← Book details A Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 84

Sashe 15

A Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

rashin d'a da rashin mutunci,da wannan muryartata da sautinta ke cike da sanyi da nutsuwa tace "Ina kwana kawu?" "Lafiya qalau na kwana,sai uban baqinciki da takaicinki dake shirin hallakarmin da rayuwa" Ya furta cikin hargagi tamkar dama yana jiran ta gaidashinne. Har yantsu dogon yatsanta yana saman labbanta,yayin data kafe mutumin data kira a dazu da kawun nata da idanunta,tana dan motsa yatsan nata saman lebenta tana kuma nazarin fuskarsa furucinsa dama motsinsa. Ko sau daya bata taba ganin mutunci kima da martabarsa ba......daidai da misqala zarratin bata taba daukarshi da wani babban matsayi ba......abu daya ta sani,komai lalacewar fura tafi kashin shanu......komai kashinsa da zabgewa gami da lalacewar martabarsa a idanunta sunanshi kawunta kuma qani ga mahaifinta. Maida idanunta tayi ta lumshe kawai kaman yadda ta saba masa a yawancin lokuta......tasan me ya sanyashi wannan zuwan,wani boyayyen buqatarsa ne dake a qasan rai da bai samu biyanta ba. Ta tuna haduwarsu ta qarshe dashi a wancan satin daya wuce. Dama ta sani ba zai haqura ba.....shine zai fake da wasu abubuwa wanda shi kansa ba kubuta yayi daga su ba.....yazo ya samu wannan matar da qiyayyarsu ta jima da yin tsiro da jijiyoyi a cikin jikinta. Takai qarshen maganar sanda take bude idanunta saman fuskar bibo. Haduwa idanunsu sukayi waje daya da nata,ta juya qwayar idanunta tana watsa mata wani kallo "Ki dain kallona da wadannan tsayyayun idanun naki na rashin kunya masu kama da idanun mage.......kai ya kamata ka tsaya a kanta saboda tana jawowa bawan Allah zagi,wanda ya jima da mantawa ya zauna a duniyar.....amma ina kyautata zaton kullum ta Allah sai mala'iku sun tadashi zaune sun nuna masa qazantar da d'iyar cikinsa ke aikatawa. Ya rasu yabar yara sama da goma sha takwas amma ba wadda ke hana masa kwanciya lafiya a kabarinsa sai ke?,ai wallahi Allah wadai da haihuwar d'iyoyi irinki.....indai haka haihuwar take gwara mutum ya zauna a haka" Tana maganar tana jujjuya hannunta guda daya gami da yarfeshi,idanunta a kafe saman fuskarta,kaman yadda itama tunda ta fara maganar ko sau daya bata dauke dubanta daga kan bibo ba. Maganganun nata sunkai mata iyaka,tana jin ta gama daukar iya abinda zata dauka a iya wunin yau,saboda haka a nutse ta sauke qafafunta qasa ta miqa hannunta ta dauki handbag dinta ta miqe tsaye tana gyara rolling din mayafinta "Fita zanyi,kuma ina da buqatar na kulle mana dakin kafin na fitan,idan ba damuwa ko zamu koma tsakar gida mu qarasa maganar a can?" "Kaji ko?......dama ai na sani,babu wani sauran wanda take gani da kima a duniya.......yau koda fadima zata dawo duniya bata isa ta juyata ba bare alhaji" Tayi saurin cafe zancan. Wani irin juyowa tayi gareta ta zube mata manyan fararen idanunta "Kaman bakiji me nace ba ko?,nace muje tsakar gida mu qarasa......bankai ga furta cewa banda lokacin sauraro ba" Ta mata maganar dalla dalla tana kallonta. Sosai bibo ta kafeta da kallo,har yanzu babu abinda zai sauyata......wannan rashin shakkar da rashin tsoron suna nan rubuce baro baro cikin ayyukanta da dukka motsinta,dakiyarta da shariyarta da daukan abu me zafi ta wulwulashi ta sauya masa mizani idan taso. "Idan ta fito kawu qofar kawai zakaja jam lock din zai shige,ka sameni a qofar gida muddin baka wuce minti biyar ba" Tayi furucin sanda take takawa zata fice a falon tana riqe da vail din abayarta daya zame tana qoqarin mayar da rolling dinta yadda yake. "Tashi muje na sameta a waje din inji da wacce hujjar zata kare kanta kuma" Ya furta dukka jikinsa na nuna zumudi da qaguwar yaga ya bita. Da kallo bibo ta bishi tana daga zaune a kujerar ba tare data motsa ba baqinciki yana kasheta. A yau tana jin kaman ta tashi ta rufe rufa'i da duka. Yau ya tabbata mara amfani kwata kwata a garesu gaba daya. "Ko nayi gaba kya rufe musu dakin?" A zafafe ta miqe tana gyara daurin dankwalinta "In zauna inyi me a nan?,Allah ya sawwaqe,ai ni tawa son zuciyar bai fara sauka har takan kayan haramun ba" Ya jita sarai,ya kuma san da biyu take maganar,saidai a yanzu baya jin yana da lokacinta,dukka tunaninsa yana ta'allaqe akan sabreen. Yasan halinta sarai,muddin ya haura mintunan data dibar masa,yayi imanin da gaske zai iya zuwa ya tarar ta wuce din abinta. Tana rungume da hannayenta sanda take tsaye a qofar gidan nasu ta bashi baya. Fuskar nan dake shimfide da wani irin kwarjini yau din cakude take da ninkin rashin fara'a da walwala na tun asali da aka santa dashi. Har tsakiyar zuciyarta takejin wani abu yana tsikarinta duk da yadda iskar dake yawo sararin subhana ke kada doguwar riga da dan mayafin saman kanta tana watsa daddadan qamshin turaren dake tashi a jikinta. Turaren da ita kanta yake sanya mata nutsuwa da kwanciyar hankali,dadinsa ya sanya ta zabeshi a matsayin turarenta na dindindin,duk da batayi tunani matsayinta zaikai a nan kusa ta mallakeshi ba. Ta kalli agogon hannunta,yaci mintuna hudu cikin minti biyar din data bashi,don haka ta fara takawa sannu a hankali tana matsawa daga gaban gidan nasu. Tun batayi nisa ba ta jiyo taku da kuma muryar kawun nata,bata da buqatar kallon fuskarsa ko doguwar magana ta hadasu,buqata gareshi zata sallameshi.....kamar yadda tun tale tale.....kaman yadda tun can baya bashi da amfani a garesu a yanzun ma bata tunani akwai wani sauran amfani da yake dashi a rayuwarsu,don haka ta sabule jakarta,ta zuge ta zaro wani abu daga cikin kudin da yayi saura a ciki ta dunqule a hannunta tana jiran isowarsa "Ke sabreena......sabreen" Ya hada da qwala mata kira tamkar ya bata bashin kudi tana kuma shirin gudar masa dashi. Ranta ya sake baci,ta tsani kwakwazo,a banza ma idanun 'yan unguwar da dukka kunnuwansu harma da hankulansu suna kanta,kowanne motsi ko taku nata a biye suke dashi,sauraro suke.....jira sukeyi na samuwar dukkan wata dama da zasu samu abun magana a kanta. Wannan ya sanya tadan saurara daga tafiyar da takeyi tana dakon isowarsa. Ko a sannan tana iya ganin idanun tsirarun mutanen unguwar da suka samu sararin fitowa da safen kamar ita yana karakaina a kanta. Irin wannan kallon nasu gareta ya zama tamkar jarrabi ko masifa cikin rayuwarsu. Akwai abubuwa da yawa tasan da akeson gaya mata amma babu wannan fuskar. Bataga dalilin zallar rashin adalci irin nasu da suke gwada mata ba suke kuma gwadawa rayuwarta ba. Sun sany hannu dukka da qafafunsu sun tankwabeta sun kuma tankwabe rayuwarta a sanda take da tsananin buqatarsu......a yanzu kuma data yankema kanta bata da buqarsu.....a sannan su kuma suke qoqarin dawo da ita su dankwafar da ita.....suka kuma fidda makamansu da harsunansu wajen illata mata gangar jiki da zuciya. "Me na samu?" Ya iso gareta yana tambaya sanda motar da take da tabbacin waye a ciki ke dab da isowa inda take. Kowanne mutun da zatayi mu'amala dashi ko kuma tayi mu'amala dashi din......sau daya tak take masa wani karatu a taqaitaccen lokaci.......fahimtar waye kai?......meye qudurinka.......meye motsinka?.....mene manufarka......da sauran dukkan wani abu daya shafi rayuwarka yana zama RUBUTACCE cikin shafin qwaqwalwarta. Bata fiya manta abu ba,haka bata missing target saidai idan bata nufaci abu ba. Ta baya ta miqa masa kudin sannan ta fara takawa zuwa ga motar da tuni ta iso inda suke harma ta samu wajen tsaiwa. *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 17 daga inda yake a zaune din yakejin kamar gilashin window din motar ya masa shamaki daga kallonta duk da yadda yake tarwai yake kuma iya baka daman gano komai dake ta wajen motar......duk da haka yana jin kamar ya rage ma idanunsa armashin kallonta,don haka ya kasa haqurin isowartata,ya sanya hannu ya sauke dukka gilashin nasa qasa. sau daya tak ta taba ganinsa ido da ido,amma ta haddaceshi tsaf,tun daga abun hawansa har zuwa halayya da kamanninsa....... Kakkaura kuma faffada da zaka iya kiransa me jiki saidai bai cancan ba. Maabocin iya ado sosai da murza hula ta zauna a kansa kamar shi yake saqa ma kansa ita. Yadda turarensa da shigarsa keda kyau da tsari haka ma kalaman bakinsa,saidai kash!.....daidai da wucewar daqiqa guda bata taba jin wani abu me kama da SO K'AUNA KO BEGE nashi ya tsartu a ranta ba. Waishin mcikina meye SOYAYYA ne?. Ita kanta jerin kalmar SOYAYYA da yadda mutanen duniya suka daukaketa na daya daga cikin abinda ke sanyata dariya koda bata shiryawa hakan ba. SHIRME shine cikakkiyar ma'anar da take ganin yafi dacewa da a kirata ko kuma CUTA,idan akwai sunan da yafi haka lalacewa ma a nata ganin daidai ne a kirata da wannan sunan. Yadda yake tsareta da kallo ya sanya qirjinta ya dinga suya duk kuwa da cewa ta saba da irin wannan shegen kallon. Kwarjininta na daya daga cikin abinda ya sanya take tsira daga guba da dafin MAZA duk kuwa da cewa ita da kanta take tsalle ta afka tsakiyar tarkon bisa tsananin lissafinta,ta kuma samu sa'a da nasarar zame kanta cikin SALO da kuma qwarewar iya wasa. Da hanzarinsa ya fito ya zagaya don bude mata qofar motar,hakan ya bawa kawu dake lafe yana kallon komai qare masa kallo. "Iya shaddar jikin yaronnan kawai ta isheni jari wallahi,wannan tsinanniyar yarina,yanzu meye aibun wannan da ba za'a aureshi ba?" Ya tambayi kansa da kansa yana naniqe da kudin hannunsa. Idanunsa ya aza a kanta bayan ya bude mata motar,sai ya sakar mata murmushi,tadan lumshe ido tana qaqalo nata murmushin cikin dauriya da son maida masa. Gefe guda zuciyarta na cike fal da qarin wani mamakin akan D'A NAMIJI. ta tuna kalamansa akan matarsa dazun dazun nan,amma a yanzun gashi a gabanta ita kamar zai narke. Ta yaya zata yadda tayi aure a duniya?,ta yaya zata bari zuciyarta ta kamu da soyayyar wani namiji?,yaya za'ayi ta banzatar da lafiyar zuciyarta cikin soyayyar wani?,soyayyar halittar da babu tausayi ko jin qai a tare dasu?,halitta mafi son kai cikin halittun duniya gaba daya?,halitta me tsananin mugunta da son cutar da halittar mace 'yaruwarta?. Ba zata iya sadaukar masa da murmushinta na dogon lokaci ba,duk kuwa da cewa fake smile ne,don haka ta zame jiki ta shige cikin motar ya mayar ya kulle yana sauke ajiyar zuciya. Yana jin duk duniya ba wanda ya kaishi sa'a a yau din. Yana jin kamar duka ranar tashi
Chapter 15 · 0% Book details