← Book details A Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 84

Sashe 40

A Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kudi ba?,ai amfaninki kiyita kawo mana kudi tunda hanyar da kika zabawa kanki kenan" Ya fada yana yarfe hannuwa shi daya a gefen titi,kai kace ya samu matsalar kwanya. Juyawa yayi da zummar barin wajen,saidai taku biyu rak yayi wayarsa keypad dake aljihunsa ta dauki kururuwa. "Kai jama'a......Allah yasa ba bala bane.....kash.....shine wallahi" Ya fada yana qoqarin danna madannin wayar da yayi tsananin tauri saboda ganin rayuwa da yayi. "Hel.....helo bala.....don Allah kar ka damu.....ai in sha Allahu ina me tabbatar maka damu za'a shiga wannan cacar.....yo ta ina zamuyi wasa?,bayan kai da kanka ka tabbatar min mutumin nan attajiri ne......ai ina maka rantsuwa da Allah baka bina bashin rantsuwa wannan karon arziqi ne yake kiranmu....inata buga buga naga na samu adadin abinda akeso a shiga cacar dasu....kada ka damu,zuwa nan da dare in sha Allahu zaka jini,yauwa na gode" Ya fada yana sauke wayar,ya soma laluben aljihunsa don maidata ciki yana sake magana a fili. "Idan ma Allah ya taimakeni na haye da wadannan kudaden ina zaki sake jina?,ai nima na zama attajirin kaina don ubanki" Sai yaja qwafa sannan tsaki ya biyo baya,ya juya yana sauya hanya. *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 38 Sau biyu yana sake juyawa yana kallonta. Tun bayan sallamar da tayi yayin shigowa motar bata sake cewa wani abu ba. A nutse take da dukkan nutsuwarta,nutsuwar data sake janye ra'ayinsa a kanta matuqa. "Erhmmm" Ya danyi gyaran murya kafin ya dora da "Na gode qwarai da baki wofantar da magiyata ba.....hakan ya nunamin kinsan darajar dan adam....." Maganarsa ta sanyata dawowa tunaninta tare da tunasar da ita a inda take. Batace masa komai ba,tadan dai motsa kadan alamun tana saurarensa,hakan ya bashi damar ci gaba da magana. "Da farko dai sunana alhassan.....ko zan iya sanin sunan malamar?" Sunan daya kira kanshi dashi ya sanyata juyawa kadan ta kalleshi sannan ta maida dubanta ga kwaltar da suke bisa kanta. Kaman ba zatac e komai ba sai kuma ta motsa bakinta "Sunana....." Sai tayi hanzarin dakatawa. Shima kaman sauran?,yana buqatar a bashi stamp?,yana buqatar personal suna nashi tamkar dai sauran 'yan uwansa jinsinsa?. Eh yana buqata,saidai shi din bata jin zatayi wani doguwar mu'amala dashi da har zai buqatu ya zuwa stamp na musamman "Da alama sunan nan me tsada ne ko?,sai na siyeshi?" Ya fadi yana dan satar kallonta kadan fuskarsa dauke da murmushi. Kai ta girgiza a hankali "Sunana sawwama" "Nice and good name.....me azumi kenan?" Ya fadi yana dubanta kadan. Kafada ta daga,koma meye ma'anar sunan bai zame mata damuwa ba,kawaidai ta bashi sunan ne don shine sunan da yazo kanta. "Ma sha Allah......gashi mun iso inda kika cemin,kuma ina da tarin abubuwan fadi don inason alaqar tamu tayi nisa,tafi haka zurfi,za'a bani wani abu kaman number waya ko adress nazo na sameki?" "Wayata bata da guarantee adress kuma bani da" Ta bashi amsa ta kai tsaye daidai sanda yake tsaida motor din a inda ta nuna masa. "Waya ba guarantee adress aishi zai zama babban guarantee ko?....me yasa kikace baki da adress?" "Saboda bamu da gida" Ta sake bashi amsa kai tsaye sanda take dubansa da fararen idanunta masu sheqi da hasken rana ya qara musu qyalli,abinda ya sake daukan hankalinsa kenan. Murmushi ya saki yana jin tana sake burgeshi "Alright.....nasan dai ba dan adam din dake rayuwa a titi.....amma bazan takurawa zabinki ba......zaki iya bani dama ta uku?,damar yin magana dake a nan?" Numfashi ta sauke a hankali tana jin ya takurata da yawa,ta daga hannunta dake daure da agogo ta kalla sannan ta sauke tana juya idonta daya sashen alamun qosawa "Mintuna biyar kawai" "Na gode" Ya fada yana gyara zamansa sosai. "Bari na tafi kai tsaye kada na cinye mintunana ko?" Ya furta yana sake sakin murmushi. Batace masa komai ba still,saidai ta kafe idanunta ne saman qofar gidan dake gabansu kadan. Tunaninta yafi karkata akan gidan,tana tunanin me zataje ta taras?,wanne abu zata samu cikin gidan. "Tunda na ganki sawwama naji zuciyata ta kwanta dake.....ta kuma kamu da sonki......naji kuma a raina na samu matar aure.....ina fatan zaki bani dama....." Statement dinsa na qarshe data samu fahimta kenan. Waiwayawa tayi ta dubeshi,shima idanunsa yana kanta,da alama ya gama dukkanin bayanansa ita yake da buqatar jin ta bakinta. Dauke duban nata tayi,sannan ta saka hannu ta bude murfin motar ta zura qafafunta ta fito. Da mamaki yake binta da kallo har zuwa sanda ta maida masa murfin motar ta rufe,tadan rage tsaho kadan tana dubansa da shiny eyes dinta "Na gode da karamcinka......amma kayi haquri.....babu aure a rubuce cikin rayuwata.....na barka lafiya" Ta motsa labbanta a hankali sannan ta janye jikinta daga motar. Soma takawa tayi a hankali tana barin wajen,AURE na daya daga cikin abinda take mantawa dashi a rayuwarta. Aure yana cikin abinda yake a lissafin qarshe cikin abubuwan da suke ba dole ba a rayuwarta. Aure yana daya daga cikin abinda take masa wani irin kallon da batasan ajin data zubashi ba.....babu shi ko kadan a dictionary dinta,idanma anyi zancensa,tana masa kallon wani baqon abu wanda batasan ranar da zata saba da ji ko ganinsa ba,bare azo da batun wanzuwarsa akan kanta. Ko kadan bata damu da tsaiwarsa a wajen ba,abu daya ta sani.....kaman sauran mazan,yadda basu da masaniyar daga inda ta fito......hakanan bata basu qofa ko qanqani game da sanin inda zata ko inda zata shiga. Don haka bata kutsa kanta cikin gidan ba sai data kadar masa da hankali,ta kuma tabbatar ya bar layin. Da sallama a bakinta ta shiga madaidaicin tsakar gidan dake shimfide da sabon simintin da bata jima da sanyawa ayi musi shi ba saboda jin dadinsu. Yara ne aqalla kusan guda biyar wadanda shekarunsu bazai haura goma zuwa sha uku ba. Biyu daga cikinsu wanki sukeyi,daya kuma tana wanke wanke,yayin da guda dayar take jawo ruwa a rijiya tana zubawa a babban mazubin ruwan da suke amfani dashi a gidan. Sallamarta ya sanya kowacce ta watsar da abinda takeyi,suka kuma rugo da gudu suna rige rigen isa inda take. Kyakkyawar fuskarta ta fadada da fara'a itama ta buda hannunta tana tarbarsu,daidai sanda muryar matar ta iskesu "Ku da waye haka?" Ta bayyana tare da qarashen tambayarta tana qoqarin daura dankwali saman kanta. Murmushi ne ya wadaci fuskarta itama,kakkaurar matar ma'abociyar tsaho da qiba,saidai alamu sun nuna yanayi na rayuwa ya sanya qibar zubewa sai saura data zama halittarta ce ba zata iya rabuwa da ita ba. Baqace wannan ya sanya dukka kamanninta sukafi karkata ga kamannin babarbariya. "To ku barta ta qaraso mana" Ta fadi tana juyawa cikin dakin da ta fito,dukansu sai suka bi bayanta harda sabreen daketa jefawa yaran tambayoyi. Tare suka zauna da yaran saman shimfidaddiyar dardumar da matar ta shimfida saboda sabreen din,daya daga cikin yaran ta miqe ta fice sai gata da ruwa adan qaramin jug da cup,yayin da sauran sukaci gaba da zama a kewayenta. "Ina Ayshatu?" Tambayar farko da sabreen tayi mata bayan sun gama gaisawa,tambayar data sanya yaran suka miqe daya bayan daya suna fita a dakin. Bata ce komai ba matar saita miqe tana dosar wata qofa dake maqale a falon,itama batace komai din ba ta miqe ta biyo bayanta. Yalwataccen daki ne dake wadace da tsafts,ba komai a qasan sai wata lamusashiyar katifa guda daya yashe a qasa. Daga samanta idan ka duba da kyau mutum ce a kwance data lulluba duka jikinta. A sanyaye sabreen ta qarasa gaban katifar,ta saka hannu ta yaye rufar bakinta yana rawa ta kira sunanta "Aishatu?" A hankali ta ware idanunta akan sabreen din,sai kuma wani busashen murmushi ya subucewa kyakkyawar fuskar yarinyar "Aunty....kece kika zo?" Ta tambayeta da siririyar muryarta. Kasa riqe kanta tayi,sai kawai tayi qasa da kanta hawaye yana diga daga idanunta. Tana jin tausayin yarinyar kamar zai fasa zuciyarta,tana jin kamar zata narke a wajen,tana jin inama ace tana da ikon fidda ciwo ta farat daya daga jikin mutum a yanzu yanzu basai anjima ta cisgeshi daga jikin ayshatu "Ko baki da ikon cire mata shi yanzu yanzu.....kina iya sama muku dama ke da ita na samo mata lafiya a duk inda lafiyar take a fadin duniya" Wani sashe na zuciyarta ya bata amsar data motsa mata wani qwarin gwiwa daga can qasan zuciyarta. Wannan ya sanya ta sake daga idanunta tana kallon aysha. Allah ne kadai yasan bila'adadin mata da yaran da suka shiga irin yanayin da ayshatu ke ciki duka sanadin TAIMAKO. Lalacewar al'ummarmu abune me matuqar ban mamaki da daure kai. FYADE ba'a daukeshi da wani muhimmancin da me aikatashi zai fuskanci hukunci mafi tsananu ba a tsarin doka. Tana iya tuna yawan kudaden data kashe,shige da ficenta da kai kawo data dinga yi kafin ta samu ayiwa azzalumin hukuncin da doka ta tanada. A abinda ya yiwa aisha,ba hukuncin daurin shekaru take da buqata ba......lahira yafi kamata ya baqunta yaje ya hadu da hukuncin mafi iya hukuncin masu hukunci. Sosai ta bawa zuciya da gangar jikinta qwarin gwiwa,ta zauna sosai ta yiwa yarinyar komai. Ta bata abinci ta kuma dinga hilatarta,har suka dinga hira tana saurarensu murmushi yana subuce mata. Hakan ya sanyaya ranta kafin su kebe da ummaa ta sake mata bayanin data yi mata a waya. "Waje nakeson a fita da ayshatu,inason ta warke sumul taci gaba da rayuwarta,duka duka shekarunta sha uku,ya kamata ta rayu kamar kowa" Ta fada zuciyarta tana mata zafi. Allah ya dora mata tausayin yaran da matar kanta da batasan asalinsu ba,amma dukka dawainiyarsu kusan kaso tamanin cikin dari tana a wuyanta,hatta da hayar gidan da suke zaune a ciki kuwa,banda abinci da ma karantarsu rayuka shida. Da idanu ummaa take bin sabreen. Tasan cewa dukkaninsu babu wanda suka hada dangantaka a tsakaninsu,amma suna jin juna kamar 'yan uwa,suna kuma ci gaba da tsananin shaquwa da juna.....kuma a yanzun sune 'yan uwan kawunansu. "Sabreen......kiyi iya abinda zaki iya mu barwa Allah sauran.....samun maganin ayshatu a gida Nigeria ma miliyan nawa ya kama bare ayi batun fita da ita waje?,kinsan miliyoyin kudin da za'a cajemu?,daga visa passport masauki abinci da zaman asibiti zuwa kudin magani?" Shuru sabreen tayi tana saurarenta,tana jin zuciyarta na wani irin ciwo,irin ciwon da mutum kanji a duk sanda yake tsananin son abu amma babu ikon samuwar wannan abun gareshi. Numfashi taja sosai ta aje tana
Chapter 40 · 0% Book details