← Book details A Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 84

Sashe 43

A Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

barkatai da zasu yamutsa DUNIYARTA tana zaune salin alin "Kice masa gani nan" Ta bata amsa tana juyawa sashen ajiye takalmanta ta fara dubawa. Takalma ne kala kala masu mabanbantan shape kudi da kuma kaloli. Wani adadi ne me yawa ma'ajiyar takalman taci,wanda dukkansu idan ka kalla babu takalmin qasa sa dubu goma. A duk sanda ta kalli sashen suturar data mallaka a yanzu,a karan kanta mamakinta yana sake ninkuwa ne. Suturu na alfarmar da yaran masu hannu da shuni ke taqamar mallaka ko jin isar cewa sun kai. Daya daga ciki ta zaro,ta aje a qasa ta zura a qafafunta sannan ta debi wayoyinta ta jefa a jaka tayi hanyar fita tana ji a ranta ko sisi a yau din bazai samu daga wajenta ba muddin abinda ya shigo dashi kenan. *SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI* *_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_* *_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_* *_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_* *_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_* *ZAFAFA BIYAR* *_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_* *Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU* _TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_ _QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_ _K'ALBIM Mamuhghee_ _AJIYA A DUHU Billynabdul_ _DUNIYATA Huguma_ _Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_ *hudu 2k* *uku 1500* *Biyu 1k* *Daya 500* _YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_ *09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA* *IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA* *09033181070* *BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK* *ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171* *ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI* *AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA* 89825722 Nousaiba lawali maradi 1000cf *_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_* *_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_* *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 43 ___________________________ GROUP 1 https://chat.whatsapp.com/DT97XBDyEfyEwniN0a09Cz *_assalamu alaikum warahmatullah_* *_kina ta ganin kaya kala kala online?,kinason siya amma kina tsoron damfara?,tsada ko rashin ingancin kaya?_* *_wannan tsoro da taraddadi ya yanke miki indai da HUGUMA CLOSET_* *_muna da nau'ikan kaya kala daban daban bisa farashin da ba kowanne dan kasuwa ke iya bada kayansa akan hakan ba_* Shadda Laces Atamfa Kayan yara English wears dana jarirai Qawatattun handbags Mayafai Abayas da jallabiyas Inner wears Huluna na maza da mata yara da manya socks Takalma na maza da mata yara da manya Lafayas Sarqoqi agoguna banguls da rings _kai komai daya danganci kayan ado na fita kunya wa dan adam_ _bisa farashin da zaiyi daidai da buqatarka_ *_Me kike jira sallah na gabatowa?,ana can ana ruwan suturu daidai da qarfin kowa?_* *_masu manyan qarfi da matsakaita?_* *_ki dinga siya da kadan kadan kina saka kudin kina tara abinki har sukai sanda zaki karba?,ko ki siya lokaci daya a kai miki_* *_muna aika kaya ko ina a duniya in sha Allah_* *MUNA BONONZA LOKACI LOKACI NA DUKA ABINDA RABO YA TSAGA* *_MASU REPOSTING DA MASU SARI DUKA BA'A BARSU A BAYA BA,KI SIYA KI SAIDA KI SAMU RIBARKI HANKALI KWANCE,BA TARADDADIN INGANCIN KAYA KO WANDA KIKA BAIWA KUDINKI_* *_KIYI JOINING KI TURAWA 'YAN UWA DA ABOKAN ARZIQI_* *_INGANCI RAHUSA GASKIYA DA AMANA SHINE TAKENMU_* GROUP 2LINK https://chat.whatsapp.com/CKY0xZDtpby6MTkGrPkXLr _________________________ Samunsa tayi zaune dirshan saman ca rfet yana karakaina da kwanukan da suka gama breakfast. Ya buda flask din da suka zuba dafaffen naman kai wanda sukaci suka bar sauran sai zuwa dare. Yana cikin ire iren siyayyar da take musu lokaci bayan lokaci dukka a qoqarinta na ganin basu rasa komai ba......basu nema komai sun rasa ba......hakanan komai din bai gagaresu ba. Tana da buri me yawa akansu,tana da mafarki mai fadi......tana kuma fata da sanya ran wataran zata basu rayuwa fiye da wadda sukeyi a yanzu haka. Daga kai yayi yana dubanta sanda yake tauna naman,zaqin maggi yana ratsashi. "To zauna mana banda abinki,kikayi wani dogogo saman hannun kujera?" Ya fadi saboda yadda ta kame a hannun kujerar rungume da hannayenta. Sam batason ya bata mata lokaci ta kuma fahimci zuwa yayi yaci mata lokacin "Kawu ai ina tunanin wancan maganan mun gama da ita ko?,fita nakeso nayi ne ana jira na" Ta fada tana duba agogon hannunta. "Kefa kin fiya tsiya da hurwar banza da wofi,ayita tattaroki kina wargajewa?,har sai kin jawo magauta sun jimu?" Shuruuuu tayi tana me zuba masa idanu tare da mamakin fitar kalamin daga bakinsa. Wai magauta,ji kuma na nawa?,ko yana tunanin cikin gidan yana da wani magauci a tsakaninsu da ya wuce shi karan kansa?. "Tunda sauri kike bari nayi a gaggauce" Ya fada yana sude hannunsa daya nado romon naman kan,ya gyara zamansa sosai yana kallonta. "Kinsan hausawa sunce ko kana gudu haifi ka yar.....kuma ita haihuwa rana gareta" Yayi maganar cikin sigar kwantar da murya da jan hankali. Bata ce masa ta tafasa ya sauke ba,tadai ci gaba da kallonsa yana bayanansa tare da son jin inda zantukansa zasu tuqe "Wato wata gwaggwabar mu'amala ce ta taso mana,wadda cikin ikon Allah take buqatar adam zuba wasu kudade kuma a kwashe da riba me tarin yawa.......to kinsam harka ta samu dai ba'a wasa da ita a lokaci irin wannan,duba da yadda al'amuran qasa suka yamutse....to na duba na dubo......na laluba na lalubo kaf 'yan uwa na kusa dana nesa......ba wanda zai rufan sittira ya bani kudin nan aro ko bashi banda ke diyar albarka" Ya qarasa maganar yana addu'a qasan ransa. Ya santa sarai.....yasan aikinta,yasan kuma abinda zata aikata da wanda ba zata yi din ba. Ya jima baiga yarinya mai zubin matsorata ba,wadda kuma a zahiri zuciyarta a tsaye take carrr babu tsoro ba irin sabreen din. Tsam ta miqe abinta bayan data fahimci cewa yakai aya a maganarsa
Chapter 43 · 0% Book details