Sashe 12
A Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ISO NE?_* *MAZA MAZA JEKI KI GWADA WANNAN_* *INCENSE BY KABO DAUGHTER 08032119803* *_zaki dariya za kuma ki godemin_* *_gani ya kori ji_* *hakanan sai an gwada akan san na qwarai* ________________________ Sanye take cikin lallausar doguwar rigar bacci me kauri me gajeran hannu off white wanda ta tsaya daidai idon sawunta. Zaka iya kiranta doguwa saidai ba cancan ba,irin tsahon da yayi daidai da tsahon da za'a iya kiran diya mace doguwa,wanda siririn jikinta ya sake taimakawa wajen bayyanar tsahonta,muddin kuma ta samu damar mujewar jiki ko ta dan qara qiba to tsaf tsahon zai shanye da ba lallai a iya ganinsa ba. Tana da wani irin launin fata,fari me cakude da sirki sirkin ja,fara ce tas irin hasken fatar da kana kalla zakasan ba zallar hausa fulani bace,lallai ita din ruwa biyu ne halittarta ya hada nasaba da wani yaren(half cast). Ma'abociyar yalwataccen gashi me santsi da tsahon da kana iya hangensa ta cikin hular bacci dake kanta,a cukurkude kuma a daure cikin siririn band. Yanayin zubin idanunta shike fusgar hankalin maza da dama,bama maza kawai ba,harda mata 'yanuwanta suke kallonta a matsayin me tsananin kyau,duk kuwa da cewa ita din kanta ta sani,ba wata me mugun kyau bace na azo a gani,amma batasan meye yake janye hankalin mutane haka a kanta ba?. Tun tana mitsitsiyarta wannan abun yake tare da ita,FARINJINI ....wanda a sanda take da gatan uwa mahaifiyarta ke yawaita tofeta da addu'a ko yaya ne idan zasu fita. Mata ukune cikin falon,matashiya ta biyu wadda shekarunta zasu iya kaiwa sha shida na zaune dirshan saman lallausan carfet din nasu daya wadatu da tsafta,hannunta riqe da cup na tea,daga gefanta kuma bowl ne dake cike da chips. Sanye take da uniform irin na sauran 'yan uwanta dake alamta maka ta kammala nata shirin zaman tsimayinsu take bayaga breakfast data kasa kammalawa har yanzu. Yanayin yadda take cin abincin kawai zai gaya maka bawai dadin abincin takeji ba,idanma ba haka bane to lallai akwai abinda yake damunta. Ta biyun na gefan kujera tana qoqarin saka fara qal din sucks dinta. A qiyasce nata shekarun na haihuwa zai wahala ya wuce sha uku. Sannan qaramar data isa gareta tana gyara hijabin hannunta tana qoqarin sanya mata fuskarta shimfide da wani sassanyan murmushi nata shekarun tsakanin tara zuwa goma suke. Idanunta akanta da wani irin kallo na tausayi da rahama,zuciyarta na sake narkewa cikin tausayinsu gami da jin qwarin gwiwar basu kariya da samar musu da komai na buqatar rayuwa duk rintsi,komai wuya komai dadi. Wanzuwarsu a yanayi na farinciki yafi komai dad'ad'a mata rai da sanyata cikin nutsuwa da kwanciyar hankali duk kuwa da irin birkitacciyar rayuwar da take fuskanta,wadda bata da dadi sam sam ballantana ban qaye. "A'ah.......kaga haneefata anyi kyau" Ta fadi da sassanyan muryarta me wani irin amo me dadi da daukan hankali idanunta saman fuskar yarinyar data kira da haneefa......yarinyar da ake cewa duk cikin qannenta ba wanda ke kama da ita irinta,duk da ansha cewa haneefan ta fita kyau,hasken fata kawai zata darata dashi. Dariya haneefan ta saki ta daga hannunta zuwa ga 'yar uwartata alamun su tafa,sai ta daga nata dogayen yatsun ta bata suka tafa din. Batasan wanne irin son karatu Allah ya dorawa qannen nata ba,wadda karatun bai fiya damunta ba huda ce,saidai a sannu da tayi tsaiwar daka a kanta yanzun abun ya shiga jikinta itama. Hudan ma bawai karatun bane bataso,a'ah,kawai hankalinta yafi karkata zuwa ga wasu bangarori. Kaman koyon abubuwa na qirqire(creatives),irinsu zane zane,dinki,decorations da sauransu. Bata jin akwai wanda zata matsawa kan abinda yakeso yayi muddin bai kaucewa hanya ba.....to amma kafin sannan tana da buqatar suyi karatu.......tana da buqatar su karantu da kyau ta yadda koda bayan ranta sun zarcewa raini da wulaqanci......tana da buqatar suyi karatun da duniya gaba daya zata tabbatar sun gagari rainin me raini ta fannin ilimi.....tanaso suyi irin nau'in karatun da hattana da maqiyi babu yadda zaiyi zai sallama cewa eh lallai......jinin hindu sun zama wasu taurari na daban a cikin familynsu gidansu dama unguwarsu gaba daya......zata nunawa wadanda suke ganin ba zasu iya ba.....ba zasu kai ba......zasu tozarta cewa......zasu iya iya.....za kuma sukai labarin da su basu kai ba. A nutse ta waiwaya ta kalleta. Tadan zuba mata idanu na second tana nazarinta. Tun tuntuni ta fahimci akwai kwantacciyar damuwa a qasan ranta,kasancewarta mutum me wani irin kakkaifan hange da saurin gano abu. Kaifin fikirarta ya fita daban dana dukkan wani yaro dake cikin gidan,don haka take saurin fahimtar kowanne motsi taku da kuma sauyawar yanayin qannenta. "Huda......wai baki duban lokaci?" Batace komai ba huda din,saita zare cup din bakinta ta direshi tana niyyar miqewa,abinda ya sakata maida idanunta ga cup din kenan. Ko rabin tea din bata sha ba,ta sake maida kallonta a kanta "Kin qoshi kenan?" Kai ta jinjina mata kafin tace "Banajin yunwa dama kwata kwata" Kyawawan idanun nata masu wani irin shape ta lumshe,can qasan zuciyarta tana furta "Alhamdulillah,astgafirullah" A duniya daya daga cikin sauti da take matuqar son ta yita ji kenan daga harsunan qannenta "BANA JIN YUNWA" Sauti mafi dadi kenan daga bakinsu zuwa kunnuwanta. Waiwayawa tayi gefanta ta kalleta sanda ta kammala saka takalmi da socks dinta "Nadra......shiga daki gefan katifata ki daukomin jakata na sallameku......yau din kamar babu me laka a jikinku" "Tom" Ta amsa tana saukowa daga saman kujerar da saurinta ta wuce dakin. Sanda take maido dubanta cikin falon sai suka hada idanu da hudan. Huda ta janye daga kallonta,sai ita din taci gaba da kafeta da kallo tana dubanta "Huda" "Naam" Ta amsa mata ba tare da sun hada ido ba "Wai meke damunki?" Ta jefeta da tambayar tana kebe baki......harta bude baki zatayi magana ta dakatar da ita a tsaurare "Karki soma cemin ba komai.......na gani a idanunki da motsinki......" "Gida......" "Ba damuwar mutanen gidan nan ba?" Ta jefa mata tambayar tana duban idanunta,a yanzu akwai sirkin bacin rai kadan a maganarta da idanun nata "Yaushe kika fara saka maganarsu cikin ranki?" Ta kuma tambayar tata tana kallonta "Ashe har yanzu baki saba da halayyarsu ba?,bakisan yadda zaki zauna dasu ba?,huda ina duk qoqarin da nake a kanki ke da kike babba ki fahimci yadda zaki zauna da kowa a cikinsu?" "Anty bakisan me suka ce ba a kanki.....bakisan me suke fada ba kullum" Ta qarashe maganar muryarta tana raurawa sosai da alamun zuciya da ruhinta gaba daya sun sare. "Kome zasu fada huda su fadi,indai a kaina ne karki azawa kanki damuwa.......kome ma zakiji sun fada,ba wani baquwar kalma da zakiji daga bakinsu ko sabon abu.....me yasa sai yanzu zaki fara sawa kanki kina damuwa?" Ta qarashe da sigar tambaya. Qasa tayi da kanta ba tare data amsa mata ba,ita kanta batasan me yasa sai yanzun abun ke damunta ba duk da sun share shekaru dasu a haka. Daidai sanda nadra ta qaraso ta miqa mata kyakkyawar hand bag din nata fara tas me adon brown duka jikinta dake dauke da tambarin kamfanin Gucci. Idanunta masu sheqi ta juya zuwa ga nadra,ta saka hannu ta karbi jakar tana qoqarin zugeta. "Anata kiran wayarki tunda na shiga" Nadra dake goya jakarta ta fada. "Okay,barta" Ta amsa mata a taqaice,don ta tabbatar a cikin mutum biyu daya ne yake kiranta,tafi kuma gasgata zatonta akan dayan. Zip din da take ajiye canji ta zuge,ta fidda kudin ta lissafa daidai yadda tasan zai ishesu break da kudin mota,saboda yau din basuyi abinci yadda suka saba ba kasancewar kayan abincinsu ya qare. Daga bakin qofar falon nasu tayi tsaye hannayenta goye a qrijinta tana dubansu har suka kammala ficewa daga gidannasu,sai taja Qaqqarfar ajiyar zuciya tana sauke hannayen nata ta juya a hankali don komawa falon don kwata kwata bata samu isashen bacci ba a jiya,tanaso ta runtsa sosai sannan ta shiga kasuwa tayi musu saye saye *SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI* *_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_* *_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_* *_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_* *_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_* *ZAFAFA BIYAR* *_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_* *Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU* _TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_ _QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_ _K'ALBIM Mamuhghee_ _AJIYA A DUHU Billynabdul_ _DUNIYATA Huguma_ _Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_ *hudu 2k* *uku 1500* *Biyu 1k* *Daya 500* _YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_ *09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA* *IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA* *09033181070* *BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK* *ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171* *ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI* *AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA* 89825722 Nousaiba lawali maradi 1000cf *_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_* *_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_* *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 14 ________________________ *_CIKIN DUBU DABAN TAKE_* *_TABBAS AKWAI TURARE AKWAI MUNA TURARE_* *_NA GWADA NA GANI_* *_YA SUBHANALLAHI_* *_QAMSHI NA TASHIN KAN ME GIDA_* *_QAMSHIN DAKE DAGAWA KISHIYA HANKALI_* *_NATACCEN QAMSHI DAKE KAMA GURI DARAM_* *_WANNE GANGANCI NE YA SAKAKI TSAIWA SANYA?_* *_ME KIKE JIRA?_* *WANNAN DIN GUARANTEE NE FA* *TASTED AND TRUSTED 100% PERCENT* *KI SIYA KI GODEMIN HAJIYA* *INCENSE BY KABO DAUGHTER* *_DUNIYAR TURARE ME BADA ASALIN QAMSHI ME KAMA JIKI DA MUHALLI,NUTSATSEN QAMSHI ME SANYAYA ZUCIYA DA DADEWA A WAJE_* *_IDAN KINA DA MATSALA KINA NEMAN TURARE ME KAMA WAJE,KINASON SAKEWA OGA SABON QAMSHIN DAKI DA PARLOR,KE KANKI KINASO KI SHIGA WAJE A DINGA TAMBAYAR WACE TA ISO NE?_* *MAZA MAZA JEKI KI GWADA WANNAN_* *INCENSE BY KABO DAUGHTER 08032119803* *_zaki dariya za kuma ki godemin_* *_gani ya kori ji_* *hakanan sai an gwada akan san na qwarai* _________________________ Saidai dai dai sanda ta saki labulayen da zummar shiga ciki din taji sallamarsa ta karade tsakar gidan. Qaramin tsaki taja,tabbas tunda aka jishi da sassafen nan kamar haka to ba a shakka wata tijarar yazo yi,ko kuma akwai abinda ya hadoshi da wani. Idan da sabo zata iya cewa sun saba da halayyarsa,macce daya ce cikin gidan suke dasawa har baka iya jin kansu. Har gwara ita tasan maganinsa,ta kuma san ta yadda take bulloma tsiyarsa,duk da bata taba tsaiwa ta