← Book details A Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 84

Sashe 28

A Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

dazu kawai ke mata yawo a idanu "Meye amfanin dukiyar da bazaka bayar da ita ba fisabilillahi saidai qarfi ya qwata?" Ta furta a qasan ranta tana tambayar kanta da kanta. Daga mashkur har mika'il tayi imanin cikin budin da Allah yayi musun,inda zasi fidda abinda suka mallaka su dinga narkasu cikin nutsuwa a hanyar data dace......dubban jama'a zasu samu sauqi da radadin da yake damun zukatansu da gangunan jikinsu. "An kawo miki saqo" Taji muryar huda daga gefanta tana fada. A nutse ta daga kai tana duban hudan kafin ta maida dubanta ga akwatin data jawo gabanta. Zuba masa idanu tayi tanason tuna daga ina?. A hankali sai kuma abun ya fado mata,ita sam ta manta sunyi dashi ma zai bada saqon "Kaishi daki" Ta fada tana maida kanta ga waya. Wata number ta lalubs a gajarce kuma ta tura mata gajeran saqon karta kwana "Received......thanks". Shi daya ne cikin qawataccen falon da aka qawatashi da dukkan wani nau'in kayan alatu da qawa na rayuwa. Madaidaicin falone wanda ke da saurin janye idanun me kallo da kuma sauqin shiga rai lokaci daya ya kuma dace da kowanne mode da mutum yake ciki. Shi daya ne tal cikin falon,sanye yake da shirt me gajeran hannu sky blue,sai gajeran wandon da duka duka iyakarsa gwiwarsa. Yana a tsaye ne yana fuskantar qatuwar t.v plasma dake zaune dirshan saman kyakkyawar tv stand suna haska wasan qwallon qafa,saidai fiye da rabin hankalinsa baa wajen yake ba. Bayan gilmawar kowanne minti ko second sai fuskarta ta dawo masa. Ya lumshe idanunsa sanda aka buga qwallo na qarshe cikin tazarar bada sa'a game rabo wato penalty,ya daga ragowar tsadajjiyar giyar data rage a qasan glass cup din hannunsa ya qarasa kurbeta,ya dire cup din yana fidda iska daga bakinsa. Tsakanin awannin daga dazu zuwa yanzu ya gama tsara yadda zai baibaye rayuwarta da tsadajjiyar rayuwa......yadda zai narkar mata da zuciya da masu gidan rana......yadda zai maidata tashi shi kadai......yadda kuma zai siye mata zuciya da kuma rayuwa da kudi wadanda yayi imanin a wannan lokacin da muke ciki sune maganin kowacce matsala.....suke iya siya maka dukka nau'in macen da kakeson ka mallaka.....don babu yaren da matan sukafi ganewa irin yaren LUXURY LIFESTYLE. Kallonsa ya mayar saman system dinsa dake kunne,yana jiran kirane daga wajen CEO na JADDA DIAMONDCHORE RESOURCES (JDCR). A duk sanda sunan ya fado masa a rai,ba abinda yake fara zuwa ransa sai GIDAN KUDI. wanna shine sunan da yafi kiransa dashi......wannan shine full definition nashi da yake ganin ya dace dashi gaba da baya. Sake matsawa yayi ya gani koda ya nemeshi?,amma ba wani saqo ko kira kai tsaye ta yanar gizo. Mamaki yadan kamashi,saboda sanin da yayi masa na zamantowarsa mutum me girmama lokaci tare da bawa lokaci muhimmanci,yasan tabbas akwai abinda ya riqeshi ne hala. Baiso yasha komai ba har sai sun kammala duka maganganun da zasuyi through video call. Yasan halinsa,yana da tsananin zafi yana kuma da masifar kaifin karantar mutum,wanda banda shima ya zama mutum me tsananin iya takunsa yayi imani da tuni labari ya jima da shan banban. Yaci wuya ya kuma tsallake turaku gwaji da jarrabawoyinsa sosai kafin yakai matsayin da yake kai a yanxun. Saidai kuma tsakanin jiya zuwa yau burinsa ya fara fadada. Ya fara jin cewa yana buqatar budawa a harkokinsa fiye da wannan da yake ciki a yanxu,yana buqatar qarin kusanci da CEO fiye da wannan kusancin........yana so matakin da suke kai sufi haka shi da shi na qullewa da kusanci tare da sakar masa ragamar komai na kamfanin fiye da yadda yake kai a yanzu. Sai ya zagayo saman kujera ya zauna saboda yadda yaji jikinsa ya fara week,alamu dake nuna abinda yasha din ya fara tasiri a jikinsa,duk da giya ce me tsadar gaske da yake kashe kudade masu kauri wajen siyota,bata bugar dashi buguwar da zata sanyashi fita daga hayyacinsa gaba daya. A sannan sai yaji bashi da wani sauran muradi daya wuce yaji muryarta,gaba daya taswirar qwaqwalwarsa ita take hasko masa cikin shiga da dressing daya dinga ji kamar yayi fiffike ya kamo ta,don haka ya jawo wayarsa ya fara gwada number dinta. A karo na uku kenan daga dazu zuwa yanzun da ya fara kiran nata bai samu isa gareta ba,saidai a yanzun cikin sa'a......har ya fidda rai da tsammani......dab da zata tsinke sai aka daga. "Kin barni da kewarki ko?" Ya fada murya can qasa. Shuru tayi tana sauraren yadda muryar tashi ke fita kafin ta motsa bakinta a hankali "Ka wuni lafiya?" "Ba lafiya ba......nayita kewarki ne kamar na zauce.....don Allah.....ki bani daman ganinki koda zuwa gobe ne MEENAL". Wani siririn murmushi ta saki,irin wanda take saki din a duk sanda wani cikinsu ya kirata da stamp name dinsa " Ba yanzu ba" Ta bashi amsa,amsar da a zahiri da gaske take,ta fito ne daga qasan zuciyarta. Ba kasafai take baka damar ganinta ba a sanda ka damu da ka ganta din,muddin akwai mission a kanka saita kaika matakin da take da buqatar kaje din. "Zan katse kiran,bacci ne a kaina,zan sauka saida safe?" Tayi furucin da sigar tambaya,bawai don tana da buqatar amsa ba. Bai samu sararin cewa komai ba t gintse kiran tana aje wayar a gefanta tare da bin wayar da kallo "Mika'il" Ta sake maimaita sunan tana gyada kai. Shima bin wayar yayi d kallo kaman sakarai "Zatayi girman kai,zatayi izza tun a ganin farko na sani......amma kuwa zuwanki hannu bazaiyi wahala ba 'yammata" Ya fada a sarari yana lashe baki hadi da sakin wani shu'umin murmushi. Yana shirin aje wayar wani kiran ya shigo masa. Mato sunan dake rubuce da number dake kiran nasa. Wani zunkudawa yayi sanda ya gama hada haruffan me kiran nasa saboda yadda kanshi ya fara nauyi,ya daga wayar ya sakata a hands free ya ajiyeta,sannan ya koma da baya ya jingina yana saurarensa "Sai ogaaaaaa.......sai bosssss" "Ya akayi mato......nasan kiranka alkhairi ne da kuma samuwa" "Ba kadan ba kuwa.......na samo mana wani sabon zone na caca.......harka ruwa ruwa.......kudi faca faca.......A wanki gara......abun kuma babu kama" Gyara zamansa yayi sosai yana bashi hankalinsa. Baya wasa da harkar caca kwata kwata,suna daya daga cikin abinda ke kawo masa maqudan kudade bayan kamfanin jadda DIAMONDCHORE da ya zame masa lamba daya "Kaman yaya?,yimin dalla dalla,don wutata ta kusa daukewa" Ya fada muryarsa tana dan rangaji. Yasan waye ciki da bai dinsa,tunda ya fadi hakan kuma ya gama fahimtar abinda ke faruwa,don haka ya tattara bayanansa ya gyara zamansa yana cewa "Wani gurin caca wanda na tabbatar a wajenka me gida local ne......akwai 'yan wasa na haqiqa amma kuma kai tsaye na fahimci cewa gidadawa ne.......basu da wani wayewa kwata kwata a cikinta.......akwai kudade amma fa a qasa,na tabbatar a bugu daya zaka tarwatsasu ka kuma yi gaba da duk wani abu da suka shigo cacar dashi" Wata shu'umar dariya ya saki "Mato nawa" Ya furta maganar mato din na masa yawo saman kai,saidai gajimaren da yahau ya hanashi tsaiwa su qarasa maganar,don haka ya sanya hannu ya katse kiran kawai yana furta "Munkaila bisa kansu" Cikin mutuwar jiki da kasala. *_ALBISHIR A GAREKU!!_* *_SHIN KUNSAN UMMUMAHNOOR LUXURIES TA TANADAR MUKU INGANTATTUN KAYAN ADO NA FITA KUNYA KUWA?_* *_KAMAR SU_* Atamfofi Laces Shadda Materials Takalma Jakunkuna Mayafai Trolley Sarka da dan kunne Oil perfumes *_karki tsaya sanya har ayi babu ke,maza garzaya ta nan_* Numbers 08034469681 08135142610 Handles Instagram @ummu_mahnoor_luxuries TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries Facebook ummu_mahnoor_luxuries *_inganci da kwalliya shine muradinmu_* _________________________ *SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI* *_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_* *_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_* *_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_* *_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_* *ZAFAFA BIYAR* *_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_* *Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU* _TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_ _QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_ _K'ALBIM Mamuhghee_ _AJIYA A DUHU Billynabdul_ _DUNIYATA Huguma_ _Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_ *hudu 2k* *uku 1500* *Biyu 1k* *Daya 500* _YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_ *09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA* *IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA* *09033181070* *BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK* *ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171* *ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI* *AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA* 89825722 Nousaiba lawali maradi 1000cf *_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_* *_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_* *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* *Arewabooks:@Huguma* https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997 PAGE 29
Chapter 28 · 0% Book details