Sashe 8
A Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
iya tsaidashi ba har sai da suka isa qofar gidansu dake garqame. Sai sukayi carko carko suna kallon kallon shi dashi. A yadda ya hangi kwantaccen fushi da bacin rai akan fuskar me babban suna sai ya rasa da wadanne kalmomi zai iya shawo kan me babban suna?,wacce kalma ce zatayi masa aiki?. "Kayi haquri kazo mu koma,tunda gidan abba ne ba nata ba bata isa ta hanaka zama ba,yau ko kasheni zatayi saidai ta kasheni" Wani irin kallo ya yiwa Faruqee,ga mamakinsa murmushi ya gani ya subuce masa. Da wani irin zafi ya waiwaya ya dauko dutsen dake yashe gefan malalen simintin dake gaban gidan nasu,har tsoro ya kama Faruqee yaja da gefe,sai yaga ya doshi qofar gidan,ya kama kwadon dake jiki ya fara bugeshi baji ba gani. Tsakiyar azahar ne,wannan ya sanya ba yawaitar jama'a a layin bare a samu me dakatar dashi. A yanayin da yakejin zuciyarsa da kansa a ciki,bayajin akwai ma wanda ya isa ya dakatar dashi din sai MUTUM DAYA TAK A DUNIYA.....ALHAJI HAMZA KIBIYA. Zare kwadon yayi ya watsar gefe,kansa tsaye kuma ya soma cusa kai cikin gidan ba tare daya damu da yana datti ko qurar data lullube qofar ba. Wannan shine mafarin komowarsa gidansu......tushensa......asalinsa da yaji yafi masa kwanciyar hankali sau dubu akwan kwanansa cikin babban bedroom din gidan alhj hamza dake dauke da wuta 24/7 da kayan alatu na rayuwa. Tun a asalin halittarsa shi jajirtacce ne tsayayye da bai yarda da faduwa ba......sanda komai ya dinga faruwa kuma daki daki,sai zuciyarsa ta qara qeqashewa ta kuma tsaya kyam......ya karantawa kansa da kansa cewar shine uwa kuma uban kansa da dan uwansa sadiq.......shine gatan kawunansu,ya fidda kowa daga cikin zuciya rayuwarsa dama hasashensa. Wannan ya sanya tun rana ta farko da suka dawo gidan bai kuma karbar koda ruwa daga gidan alhj hamza ba. Duk da yadda ran Faruqee ke baci da yadda yake wofantar da komai da ya kawo musu din kuwa koda ruwan sha ne. Da kansa ya tsaya,sadiq na debo ruwa shi kuma yana wanke komai da yayi saura na gidan wanda zasu iya amfani dashi. Cikin kwanaki uku kacal ya fara Qwadago. Duk wani aiki da zai samar masa kudi......komai wuyarsa kuwa muddin halas ne yana karba yayishi hannu bibbiyu. Da wannan din ya dogara.....da dan abinda yake samu din ya dauke musu abinci dama abin sha......idan faraga ta samu harda kudin transport na makaranta koda na zuwa kadai ne banda na dawowa. Sauyawar yanayi da kuma tsarin rayuwarsa ya sake canxashi gaba daya. Yana tsananin son karatu kowanne iri ne,na addini dana boko gaba daya *_TURQASHI_* *_BIGI SAI BIGI_* *_BABBAN GORO SAI MAGOGIN QARFE_* *_TASTED AND TRUSTED_* *_TASTED AND TRUSTED_* *_TASTED AND TRUSTED_* *_Kina da burin samun ingantaccen TURAREN WUTA me TSANANIN KAMA GURI?_* *_TURAREN WUTAR DA ZAKI SANYAWA DAKI AMMA HATTA DA LABULAYE KAYAN SAWAN DAKE SAQALE A DAKIN SU KAMA DA QAMSHI?_* *_TURAREN WUTAR DA KUJERUNKI ZASU KAMA QAMSHI DARAM?_* *_KI BANKADA LABULAYENKI KIJI SASSANYAN QAMSHI?_* *QAMSHI IYA QAMSHI 24HR* *HUMRA ME TSAYAWA A ZUCIYAR ME GIDA* *NASAN ZAKI TAMBAYI KANKI A INA ZAN SAMU WANNAN?* *INCENSE BY KABO DAUGHTER* *_tayi muku tanadin abubuwa da yawa irinsu_* Khumra Turaren wuta Kulaccam Lablab Oil perfumes Original musk tahara Multipurpose spray *karki kuskura kada kiyi ganganci ayi babu ke,kai tsaye tuntubeta ta wannan number* 08032119803 Ko ki lalubeta ta nan *Instagram handle_incense by kabo daughter* *Facebook_kabo daughter* *Twitter_kabo daughter* ________________________________ _QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_ _K'ALBIM Mamuhghee_ _AJIYA A DUHU Billynabdul_ _DUNIYATA Huguma_ _Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_ *hudu 2k* *uku 1500* *Biyu 1k* *Daya 500* _YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_ *09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA* *IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA* *09033181070* *BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK* *ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171* *ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI* *AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA* 89825722 Nousaiba lawali maradi 1000cf *_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_* *_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_* *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* *Arewabooks* https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997 PAGE 10 Baya wasa da islamiyya,amma wahala da nauyin kansa dana saddiq ya sanya ya sallamawa zuwa islamiyya. Duk da haka bai sare ba,ya lalubi makarantar magariba ta manya ya soma zuwa don karantar litattafan addini,duk kuwa da nisan zangon tafiya dake a tsakaninsu. Su kansu ba 'yantattun 'ya'ya bane cikin gidan mahaifinsu......amma duk da wannan ya gaza barin me babban suna yakuma qyaleshi kamar yadda ya fuskanci yana da muradin hakan. Duk da basu da 'yanci ko fada aji a gidan......amma hakan baya hanashi dauko abinci daga cikin nasa kwanon data qayyade musu cikin gidan ya kawo don suyi tarayya suci tare,amma koda wasa me babban sunan bai taba dangwala yatsarshi a ciki ba. Abun yana ma Faruqee zafi da ciwo matuqa,har daga qarshe hakan ya sanya suka samu sabani "Don mama tayi maka laifi ai ba abincinta bane,abincin abba ne wanda har yanzu a nasa zaton kuna cikin gidansa ne cikin aminci bisa kulawarta,iyakarta da abincin nan tazo ta diba itama taci,don ko dafawa ba ita ke dafawa,larai ce......kuma ita ke qaramin yawan abincin a boye ba tare da saninta ba,to indai bawai nima gaba da fushi kakeyi dani ba banga abinda zai hanaka ci ba.....idanma kai ba zakaci ba....kada ka sake hana saddiqu yaci,kai ka zauna haka can ta matse maka". Busashen murmushi ya saki yana jin yadda cikinsa ke qugin yunwa,don yau ba wani abun kirki ya samo a aikin ba,wannan ya sanya basu wani qoshi ba wunin ranar sur.....ga kuma tafiya makaranta a gabansu gobe juma'a. Yadda Faruqee yayi fushi ya kuma dauki zafi da abun ya sanya yake barin saddiq din suna hadaka dashi. Shikam yasan bazai taba iya sanya abincin cikin bakinsa ba. A duk sanda yayi yuqurin hakan sai maganganunta su dawo musu kar kar cikin qwaqwalwa "Tunda uwarka ta zube ku ta tafi ta barku,banga uban da zai iya zama daku ba......uwarku ma ta barku ballanta wani?" Aduk lokacin da zai tuna da irin wannan maganar a take yakanji komai ya fita a kansa ne,tsananin baqinciki ya mamaye walwalarsa,wata irin wuta me zafi na taso daga qasan zuciyarsa da ruhinsa dangane da imaninsa. Ta wani fuskar da mama da sauran 'yan unguwa dake jifansu da muggan kalamai sai yaji sam baya jin zafinsu ko kadan,da uwa da uba da kuma dangi ake ado,su kuma basu da ko guda daya!. Ya tabbata lallai su din cikakkun marasa gata da galihu ne,kuma kowanne suna aka kirayesu dashi sun cancanta. Yayi imani inda har jadda tana raye.....koda sunfi kowa talauci da matsin rayuwa......to babu shakka zasu zamo na sahun gaba gaba wajen zama yaran da sukafi kowa samun gata na kulawa da soyayyar kaka. Saidai Allah baya barin wani don wani yaji dadi,ya tabbatar haka ubangiji ya tsara musu tasu DUNIYAr,haka kuma yaso ganinsu a cikinta. A wannna tafiyar abba yayi nisan kiwon da ya jima baiyi irinsa ba. Yana rayuwa bisa yaqinin lallai gidansa da marayun Allahn daya dauka riqo suna lafiya,tunda duk sanda zaya kirata hakan take gaya masa,sannan lokaci bayan lokaci tana hadashi da musaddiq,shima kuma "Lafiya qalau muke abba" Shine amsar da yake bashi bisa jagorancin mummunan gargadi da idanuwa da maman take aike masa duk sanda suke wayar. Faruqee ne bata taba yarda ta bawa wayar ba,sai a wani yammaci da abban yace ya jiyo muryarsa ta hadasu. "Lafiya amma ba qalau ba amma.....muna buqatar ka dawo a kusa abba" Bata iya barinsa ba ta fusge wayar daga hannunsa cikin hanzari ganin yana niyyar sauka daga layi. Maganar ta tsayewa abban a rai,ta kuma sanyashi yaji dukkan hankalinsa yana tarkatowa yana yowa gida. Duk kuwa da akwai sauran abu daya tsara zaiyi a can din,amman sai yaji komai ya fita a kansa tahowarsa gida ce abu na farko da yake kwana yana tashi dashi. *******Kusan dukkansu jan qafafunsu sukeyi,zafin rana yunwa ga gajiya dake tattare dasu. Akwai nisan tazara me dan dama tsakaninsu da makarantar wanda suke shanyeta a qasa daga tafiya zuwa dawowa. Babu ranar hutu a garesu idan ba asabar ko lahadi ba. Ga me babban suna kuwa,baya gane asabar ko lahadin cikin rayuwarsa da DUNIYARSA. Rayuwar tasa gaba daya a birkice take,bashi da wata dogon hutu daya wuce makaranta zuwa neman kudin abinci. Yayi wani irin duhu,dukkan hasken fatar nan da suka gado babu shi,ya rame daga ainihin halittarsa zuwa wata halitta ta daban. Tun daga nesa ya soma hangen wani abu da yayi matuqar girgiza hankali da kuma tunaninsa,ya sanya dukkan wani tunani nashi ya fara sauka daga kan layi,ya kuma daina gane me Faruqee daketa faman bashi labari yake fadi. Wata qurace take tashi daga wani sashe na gidansu gami da qarar zubewar bulalluka. Gefe guda akwai tsaiwar tsirarun mutane da kuma yara wadanda basa raina abun kallo,hakanan basa bari abun kallon ya wucesu kamar qanqantarsa. Zame hannunsa yayi daga jikin na Faruqee,a gaggauce da kuma hanzari ya soma tattaki har zuwa inda aikin ke gudana. "Gidanmu ne fa.....me yayi ake rusheshi?" Ya furta bayan ya tabbata ya tsaya gaban mutanen dake gabatar da aikin futu futu cikin qasa da qura. Dukkansu suka waiwayo suna dubanshi,kafin daga bisani wani dan tsamurmurin mutum dake sanye da milk riga da wando na shadda,da kuma babbar riga ta koriyar shadda gami da baqaf hula daya karkatata gefe ya qaraso gabansa yana dubansa. Bakinsa cike da gashin baki,kai kace daya daga cikin qabilun da suka shude ne shekaru aru aru. "Yaro me kake cewa?" Ya fadi yana saba babbar rigar da a zahiri an tafka babbar asara wajen ware shaddar aka masa rigar da ita gaba daya,don kuwa yadin ya masa yawa,alamu ma suna nuna kamar rinjayarsa takeyi "Gidanmu ne nace,me yasa kuke rushe mana gida?" Ya sake jefa tambayar ga mutumin yana tsareshi da ido da zummar jin ba'asin maganar. Qaramar dariya yadan saki yana sosa gashin bakinsa da alama qaiqayi yake masa. "Yaro man kaza......kai!bakasan tsohuwarka ko ince uwarka ta karbi rabin kudin gidan daga hannun matata ba sanda zata bar garin?". Fuska da idanu gaba daya me babban suna ya yamutse yana duban mutumin cike da zallar mamakin da kwanyarsa ta gaza dauka. " Ko da yake ma.ba fahimta ai zakayi ba,wannan zancan na babanka ne inda yana raye,ba abinda zaka gne