Sashe 6
A Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
daya daga cikin abinda ya sanya zuciyarsa ke qarfafa,tana sake jadda masa zai dauki komai ya kuma jure komai din saboda ingantaccen ilimin da yake hangowa zaya samu. Dole ya daga idanunsa da suka fara sauya launi ya kalleta dasu "Kalleni da kyau......ba wani karatu da zakuyi cikin gidan da ba na ubanku ba,idan kuma kallon mamaki kake yimin ai uwarka yafi kamata ka yiwa wannan kallon,ita kanta ta kasa jurewa zama daku sai ni da bani da galihu akeson hadani da alaqaqai,to wallahi yadda ban samu yadda nakeso ba,haka kuma ba zaku samu ba......." "Me kikeso ayi mama?" Ya furta tana aje numfashinta daga tijarar da takeyi. Tsananin mamakin yaron takeyi yadda yakeyin komai cikin dakiya da taurin rai dana zuciya "Ko baka tambaya ba ai zan gaya maka kuma dole kabi,ka sauke wannan munafukar jakar ku wuce ciki,sudai da babu yadda zanyi dasu gidan ubansu ne saisun dawo,a sauka lafiya" Ta fadi tana nunawa su Faruqee hanya da yatsa. "Mama.....amma" Zakayimin shuru ko sai ka jawo kuma na hanaku?" Wani dunqulallen abu ya hadiye can qasan ransa yana jin kamar ana masa suya "Kudin mota" "Kudin ubanka dai,sayyadarku zaku taka sisi bazan bayar ba" Ya fada tana zazzare masa idanu hadi da dukan hannun kujerar da take kai "Ku tafi Faruqee don girman Allah" Ya furta da rinannun idanunsa da kuma muryarsa da tayi laushi qwarai yana duban Faruqee din,don kunnuwansa sun soma gajiya da jin zagin da take nausawa bawan Allahn da baisan hawa ba baisan sauka ba. Kallon kallo suke ma juna shida Faruqee din,kowanne cikinsu zuciyarsa cike take fal da zallar bacin rai daya haurawa shekarunsu. A zahiri tausayin me babban suna shi yafi rinjaye a zuciyar Faruqee. Ba yau ba ba kuma jiya ba ya sani......muddin ka ambaci kalmar UWA ko mahaifiya a gabansa takan zame masa kamar tabo ko kuma ciwo koda ba dashi kake ba,ballantana a yanzun da aka kirata muraran. Abun ya jima da zame masa kamar wani ciwo,tunda zancan ya bulla cikin unguwa sai ya zama abun yamadidi da magana tsakanin maqota da mazauna unguwar. Sam baa tallafi rayuwarsu ba,ba'a agajesu ba,ba wanda ya waiwaya ya dubi tsanani bayan tsananin da suke ciki,ba wanda ya bawa rayuwarsu tallafin da zai rage musu radadin da sukeji,a maimakon haka,sai suka debo DAFI na cecekucen maganganu akan rayuwarsu suka sake watsawa ciwuka da raunukan dake ciki zukatansu shi da d'an uwansa. "Kaje Faruqee" Ya sake maimaita masa yana tsareshi da ido. Ya karanci komai ta cikin idanunsa,ya karanci abinda yake nufi da maganarsa,don haka bai qara koda minti daya ba ya kama hannun musaddiq suka suma takawa suna barin falon. "Na dawo gareka" Ta furta cikin izza da dagawa tare da jinta can saman qololuwar isa da kuma 'yanci "Ka koma ka zare wadannan kayan,don basu dace da agola irinka ba,tabbas da 'ya'yan da mahaifiya zata wofantar dasu,ta tsallakesu ta gudu ta barsu to ba'a banza ba......don haka banga dalilin da uwar data haifeku bata tausaya muku ta zauna daku ba ni zan tausaya muku ba......tunda kun iso inaga ya kamata me mana wanki da guga ya tafi hutu hakanan,ka shiga dakin ajiyar kayan wanki ka debo duk kayan da ka gani ka fita dasu bayan gida wajen fanfunan can ka wankesu......wallahi wallahi kace zaka saka iskanci a aikin kaga ikon Allah,banaso kuma azahar tayi maka baka kammala ba". Baice komai ba yakau da kai ya soma takawa yana komawa dakinsu ranshi yana wani irin tafasa da suya. Tsanar maama tana sake wani mahaukacin tasiri cikin ransa. Inda bata tafi ta barsu ba duk tsanani duk wuya,komai girman talaucinsu sunfi gaban a goranta musu,don da iyaye ake ado,sune abun adon diyoyinsu. Me yasa ta aikata hakan?,me yasa ta kasa jurewa?,tsabar son kai ne irin na jinsin DIYA MACE da ya tabbatar a yanzun haka halittarsu take?.ko kuma son duniya da qyale qyalen cikinta ne ya rudeta?. Me yasa batayi haquri ba kaman yadda Abbie ya dinga kira mata?. Har yau har kwanan gobe sashen qwaqwalwarsa da ya nadi muryar Abbie ta qarshe.....magiyar Abbie ta qarshe akan roqarta ta zauna ya gaza goge su......ya gaza goge wannan rarraunan sautin nasa daga nemory dinsa. Abinda ke sake aza masa wata mahaukaciyar wuta,tare da dasa masa fara kallon halittar diya MACE a baibai. Yana cire kayan saddiq yana kallonsa,a duk sanda zuciyar dan uwansa ta motsu shine mutum na farko dake fara fahimtar hakan. Ya kammala cire kayan tsaf ya musanya dana gida sannan ya juya ya adana na makaranta yana musu kallon tsanaki,dukka ruhinsa da zuciyarsa tana makarantar,yana wassafa malami na farko ya fita zuwa yanzu,malami na biyu kuma na dab da shiga ajin komai yana ciki. Hannu ya sanya ya share fuskarsa yana qoqarin lanqwasa zuciyarsa. Farat daya qaunar da yakewa karatu ya ninku a zuciyarsa ganin abba ya bashi dukkan wata dama da zaiyi karatun,sai gashi farat daya tana nema ta zama silar da zaiyi nisa sosai da MAFARKINSA?. _________________ *_CIKIN DUBU DABAN TAKE_* *_TABBAS AKWAI TURARE AKWAI MUNA TURARE_* *_NA GWADA NA GANI_* *_YA SUBHANALLAHI_* *_QAMSHI NA TASHIN KAN ME GIDA_* *_QAMSHIN DAKE DAGAWA KISHIYA HANKALI_* *_NATACCEN QAMSHI DAKE KAMA GURI DARAM_* *_WANNE GANGANCI NE YA SAKAKI TSAIWA SANYA?_* *_ME KIKE JIRA?_* *WANNAN DIN GUARANTEE NE FA* *TASTED AND TRUSTED 100% PERCENT* *KI SIYA KI GODEMIN HAJIYA* *INCENSE BY KABO DAUGHTER* *_DUNIYAR TURARE ME BADA ASALIN QAMSHI ME KAMA JIKI DA MUHALLI,NUTSATSEN QAMSHI ME SANYAYA ZUCIYA DA DADEWA A WAJE_* *_IDAN KINA DA MATSALA KINA NEMAN TURARE ME KAMA WAJE,KINASON SAKEWA OGA SABON QAMSHIN DAKI DA PARLOR,KE KANKI KINASO KI SHIGA WAJE A DINGA TAMBAYAR WACE TA ISO NE?_* *MAZA MAZA JEKI KI GWADA WANNAN_* *INCENSE BY KABO DAUGHTER 08032119803* *_zaki dariya za kuma ki godemin_* *_gani ya kori ji_* *hakanan sai an gwada akan san na qwarai* _________________ *Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU* _TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_ _QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_ _K'ALBIM Mamuhghee_ _AJIYA A DUHU Billynabdul_ _DUNIYATA Huguma_ _Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_ *hudu 2k* *uku 1500* *Biyu 1k* *Daya 500* _YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_ *09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA* *IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA* *09033181070* *BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK* *ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171* *ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI* *AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA* 89825722 Nousaiba lawali maradi 1000cf *_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_* *_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_* *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 08 __________________________ *_CIKIN DUBU DABAN TAKE_* *_TABBAS AKWAI TURARE AKWAI MUNA TURARE_* *_NA GWADA NA GANI_* *_YA SUBHANALLAHI_* *_QAMSHI NA TASHIN KAN ME GIDA_* *_QAMSHIN DAKE DAGAWA KISHIYA HANKALI_* *_NATACCEN QAMSHI DAKE KAMA GURI DARAM_* *_WANNE GANGANCI NE YA SAKAKI TSAIWA SANYA?_* *_ME KIKE JIRA?_* *WANNAN DIN GUARANTEE NE FA* *TASTED AND TRUSTED 100% PERCENT* *KI SIYA KI GODEMIN HAJIYA* *INCENSE BY KABO DAUGHTER* *_DUNIYAR TURARE ME BADA ASALIN QAMSHI ME KAMA JIKI DA MUHALLI,NUTSATSEN QAMSHI ME SANYAYA ZUCIYA DA DADEWA A WAJE_* *_IDAN KINA DA MATSALA KINA NEMAN TURARE ME KAMA WAJE,KINASON SAKEWA OGA SABON QAMSHIN DAKI DA PARLOR,KE KANKI KINASO KI SHIGA WAJE A DINGA TAMBAYAR WACE TA ISO NE?_* *MAZA MAZA JEKI KI GWADA WANNAN_* *INCENSE BY KABO DAUGHTER 08032119803* *_zaki dariya za kuma ki godemin_* *_gani ya kori ji_* *hakanan sai an gwada akan san na qwarai* ___________________________ "Hamma" Ya tsinkayi muryar saddiq tana kiransa,sai ya waiwaya ya zubawa qanin nasa ido "Wai sai yaushe maama zata dawo?,yaushe za'a daina yi mana gori?" Tambayar ta tsinka zuciyarsa sosai ta kuma sake yi masa tabo. Ya zuba masa idanu sosai,kamar bazai ce komai ba sai ya motsa labbansa "Duk tsanani duk wahala.....kada ka sake zancanta sadiq,ta tafi kenam,ba kuma zata sake waiwayomu ba.....ni zan tsaya dakai a kowanne yanayi da.mataki na rayuwa,bazan bari kasha wahala ba in sha Allahu,bazan bari ka zubda hawaye irin wanda na zubar ba.....kayimin alqawari ba zaka sake zancan maama ba?" Ya qarashe maganar yana ritsashi da idanu. Kai ya jinjina a sanyaye yana maida jikina ga bango ya jingina,wani abu sosai yaron yakeji da baisan yadda zai fasalta shi ba "Ka cire uniform din" Ya bashi umarni ya sanya kai yana nufar qofa bayan muryar mama ta karade ilahirin gidan ta cimmasa har dakin nasu "Yaaya zan tayaka wankin" Sadiq ya fada a gaggauce "Aah banaso,kayi zamanka" Ya amsa masa yana qarasa ficewa. Tun daga wannan rana ta sauya lokutan zuwansu makaranta zuwa lokuta na bauta da wahalar ayyukan gidan da basu ratayu a wuyansu ba. Duk wani aiki ta kallafa masa,har takai ta bawa ainihin masu gudanar da aikin hutu tace saita nemesu,hutu ba tare da an yanke musu albashi ba. Dukka yawa da azabar aikin aikin banza ne a garesa idan aka kwatantashi da maganganu masu dafi da take jifansu dashi. Duk kalmarta guda daya me tsananin guba ce tana kuma same zuba masa dafi da guba me daci ne cikin zuciyarsa. Rashin ko inkula dinta a kansu da dukka dabi'unta basi fiya bashi mamaki ba,saboda ya riga da ya yiwa mata kudin goro gaba daya,tunda ya fara ganin sample daga kan mahaifiyar data tsugunna ta kawoshi duniya kuma. MATA BASU DA IMANI,BASU DA KIRKI,BASU DA TAUSAYI,BUQATAR KANSU CE A GABA DATA KOWA. Wannan shine rubutaccen abu daya zauna radam cikin kwanyarsa da zuciyarsa,wanda baya jin akwai lokacin da zaizo wanda wannan zai wanke daga cikin kundinsa. Duk yadda Faruqee ke cikin tsananin fushi da daukar alwashin sai ya gayawa abba idan ya dawo,in yaso ta kamashi ta gutstsira namansa ta kacalcala amma me babban suna ya danneshi ya kuma haneshi "Maama ma data haifemu ta gujemu,ta gaza tausaya mana?,ta kasa haquri damu?,ina ga mama......mu din ba dolenta bane Faruqee,iya abinci da take sawa ana bamu da gurin kwana ma kawai tayi qoqari" "Abincin nata ne?,ko gurin kwanan nata ne?,sannan shi kansa abincin waye yake qoshi?,bayan store din gidan nan cike yake da kayan abinci?" Qaramin murmushi ya saki. Duk da qarancin shekarunsa amma kwanyarsa tana aiki yadda ya kamata. Dukka wannan bai cika masa ciwo bafa,abinda maama tayi ya danne dukka wadannan ciwo da zafi da kuma tsaiwa a zuciya. Abu daya ne yakejin yana dab da kasa jureshi,hanashi zuwa makaranta......yana qaunarta