Sashe 41
A Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
duban maama "Allah zaiyi cikin iko da isarsa......na tabbatar Allah bazai taba wofantar da bayin da aka zalunta ba" Kai ummaa ke jinjinawa tare da yaba tauhidi da yaqinin sabreen. Ta jima dasu saidai hankalinta yana kan asibiti,don haka lokaci kadan ta qara akai tayi musu sallama bayan ta aje musu kudi kaman yadda ta saba da basa wuce cefane da zirga zirgar makarantar yaran. Tana hanya zuciyarta kamar ta fashe,hakanan ta sake jinta a rikice bayan fitowarta daga asibitin bayan taji bayani daki daki na yadda zata fita da ayshatu waje ayi mata aiki. Kudade ne masu kaurin da a yanzun bata dasu bata kuma bawa wani ajiya ba. Batasan tayi farautar kudi don ta ajiye ta tara abun duniya ba......tana farautarta ne don ta raba a tsakanin mabuqata marasa galihu irinta,yanzun ka buqata ta taso mata wadda take da girma da muhimmanci a rayuwarta. Sai taja numfashi mai nauyi,tabbas a yanzun zatayi FARAUTA ta ainihi,tsakanin MIKA'IL YA'AQOUB da kuma MASHKUR waye zaiyi aman wadannan maqudan?. _tofa zamuji waye,komarta zatayi kamu ko kuma wannan karon ita zata shiga komar?_ *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* *_Arewabooks:@Huguma_* https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997 __________________________ PAGE 41 Kusan a tare wayoyi uku suka dauki ruri dake nuna alamun ana kiranta. Mashkur mikail da ya'aqoub,abubuwan farautarta da batasan waye a ciki zai fada komarta ba. Ta dinga bin sunayen da wayoyin da kallo cikin canki cankin wanda zata fara daga wayarsa a ciki har sai da suka katse,sai ta barwa ranta wanda ya soma sake kira. Saidai kuma cikin rashin sa'a sai ga mashkur da mikail suna kiranta lokaci guda. Plate din hannunta ta ajiye,ta sanya hannu tana daukan kiran mikail. A lissafinta shine mutum na farko da takeson saukewa daga layinta. Dukka wani binciken halayya nasa suna gwada mata tsantsar dacewar ya karbi sakamako da horo yadda ya dace. Ita kanta batasan adadin abinda zata diba daga gareshi ba,saidai ko banza ta sanya zata sanyasu a muhalli da guraben da suka dace. A jirkice yayi mata sallama da muryar data sanya ta saka masa ayar tambaya. Ta daga wayar daga kunnuwanta ta duba fuskar wayar tana mamaki "Bayan neman mata harda caca da harqallolinsa harda shaye shaye?" Ta tambayi kanta cikin mamaki,sai ta maida wayar kunnenta kawai tana saurarensa. "Sai yaushe zaki bani dama ne?......ina tsananin kewarki......ina son kasancewa dake" Abinda ya fada kenan yana jin kamar ana fusgarshi zuwa gareta. Katse wayar tayi tana jan dogon tsaki. Baci kawai takeji ranta yana yi kota ina tare da azalzala mata akan mikail. Sai ta jawo wata qaramar waya daga gefanta wadda bata hasken komai ba ta turawa JIB qaramin saqo. Tana jin ya kamata aikinta ya fara ta kansa. Yadda mashkur yaketa kiranta ba daga qafa ya sanya ta share kiran ya'aqoub ta daga nashi. Kiran ya'aqoub din ma bata mata rai yakeyi,ta tabbatar dukkan wani magidanci me mata irinsa a yanzun yana cikin gidansa ne koda a dakinsa ko a sassan yake. Taga maza da yawa da halayensu,daya daga cikin halayyar tasu kuma da tafi baqanta mata rai take tunzurata shine wannan. Wai ta yaya ma zatayi Aure?,bayan bataga komai ba a tattare da mazan sai munanan dabi'u dake girgiza zukatan matan su haifar musu da muguwar illar hawan jini ko ciwon zuciya?,ko mummunan zawarcin da har ki mutu bazai fita a tarihinki ba?. Har abada tana kallon zaman 'ya mace me cikakken 'yanci a yayin da ya kasance babu igiyar wani a kanta. "Saura kadan ki kashemin raina muhseena......hala bakisan girman soyayyar da nake miki ba har yanzu?......kinsan Allah?,banqi a daren nan ace an daura aurena dake ba?" "Aure?" Ta furta a hankali tana jin kalmar tayi mata girma da yawa. "Yes aure muhseena....." Ya maimaita fada yana gyara zamansa cikin tattausar sofa din da yake kai. Yana fatan samun gamsashen amsa tare da mamakin kansa yadda yarinyar ta sauya masa tsari gaba daya. "Gaskiya ne" Ta amsa masa a taqaice tana aje numfashi. Hira ya dinga qoqarin janta dashi,duk da ita din bame doguwar hira bace amma ta dan sake masa,don itace hanya guda daya da take dashi da zata haska mata hanyar gano gurbin da zata dasa bomb dinta. "Kiyimin alfarma daya mana......ki gaya min credit dinki na yimin rakiya dubai for just one week......ni kuma nayi alqawari zan biya ko nawa ne" Ya fada yana sake jin kowacce gaba tasa tana narkewa da sha'awarta da sonta. Yanajin koda bata shirya aurensa ba......zai kashe mata ko nawa ne suyi irin rayuwar da yake muradi......idan da yiwuwar ta zama tashin a gaba sai ta zama.....idan ma hakan bata samu ba yana ganin duk inda ta kwana sha ne muddin ya tsira da abinda yake qulafucin samu. "Zan baki dama kiyi tunani......sannan ki yanke ko nawa kikeso muhseena.....ko nawa ne muddin raina zaikai ga muradinsa". Maganarsa t qarshe kenan data sake sanyawa sabreen mummunan zato ga maza......maganarsa ta qarshe data sanyata ta kusa raba dare tana kuka......ta kuma dinga godewa Allah ta wasu fannin. Mashkur din data tura masa mabanbantan mabuqata da buqatar neman tallafin da duka duka baikai ko digo cikin abinda ya mallaka ba yasa aka koresu?......yace bashi dashi?.....yace bazaya bada ba?......wannan mashkur din yau shike bada damar a nemi ko nawa ne zai iya mallaka mata bisa rashin sanin WACECE ITA?. Hakan tamkar wata dama ce a gareta kenan da zata samu dukka kudaden da takeso......amma bisa sharadin sadaukar da abinda yafi komai mutunci a tare da ita?. Koda ta saba ko tana da damar accepting masa abinda yazo dashi.......tabbas ba zata lamunce ba......tanaso ta debi kudadensa ta hanyar data saba azabtar da sauran.......tanaso ta debesu ta hanyar da zaiji ciwon da bazai kankaru ba a zuciyarsa.......tanaso ta debi kudin da zai tsaye masa a rai......yayi masa ciwo fiye da yadda rayuwa da zukatan matan da ya fadawa mutuncinsu sukayi musu ciwo......tanason bashi darasi me girma a rayuwa.......tanason shima ya girgiza girgizar da zata tsaida masa komai na rayuwarsa cakkkkk koda ba tsaiwa bace ta har abada......to amma kuma ta sani.......babban plan da yake buqatar nutsuwa da tsare tsare masu yawa. Don haka da safiyar washegari ta tura JIB wani saqon da sunan mutum biyu. Tana tsaye tana shan ruwan dumin da takesha duk safiya kafin shigarta wanka saqo ya shigo wayarta. Sanda ta duba sai ta samu alert na kudi daga wajen ya'aqoub. Five hundred thousand ce,sai ta gyada kai a hankali tana sakin murmushin takaici. Don kyauta yana da kyauta ya'aqoub ba daga baya ba......abinda bata da yaqini shine haka yake a cikin gidansa?,ko shima fankan fayau ne?. Saqon godiya ta tura masa a gajarce,ta aje wayar tana shirin wucewa wanka wani saqon ya sake shigowa "Patiently waiting for you" Share saqon tayi hade da sauran. Tasan me saqonsa ke nufi a gajarce. Kowacce safiya izina ce a gareta,kowacce rana kowanne sati da kuma kowanne wata cikin rayuwarta yana bude mata babi na abubuwa da yawa cikin rayuwarta. Waishin akwai ragowar NAGARTATTUN MAZA kuwa?,tambayar da kullum idan ta yiwa kanta ita take bawa kanta da kanta amsa da BABU. Kanta tsaye take takawa cikin tsakar gidan nasu ba tare data daga kai ba bare ta lura da waye a hagunta ko damanta?. Ba tare data damu da kallon nan nasu data tabbatar a safiyar yau zai ninka ko ma ya canza salo saboda abinda ya faru a jiya. Dab da zata sanya qafarta a qofar toilet din nasu dake da sassa biyu bathroom da toilet ta jiyo muryarsa yana koda sallama. Sallamar da muddin ya yita duk wani dake da hadin kai dashi take masa dadi......duk wani wanda yake da qulli dashi Kuma yake neman yin ta kansa,mutane kuma kamar ita sukejin kamar su turashi ya koma muhallin da ya fito. Koda taso tayi shigewarta toilet din ta tabbatar sai ya ganta don ya iso dab da wajen. Don haka ta tsaya a nutse tana bude toilet din ta hanyar murza handle,abinda ya bashi damar qarasa shigowa farfajiyar tsakar gidan. Da ita ya fara hada idanu kamar yadda nata idanun suka zube a fuskarsa. Kamanni dai da mahaifinta har kullum sune,bata kuma fasa ganinsu shimfide a fuskarsa,saidai nisan tazarar halayya da dabi'un sun kai girman tazarar dake tsakanin sama da qasa. "Yauwa alhamdulillah......ai gwara dana sameki cikin gidan.....zuwan dama naki ne" Kallonsa kawai tayi ba tare da wani mamaki ba,dama wanne zuwa ne zaiyi gidan ba nata ba?,koda yayi zuwan daba nata ba to lallai daga qarshe sai ya zama nata ko kuma ya hado da ita a abinda bai zama damuwarta bama bare y shafeta. Amma tun a jiya tasan tabbas dama zayazo,shi yasa taso su fice kitso da wuri yazo ya taras da sararinsu kawai. "Ina kwana kawu?" Ta fada cikin girman nan da bata fasa bashi shi kaman yadda kowa cikin gidan ke bashi duk kuwa da farin sanin da tayi na waye shi?,sanin da kaf gidan tayi yaqinin ba wanda ya masa shi......sanin da a qa'ida ya cancanci ta rainashi......amma sai kuma batayi hakan ba.......sanin da ko yaushe ta tunashi dashi take jin kaico da bacin rai da rashin sanin son ganin gilmawarsa. "Lafiya qalau......idan kin baro bandakin ki sameni a dakin bibo" Ya fada yana saba babbar rigarsa yana wucewa ciki tare da jaddada sallamarsa. Da kallon takaici ta bishi,tasan dama zaa rina,ba wani abu da zai fari cikin gidan ya kwana ya hhantse baije kunnuwansa ba.......yana kuma zuwa kunnuwan nasa ne ta hanya guda daya rak wato BIBO. Idanma akwai ta biyunta to bata bayyana ba tukunna. Cikin rashin damuwa da lamuransu gaba dayansu ta kada kanta ta wuce bandakin. Babu wani abu da zai sanyata gaggawa a zuwa kiran data tabbatar babu alkhairi sam sam a tare dashi. Wannan ya sanya ta kammala wankanta a nutse,takuma tsaya gaban madubi ta shirya tsaf kamar yadda ta saba. Tun bata kammala ba ya aiko kiranta ya kusa sau biyar. Ana shidan ta tsaida nadra da taji tana gaya musu cewan kaya take sanyawa "Kace gani nan zuwa" Ta fadima usman daya aiko. Rigar lace tayi niyyar sakawa,don haka ta fara sanya 'yar cikin rigar ta yane kanta da mayafi ta zura slippers dinta tana cewa "Ku kammala shiryawa ina dawowa zamu wuce" Ta qarasa fada tana sanya qafafunta a waje,huda kuma ta bita da kallo. Sam