Sashe 25
A Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Idanunsu cikin na juna na wasu sakanni,sai ta fara janye nata duban daga kanta tana ci gaba da nufar soron. HADIYYA......Idan har a baya za'a gaya mata rayuwa zata ajeta a bigiren da suke kai a yanzun ita da ita zata qaryata......idan har a baya za'a gaya mata rayuwarsu zata koma kaman yadda take a yanzun zatace mummunan mafarki ne mara ma'ana....wanda bashi da tushe ballantana makama. Hadiyya 'yaruwar haihuwarta,wanda mahaifi yayi silar zamowarsu jini daya......hadiyyan da suka taso qarqashin rainon mahaifiyarta......cikin daki guda saman shimfida guda,duk da murdadde kuma zazzafan kishin da mahaifiyarta ke bazawa.......amma hakan bai sauya komai ba na kusancinsu. Sai gashi a yanzun sunyi irin rabuwar hannayen riga. A yanzun haka tana nata karatun cikin makarantar koyon aikin jinya bisa daukar nauyi da kulawar yayan mahaifiyarta......yayin da tata rayuwar tayi matuqar shan banban da ta hadiyyan.......take neman ta nutse cikin neman dauki da tallafin data gaza me kawo mata,har sai da tayi wani irin wawan tsalle da batasan zata sauka a daidai ko kuma garin saukar tana iya gamuwa da karaya da tarin raunukan da zasu zamewa rayuwarta tabo?. Takai qarshen tunanin sanda takai bakin qofar farfajiyar gidan ta farko,saita aza tafin hannunta saman fuskarta tadan shafi fuskar. Tasan bawai kuka takeyi ba,don a yanzun batajin cikin qwayar idanunta akwai sauran ruwan hawayen da suka rage da zasu bata hadin kan yin kuka. Kawai huci da dumin da fuskarta ya dauka takeso taji ya huce,idanunta sake mata dan zugi zugi tanason rage musu adadin iskar dake shiga cikinsu. Karo sukayi da huda sanda take shirin fita shigowa su suna shirin shigowa. Suka ja baya dukkansu hudan tana dan riqe goshinta "Ke kuma ina kuka tsaya haka dukka ku ukun har ana shirin kiran salla?" Ta jefa mata tamabayar tana tsareta da ido. Kafin huda tace komai haneefa ta tsinke da dariya "Anty.......yaa nadra muka tsaya jira......bata bada hadda ba sai malam ya tsareta" Idanunta ta mayar kan nadra wadda fuskarta ke a daure "Garin yaya?,kin soma wasa da haddar ne?" Kai ta girgiza da sauri,tana shirin magaa hudan ta rigata "Kallo suka tsaya yi jiya da daren bayan kin kwanta" Fuska a daure ta sake maida kallonta a kansu "Ashe?,yau zaku jawa kanku,sai na tsinke kowanne cable na kallo dake dakin nan" "Ah wai.......ni abunnan yana dauremin kai?,wai lalatacce shike tarbiyya" Murya bibo ta ratsa kunnuwanta sanda take dubansu nadra. Dukansu ido suka azawa bibo din lokacin da take kutsowa cikin gidan. Kaman yadda suka fita ne dazu,ita da daada,saidai kaman dazun ma daada ratsewa tayi ta wuce abinta ba tare data tsaya yiwa bibo tayin su wuce ba kamar dazun. Motsawa kadan huda tayi wanda motsinta kadai ya sanar da SABREEN abinda take shirin yi. Yatsarta ta kada mata sautin da ya sanyata tsaiwa can tare da hadiyar wani abu me tauri a wuyanta *SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI* *_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_* *_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_* *_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_* *_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_* *ZAFAFA BIYAR* *_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_* *Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU* _TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_ _QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_ _K'ALBIM Mamuhghee_ _AJIYA A DUHU Billynabdul_ _DUNIYATA Huguma_ _Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_ *hudu 2k* *uku 1500* *Biyu 1k* *Daya 500* _YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_ *09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA* *IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA* *09033181070* *BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK* *ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171* *ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI* *AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA* 89825722 Nousaiba lawali maradi 1000cf *_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_* *_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_* *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* *Arewabooks:@Huguma* https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997 PAGE 26 __________________________ *_ALBISHIR A GAREKU!!_* *_SHIN KUNSAN UMMUMAHNOOR LUXURIES TA TANADAR MUKU INGANTATTUN KAYAN ADO NA FITA KUNYA KUWA?_* *_KAMAR SU_* Atamfofi Laces Shadda Materials Takalma Jakunkuna Mayafai Trolley Sarka da dan kunne Oil perfumes *_karki tsaya sanya har ayi babu ke,maza garzaya ta nan_* Numbers 08034469681 08135142610 Handles Instagram @ummu_mahnoor_luxuries TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries Facebook ummu_mahnoor_luxuries *_inganci da kwalliya shine muradinmu_* __________________________ "Ku wuce muje" Sabreen tace dasu,suk sai sukayi gaba tana biye dasu a baya. Nadra ta hadawa kayan duka ta wuce musu dashi daki. Ita tayi tsaye dasu kowacce ta gama buqatarta suka daura alwala suka wuce daki. Sallah sukayi bayan sun sauya uniform. Har a sannan tana ankare da yadda huda din keta hadiyar zuciya. Ta sani muddin tace zata saki huda tayi abinda takeso zaman bazaiwa kowa dadi ba......tafi huda zuciya nesa ba kusa ba......tafi huda dabi'ar take yanke.....amma me?,daga baya ta fahimci me irin wannan dabi'ar ba kasafai yake nasara ba. Sai data kammala sallar magariban sannan tabi takan wayar. Ta samu miscal biyar hade da wasu saqonnin daga gefe. Tabi number tasa da kallo,sai a yanzu takejin ta shirya saurararsa. Kamar yasan tana riqe da wuyar saiga wani sabon kiran ya sake shigowa,don haka ta miqe a nutse ta koma daki tana matsawa daga inda su nadra dake cin abincin dare suke. "Laifin me nayi dana cancanci wannan uqubar fateema?" Numfashi ta saki wanda sautinsa ya isa har kunnensa "Ki gayamin ko meye nayi a shirye nake da na nema afuwa" Shuru ta sakeyi tamkar bata layin,saidai tana sauraren dukka maganganunsa "Fateema" Ya sake kiranta da sunan da shine nasa STAMP din,sunansa ne shi daya,duk duniya shi ta mallakawa wannan sunan "Naam" Ta amsa a karon farko tunda ya fara maganar "Kinsan irin rayuwar dana tanadar miki?,kinsan irin gatan da nakeson miki?,kinsan yadda nakeson maidaki tauraruwa a cikin mata?,kinsan yadda nakeso ki koma tamkar sarauniya?" "Dukka wadannan dama abinda ka lissafa basu nake da buqata ba" "Me kike da buqata fateema......ki gayamin,a shirye nake na mallaka miki su......" "Zamu iya haduwa?" Ta jefa masa tambayar "Ko a ina nake a duniya a yanzun haka kika ce kina buqatar ganina zan wanzu a gabanki" Maida idanunta tayi ta lumshe sannan ta budesu "Mu hadu yanzu fateema?,ko dan kadanne inaso naga fuskarki" "Alright" Ta amsa masa a taqaice,abin da yazo masa a bazata,don haka a rude yace "Venue?" "Zan gaya maka,i will call you" Bata sake bashi daman cewa komai ba ta yanke kiran. Wayar ta riqe a hannunta tana juyata a hankali bayan ta zubawa guri daya idanu. Lissafi ne fal Qwaqwalwarta,dole kafin ta samu abinda take nema saita yi haquri ta sake masa,dole ta dinga bashi mabanbantan gurare har zuwa sanda tsarinta zai fada aikinta zai cimma nasara. A nutse ta miqe tana wassafa yadda zata fita yau din da dare,abinda sam ba dabi'arta bane saiya zama mugun dole,ba kuma zata iya tuna lokaci na qarshe da hakan ya taba faruwa da ita ba,amma yanzun dole ta fitan,tanason ta amintar dashi sosai a kanta. Kai tsaye ta wuce ma'ajiyar kayanta tana duba suturar da zata dace da ra'ayinta a wannan lokacin. Da idanu ta gama qare musu musu,daga qarshe ta tsaya saman wasu Turkish dress masu strip skirt long sleeve shirt da doguwan kinomo sai madaidaicin veil da zai lullube saman kanta. Sam bata da ra'ayin sutura me matse jiki duk kuwa da yadda mutane da yawa suke kallon ita tafi dacewa da irin wannan shigar. Tsaf ta shirya cikin kayan kalolin navy blue da gray color. Sanda ta gama nada veil din a kanta sai data sake duban kanta sosai ta cikin madubin. Tayi wani irin sassanyan kyau me matuqar daukar hankali. Ta miqa hannu a nutse ta dauki turarenta ta feshe jikinta can qasan ranta tana jin fargaba kadan kadan kan haduwarta da mashkur,saidai kuma wani sashe na zuciyarta yana qarfafa mata gwiwar ba komai,wannan ne haduwan farko,nothing will happen. Asalin wayarta ta jawo tana lalubar number JIB. bugu daya tak ya dauka,tadan motsa bakinta a nutse "Ina fatan kana available kuma free" "Ko ba hakan bane ai ya zama dole nayi creating time wa ke.....me kike buqata?" "Connection" Ta fada a gajarce " A daren nan?" "Haka abun yazo,mashkur......mashkur alqali abdulkreem" "Done.......wancan aikin ya kusa kammala......akwai ragowar information dana kasa accessing.....but...." "Karka damu.....mu sanya wancan a mala.....wannan din shine yafi muhimmanci a yanzu" "An gama.....bani code......let me write it" Ya fada yana dan riqe wayar kadan kafin yace "Okay.....karanto" A nutse ta karanta masa wasi gajerun lambobi guda uku sannan ta katse kiran. Ta jawo locker madubinta ta ciro Bluetooth tayi danne danne saman wayar tata ta bada wasu sakanni sannan ta maqala a kunnenta. Saita aje wayar,ta dauki wancan Samsung din ta kunnata sannan ta fara yunqurin kira. Bugu daya tak tayi aka daga,ta kalli wayar da mamaki sanda yake cewa "Am ready to go princess......ina zaune a mota nida driver a parking lot na gida" "Yayi.....but if possible ka taho kai daya mana" "An gama" Ya amsa mata cikin farinciki hankali kwance. Tana kammala saka takalma huda na shigowa dakin. Kallo daya tak tayi mata taga yanayinta ya sauya. Hudan tadan ritsata da idanu tana dubanta,saidai tun kafin takai ga tambayarta ta bata amsa "Zan dan fita kadan amma yanzu zan dawo" Iya abinda ta gaya mata kenan ta fara takawa zata fice. A jikinta taji yarinyar kallonta take,a jikinta taji tana tsaye ne kawai har yanzu,don haka ta tsaya cak sannan ta waiwayo. Ido suka hada,sai a sannan hudan ta kauda kanta. Iya hakan ya gayawa Sabreen maganganune sosai cikin zuciyarta,wataqila girma da kimarta kadai zai hanata ta furta mata su. Taku hudu tayi ta iso gaban hudan "Dole ce ta saka zan fita huda......amma bazan wuce awa daya ba,idan na dade biyu" "Amma anty...." Hudan ta furta fuskarta fal damuwa. Yatsanta ta dora saman lips tana duban hudan,sai kuma daga bisani ta dauke yatsan tana aza dukka hannuwanta saman kafadarta,ta kuma zaunar da ita saman stool na madubin dakin "Ke daya ce tal cikin mutanen da sukasan wace Sabreen gaba daya baya,kada kiyi tunanin na canza......ban canza ba huda.....kuma har abada bazan canza ba.....nayi alqawari......mommu da abba dake qarqashin qasa bazan bari suyi kaico dani ba" Kai ta gyada a hankali tana kallon Sabreen kamar yadda