Sashe 33
A Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Waya kuma ake amsawa? Ta tambaya cikin wata irin isa sa ginshiri tana qanqance idanunta,qwayar idanun nata suna kan wadda tayi maganar. Kai ta jinjina mata cikin bata tabbaci Eh haka ne . Juyawa tayi ta zauna sosai tana fesar da iska me zafi daga bakinta. Ta qanqance idanu sosai tare da zubawa guri daya idanu,abinda zai baka tabbacin akwai wani radadi me yawa da take ji daga cikin zuciyartata Alamu kenan suna nuna yaga kiran,nice dai .nice dai da bazai amsa wayata ba,nice dai da bazai saurareni ba sai a sanda yaga dama ko kuma aka bashi umarni? Ta qarashe maganar ta hanyar yiwa kanta da kanta tambayar. Tambayar da bata haifar mata da komai ba sai qarin qunci da bacin ran da ya sanyata miqewa tsaye. Hannunta ta dunqule ciki juna,ta fara kai kawo tana naushin tafin hannunta da daya hannun data dunqule waje guda. Ba shakka tayi sake ba dan qarami ba,ba shakka kuma hajiya mariya tana son jefa kanta tsakiyar shingen da ba nata ba. A baya tayi tarin ayyuka game da hakan,amma idan har tace taga nasara tattare da hakan to tayi qarya me yawa ma,zata iya kiran ayyukanta na baya da JIYA I YAU,tana tsaye a waje daya babu sauyi ko qanqani,zata zuba idanu ne abubuwa mafiya daraja da kima a rayuwarta ..kuma mallakinta amma ace suna ci gaba da subuce mata?,suna ci gaba da zama haramiya a gareta?,shin zata yarda da zamowa YAR RAKIYA ko kuma taci gaba da wanzuwa a mazaunin yar kallo?. Ba zata sabu ba! Ta furta a zabure sannan ta juya da sassarfa tana daukan mayafinta dake yashe saman kujera Tashi samira muje ta bawa hadimar tata umarni,wadda ke zaune tun dazu guri daya tana duban kai komo da maganganun da takeyi ita daya Ina hajiya? Ta tambayeta murya a lanqwashe. Tayi imanin tunda har ta buqaci fita irin wannan afujajan ba shakka ba alkhairi a cikinta sam Gidan alhaji hamza! Ta bata amsa a tsawace da salon abun nan da ake cewa haushin kaza huce kan dami. Tsam ta miqe tana gyara daurin zaninta sannan ta wuce da sassarfa zuwa shiyyar dakunansu don dauko hijabi. Cikin jerin amintattu kuma lafiyayyun dakunan da mansion house din na alhaji hamza kibiya ya mallaka. Zaune take tsakiyar wani lallausan rug dake a gefe daya na dakin wanda aka masa rukuni da lausasan sofas qwaya uku da suka zamewa wajen tamkar wani dan qwarya qwaryar falo ne na cikin bedroom. Wani irin lafiyayyen daki ne da ba zai barka kasan safiya ko dare ba,zafi ko sanyi,damuna ballanta rani ba muddin ka kasance wanzajje a dakin. Daga saman rug din take zaune saman abun salla da zai baka tabbacin bata jima da kammala sallar walaha ba. Salla ceda bata taba wuceta a rayuwa muddin ba wani qaqqarfan dalili ya gifta ba,tun zamanin quruciyarta har kawo yanzu da girma da shekaru suka hau kanta. Shine kuma ya same mata sila da tsani na dawowa rayuwa hamza a shekarun baya,a sanda ta yanke zato da tsammani daga sake rayuwa dashi da kuma yaranta da suka zame mata sanyin idaniyarta. Wataqila nutsuwa da kamalar da fuskarta ta wadatu dashi yana da alaqa da wannan din,yawan ibada,yawan bautar Allah,yawan azumin tadawwu i da babu wanda yayo gadonta a wannan fannin qafa da qafa irin muhammad fu Akwai haske sosai saman fuskarta,tana saye da atamfar chiganvy gold mekauri kyau da asalin tsada. Jikinta lullube da mayafi me kauri,yayin da yatsarta ke maqale da qaramin carbi irin na ma tsawa. Daga gefanta saitin kafadarta shine a kashingide,kana kallonsu zakasan magana sukeyi,magana kuma irin ta da da uwa,hira cikin nutsuwa qauna da kuma kulawa Nikam saddiq sake kiramin wayata mana,jakata tun ranar da akayi asibiti dani ban sake ganin gilmawarta ba,akwai muhimman abubuwa a ciki,harda kudaden Amna data bani ajiya idanu ya zaro sannan ya miqe yana zama sosai What?,anni?,dollars fa? Wallahi sadiq ta fada a nutse. To Allah ya tsananta rabo,don auta ta saka buri akan wannan ajiyar,naji tana lissafin abinda zatayi dasu idan ta dawo ya fada yana cusa hannunsa a aljihu yana laluben wayarsa. Fuskarta anni ta shafa tana fadin Idan har ba a gansu haka zata haqura ai,tsautsayi da qaddara tana wuyan kowane bawa Shuru sukayi dukkansu suna saurareb sautin din ..din,sautin dake gaya musu lallai kiran ya isa ga wayar anni dake tare da documents dinta da kuma sauran kudade masu kauri cikin jakar. Kamar cikin mafarkinta ta dinga jin wani sauti mara qarfi yana ratsa kunnuwa zuwa kwanyarta. Shuru tayi ba tare data motsa ba,daddan ring tone din mara hayaniya yana tasowa can qasa qasa,da alama akwai abinda ya sake rage kaifin sautin. Sai data fahimci ba cikin bacci bane sannan ta qarasa bude fararen idanunta da suka qara girma saboda bacci. A hankali ta yamutsa fuskar tata sannan ta sanya hannunta ta maida lallausar sumarta me tsaho data rufe rabin fuskarta baya,ta juya daga rub da cikin da tayi zuwa rigingine sannan ta miqe ta zauna sosai tana wuwwurga idanunta zuwa kowanne sashe na dakin don gano ainihin ta inda sautin yake fita. Ba kowa a dakin,don tuntuni su huda sun gama shiryawa sunyi abincin safe kaman yadda suka saba sun wuce makaranta,don ko idanunta bata iya budewa tace dai kawai su buda jakarta su dauki kudin makaranta su kuma ja mata qofan idan sun fita. Fes dakin yake kamar kullum kamar kuma ko yaushe,sai ta saka hannunta ta tattare gashinta ta qulleshi tsakiyar kanta idanunta ta tsaiwa kan medium luggage din dake cike da tsarabar da aka kawo mata,wadda ko samun damar budeta batayi ba. Tayi matuqar gajiya a jiyan,tana fita kusan kowacce rana.....amma bata yin awanni masu yawa kaman haka a wajen. Komai nata yana da lokaci tsari da kuma iyaka. Ta zube fararen qafafunta saman qaramin carfet data sanya musu daga gaban gadajen nasu saboda sanyin tile,ta jawo dankwali me santsi ta daura sannan ta miqe tana isa gaban luggage din. Sai a sannan ta kuma gasgatawa daga cikin qaramar handbag dinta sautin ke fita,jakar ma da gaba daya ta mance da ita tun ranar data je musu siyayya ta dawo,ko tarkacen ciki bata kwashe ba. Hannu ta zura tana laluben meye yaketa qara din haka cikin jakar,sai kawai ta wuce gaban gadon ta zazzage jakar gaba daya saman gadon. Kyakkyawar purse baquwa ta gani cikin jerin tarkacen dake cikin jakar wanda ta tabbatar duka nat a ne. Onion color me ratsin maroon a jiki. Hannu ta miqa ta jawota,ta dagata a hannunta tana jujjuyata cikin mamakin a ina ta samo ta?,kuma ta waye?,tun yaushe take cikin kayan nata?. Kamar anason sanar mata da amsar duka tambayoyinta ne sai wannan siririn sautin da ya tasheta a bacci ya sake kadawa daga cikin jakar. Kai tsaye ta zuge jakar,ba wani ba wata ta sani waya ce. Wayace qila da take da alaqa da mamallaki ko mamallakiyar jakar. Wata siririyar Samsung ta gani,ta sanya hannu don cirota da gaggawa gudun kada kiran yanke,take sabbin dollar din dake maqale a zip na daban na jakar suka biyota suka fada saman cinyarta hade da qananun hotunan passport. Ba wannan bane a gabanta,don haka batabi ta kai ba ta fara duba sunan dake yawo saman screen din wayar MUSADDIQU NA....shine full name din dake jikin number. Tadan tsaya tana sake duba sunan da kyau tare da bitar karantashi,sai kuma tadan tabe baki kadan sannan ta daga kiran ta Kara wayar a kunnenta "Alhamdulillah.....an daga anni" Musaddiq ya fada yana sanya wayar a kunnensa. Shuru tayi tana sauraren motsin dake fita daga daya bangaren,kafin daga bisani sallamarsa ta maye gurbin shurun. Muryarsa a nutse dake dauke da kamala yayi cikakkiyar sallama data sanyata motsa bakinta da tata siriryar muryar tana amsa sallamar. "Barka da warhaka" Ya fada a nutse. "Yauwa.....barka" Itama ta amsa masa a taqaice "Don Allah idan ba zaki damu ba zan iya tambayarki wayar nan ta waye?" Banbarakwai taji tambayar tazo mata,har sai data sake duba sunan dake jikin wayar,amma yanayin yadda muryarsa ke nuna kamalarsa da nutsuwarsa ya sanya tayi gyaran murya daban "Kaman sunan me kiran dana gani akan wayar yana da alaqa me qarfi ko kuma mafi kusanci dame wayar ko?". Murmushi ya saki,yadda tayi maganar cikin fasahar harshe da tsari sai yaji ya burgeshi,hakanan kuma a karon farko ya gano muryar,yakuma dago ko wacece "Hakane ranki ya dade.....idan na canka dai dai.....kamar mutuniyar kirkin nan kuma baiwar Allahn nan data ceci rayuwar mahaifiyarmu ko?" Dan jim tayi tana son gano ma'anar zancansa,don tuni rayuwarta taci gaba daga inda ta tsaya,tuni ta shiga wani babin kuma na daban,ta manta abinda ya faru dazu jiya bare shekaran jiya. Haka policy na rayuwarta yake. Ba kasafai take bawa komai gurbi cikin rayuwarta ba bare ta hadu da traffic akan dukka plans nata da kuma tunaninta ba. "Dattijuwa me asthma a masallacin HGMS store?" "Oops....." Ta furta a hankali,yanayin daya sanya musaddiq sakin murmushi don ya fahimci abun ya kwanta mata "Kayi haquri don Allah,ka kuma nawa mama haquri,na hada da purse dinta ne a cikin kayana bisa rashin sani,bansan ma da ita din ba sai yau da aka kira" "No....karki damu......mune ma muke fata Allah yasa bamu takuraki ba....." "Zaku iya karbanta a jambulo third gate.....link 5" Abinda ta furta kenan ta yanke wayar,daidai sanda anni ta miqa hannu da zummar karbar wayar su gaisa. "Ya ka katse wayarwayar inaso mu gaisa nayi mata godiya da ban gajiya" "Daga canne anni ta yanke......" Ya bawa anni amsa yana duban wayar tare da mamakin yadda take magana da bada amsa haka cikin taqaice komai "Babu matsala.....amma zanso sake ganinta ko magana da ita......zanso nayi mata godiya sosai,dukan wanda yayi saving rayuwarka ai baka da sama dashi.....mutum ne me matuqar kima da martaba cikin rayuwarka.....har yanzu ina iya jin sanda ta rungumeni sosai a jikinta kamar ta sanni......sai na dinga jin kamar amna ke riqr dani......ta damu sosai kamar mahaifiyarta ce a cikin halin" Ta qarasa maganar tana duban fuskar musaddiq,fuskarta kuma na nuna abubuwa da dama da zuciyartata taji. Zamanshi sosai ya gyara yana murmushi. *SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI* *_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_* *_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_* *_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_* *_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_* *ZAFAFA BIYAR*