← Book details A Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 84

Sashe 66

A Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

don saboda jin dadinta ko walwalarta ba......aah......tana yin komai ne kawai don jin dadin wasu. "Zamu kammala da izinin Allah......amma a wannan karon indai komai yayi kyau,adadin kudaden an samesu daidai ya kamata kema ki inganta rayuwarki sama da yadda kike a yanzu". Dan qaramin murmushi ne ya subuce mata,har jib yana iya jiyo sautinsa kadan "JIB.....kune a gabana......har yanzu inajin mutanen dake tare dani ban kaisu matakin daya dace sukai ba". Zuciyarsa ce ta karye girmanta na dada qaruwa a ranshi "Ko yanzun ma me ya rage?,kinyi mana komai,tunda muna iya tsaiwa da qafafunmu......mu ya kamata mu tallafeki kikai inda ya dace kikai din.....kusan dukkanmy burinmu ki samu nagartaccen miji......" "Mubar wannan maganar jib yanzu" Ta katse numfashinsa. Murmushi kadan ya saki,shima kansa yasan ya taba inda batason aje. Sau tari yakanyi mata uzuri......koda shine yaga abinda ta gani,yaji kuma abinda taji ba shakka iya hukuncin da zaima rayuwarsa shine nisantar kowacce diya mace,saidai kallo daga nesa,indai ba qaddara me qarfi da zata hada tarayyarsu guri guda ba. "Zakibi mashkur abuja bayan mun gama da mika'il" Ya furta a nutse bayan shurun daya gifta a tsakani na wasu 'yan mintuna ".....banason tafiyar nan jib" "Itace hanya guda daya mafi sauqi da zamu kammala komai hankalinmu kwance......na sani baki taba bin kowa ko ina ba......amma a yanzun zakije,na miki alqawarin ba abinda zai faru,zan baki kariya da support harki dawo,zan bi bayanku idan ta kama......kwana daya tal zaki bani zan kammala aikinsa.....mashkur din nada tsananin wayo fiye da yadda kike tunani......amma kuma kinsan kutsa kai asusun mika'il yafi na mashkur hadari da kuma tsauraran matakai da sai an masa shiri na gasken gaske?" Shuru tayi tana son fasa maganganunsa daya bata su a cure. Kanta har ya soma dan hargitsewa,sai ta gyara zamanta kadan tana cewa "Ka rudar dani jib......mashkur nada wayon da lallai sai an bishi qafa da qafa kafin cimma nasara......mika'il sassauqan wayo ne dashi......amma nasu account din yana tattare da tsaro sosai haka ne?" "Exactly boss lady" Ya fada yanason jefa raha cikin zancan. Ya jefawa fuskarta murmushi kadan kuwa,sai taja dan qaramin tsaki "A ajjiye wasa jib.....na soma gajiyawa da wadannan hadarurukan......inason muyi babban aikin da zan huta nima hakanan na kula da rayukan dake gabana da kyau" "Haka nakeso miki nima......bari na qara miki wani bayani kadan......mika'il yana riqe da ragamar babban account din dake mallakin wani kamfanin sarrafa diamond......kamfani ne ne matuqar qarfin jari da huldodin kasuwanci da qasashe daban daban.......kusan rabin kudin wannan kamfanin asusunsa mika'il yana da access dashi.....hakanan duk wani kudi da zai shiga ko ya fita yana da access da hakan.....a bincikena na lura yana wadaqa da kudin yadda yakeso,saidai kuma yana bi ta hanyar lura da saka tsantseni ta yadda ba lallai a gane hakan ba,saboda mahaukaciyar riba da matsiyatan manya manyan kudaden da kamfanin ke samu a kowacce rana....." "Matsiyata.....manya manya?" Ta jefawa jib tambayar. Qaramar dariya ya saki "Sorry......maqudan kudade" "Okay......naji kana amfani da wasu kalmomi ne.....eheeen......kaga kenan komai zaizo mana akan daidai?" "Haka nake tunani......amma ki bani kwana uku,zan duba yadda zamu kutsa cikin asusun.....amma shima dole ku hadu a ranar Koda na awa daya zuwa mintuna talatinne......ki sassauta riqon tsaurinki kiyi kaman kin sakar masa komai....." "Mtseewww....ya isa don Allah" Ta dakatar dashi,don zuwa yanzun abubuwan sun fara barin kanta,tana ji kawai lokaci ya tunkarota da zata maida kai sosai ga 'yan uwanta. Dukkansu girma suke qara yi,kuma suna da buqatar attention dinta sosai fiye da wanda take basu a baya. Jib na 'yar dariya yace mata "Shikenan......cikin kwanaki ukun zaki iya jina koda wanne lokaci,kibar wayar a bude,ki kuma fara shirin zuwa abujan.....nima zanyi nawa shirin" *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 62 "Yayi" Ta amsa masa a taqaice tana katse kiran. Shuru kawai tayi tana jin yadda iska ke kai kawo a farfajiyar wajen. Yadda iskar ke kadawa sai take jin kamar kwatankwacin yadda tata rayuwar ke garawa kenan,daga hagu zuwa dama,daga dai dai zuwa rashin daidai,amma a yanzun cikin ranta takejin lokaci yayi da zata tsaida komai.....ko a iya haka ta tabbatar tayi qwarin da rayuwarsu ba zata tagayyara ba. Tunda ta tabbatar ta fita zuwa farfajiyar gidan ta rufe qur'aninta,ta kuma miqe da hanzari ta wuce zuwa cikin dakinsu. Cikin mintuna qalilan ya cire dari darin da take na amsa wayarsa da takeyi cikin dakin. Tun tana a tsaye tana kai kawo da kuma leqe tsakanin labulayen dakin har ta koma ta zauna sosai a gefen gadon tana sauraren kalamansa dake da wani irin dadi suke kuma sake samun matsugunni me kyau a zuciyarta. Yadda dukka kalamansa suke a tsaftace,ba wani kalma ko furuci maras kyau ya sanya take sake jinsa sosai cikin ranta,wani bangaren na zuciyarta kuma yana yabawa kamalarsa da kamewarsa. Ba wani abu me muhimmanci da zaman zaiyi mata,don haka ta yanke duka tunanin tana miqewa daga inda take din tana nufar cikin gida don komawa dakinsu. Tun daga nesa kadan dab da qofar da zata sadaka da ainihin tsakar gidansu ta hangi hadiyyan. Ta ganta sarai zance takeyi,wanda dama takanyi din lokaci bayan lokaci. So samu tabi ta wata hanyar da bazata hada numfashi da ita ba,to amma kuma babu hanyar,saidai tabi zabi guda daya daya rage mata,ta koma ta zauna ta jirata har ta gama zancan tabar wajen. Wannan abunne kuma takejin ba zata iya ba,duk abinda ta niyyaci ko nufaci yi ba kasafai take bari dalilin wani ko wata ya sanyata ta juya da baya ba. Tunda ta doso gurin ta fuskanci hankalinsa ya dauku a kanta. Ba baqon abu bane a wajenta saurin gane motsi ko manufar d'a namiji a kanta daga kallo daya tak. Dauke hankalinta da idanunta tayi daga wajen kamar bata san da zamansu ba tana wucewa ciki. "Wannan 'yar gidanku ce itama kenan?" Ya maida hankalinsa ga hadiyya yana tambayarta wadda tuntuni idanunta suna a kanshi,cikin wani irin banzan kallo da bacin ran yadda yake kallon sabreen din "Eh 'yar nan dince.....sai akayi yaya kuma?" Ta bashi amsa a matuqar fusace har sabreen dake gab da wucewa tana ita jiyota. Kanta ta girgiza kawai tana sakin siririn murmushin nan nata maras sauti me dauke da tarin ma'anoni masu yawa. Itakam daga hadiyya har dukkan wani gajan baqo da zayazo wajenta bata tunanin akwai wanda ya isheta kallo a cikinsu. "Ina kuma hudan?" Sabreen ta tambaya tana kallon sararin da tabar hudan a zaune kafin fitarta "Ta shiga daki" Haneefa ta bata amsa. Labulen daya sakaya qofar shiga dakin tabi da kallo "Daki kuma?,me takeyi a ciki?" "Ban sani ba wallahi.....naga dai ta shige" Nadra da aka miqawa tambayar ta amsawa sabreen cikin rashin taqamaimen amsa "Tun yaushe ta shiga din?" Ta sake tambayar nadra wannan karon qasa qasa. "Baki jima da fita ba" Ta bata amsa itama da yanayin yadda tayi mata tambayar. Bata son saka ko darsa wani abu a ransu,don haka tadan sake rantabrana kallon nadra "Rufe littafin data bari a bude din" Batayi gaggawar shiga dakin ba don kada ta barwa zuciyar yaran wani hasashe,saita koma ta bude fridge ta dauko ruwa,ta qarasa gaban first aid box dinsu dake ajiye cikin falon t dauki paracetamol ta taka zuwa dakin. Daidai sanda ta shaqi wani sassanyan numfashi daya cika fal da farinciki da kuma shauqin soyyayya,daidai lokacin ta daga labulen dakin tana takowa zuwa ciki. Mutuwar kwance tayi sanda idanunta suka ga shigowarta,sai ta kasa ci gaba da maganar da taso ci gaba da yi. Tana iya jinsa yana cewa "Hellooo.....my love.....hello" Amma ta kasa kowanne motsi. Duk sautin maganarsa qwaya daya ji takeyi kamar zata saki fitsari,don tana ganin yadda sabreen din ke matsowa tsaf zata iya jin sautinsa. "Me kikeyi a kwance bayan sallar magariba?.....kuma na barku ne kuna karatu?" Ta mata tambayar tana kafeta da idanu,gami da zama saman drawer dake tsakanin gadajen nasu. Shuru yayi daga inda yake zaune yana bin sakannin da suka kwashe da ita akan waya suna qara gudu,yana kuma sauraren sautin muryar sabreen dake ratsowa ta cikin wayar zuwa kunnuwansa tare da sake tuna masa abubuwa masu yawa da suka shude tsakaninshi da ita. Numfashi taja ta sauke,lokaci daya yadda zata sauya daga ainihin yanayinta yazo mata,saita bata fuska "Banajin dadi ne". Inda hankalinta cikin jikinta yake a lokacin ba shakka babu abinda zai hanata jiyo sautin fitar murmushinsa. Ko iya hakan yana gwada masa samuwar matakin nasara daga gareshi. Ta yadda ya bibiyi diddigin rayuwarsu.....a yadda bincike ya fito masa.....basa iya boye mata komai.....komai girman laifinsu ko gaskiyarsu.....komai tsanani ko maslaharsu.....ba wani abu da suke iya lullube mata shi,yau gashi ya fara taka matakin nasara......ta koya qarya saboda shi. "Me yake damunki haka nan da nan?" Cikin qwarewa wajen iya bankado abinda ke lullube ta tambayeta. Tambayar data sanyashi jingina bayansa da kujera yana jiran jin amsa ta biyu "Kaina ne yake ciwo" Sai ya tsinci muryar sabreen din tana bada amsar da hudan ce ya kamata aji haka daga bakinta. Yadda ta bada amsar ya sanya huda daukewar numfashi daga jikinta na wucin gadi,tare da sanya Naseer tattara hankalinsa akan wayar,kadan kadan fargabar kada ya zamana ta gano meke lullube tana son saukar masa. "Ga magani tashi kisha" Ta sake cewa da huda tana miqa mata kofin ruwan dake hannunta tare da satches na maganin. Ruwan da maganin duka tabi da kallo,ta fara motsawa kadan sannan ta miqe da sauri ta zauna tana sakin wayar. Santsin pillow din ya sanya ta zame ta kuma sulale ta sauka a gefen cinyarta saita matsa kadan tana qarasa danneta. Ci gaba tayi da dubanta har zuwa sanda ta balla maganin tasha,sai ta miqa hannu ta karbi rayuwar ruwan da maganin itama ta balla ta sanya a bakinta tabi da ruwa "Ba abu mafi sauqin fade irin ciwon kai.....amma ki sani,yawan kiran sunansa yana iya jawoshi koda babu shi a wajen" Ta fadi tana qarasa sauke idonta a kanta. Tsoro da fargaba ya sake cikata,saita lumshe idonta tana son dasa gaskiyarta a zuciyarta "Nima zamana kenan na jishi ya saukar min,na dauka nadan lokaci ne xai sauka idan na kwanta" "Allah ya sawwaqe" Ta fada a taqaice tana takawa a hankali hadi da ficewa daga dakin. Wata ajiyar zuciya ta sauke tana fidda idanunta waje,tana iya jin yadda bugun zuciyarta ke kai kawo
Chapter 66 · 0% Book details