Sashe 61
A Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
da mamaki dukka suka hade mata har ta rasa wanne tunani ma zatayi. Bugun qofar bandakin da akayi ana jiranta ya sake rudata,sai kawai taja qofar ta bude ta fito ba tare da tayi komai ba,taja burki bakin famfo ta daura alwala tayo dakin nasu. Gaba daya tunaninta ya karkata ga saqon,har ta mance da batun kwashe abinci tayi zaune saman kujera tana bitar saqon da ya riga ya rubuta kansa da kansa a kwanyarta. Fitowar sabreen din ya sanyata tunawa,ta miqe da hanzari ta nufi kitchen. Yanzunma da kallo sabreen ta bita har ta shige kitchen din. To wai me yake samun huda take wasu wasi haka?. Bata sani ba,sai ta girgiza kai ta taka hannun kujerar tana dauko babbar dardumar da sukan shimfida suyi magariba da ishai akai suyi bitar karatun makaranta ta taimaka musu da wanda zata iya. Da ruwan zafi sosai tayi wanka bayan wucewar hajja saboda ciwo da jikinta yake mata sakamakon zaman mota data jima batayishi kaman haka ba. Ta shirya kanta cikin fafi indian abaya me laushi,ta yane kanta da mayafin abayar daya kasance medium cotton kaman yadda jikin dogon rigar yake. Cikin falon tayi zaune bayan ta kirayi me aikinta ta canza mata channel. Qafafunta a miqe saman side glass table din,hannunta dauke da glass cup dake cike da lemon raspberry tatacce me asalin tsadar. Babu wani abu da zata ci ko tayi amfani dashi cikin gidan da yake da qaramin kudi. Komai nata me tsada take zaba,hatta da ruwan da zata sha kuwa ballantana akai ga sutura ko wayar hannunta. Ko a yanzun haka ta gaya masa tana buqatar ya sauya mata iPhones din hannunta guda biyu. Iphone 15 da wata tsaddadiyar waya sabuwar qira da kamfanin Samsung's. Duka duka wayoyin ba wadda tayi wata uku,to amma garin gane ganenta ta hangi wasu sabbin fitar,su kuma takeso ta riqe. A komai tafison ta zama cikin sahun mutane na farko da ake ganin komai sabo a wajensu. Inda tana da iko komai zai zamana ana ganinsa ne ta wajenta,sanda zai soma zagayawa hannun masu kudi irinta ita ta dade da cin zamaninta. Ta sani,a dukiyar da d'anta yake dashi yana da qarfin kudi da mulkin da zai iya sanyawa a qera mata duk abinda take buqatar ya kasance nata ita kadai daga kowanne kamfani a fadin duniya,to amma ta fahimci rayuwarsa baya daidaitata dai dai data sauran masu kudin irinsa. Ba kuma haka takeso ba.....ba haka take muradi ba......tanaso ta gansu suna rayuwa daidai da matakin arziqinsa. Ta fahimci yana cikin sawun mutanen da ba kasafai suke bayyana arziqinsu ba,sai abinda ya riga ya bayyana ba yadda zasuyi dashi. Aka idar da magariba akayi ishai shuru. Tun tana tattalin maganganun da zatayi dashi har wasu suka fara bace mata. Ta daga kai ta kalli agogon dake shirye saman tv din falon takwas da rabi na dare,to shin sai yaushe zai shigo?,sai yaushe wannan abun zaizo qarshe?. Sannu a sannu sanda taga an doshi tara na dare babu alamunsa,wayoyinsa dukka a kashe shida musaddiq din da zata sanya ya kira mata shi a duk inda yake. A ranta ta dinga jin cewa hadin baki ne......a ranta kuma ta dinga ji aminatu ce ta hanasu.....a yanxun haka qila suna can gabanta......ta zaunar dasu sai abinda tace musu. Wannan tunanin ya dugunxuma mata zuciya,har taji bata da wani sauran zama cikin gidan. Dakinta ta wuce kawai bayan ta ajiye kofin lemon,ta shiga zaro takalmi cikin jerin takalman alfarma dake adane a shoe rack dinta. Cikin zuciyarta takeji yau din Alhaji hamzan zata tunkara......tanaso taji shine yayi mata cikin yaran ko ubansu?,tana so taji da ita dasu wai waye ahaqqu dasu?. "Nazo muje ne?" Zuwaira ta tambayeta sanda taga tana dosar qofar fita daga falon "Zauna basai kinje ba" Ta amsa mata a gaggauce tana fita a gidan. Mugun bugun da takewa tafekeken gate din gidan ya fusata securities din gidan,saidai kuma lokacin da suka duba wadda ke bugun ta na'uarar tsaro dole kowannensu fusatarsa tayi nata guri. Basusan ainihih matsayinta ko ita wacece ba......amma yadda suka fahimci girmamawar da take samu daga mazauna gidan ya basu alamar cewa tana da nata matsayin na daban. Ko kallo security din daya bude mata qofar bai isheta ba ballantana tabi takan welcoming nata da yakeyi tare da bude mata qofa ta biyu da zata sadaka da farfajiyar gidan. Daga nan wasu security din su sake marabtarka kashi na uku kenan kafin kakai ga ainihin cikin gidan ka zarge qofar da zata sadaka da babban falon anni na farko. Bata taba tunanin zata sake takowa cikin gidan ba karo na biyu.......don duk lokacin data tako din alatun gidan yakan zame ma idanu da zuciyarta barazana. Tana jin kamar kowanne abu idan ta kalla a gidan yana mata izgili ne tare da gaya mata da dukiyar danki aka samar dani......baki kuma da wata izza ko power ta mallakata. Kowanne taku daya idan tayi cikin gidan ranta quna yake......sak fasalin yadda takeso gidan da zata rayu ya kasance sai gashi kacokam a yau din irin wannan dream house din nata mallakin aminatu ne.. Wasu mutane da basu da masaniyar sanda ta dauki cikin fuad har ta haifeshi. Qofa ta qarshe da zata bata daman shiga falon annin nanma sai data jinkirtawa na'ura sannan ta bata izinin shiga,ta dauke kanta ranta yana suya da wani irin fushi. Tafi qarfin ta tako gidan alhaji hamza har abada.....inda sun bata girma da martabarta da a yanzun ba shakka ita ake zuwarma haka neman gindin zama. Tana sane da yadda mabuqata ke yawan ziyartar gidan karbar taimako a duk sati......taimakon da ta tabbatar daga fuad ake rabashi.......sai gashi ita duk yadda taso ta dinga cina farfajiyar nata gidan da mabuqata,tana raba musu kudi a envelope yadda taso abun bai samu yadda takeso ba. Bai hana taimako,amma saidai ta rubuta list na mabuqatan ya hadasu dana gidan alhaji hamza a raba musu taimakon tare. Bata samu yin sallama ba,sai Allah ya sanya tana sanya qafafunta a falon idanun anni dake kashingide cikin lausasan sofa ya sauka a kanta. "Ikon Allah" Anni ta furta tana miqewa daga kashingidar da tayin tana sauke qafafunta qasa idanunta akan maamah "Da kinyi zamanki ma.....don ni ba wajenki nazo ba kaman yadda na alqawarta zuwa na na qarshe gidan nan......wajen hamza nazo" Maganar tata tazo qarshe dai dai sanda amna ke fitowa daga kitchen ta zuba abincin dare,don tace yau zaman cin abincin abban yayi dare da yawa,ba zata iya jiransa ba da wuri takeso ta kwanta. Kallon kallo sukayi tsakanin maamah din da amna. A kallon farko ta fahimci wacece duk da wannan shine karon farko da ta fara ganin yarinyar ido da ido. Autar alhaji hamza kenan,yarinyar da ake gaya mata irin sabon dake tsakaninta da fuad......yadda take ji dashi da yadda shima yake ji da ita "Idan har kikayi da wasa kina zaune zakiji ance 'yar gida akayi.....wannan matar zata aura masa autarta..... Kinga shikenan komai ya qarasa watsewa" Muryar hajja ta dawo mata akai cikin tattaunawar da sukayi da hajjan a dazu dazu kan hanyarsu ta dawowa gida. "Ke amna......dubamin abbanku idan ya kammala,kice maza maza yayi baquwa" "To" Ta fada tana ajiye plate din sannan ta miqe tana nufar qofar da zata sadata da sassan abban nasu ba tare da tabi ta ainihin farfajiyar gidan ba. Tana tafe tana waiwayen maamah,itama ta lura da hakan,sai taja wani tsaki me matuqar qarfi abinda ya sanya amna din maida kanta tana yin gaba. *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 58 ___________________________ https://chat.whatsapp.com/D4mOQ8gmKb7EXZ2sNcmLdy Assalamualaikum Yar uwa kinason kiga kitchen dinki a cike da kayan amfani masu kyau da inganci amma Kuma kina tunanin chake kudi kisaya a dunkule?? Koda yarinyace Dake da takusa aure kinason kifara Tara mata kayan kitchen?? To damuwarki tazo karshe Yar uwa kinzo inda za'a share Miki hawayenki *ALFAT KITCHENUTENSILS* (Adashen Yar gata), sun shirya tsaf dan ganin sun sama Miki ingantattu Kuma masu kargo Yan zamanin kayan kitchen. Zaki dinga tura kudinki idan yakai wani minzali saiki karba duk abunda kikeso daide kudinki. Ba iya nan muka tsayaba, farashin kayanmu daban yake a ko ina. Dannan link dinnan domin kisamu damar shiga group dinmu don zabar kayanda kikeso da Kuma ganin yadda abubuwan suke kasancewa. Nagode https://chat.whatsapp.com/D4mOQ8gmKb7EXZ2sNcmLdy _________________________