Sashe 10
A Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
wuri,tun gabanin yayi masa umarnin shiga gidan irin haka. A gaba ya jeresu yana biye da bayansu har zuwa sanda suka isa ainihin falon gidan. Daidai sanda take fitowa daga kitchen hannun ta dauke da jug data tanadarwa abban lemo,haka kuma tasha ado da lace bakinta ya cika taf da lipstick ja shar dashi. Har cikin zuciyarta takejin bala'i da masifa suna tsarga mata. Yau kam dukkan juriyarta da karar da take masa ta qare muddin dai yace dawowa yayi da yaran nan masu zubin mayu. Iya zamanta da yaranshi ma ya isheta jarrabawar rayuwa bare ya qaro mata yaran da batasan matsayinsu a gidan ba,suba agololi ba,su kuma ba yaran masu gida ba. A gaggauce ta isa dining ta ajjiye jug din idanunta bisa fuskarsu "Ku kuma daga ina?,daga dawowarsa shine kuka biyoshi saboda tsabar maita?" Ta furta tana zazzare idanu hannuwanta riqe da qugunta. "Ya isa da Allah asama'u" Abba ya fada da hanzari yana daga mata hannu,don wasu maganganun bai dace ace an yisu gaban yaran ba,koda saddiq da musaddiq basu da shekaru sosai,ai Faruqee da me babban suna zuwa yanzun sun fara kammala hankalinsu tunda sun shiga shekara ta goma sha biyar. "Ku wuce dakinku ku canza uniform" "Ba inda zasu a gidannan dai wallahi,basu da daki kuma basu da matsugunni tunda dai bakai ka haifesu ba.....danginsu ma sai watsar dasu wai ballantana kai abba?" Ta fada tana sake matsowa hanyar da zasu wuce zuwa dakin "Abba babu kayansu ko daya a gidan nan fa.....baka dade da tafiya ba ta koresu,tunda.ka tafi suma suka koma kwana a gidansu" Faruqee ya fada gaba gadi,yana jin cewa shima yau yakai bango,komai ta fanjama fan jam. "To baqin munafuki,na koresu din,kuma wallahi wallahi koni ko su a gidan nan" Maganar faruqee ta dagawa abba hankali. A cikin gidan da bashi da maraba da kango suke kwana?,gidan dake cike da memories na iyayensu da suka gushe?,ta yaya suke iya bacci su biyu rakkin wanda har zuwa yanzu ba wanda yakai shekara sha bakwai ma bare sha takwas a tsakaninsu?. "Abba abinci ma aiki me babban suna yakeyi a tasha kullum yana kawo musi gari ko dan wanke" Musaddiq ya fada a dan tsorace yana satar kallom fuskar mama bayan ya riqe hannun mahaifinsa da kyau yana boyewa a jikinsa. Sosai maganar ta dakeshi,zaka fahimci hakan ta yadda kalolin idanunshi suka sauya duk kuwa da tarin haqurinsa. Farat daya yaji asama'u ta fita a kanshi gaba daya. Duk matar da zata iya yiwa maraya haka tabbas ya sani nashi yaran ba zasu tsira ba wadanda suke da uwa da uba,Allah ne kawai mafi sanin haqiqanin abinda su kansu su musaddiq din suke kwankwada daga hannunta idan baya nan. Bai taba barin garin ya tafi gurin neman kudinsa hankalinsa a kwance ba tun daga ranar daya saki mariya. Tun daga ranar daya rabu da mariya bai sake samun nutsuwa cikin gidansa ko aminci akan 'ya'yansa ba. "Asama'u?,bakya tsoron fushin Allah kike cutar da marayin Allah?" "Ni babu abinda Allah zaiyimin,don su din ba dole na bane,wadanda ma suka zame musu dole sun yakicesu sun zubda bare ni da aka tsinceni da haqorana talatin da uku.....don haka wallahi bazanyi riqonsu ba,yaranka dai ba yadda na iya dasu saboda ubansu nake aure" *_TAFIYA DA GWANI ME DADI_* *ZAFAFA BIYAR* *zafafa biyar* *ZAFAFA BIYAR* *A DADE ANAYI SAI GASKIYA* _FITATTUN GWARAZAN MARUBUTAN LITATTAFAN NAN NE MASU DAUKE DA SALON LABARAI IRIN DABAN DABAN BISA TSARIN TAFIYA DAYA SUKA SAKE YUNQUROWA _WADANDA SUKA SABA GABATAR MUKU DA QUNSHIN ZAFAFAN LITATTAFAI DA LABARAI MASU TAFIYA DA HANKALI DA TUNANI_ *_IRINSU_* BURI DAYA INAYA AMEENATU DALAAL BAQON MUNAFUKI KAIMIN HALACCI TSUTSAR NAMA WUTSIYAR RAQUMI BAQAR INUWA SIRADIN RAYUWAR BILKISU TABARMAR QASHI KUFAN WUTA *SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI* *_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_* *_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_* *_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_* *_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_* *ZAFAFA BIYAR* *_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_* *Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU* _TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_ _QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_ _K'ALBIM Mamuhghee_ _AJIYA A DUHU Billynabdul_ _DUNIYATA Huguma_ _Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_ *hudu 2k* *uku 1500* *Biyu 1k* *Daya 500* _YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_ *09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA* *IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA* *09033181070* *BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK* *ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171* *ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI* *AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA* 89825722 Nousaiba lawali maradi 1000cf *_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_* *_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_* *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* *Arewabooks:Huguma* https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997 ___________________________ PAGE 12