← Book details A Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 84

Sashe 69

A Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kasance daga kujerar dake facing dinsu. Serving nasu komai da komai tayi,tana yi tana jansu da hira tare da qoqarin tuna musu wani abu na daga quruciyarsu. Shidai fu'ad idanu ne kawai nashi ba tare daya iya maida komai ba,har ta kammala tana fadin "Gashinan kowa ya dauki nasa". Duban abincin yayi da kyau,gaskiya ta fada batayi kuskure ba,a baya baida abincin da yakeso irinsa,amma tun daga ranar data dafa abincin cikin gidansu,ta kuma yiwa mahaifinsu haramiyar abincin a sanda yake kwance yana jinya.....yunwa take sake take rawa wajen galabaitar dashi,ta hana masa abincin,abinda yayi silar kwanansa da yunwa,tun daga ranar har kawo yau bai sake saka irin abincin a bakinsa ba,daga ranar ya fita a ransa,fita ta har abada wadda har yau bai sake dawowa zuciya da rayuwarsa ba. "Shikam hamma ai maamah yanzun wannan ba cimarsa bane......nima kuma kin manta dama ba kasafai na fiya ci din ba?" Musaddiq ya fada yana shafa kanshi idanunsa cikin na maamah din. *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 65 Wani abu ne yaso ya tsaye mata a rai,tunzura takeso tayi amma kuma tana gayawa kanta ba yanzu ba......idan ma basuci na yau ba ai na gobe yana nan,muddin kuma zasu ci gaba da taka qafarsu cikin gidan yau ko gobe nasara tana nan tare da ita. "Yaushe Muhammad ya daina ci?" Ta yiwa musaddiq tambayar sai kuma ta maida dubanta ga fuskar fu'ad din a mamakance,saidai kuma sanda suka hada idanu dashi sai komai daya faru a wancan ranar ya dawo mata a take,amsar tambayarta ta fita kamar budewar shafukan littafi. Wani abu taji me nauyi wanda sam baiyi kama da kunya ko nadama ba,tabbas a baya din don ba cikin daidanta take ba.....ba yaran bane a gabanta ballantana abinda ya shafesu da har zata lura da meye ya damesu da wanda bai damesu ba.....amma tabbas sai yanzu ta tuna,tun daga ranar yake bar mata kwanonta gaba daya yadda ta zuba. "To amma bai kamata ace bakuci komai ba koda lemo ne" Ta sake fadi tana jan jug din gabanta tare da qoqarin raba kofunan ta zuba musun kada ya zamana komai da komai ma tayi asararsa a yau din. Idonsa still a kanta,ya miqa hannu ya jawo gorar ruwan daya tabbatar a kulle take ya soma budeta,qarar budewar ya sanya ta daga kanta zuwa gareshi tana dubansa "Ruwa kuma muhammadu?,ga lemo dai" Ta fada tana tura masa wanda ta zuba "Maamah dare ya soma yi.....idan kuma dare ya fara bana iya cin komai...." Dubansa ta sakeyi kadan sai kuma ta dauke kanta tana qirqiro murmushi "Kowa time table zai bani na abinda yakeso yaci kullum har sati guda koma sati biyu.....masu girki na musamman zan ajiye muku.....burina naga kun kusanta dani......na maida tsohuwar alaqar dake a tsakaninmu" Ta qarasa maganar tana duban cikin idanunsu. "Fu'ad" Ta sake kiran sunansa,ya daga fararen idanunsa da suka fara rusuna saboda gajiya da zama a wajen,sam baya jinsa comfortable sam sam "Me yasa kabar musaddiq tare da farouq......duk da ba laifi bane.....amma kaman zaifi cancanta ya kasance tare dakai qarqashin naka kamfanin" Shuru ya biyo baya na second uku,sai ya maida idanunsa ya kulle yana jan boyayyen numfashi. Shikam yayi imanin ba zata canza ba,ya tabbatar abune me wahala da girman gaske da zai sauya mata hali farat daya. Wannan ya sanya kowanne taku ko motsi nata yake sanya masa ayar tambaya,wani lokaci idan tayi wani move din sai yaji gaba daya kanshi ya juye yana tambayar kansa anya da gaske maamah din itace uwa ta asali a garesu?. "Kowanne bawa da abinda yafi shaawar yi yafi qwarewa a rayuwarsa......yadda abba ya ginemu shine kowa ya dauki zabinsa da ra'ayinsa a rayuwa muddin bai kaucewa hanya ba....inda kikaga farouq da musaddiq su suka zabi wannan sashen duk kuwa da cewa tare da farouq mukayi gwagwarmayar samar da abinda na gina din a yanzu.....ba wanda ya zaba masa ko ya tursashi gashinan maamah ki tambayeshi" Juyawa tayi tana duban musaddiq ranta duka a jagule,bata son kowa ya rabi fu'ad a duniya idan ba dan uwanshi ba,batason kowa yasan sirrin dukiyarsa idan zaiyuwu sai ita daya,wannan tunanin ya sanya ta yanke shawarar sanya ido me tsananin a alaqar fu'ad din da amna......don ba zata taba yarda amina ta dauki d'iyarta ta qwaquma masa ba su qarasa nadeshi. "Shikenan,Allah ya taimaka" Ta fadi tana sauke numfashi bawai don ta haqura a zuciyarta ba. Kawai tana ganin tunda komai yana kan turba bai kamata ta bata lokacinta tana dogon zance dasu ba,lokaci kadan take jira ta soma bada umarnin wanda zai shiga ko ya fita daga rayuwarsu. "To yaya sunan surukar tamu musaddiq?....koda wasa baka taba attempting kawota ta gaida mamarka ba?" Ta yiwa musaddiq tambayar tana dubansa da murmushi,cike da zaquwa da son jin kalar matan da suke shirin kawowa rayuwarsu. Wani babbab abu da yake cikin tsarin abubuwan da takeso ta yiwa garambawul idan damar da take tsimayi ta samu,tanason surukanta su zama qarqashin ikonta fiye da yadda hajja ke juya nata mulkin a gidan. Murmushi kadan ya saki,karon farko da yaji 'yar kunyarta ta sauko masa "Minal bata iya zuwa ko ina,daga makaranta sai gida.....zata zo wataran in sha Allah". Ba haka takeson ji ba,don haka ta gyara zamanta tana sake sakin fuskarta "Aah wataran yaushe kenan?,ina buqatar ganinta mu tattauna ka shaida mata mamarta nason ganinta......" Ta fadi din don da gaske tanason ganin wace ita?. Zuwan nata kuma a nan ne zata samu amsoshin tambayoyib data tabbatar ba zata samesu daga bakin musaddiq ba. "In sha Allah" Ya fadi a taqaice yana auna yadda abun zai kasance. "Kai kuma fa?" Ta waiwaya tana duban fu'ad daya tattara hankalinsa duka saman wayarsa tamkar ma baya jin abinda suke fadi. Gajiyayyun idanunsa dinnan ya daga ya kalleta,sai kuma ya maida dubansa ga musaddiq. Kan musaddiq din a qasa yana satar kallon fu'ad din ta qasan idanunsa,boyayyan murmushi nason qwace masa. "Me maamah?" Ya tambayeta da sautin muryarsa da tayi laushi sosai. "Wa ka daukomin a matsayin suruka?" Ta sake maimaita tambayar tata. "Babu fa maamah...." Musaddiq ya fadi muryarsa na nuna murmushin da ya boye. Debe kallonta kacokam tayi ta maida kan musaddiq tanason sake samun tabbacin hakan "Kamar yaya kenan?" Satar kallon fu'ad yayi sannan ya dubi maamah,yayi qasa sosai da muryarsa,duk da yasan dole ya jishi don yana da wannan baiwar ta kaifin ji "Ba wata budurwa.....tsoronsa ma suke......ba wadda take iya tararsa maamah tace tana sonshi" "Very good" Ta fada qasan zuciyarta. Tsananin farincikin da taji ya bayyana har saman fuskarta,tadan danne tana hada rai "Garin yaya?.....har yanzu halinka dinnan bai canza ba?" Ta watsa masa tambayar . Karon farko kenan da magana kwatankwacin wannan ta taba hadasu,don haka ya rasa ma da abinda zai bata amsa illa cewa da yayi "Ba yanzu ba....lokaci baiyi ba.....in fact ma da sauran lokaci" "Lokacin lokaci na ne,yana kuma tafe" Ta bawa kanta da kanta amsa a zuciyarta,amma a fili sai tace "Allah ya nuna mana lokacin". Duka hirar ba wani armashi gareta ba,amna haka suka sadaukar da lokacin har zuwa sanda ta basu izinin tafiya sukayi mata sallama suna ficewa. Suna tafe ne kawai suna dosar gidan,daga shi har musaddiq din ba wanda yace da dan uwansa komai. Sai da sukazo mabanbantan qofofin sassansu,fu'ad din ya murza key yana bude qofarsa yace da musaddiq "Shigo ciki ka zauna muyi magana" Ba tare daya dubeshi ba,ya gama budewa ya shige musaddiq din yabi bayanshi. Zaune kawai tayi tana duban kwanukan abincinta da suka barta dashi,banda ruwan gorar dukkaninsu ba abinda suka taba ko qanqani. Lemon data zuba ta turawa musaddiq din ma tana saka ran zaiyi koda kurba daya ne amma baiyi din ba shima sai ya buge da shan ruwa. Ta fahimci yana bin sahu tare da matuqar kwaikwayo ga fu'ad,iya wannan ya isa ya bata amsar cewa,muddin ta samu fu'ad ta samu musaddiq......wanda kuma wannan din shine babban qalubalen da aikin data sake amanna ba qarami bane. Furzar da iska tayi me zafi daga bakin ta,kusan komai data tsara ya wargaje babu shi,dan abinda ta amfana dashi daga zuwan nasu bai taka Kara ya karya ba. Akwai damuwa sosai a ranta da take da buqatar abokin tattaunawa,don haka ta sauka daga dining area din zuwa ainihin falon ta dauki wayarta ta lalubo hajja. "Musaddiq" Ya kira sunanshi kai tsaye sanda yake zaune saman wata qawatacciyar kujera da irinta qwaya daya ce tal cikin falon. "Na'am" Ya amsa masa. Shuru kaman bazaiyi magana ba,sai kuma ya zauna sosai yana goye hannuwansa a qirji "Inaso ka zama me takatsantsan sosai......inaso kuma ka zama me kula.....bazan hanaka zuwa gidanmu ba duk sanda kake da muradin hakan......amma kayi aiki da hankalinka da kyau......yanzun kai ba yaro bane.....ba wannan musaddiq din da ko yaushe sai hammansa yana gefansa bane don ya kula da abinda zai cutar dashi ko ya amfaneshi bane.....abubuwa sun yiwa hammansa yawa......kula da rayuwarsa yana hannunsa". Wadannan kalaman na hamman su suka dinga juyawa cikin kanshi. Duk da bai fito qarara ya masa bayani a bayyane ba,amma kamar yadda yace din shi ba yaro bane yanzun,hakanan shi a karan kansa hankalinsa ya fara dauko masa wasu abubuwan a iya zuwansu gidan yau kawai. Haka kawai ya kasa bacci a daren,har yanzu musaddiq baisan ainihin wace maamah din ba. Iya matakin da idanuwan basira da hankalin musaddiq kadai ya kaishi bai sadar dashi da ainihin wacece maamah ba........meye zata iya yi?,da wanda ba zatayi ba.......dole koda a fakaice ne ya sake nesantashi da tunkudeshi daga dukkan abinda yake ganin zai iya zama cikas a rayuwarsa. Bugu biyu tak hajja ta dauka,hakan ya yiwa maamah dadi,sai ta miqe da wayar tana nufar bedroom dinta "Na zaci kinyi bacci ai" "Aah inadai shirin tashi.....labaran ne ya zaunar dani muna lissafin abinda kamfaninsa ya samu na shekara". Ido maamah tadan fiddo cike da mamaki "Kamfaninsa fa?,yanzu lissafin shima tare kukeyi?". Dan qaramin murmushi me sauti hajja ta fidda tana aza hannunta saman kan budurwar dake kwance saman cinyarta tana amsa waya itama "To meye a ciki?,nice uwarsa fa?,akwai wani abu da suka isa su boyemin?,koda cikin gidajensu akayi abu koda da darene da safe kuwa rana bata bullowa bansan komai ba......ke banda ma ina taka birki ma wasu abubuwan......ai hatta
Chapter 69 · 0% Book details