Sashe 5
A Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA* *IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA* *09033181070* *BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK* *ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171* *ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI* *AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA* 89825722 Nousaiba lawali maradi 1000cf *_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_* *_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_* *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* *Arewabooks:Huguma* Page 06 ___________________________ *_TURQASHI_* *_BIGI SAI BIGI_* *_BABBAN GORO SAI MAGOGIN QARFE_* *_TASTED AND TRUSTED_* *_TASTED AND TRUSTED_* *_TASTED AND TRUSTED_* *_Kina da burin samun ingantaccen TURAREN WUTA me TSANANIN KAMA GURI?_* *_TURAREN WUTAR DA ZAKI SANYAWA DAKI AMMA HATTA DA LABULAYE KAYAN SAWAN DAKE SAQALE A DAKIN SU KAMA DA QAMSHI?_* *_TURAREN WUTAR DA KUJERUNKI ZASU KAMA QAMSHI DARAM?_* *_KI BANKADA LABULAYENKI KIJI SASSANYAN QAMSHI?_* *QAMSHI IYA QAMSHI 24HR* *HUMRA ME TSAYAWA A ZUCIYAR ME GIDA* *NASAN ZAKI TAMBAYI KANKI A INA ZAN SAMU WANNAN?* *INCENSE BY KABO DAUGHTER* *_tayi muku tanadin abubuwa da yawa irinsu_* Khumra Turaren wuta Kulaccam Lablab Oil perfumes Original musk tahara Multipurpose spray *karki kuskura kada kiyi ganganci ayi babu ke,kai tsaye tuntubeta ta wannan number* 08032119803 Ko ki lalubeta ta nan *Instagram handle_incense by kabo daughter* *Facebook_kabo daughter* *Twitter_kabo daughter* __________________________ Tayi zaune kawai saman kujerar falon tana duban kowa d'ai d'ai da yadda yaran keta walwalarsu da sabgoginsu. Ta yita juya zancan haleema a ranta,anya zata iya kuwa?,zata iya jurewa?,daga bisani data tabbatar muddin taci gaba da zama a wajen zata karya dukka tsarinta saita yunqura kawai ta miqe tana bar musu falon. Cikin satin ya tabbatar yayi musu dukkan abinda ya dace,ya kuma sauke duk wani abu da uba zai saukewa 'ya'yansa,tun daga suturunsu xuwa takalmansu,kayan makaranta hadi da jaka takalmi da duk wani abu daya zama dole ga dan makaranta. Zai iya cewa Kansa da kansa sauyi ne na dare daya yazo cikin rayuwarsu,duk kuwa da cewa har yanzun.....daidai da second dayahasashe,koda da wasa irin na qwaqwalwa zuciyarsa bata taba hasashen ta manta da abubuwa guda ukun nan da suka shafi rayuwarsa ba......suka shigeta da wani irin yanayi,yanayin daya tilasta canzawar zubi da kuma tsari na dukkan feeling na zuciyarsa da gangar jikinsa. Abbansa Jadda Da kuma uwa uba mahaifiyarsa da zuciyarsa ke mata wani irin bahagon kallo. Halitta mafi girma da daraja cikin rayuwarsa......amma kuma dukkan wani matsayi da girman suna da halittar ta mallaka baya jinsa ko dis cikin jininsa da zuciyarsa. Eh tabbas......a tsukin kwanakin rayuwarsu tayi wani wawan sauyi,saidai nashi sauyin ya tsayane cak iya zahirinsa. Darare da yawa suna wucewa cikin idanunsa. Alfijir dake cikin kowacce asubahi da Ubangiji ya halittama kwanakinmu sun sha ketowa ta cikin qwayar idanunsa. Ta tsakiyar qwaqwalwarsa yana jin kamar an tsatssagarta da wani abu me kaifin tsini "Me yasa maama taqi zama damu?,me yasa ta kasa jurewa lalurar Abbey?" "Saboda bashi da komai yanzun,saboda shi talaka ne" Amsar da kullum yakeji ana rada masa kenan cikin kunnuwansa. Sau tari yakan sanya dukka tafukan hannayensa ya toshe qofofin kunnuwansa wai ko zasu daina jiyo masa wannan amsar......waiko amsar tambayarsa zata iya sauyawa?.....saidai aah,koda wasa bai taba jin amsar nan ta sauya ba. Tun baya daukar gaskiya ake rada masa ana kuma sake jaddada masa har zuciyarsa ta gamsu da hakan. "Indai haka ne maama ita tayi silar mutuwar Abbey......indai haka ne maama itace tayi ajalin jadda" Abinda yake gayawa kansa kenan a duk sanda ya kalli fuskarsa dake dauke da qananun shekaru "Amma ta yaya ta kashesu?" Tambayar da daya kasa lalubo amsarta,saidai yasan koda duniya zata taru ta hanashi wannan tunanin bazai taba kankaruwa daga qwaqwalwarsa ba har ABADA. ******* Safiyar litinin ce dake dauke da yawaitar hazo da kuma lullumin sanyi daya soma tun a daren shekaran jiya. Cikin dakin nasu a cikin su hudun kowanne shirin tafiya makaranta yake yiwa kansa don ba wanda baya iya yiwa kansa da komai da komai a cikinsu,daga su Faruqee da suke 'yan gidan,har su da suke baqi ko kuma ace 'YAN RIQO. Kusan za'a iya cewa banbancinsu dasu Faruqee din shine,mamarsu da babansu dukkansu suna a raye,sannan komai tsanani suna da gatan dangi da kuma muhallin da zasu kwana a ciki. Amma ta fuskar samun cikakken gata da kulawa na iyaye,sun tashi kusan a mizani guda,don sun rasa kaso tamanin a cikin dari sanadiyyar RABUWAR AUREn mahaifansu. "Ya kamata kayi ka gama,wannan laqai laqai din naka ba abinda zai haifar mana sai bata lokaci,kasan dai abba ya koma a motan haya zamu je yau" Faruqee dake saba school bag dinsa yace da saddeq dake kurba shayin da Faruqee ya hado musu dukkansu suka gasa cikinsu. Kusan ya zame musu jiki,duk randa mahaifinsu ya sanya qafa ya koma Lagos lunch box dinsu yakan koma hoto,zancan breakfast kuwa saidai da tsananin rabo Faruqee ya faki idanunta ya hada musu tea susha su wuce kaman yau. Tasha kamashi bayan anyi hakan,tasha gargadarsa amma a banza wai man kare,gobe ma sai ya qara. Tun tana hukuntashi ta hanyar duka har yakai shekaru sha biyar. Tayi niyyar masa wani wawan duka,amma da yake ance qashin namiji dana mace ba daya bane saita samu targade a hannun nata madadin shi yaji rauni. Yayi dariyar ranar kaman ba gobe,ya dinga maimaitawa qaninsa "Alhakina ne". Hakanan taji jiyyar hannun nata ba tare da kowa ya sani ba. Tun daga ranar ta canza kalar horo,saita hadashi da aiki me tsanani,kota hanasu abinci a ranar gaba daya. Irin wannan horon yafi mata dadi idan ya zamana abba baya gari,idan kuwa yana nan abubuwa da dama saidai tayi haqurin dole ta tarasu sai randa ya wuce. Saddiq da musaddiq ne a gaba,sai shi da Faruqee a bayansu. Kana musu kallon farko zasu burgeka,ka kuma dauka set din tagwaye ne guda biyu,don dukkansu kusan sa'annin junansu ne. Yanayin zubin kyan halitta da suke dashi,ga kuma wadatacciyar tsaftar uniform da Faruqee bai yarda wahalar cikin gidansu ta sanyashi qazanta ba. Ba wanda gabansa bai fadi ba cikin su ukun bayan ratsowarsu ta falo da zummar fita daga gidan idan ka dauke me babban suna da ya dauke idanunsa daga kanta tuntuni. Qafarta daya saman daya tana karkadata a hankali,kamar yadda ta zube musu idanunta tana binsu da kallo kamar qwayar idanun nata zasu zuba a waje. A darare dukkansu suka gaidata,saidai idanunta suna kanshi ganin yadda ya gaidata hankali kwance,sam kuma kwata kwata babu wannan razani da kuma d'ar d'ar dake kwance a fuskokin 'yan uwansa dake takawa cikin sanda suna fatan wucewa daga falon lafiya. "Zo nan dan qaruna!" Ta furta da wata kakkausar murya tana sake jin haushi da tsanar yaron. Dukkansu suka waiwayo,ta sake binsu da ido "Duk ku dawo nan" Ta kuma fada tana gyara zamanta. Ba wanda ya musa mata suka tako dai dai da dai dai suka zube saman carfet din "Kai don ubanka waye yace ka shiga kitchen ka taba madarar gidan nan?" Ta jefawa Faruqee tambayar tana watsa masa zagi da hannayenta. Kiran uban da tayi shi ya sauka har tsakiyar zuciyarsa ya sosata. UBA wani abu mafi daraja da yake ganin kimarsa cikin DUNIYARSA fiye da uwa,ubansa da kuma ABBAN Faruqee mutane biyu da basu da tamkar da bayajin zai iya jurewa zaginsu. Idanunsa ya maida ya lumshe yakuma yi qas da kansa yana hadiyar wani abu me tauri da zafi tamkar shi mama ke tambaya. Wai haka iyaye mata suke ne marasa tausayi?,marasa imani?,me yasa iyaye maza yaketa gani da tambari da dukka wani tabo na tausayawa 'ya'ya?,me yasa kalmominsu suke tsauri akan 'ya'ya cikin rashin tausayi da kyautatawa?. "Makaranta zamuje,kuma yunwa mukeji" "Ubanka nace......saboda ubanka ne ya kawo madarar shine kake ganin kana da right na shigarmin kitchen yadda kakeso?" *_Dukkan godiya sun tabbata ga Allah_* *_yadda muka fara lafiya Allah yasa mu gama lafiya_* *_kusa kurai da zaa gani a ciki ajizanci ne irin na dan adam,da fatan za'ayi afuwa a kau da kai_* *_Don Allah don Allah ina roqo da fatan zaku zama masu uzuri a gareni,saboda yanayin sabgogin rayuwa,kowa ya sani yau da gobe tana iya sauya bawa daga ainihin yadda aka sanshi_* *_duk sanda kuka samu wani sauyi tattare dani game da tsaiko na posting,tsahon pages da sauransi,ina kyautata muku zaton soyayyarku gareni zata sanya ku zama masu yimin uzuri_* *_ina godiya qwarai game da yadda bakwa gajiya da bibiyata,da bibiyar zafafa biyar gaba daya_* *_alkhairin Allah yakai muku a duk inda kuke,tare da fatan ubangiji zai tsareku kuma daga dukkan abunqi_* *_na gode qwarai,kuma in sha Allah a duk sanda dama ta samu zaku samu komai fiye da yadda kuke so ma cikin wannan tafiya ta DUNIYATA_* *_LABARIN ZAI TABO BOYAYYAR MATSALAR DA MUKE FAMA DA ITA,na muku alkawarin nishadi da sassanyar soyayya kan bigiren salon da kukafi so *MU KASANCE TARE IN SHA ALLAH DAGA FARKO HAR QARSHE* *HUGUMANKU CE* *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* *Arewabooks:Huguma* Read My Book "DUNIYA TA " on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997 ________________________ Page 07 Dif sukayi dukkansu,ba wanda ya iya tanka mata a cikinsu. Daga can qasan zuciyarsa yake jin wani irin zugi fushi da kuma radadi,don meye zata dinga zagin iyaye a gaban 'ya'yansu?,shi abban me yayi da har ya cancanci a zageshi?. "Badai makaranta zaku ba?,ku tashi ku bacemin da gani". Kaman dama suna jiran wannan umarnin ne daga gareta dukkansu suka miqe din kusan lokaci guda,kowa yana yunqurin barin gabanta kamar yadda ta buqata " Harda su kaza a cin danqo?" Ta furta tana kama haba idanuwanta a kansa "Kai dan qaruna ina zakaje?" "Makaranta mana maama,ko kin manta tare muke zuwa?" "Na manta uban masu gida,saika karanta min,don ubanka da can makarantar suka damu da zuwa?,shine yanzu saboda wuce gona da iri da samun waje har suke rawar jikin tafiya?.to wallahi kuda makaranta saidai idan anfi qarfina" Ta fada tana kada hannu da kyau cikin hargagi tana nunasu da yatsa. Hukuncin nata yazo masa a bazata,don bai taba tsammanin zatayi hukunci me tsauri har irin haka ba. Yaji abun ya taba ransa qwarai,domin a yanzun bashi da wani buri daya rage masa saina KARATU. KARATU shine cikar burinsa qwaya daya tal daya rage bai qarasa mutuwa daga zuciyarsa ba,yana jin zai iya bada kominsa don yayi karatu,zai kuma iya jure dukkan wata wahala tsanani ko tsangwama saboda karatu. Ko a yanzun yana