunyi murna sosai, haka suka reni cikin, cikin kauna da jindadi."
"Ranar Lahadi 8/8/1999, Mamana ta haifeni, iyayena sunyi murna da samuna, sunyi ma Allah godiya da ya azarta su da samun
a ruwa, dan ko Babana har kuka sai da yayi dan murna."
"Ranar sunan naci sunan kanwar kakana RUMAISA, saboda itace ta rike Babana tun yana dan shekara goma a duniya, bai da kowa sai ita,shiyasa ana haihuwata ta mani sunanta wato Rumaisa."
"Babana tun yana dan shekara goma a duniya, ya rasa mahaifanshi kuma ba mutuwa su kayi ba ya wayi gari ya tashi babu su babu dalilin su, suda Yayan shi, suka barshi shi daya shine Ba'ba Rumaisa ta rike shi har tayi mashi aure."
"Na taso cikin gata da kaunar iyaye, ban san
wani abu ba wai shi talauci, duk da ba wani bane Babana, amman duk abunda ake sawo ma Yaro yayi wasa nima Babana ya siya man, har ma da wanda ban sani ba, duk yana saya man."
"Watarana
mai gidan da muke haya yazo shida wasu matasa majiya karfi, suka kama fiddo mana da kayan tsakar unguwa suna watsi dasu a kan santa."
"Mamana, tana kuka tana tambayar Alhaji Mala tace."lafiya Alhaji kuke zubda mana kaya cikin unguwa ko kudin kune bai biya ku ba."?

Wani matsiyacin kallo yayi ma Mamana sannan yace."Lafiya lau, jiya ya kawo mani kudin ma, ga kudin nan in ya dawo ki bashi kice ni Alhaji Mala nace, na gaji da zaman ku cikin gidana, dan haka bani makullin gida."
"Kuka Mama ta fashe dashi tana neman alfarma wajen Alhaji Mala, amman yayi uwar shigu da ita, haka Mamana ta bashi makuli tana kuka, nan Alhaji Mala, ya tafi ya barmu a kofar gida munata kuka nida Mama."
"Sai dare Baba ya dawo ya tadda mu cikin wannan bakin hali, haka ya kwashemu ya kaimu gidan Ba'ba Rumaisa muka kwana."
"Itama gidan haya ne, dan haka mu ukku muka kwanan cikin dakin ta nida Mama da ita Ba'ba
Rumaisa, shi kuma Baba ya kwana a soron gida."
"Washe gari Baba ya fita neman GIDAN HAYA a cikin garin Kano, amman ba inda bai je ba bai samu gida ba, haka ya dawo jiki duk a sanyaya, sai da Ba'ba Rumaisa tayi mai fada sannan ya saki jikinshi."
"Haka ma washe gari, ya sake fita neman GIDAN HAYA, amman bai samu ba, sai washe gari Allah yasa aka dace da wani gida a Kurna."
"Nan muka hada kaya muka koma Kurna da zama, mun tashi daga rijiyar lemu, mun koma Kurna."
"Mun cigaba da rayuwarmu a Kurna hankalin mu kwance, sai dai mu Kaima Ba'ba Rumaisa ziyara duk randa babu Isilamiya don na shiga Isilamiya a nan Kurna."
"Na shiga primary school,Lokacin Babana ya bar sana'ar Ruwa, ya koma hayar machine, wani Alhaji
sanusi ya siya mashi, yana bashi balance, tun rana...
*yawan comment yawan typing, dan gsky ba zan dunga yi maku typing mai tsawo ba, ku bakuyin comment dan haka ga wannan*
*Yar'mutan Kankia ce
Share
Comment
Vote
Like
A GIDAN HAYA
_STORY AND WRITING_ _BY_
_Jameelah jameey_
*Yar'mutan kankia ce
MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION
*M.

W.

A*
'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar
da masoyan ta.
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
___________________________________
*am back nagode sosai da addu'oinku, sannan kuma jiki da sauki Alhmdulh, karku manta yanzun muka fara wasan ku cigaba da biyoni a cikin a gidan haya kuma kuna surburbu
o man ruwan comment
*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Page_31&32
"Haka mukai ta rayuwa hankalinmu kwance, ba abunda ke damun mu, kuma kullun sai Babba ya
kai balance din ci nikin da yayi wajen Alhaji Sanusi."
"Ina primary 5,mama ta haifaman kani, ranar Suna Yaro yaci sunan KHAMIS."
"Khamis sunan yayen Babane, aka sa mashi , wanda suka tafi suka barshi shi daya, bayan anyi sunan khamis da kamar wata biyu, sai Mamana ta fahimci khamis bai da lafiyar kai, nan ne fa hankinta ya fara tashi."
"Saboda taga kullun kai shi girma yake yi, nan suka fara zuwa chemist, aka bashi paracetamol na yara, nan aka fara bashi magani, aga ko za'adace."
"Khamis yana da wata shidda a duniya , amman bai fara zama ba, balle akai da sa ran rarrafe, ga kuma kanshi sai girma yake."
"Don ba'a goya shi da zane daya sai biyu ake goya shi, daya ake tare kanshi sai dayan kuma a goya shi."
Kallon Fadil Rumaisa tayi sannan tace."Yaya Fadil lokacin sallah yayi."shiru yayi na wani dan lokaci sannnan yace."to Ruma, muje muyi sallah ki cigaba ko."?murmushi tayi tana wasa da zoben hannunta sannan tace."Aah sai gobe indan Allah ya kaimu."cewa yayi."A'ah Ruma please ki ida man yau mana."cewa tayi"Yi hakuri Yayq Fadil, amman ya dace ace na koma gida yanzun, Mama nacan tana jirana dan Allah ka bari dai sai goben."cewa yayi."to shikenan Allah ya kaimu, ammam ba dan naso ba zaki tafi Ruma, dan kawai Mama itama tana bukatar ki shiyasa zan barki ki tafi."cewa tayi."hakan ma ai nagode sosai."kallonta yayi sosai yakejin tausayinta balle yanzun da ya fara jin labarinta cewa yayi."gaskiya labarin ki yana da ban tausayi, Allah ya kaimu goben ki iya da bani labarin, ina san naji
ina khamis yake, don banji kina kiranshi ba."cewa tayi tana mai mi
ewa tsaye."Allah ya kaimu zaka ji yanda komai yake, sai da safe."cewa yayi."To shikenan, amman bari na dawo mosque sai na kai ki gida."cewa tayi."to shikenan, kafin kadawo nima nayi sallah."
Bayan Fadil ya dawo daga mosque ya dauki Rumaisa ya kai ta, yace ta gaida mashi Mama, sannan kuma zasu yi waya.

Tana shiga cikin gida ta tadda Mama tana jin redio, zaune ita
aya zaunawa tayi kusa da Mama sannan tace."Mama yau bacci nike ji sosai, gashi Baba bai shigo ba har yanzun."kallonta Mama tayi sannnan tace."ai kin bari ayi isha'i sannan ki kwanta ko kasa uwar yan bacci."?

Sunburo baki tayi sannann tace."Mama ai cewa nayi na gaji shiyasa zani kwanta, kuma ba naji ana kiran sallahar ba."murmushi Mama tayi sannan ta kalleta tace."tashi kiyi sallahr to, tunda baki cin abinci sai ai ta bacci."tashi tayi tana cewa."na koshi naci abinci a gidan Mami."tafiya tayi tayo alwallah sannan ta dawo tayi sallah, kallonta Mama tayi sannan tace."je kiyi baccin ki Rumaisa, ba yanzun Babanki zai shigo ba."cewa tayi taba mai tashi tsaye."to Mama sai da safe."har ta fara tafiya taji Mama na cewa."Au Rumaisa na manta ban gaya maki ba, gobe Maman A'I zasu tashi su koma gidan su na kansu."dawowa tayi ta zauna cikin nuna farin ciki tace."Masha Allah, gaskiya ina taya ta murna, sunyi gidan kansu, su huta da zaman GIDAN HAYA, Muma Allah ya nuna mana randa zamu yi gidan kaimu."cikin murmushi Mama tace."Amin Rumaisa."tashi tayi tana cewa."bari na kwanta Mama, gobe nayi mata murna."cewa Mama tayi."to sai Allah ya kaimu."..."Allah ya kaimu."
"Washe gari, bayan Rumaisa ta gama shirya wa ta biya tayi ma Maman A'I murna, ta wuce gidan aikinta...

Bayan sun gama yin komai ita da Fadila, suka kira Fadil suka ci abinci suka maida komai ma zauninsa, sannan ta wuce part din Fadil...

Sai da ta gama gyara part din tas, dan harda bedsheets ta chanza ma duka beds din da suke cikin part din nashi, ta wuce kitchen ta hada mashi tea ta juye a flask, ji tayi yana cewa."Ruma don Allah ki ajiye wannan aikin ki zo ki cigaba da bani labarin, baki san yanda na kosa ba."cewa tayi, tana mai tahowa."to gani nan, fara shan tea din mana sai mu cigaba."kallonta yayi yana murmushi kashe mata ido
aya yayi sannan yace."to bani nasha, amman Ruma kin iya ha
a komai kedai aa duniya."ajiye cup din hannunta tayi sannan tace."rufaman asiri, badai komai ba, Yaya Fadil duk santin ne kenan."dariya yayi yana ajiye nashi shima dan ya gama sha, yace."ai dole nayi santi, kedai komai naki daban yake Ruma, kin iya komai da komai."murmushi kawai tayi bace komai ba sannan ta cigaba da bashi labarin.

"Yauwa yaya Fadil, bayan ciwon khamis yayi tsanani, tunda baya zama sai dai kwanciya, nan fa aka fara kai shi asibiti GENARAL HOSPITAL, munyi kamar zuwa biyu su kayi discarded din mu zuwa AMINU KANO TEACHING HOSPITAL."
"Haka muka koma Aminu kano, aka bamu gado, amman shi gadon sai an bada kudin har dubu hamsin, sannan za'a bamu gadon da Khamis zai kwanta a asibiti."
"Ba inda Baba bai je ba, amman bai samu kudin ba, sai dai Mama ta sai da wani dan marakin sa din ta wanda ta gada wajen Babanta, aka biya kudin gado....
*karku manta ina kan bakana yawan comment yawan typing
, much love uh all my fans*
*Yar'mutan kankia ce
Share
Comment
Vote
Like
A GIDAN HAYA
_STORY AND WRITING_ _BY_
_Jameelah jameey_
*Yar'mutan Kankia ce
MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION
*M.

W.
Chapter 13 · 0% Book details