Sashe 80
A Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
a tsakanin. Ba abinda yake iya tunawa sai wanene Muhammed jadda da kuma irin hukuncin da zai iya dauka a kansa. Duk yadda yaso ma ya yiwa kansa hasashen ta inda zai fara kare kansa a gaban mutumin da a fagen aikinsa baida maraba da zakin daya fito farauta sai yaga sam zantukan daya tsara ko kadan basu hau kan saiti ba,basu kuma dace da hankali ba. Tsananin tsoron da firgicin ya sanyashi kashe wayoyinsa gaba daya,saishi kadai cikin dakin tamkar tsohon mahaukaci. Ba abinda kunnuwansa ke gaya masa sai sautin sallamar talauci cikin rayuwarsa,an debi kudin da ya tabbatar baida abun biya koda kuwa zai saida komai daya mallaka shi da danginsa su koma yawo tsirara. Taku biyu yayi don shiga toilet ya rage gudawar da yake fama da ita tun faruwar abun idanunsa suka fada kan dan kunnen. Gabansa yayi wani mummunar faduwa sanda kwanyarsa ta haska masa wani abu lokaci guda tamkar haskawar walqiya cikin duhun dare. Tsugunnawa yayi ya dauki dan kunnen.....sai yanzu ma ta dawo kwanyarsa,sai yanzu tunaninsa ya soma haska masa wani abu "Fateema?" Ta maimaita ainihin sunan da shine nasa STAMP din data bashi. Komawa yayi ya zauna saman kujerar dake daura da qofar bandakin yanason tuna yininsu na jiyan a tare. Yayi dukkan wani flash back daga qwaqwalwarsa zuwa zuciyarsa da kuma idanunsa,ba wani motsi nata guda daya daya bashi alamun rashin gaskiya a tattare da ita "To amma me yasa na farka na nemeta na rasa?" Ya jefawa kansa tambayar data sanyashi miqewa ba shiri,ya jawo wayarsa da baiyi shirin kunnuwa ba ya kunnata,cikin ransa yana jin gamsuwar tabbas ita ta aikata ko kuma tana da hannu wajen afkuwar komai. Sanda wayar ta daidaita sai ya fara yunqurin kiranta,saidai a duk sanda zai kirata din sai computer ta datse kiran ba tare da an masa bayanin komai daga danganci network ne babu a area din da take?,ko kuma wayarce dungurun gum a kashe?. Ci gaba yayi da gwada kiran babu qaqqautawa,har sai daya sare,energy dinsa yayi qasa,ya tabbatar bazai cimmata a waya ba. "Sai kayi tattaki ka sameta a inda take" Wannan shawarar ta sakashi zabura ya miqe,ya zura takalman qafarsa a gaggauce,saidai yana daukan key din motarsa komai ya tsaya masa cak "A ina take?,a ina kuma zaka sameta din?" Zuciyarsa ta jefa masa tambayar data kusa tsaida numfashinsa "Na shiga uku" Ya fada yana jin dukka jikinsa yana rawa "Bansanta ba,bansan komai a kanta ba" Ya fadawa kansa da kansa idanunsa suna tara hawayen da babu makawa sai da suka yiwa kansu qofa "Garin ya akayi haka?" Ya sake tuhumar kansa da kansa,abinda ya sanyashi sulalewa ya zauna a wajen. Yafi qarfin awa biyu zaune ya kasa hasalawa kansa komai,kafin daga baya wata zuciyar ta bashi wata guntuwar shawarar data dan bashi nutsuwa kadan,har ya iya miqewa ya gyara rigar jikinsa ya maida hularsa ya lalubi qofar fita. Dukkan wani muhalli da yasan sun taba haduwa,cin abinci,shan ice cream,shopping da sauransu ba wanda baije ba. Saidai duk inda yaje din dogon bayani ne maras fa'ida ko kuma alfanu,domin ba wanda ya ganeta. Abinda bai sani ba shine......ita din tamkar tarwada take a cikin ruwa......tana da matuqar santsi da idan taje waje zai wahala ka sake samunta a nan... Muddin taje waje dakai sau daya ta kansile wajen kwata kwata cikin jadawalin rayuwarta,ba guri bane da take mu'amalantarsa ba a koda yaushe ballanta fuskarta ta zama sanniya a wajen mutanen dake yawan xiyartar wajen ko kuma ma'aikatansu ba. Tun yana zagayawa da qarfin gwiwarsa har ya sare. Zuwa sannan yanajin zai haukace ne idan bai gayawa kowa halin da yake ciki ba,don haka yana isa Bristol baiko koma dakinsa ba ya kira mato a waya. Tazarar minti ashirin kacal ya iso,ya shigo dakin yana cewa "Kai matsala ne dakai,wani lokacin sai ayita faman kiranka baka dagawa,tun jiya nake danna maka kira kaqi dagawa......gobe ne za'a zauna cacar nan fa......" "Shut up mato!" Ya dakawa mato din tsawa,don maganarsa a sannan daidai take da yana buga masa abu me qara a kunne. "Lafiya uban gidana?,me kuma ya faru?" "Mato na hadu da 'yar damfara......na hadu da gagarumar barauniyar data yasheni tas......bama ni ta yasheba tukunna......ta taba dukiyar kamfanin jadda ne!". Zaro idanu mato din yayi waje yana janye jikinsa baya da sauri kaman yaga wani abun tsoro tattare da mika'il din "Anya yau bakasha barasar da kanka baya dauka ba?,kasan maganganun da kakeyi?,barauniya fa kace,kuma macace?,sannan data tashi dukiyar Muhammed jadda ta kwashe?" Ya qarasa maganar kaman zaiyi ruku'u. Ba kuma ruku'u din zaiyi ba,kawai yayi hakanne don ya samu damar ganin fuskar mika'il dake zaune sosai,yanason kuma samun tabbacin maganar haka take ko kuma akasinta. "Duk yadda kaji ka sake kuma fada hakanne" Ya fada a galabaice yana tsananta fatan samun mafita daga wajen mato. Ga mamakinsa sai yaga mato ya juya yana neman hanyar fita daga dakin. Da wani irin hanzari mikail ya miqe ya damqo rigarsa yayi qarfin halin jawoshi baya sannan yasha gabansa "Ina zakaje kuma?" Kicin kicin yayi da fuska "Ka dauko bala'in da yafi qarfinka ai me gida,ni kuma bani da wani gatan da zan iya tareshi,kaga gwara na yiwa kaina qiyamulallaili nasan nayi". Sakinsa mikail yayi har yana taga taga kaman zai fadi. Cikin fusata da fushi yake duban mato,yayi taku biyu a gabansa sannan ya tsaya yana sake kallonsa *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 78 "Kai butulu......na dade da sanin alaqar bariki bata da riba.....kuma bata wanyewa lafiya qalau.....amma inaso ka sani.....ni mikail baka isa ka gwadamin wannan halin ba saboda yadda kaci a jikina,komai ka zama ta silata ne.....to ga hanya nan......kana iya tafiya......amma ka sani,wallahi.....wallahi duk abinda zan shiga zan bada sunanka da tabbacin tare mukayi komai". Ji mato din yayi kaman ya debo qarfe ya jibga masa saman kanshi,sai ya koma ya sulale ya zauna "Ya zakayimin haka oga?,kasan tun safe naga qishin qishin abun?,ya baza jaridu da jafafen yada labarai?,amma ban taba tunanin kaine a ciki dumu dumu ba?" "Mune dai a ciki,kuma zanyi maka haka muddin kaima kayimin hakan". Ya bashi amsa kai tsaye yana duban tsakiyar idonsa. Wata wawiyar ajiyar zuciya ya sauke yana yin collapse. Nadama da dana sanin taba sanin mikail a rayuwarshi tana sauko masa. Shikam ina zai iya tarar case da Muhammed jadda?,wanne ganganci ne ma zaiyi saken da koda sunansa zai shiga list na sahun wadanda ake tuhuma. Shuru yaci gaba da wanzuwa a dakin tamkar dukkaninsu ba xasu sake magana ba kafin mato ya magantu "Ita yarinyar wacece ita?,zaifi kyau kabi sawayenta ka bincikota ka damqawa jadda ita a sauqaqe su tuhume ta". Wani banzan kallo ya watsawa mato "Inda nasan ita din wace da ta yaya ma zan batawa kaina lokaci ina neman shawarar butulu irinka?......tun haduwata da yarinyar na karanci tasha banban da sauran yammata dama mata gaba daya.....tun daga yanayin kyau siffa da kuma jan ajinta......bata sake shallake tunani ba sai a yau dana karade dukkan guraren da muka saba haduwa ko na saba ganinta amma na kasa zaqulota,......ta shafe dukkan wani footprint nata,bani da sauran hanyar da zan iya lalubota". Shuru mato yayi abun yana tsimashi shima. Duk iya yawan duniyarsa bai taba cin karo da abun mamaki irin wannan ba.......duk budewar idanunsa da kuma son duniyarsa baiga gangancin da zai sanyashi tunkarar fada ko jayayya da mutum irin muhammad jadda ba.....hakan daidai yake da saida rai.....daidai yake kuma da Rungumar mayunwacin zaki. Amma irin wadannan maquden kudaden kuma ace diya mace ce ta diba?. "Me afkuwa ta afku yallabai.......yanzu lokaci ya qure ya kuma matse da zaka tsaya nemanta da bayyanar da gaskiyarka.....don koda ka samota dinma ka gabatar musu da ita to ba shakka dole saika rasa aikinka.....na tabbatar zasu sallameka ne". Wannan maganar ta mato ta sanya gumi tsatstsafowa mika'il. Ya koma baya yana zama sosai tare da kamo habar rigarsa yana sharce gumin goshinsa. "Don ubanka mafita nace ka bani bawai ka dinga haskomin makomata ba" Ya fadi da mugun tsaron ci gaba da jin sautin xai rasa gurbin aiki da kamfanin jadda diamond rashi na har abada,bayan a nasa mafarkin yana hangoshi ne wataran a kujerar CEO din ma gaba daya yana juya nasa kamfanin diamond din. "Mafita kam na samota......amma sai idan ka amince.......zaka juya hankalin kowa kayi wasa dashi.......ka kuma binne batun kwashe kudin asusu ba tare da kowa ya fahimta ba". Kaman an watsa masa ruwan sanyi haka yaji rahama tana sauka a zuciyarsa,baisan sanda ya kama hannun mato ya riqe qam qam ba abinda bai taba yi ba tsakaninsu "Dama za'a samu irin wannan hanyar na kasa yarda da ita mato?,maza gayamin......gayamin don Allah". Hannunsa ya zame yana mamakin yadda yau masifa da bala'i suka sanya ubangidan nasa zama maqasqanci a gabansa. "Caca......a caca ne kawai zaka ciyo maquden kudaden da zaka iya cike babban gurbin da zai sauke fushin me jadda daga kaso dari zuwa ashirin". Ido ya zubawa mato alamun me gama Fahimtarsa ba. "Nasan baka gane ba ko?,me gida......kana da nasibin da muddin ka zauna teburin caca saidai ka kwashe badai a kwashe ka ba,tunda kake baka taba zama teburin caca an cinye ka ba tsahon shekarun daka dauka,saidai ma ka tashi da gwagwabar ribar dake lunka arziqinka.......wannan zaman da za'ayi a gobe babban zama ne......akwai manyan gidadawan masu kudin da basu gama wayewa a sabgarba.....basu kaika qwarewa ba,sun sanya mugayen kudade masu nauyi cikin cacar saboda romon bakan shigowarka cikinta da nayi musu da yawan kudade masu nauyin gaske.......kudin da kowanne zai zuba ba qarami bane me gida......kuma ina da tabbacin kaine zakayi nasarar wawashesu......ka zuba kudade sosai ka saki jiki don ka sarqafo dukkan abinda zasu zuba.....bana jinka.....nasan da qwarewarka.....na kuma yarda dakai". "Nima na yarda da kaina" Ya fadi kai tsaye cikin confidence da kuma yarda da cewa lallai ba shakka waraka tazo. Rungume mato yayi yana jin tsananin farinciki kafin ya sakeshi yana cewa. "Muddin muka gama da wannan,na rantse da sarki Allah saina nemo yarinyar nan......saina nuna mata cewa ita din ba komai bace cikin duniyar bariki,sai na bar mata tarihi,saina sanyata tayi danasanin zuwanta duniya!!". Tunda gari ya waye yake kwance kawai lamo,ita bame bacci ba hakanan ita ba idanunta biyu ba. Su biyu ne a dakin tun bayan