← Book details A Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 84

Sashe 48

A Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

miki kaza?,ko a yiwa wane kaza wanda ba zallar kudi zaki amsa ba da hamma ya taba qinyi miki?" Ya jefa matar tambayar yanason gane ainihin gaskiyar da takeson lullubewa "Kai musaddiq.....kalleni nan......dukkanku ke da fu'ad nina haifa abuna......banyi lalacewar da don zaku yimin wani abu sai na zama tamkar almajira a wajenku ba....." "Allah ya baki haquri ya huci zuciyarki" Ya fada kawai don kawo qarshen zancan. Can qasan zuciyarsa babu gasgatawa ko yarda da ita ko kadan. Idan yayi rantsuwa ko kaffara bazaiyi ba,ba haka siddan hammansa yaqi yarda ya sakewa maamah tsurar kudi ba,ya yadda dashi dari bisa dari,yana komai bisa bayyananniyar hujja da kuma dalilai. Kawai dai mutum ne shi me tsananin zurfin ciki da miskilanci,wannan ya sanya idan ya aiwatar da abu babu lallai ka fahimci don me yayin?,kuma bazai taba zama yayi maka wani bayani ba game da hakan. Shuru ne ya biyo baya na wasu mintuna,tanata qoqarin controlling kanta don har yanzu bata kai ga cimma burinta na abinda takeson taji ba. Ta furzar da iska kadan sannan ta fara kiran daya daga cikin masu aikinta. Kamar ko yaushe da sassarfa ta iso saboda tsoro da gudun sabawa umarninta. "Ki sauke kayan abincin nan a nan....ko dining din zaka hau kaci?" Ta tambayeshi tana dubansa. A zahirance so yake ya gaya mata ya qoshi,baya buqatar cin komai,amma ya tabbata fadin ba abinda zai haifar sai wani rigima da tashin hankalin,don haka yadan gyara zamansa "Ta kawo nan din" Sai ta juya ta watsa mata kallo "Kinji ai abinda yace". Suna zaune ta dinga sauke kwanukan abincin. Warms na alfarma masu tsananin tsadar da ko a gidajen masu sukuni sai wane da wane. Da kanta maamah din tayi serving nasa don buqatarta shine ya saki jiki yaci sosai ta yadda zata samu daman yin magana dashi ta kuma samu duka information din da takeso. "Bismillah sauko" Ta fada da salon bada umarni nakai tsaye. Bai musa mata ba ya zamo ya sauko din,sai ya fara kai hannunsa ya dauki glass cup na lemo yana juyashi a hannunsa. Spoon ta dauko ta qara a plate din,ta kalleshi da murmushi "Muci tare ko?" Kai ya gyada kawai yana duban kwanon. Komai yayi masa banbarakwai. Ko a shekarun baya da suke da qananun shekaru ya iya abinda qwaqwalwarsa zata iya riqewa baya jin sun taba zama kwano daya,sai yanzun da ya zama cikakken mutum?. Ko a baya sanda bai kammala iya cin abinci ba idan ta zuba musu ta tura musu ta shiga sabgar gabanta hamma ne ke zama ya bashi komai zafinsa har sai ya qoshi. Hira take sako masa a hankali a hankali,tana cin abincin yana juya cokalin kawai a ciki bayan ya dire cup din lemon. Sai bayan data soma karantar kamar sakin jiki tattare dashi sannan ta aje nata spoon din tana dubansa cikin murmushi "Ya akayi kai da dan uwanka musaddiq wanda duk duniya bashi da kowa bayan kai amma ka nesanta *SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI* *_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_* *_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_* *_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_* *_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_* *ZAFAFA BIYAR* *_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_* *Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU* _TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_ _QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_ _K'ALBIM Mamuhghee_ _AJIYA A DUHU Billynabdul_ _DUNIYATA Huguma_ _Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_ *hudu 2k* *uku 1500* *Biyu 1k* *Daya 500* _YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_ *09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA* *IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA* *09033181070* *BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK* *ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171* *ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI* *AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA* 89825722 Nousaiba lawali maradi 1000cf *_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_* *_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_* *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 47 "Ya akayi kai da dan uwanka musaddiq wanda duk duniya bashi da kowa bayan kai amma ka nesanta kanka da kalar sana'arsa ka maida kanka baya ta hayar sanya jikinka a al'amura ta harkar gona?,bayan sana'ar ba taka bace,gadon gidan Alhaji hamza kibiya dinne zasu daukeka su cusa ka?,sannan su raba dansu da fu'ad kai su tsigeka daga gareshi?,wanne irin ragon azanci ne wannan shirme da shashanci?,sannan wannan kadai ya isa ya nuna akwai mummunar manufa da qulli cikin zuciyar amina da manufa aka shirya wannan". Maganganunta sunyi masa girma qwarai,mamaki kuma ya lullubeshi har sai daya tsaya kawai yana duban yadda maamah din ta haqiqice. ".....bazan yarda ba a rabamin kan yarana,bayan a mahaifa guda suka kwanta......don wannan zalunci ne kawai,duk yadda zakayi ka nema komawa sashen da dan uwanka yake aiki,shima kuma zan masa magana kaji?" Sai ta qarashe kuma cikin kwantar da harshe saboda magana ta gaba da takeson yi. "To" Kawai ya iya cewa da ita,ya sani basai an gaya masa ba,maamah din tayi nisan da batajin kira,hakanan dukkan wani bayani da zaice zaiyi mata yana zaman bata lokaci ne kawai a wajenta. "Yanzu bayan kamfanin diamond ai ina sanya ran zuwa yanzu addu'ata ta cicciba Muhammad izuwa mallakar wasu boyayyun mafanunnukan ko?" Ta fada tana murmushi tare da tsare musaddiq da kallo. Dubanta yayi sosai,yana ji har cikin zuciyarsa da gangar jikinsa bai gamsu xa yanayin tambayar tata ba,don haka girgiza mata kai kawai yayi "Bansan komai a kanshi ba maamah tunda ba sashe daya muke dashi ba" Wani abu ne ya tsaya mata a wuya,amma sai tayi qarfin halin danneshi ta amsa masa da "Haka ne......amma dai baka ce bakasan qarfi da nauyin kudaden da suke shigo masa ba ko?" Sake daga kai yayi yana dubanta zarginsa yana sake tabbata "Bana ce ba maamah.....abune da ya shafi sirrinsa kuma ba a qarqashinsa nake aiki ba.....ni ina qarqashin farouq" "Eh to.....maganar gaskiya sai yanzu na fahimci kimiyyar da ta sanya amina tayi kutin kutin din cusa danta wa Muhammed kai kuma ta rabaka dashi.....kana jininsa wanda bashi da na biyunsa a duniya amma bakasan komai nasa ba?.....wanda ni nayi imanin a yanzun inda zan zaunar da shi saddiqun nayi masa ire iren tambayoyin da nayi maka din yana da amsar kowacce fes?.....wannan itace hanya mafi sauqi da zata samu salwantar da fu'ad da dukka abinda ma ya mallaka". Idanunsa ya runtse yana jin zafin mummunan zaton da maamah din ke jifar 'yar tahalikar dashi.....matar data zame musu bango majingina,matar data zabi farincikinsu akan nata.....matar da silarta ne a yau suka zama dukkan abinda suka zama din.....suka kawo izuwa matakin da suke kai a yanzu......matar da banda ita da yanzu shi da muhammad din duka da take taqama dashi ba'asan a wacce shiyya nahiya ko yanayi suke ba. "Maamah..." Ya fada yana bude idanunsa a kanta ba tare da ya shirya tsaida maganarta ba. "Duk yadda kike tunanin anni fa ba haka take ba.....idan baki godewa anni ba bai cancanci ki jefeta da mugayen zato ba......kamfanin nan da rayukanki suke baci akai asalin diamond din da aka samu ba hamma bane kawai ya sameshi ba.....a lokacin suna tare da BB farouq......" "Amma shi ya haqo shi kuma ya samu nasarar tsira dashi.......ka dauka bansan dukka wannan ba?" Tayi maganar tana tsareshi da idanunta da suka cika da bacin rai. Lallai sai sun nuna mata fifikon matar can akanta?,bayan bata da masaniya akan sanda ta dauki cikinsu bare kuma haihuwarsu?. "Eh hakane.....amma shi BB farouq baida sha'awar harkar diamond noma yafi so shi yasa......" ".......shi yasa aka fidda haqqinsa aka bashi nasa kason......dukiya ta zama ta muhammad sh kadai......amma duk da haka basu qyaleshi yana amfana da abarsa shi kadai ba.....saboda nasa kason da nasa bangaren na haqar ma'adanai yafi noma albarka da kawo samu,shi yasa suka tattare shi suka kuma dora masa dukan lalurarsu suna zuqeshi sannu a hankali.....suka kuma nesantaka dashi.....suka haramta maka sanin komai daya shafeshi ta cusa danta" Ta qarashe maganar da wani irin ciwo da emotiona daga zuciyarta "Maamah....." Ya kira sunanta yana son dakatar da ita. Baya qaunar ko kadan wadannan kalaman marasa dadin sauraro suna fita daga bakinta zuwa kawunan mutanen da suka yiwa rayuwarsu tsaiwar da babu wani mahaluki daya taba yinta "Ni na zabi fannin noma da kayan abinci......basu suka sani ba....ba wanda ya bani shawara....." "Musaddiq!.....ina fada kana fada duk akan mutanen can?,to waishin ko zaka koma cikin aminatu ta sake haifarka a matsayin danta bani mariya ba?". Maganar yaji tayi tsauri da yawa,kuma ya sani uwa uwa ce komai lalacewarta,hakanan ba'a canzawa tuwo suna,don haka ya miqe tsam,don dama a qagare yake da wannan zaman da baiga ma'anarsa ko alfanunsa ba. Ya dauka zasuyi hira ne irin ta d'a da uwa?,ya dauke zata tambayeshi bayan ta barsu yaya suka rayu?,ya dauka zata nuna nadaman barinsu da tayi sun basu gama zama mutane ba?,sai gashi gaba daya hasashenta da hangenta ba'a nan yake ba?,da gaske ne abinda zuciyarsa take raya masa ta biyo DAUKAKARSU DA DUKIYARSU NE?. "Allah ya baki haquri ya huci zuciyarki,sai da safe.....na barki lafiya" Ya fada yana juyawa a hankali yana fita daga falon zuwa farfajiyar gidan. Da kallon takaici ta bishi,shi kansa me sukuni da wadata ne wanda zai iya kashe mata ko nawa take buqata ballanta a gangaro kan muhammad,mahaukatan kudade ke shigo musu daga harkar noma kayan abinci da sauran kayan masarufi da sukeyi,kuma su rabasu cikin qasashen Africa dama qasashen qetare. Tana da dukka information daidai gwargwado a kansu.....amma sai gashi wadatar kowannensu yanason zame mata hoto. Yadda ranta yake a bace sai zama ya gagareta,takai ta kawo kusan sau uku tana ji har cikin zuciyarta ya dace ta gaggauta daukan mataki,ya kamata tayi wani abu akai kada komai yaci gaba da tafiya a haka. Daidai sanda takai dab da qofar taji horn na mota da kuma shigowarta farfajiyar gidan,bata bi takai ba amma zuciyarta tana mamakin baqon daren da sukayi. Mintina uku kawai tayi sallama cikin falon. Sallamar data sanya maamah din waiwayowa tana amsa mata fuskarta babu walwala. Sanye take cikin wani lafiyayyen lace ruwan zuma. Kallo daya tak zakasan cewa ba na qananun mata bane,ba
Chapter 48 · 0% Book details